← Book details Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 29

Sashe 10

Bani Da Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hussaina ta kara shigewa jikin Adamcy tace"mon trésor ko kawai mu dauketa mu tafiyarmu?" Adamcy ya buso iskar bakinsa waje, ya matseta jikinsa yana buga bayanta ya kai bakinsa saman kunneta yace"Tawan banso kina yawan damuwa fa kinji." Ya yana dan cizon fatar kunneta ta saki dan kara kadan. Ya mata kiss ya janyeta ya kamo hannunta yana murmushi yace" Sorry tawan bari kiga yadda zamuyi dasu yanzu kwantar da hankalinki...." Bai ida rufe baki ba suka ga motar yan sanda aguje taja burki daidai bakin dakali.

Habawa Haliru a mugun tsorace ya nufi gida a guje yana kururuwa da ihu wani Police ya diro da bindiga yay kan Haliru yace" kana motsawa zan sauke kanka yanzu nan." Haba Haliru ya zube kan guiwarsa wata irin zufa tana keto masa jikinsa na rawa. Ma'azzara me zatayi idan ba dariya ba Hussaina ta toshe bakinta tana kallon Adamcy, shiko sai murmushi yake saki yana ciza lips dinsa.
Ashe duk abinda ake malam musa yana labe yana kallo ganin haka ya nufi ciki yana dariyar mugunta yana zuwa ya tashi Salamatu yace"Maza tashi wasu sunzo zasu cima Haliru mutunci jeki ki rama mashi." A firgice ta tashi ta lailayo ashar ta gyara daurin kirjinta ta saki uwar tusa d'aya ta warci mayafi a guje ta kado waje tana cewa"babu wani 'Dan magaji ko 'yar magaji da ta isa ko ya isa ya tab'a Haliru ya kwana lfy su wayene?" Bakinta ya k'ame k'am ganin police da bindiga ya nufota yana zaro mata idanu..............✍🏻Yasin nagaji

*Na kudi Ne kan farashi Nera 200 kacal +22792589446/ +22796515805*

💃🏻daga Alkalamin *Sweet Baby* ummu Fareesa😘

*💖BANI DA GATA💖*

*MALLAKIN*
👇🏻
*Real ladingo Sweet Baby*💋
Yar mutan Niger🤙🏻

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

*Chapter 8*

..... Salamatu k'asa ta zube gaban police gwiwarta a k'asa, tace"Ranka ya dade me mukayi ni da 'dan uwana? Dan Allah kamana hakuri wlh ko meye zamu gyara, ai fada da aljani ba riba, tuba muke...." police din ya buga mata tsawa yace" Ke wlh yanzu zan fasa kanki da bakin bindigar nan , tashi maza muje zakuyi bayani a can police sitetion, mugaye a zalumai." Duk ilahirin jikin Salamatu rawa yake, jin 'dan sandan nan yace zai tafi dasu policesitetion .

Haliru ya rarrafa kusan megari yace"Don girman Allah mun tuba kar akai mu gidan yari , ko police sitetion wlh zamu gyara...." 'dan sandar ya buga masa tsawa, yace"Ku tashi maza muje wlh yau zakuyi bayani, ba dai zalumci kuka saka gaba ba." Haliru ya damk'e kafar megari ya fara kuka yana rokonsa ayi hakuri.
Police ya buga masu tsawa yace"Zaku tashi ko sai na fasa maku kai yanzu..." Ai rigai-rigai tashi Haliru da Salamatu, jikinsu yana mazari sai lokacin Salamatu taga Adamcy, ta jiyo dariyar

Ma'azzara dan banda dariya babu abinda take harda rik'e cikinta.

Salamatu nan take taji ranta ya 'baci gwara ma tayi mai dalili, aikuwa tayi kukan kura tayi kan Ma'azzara tana fadin "Wai daman saboda wannan bak'ar annobar ce za'a kaimu gidan police. Hussaina ta kalli Adamcy tace"Mon trésor kalli 'yarka ashe ta iya dariyar mugunta haka kar fa ta doketa tayi kanta gadan-gadan." Adamcy bai ce komai ba ya zuba hannunsa cikin aljihu wando sa dan sandan zaiyi Magana Adamcy ya d'aga masa hannu.

Ma'azzara ganin Salamatu tayo kanta kuma tasan maguntar ta, ai ba shiri ta tsayar da dariya tayi kan Adamcy a guje tana kiransa"Uncle temako Wayyo zata dokeni" Salamatu burbur sai tusa take tana gudu kuma mai shegen karan tsiya ko malam da yake bayan kofa yaji karan tusar.

Megari yace"Ikon Allah ashe wannan mata da gaske tusar take ba sharrin yan Audaras bane tanayi din, to wai ku me kuke jira kuna kallo wannan garsaleliyar matar zata bugi yarinyar nan me zai rage ko sai tayi kisan kai tukun?" Dai-dai lokacin Ma'azzara ta iso gurin Adamcy ta koma bayansa ta rungumeshi ta baya ta zagaye hannuwanta a cikinsa, ta boye kanta a gadon bayansa, jikinta ko ina kyarrrrrma yake...

Salamatu tana isowa kusan Adamcy taja ta tsaya tana huci tace" daman iskanci da kuka koya mata shiga jikin kato ba muharaminta ba kenan?" Jin bakin bindiga a kanta yasa tayi shiru tana zaro idanu yace"Maza shiga mota wlh ko na buga maki bakin bindigar nan sai kin suma yanzu." Jin haka yasa Salamatu ta kama hanyar mota tana kuka tana cewa" yau naga rashin gata wai ni zan shiga bak'ar mota, Wayyo rayuwa tayi muni kan wannan annobar zan shiga bak'ar mota." Haliru ma kuka yake suka tisa keyarsa gaba suka nufi gun mota.

Sai lokacin malam musa ya fito yana basu hakuri.
Ma'azzara jin muryar malam musa yasa ta d'ago kanta taga shine yana ma megari magana a basu Adamcy hakuri dan Allah kar asasu bak'ar mota sunan su zai 'baci a kauyen Audaras.
Ma'azzara ta saki kuka tin karfi tana kara rik'e Adamcy, Adamcy ya dafe kansa da hannunsa daya, dayan ya juyo da Ma'azzara gabansa yana rik'e da hannunta yace"Ke lafiya? Meye aka maki kuma? Ni fa banson sangarta." Hussaina ta matso kusanta ta kamata ta rungumeta tace"bakya son a tafi dasu ko?" Ma'azzara ta shige jikin Hussaina tace"eh Aunty baba musa yaban tausayi a barsu ba sai an kaisu ba dan Allah." Adamcy yaja tsaki yabar masu gurin ya nufi gun megari. Lokacin har an saka su Salamatu a cikin motar yan sanda.
Adamcy yama megari bayani megari yace"Wlh ko yanzu sun tsorata baza su mata auran ba, muje kuma kaji da kunne ka amma da a barsu zaifi." Megari da Adamcy suka isa gun motar su uku harda malam musa, Salamatu sai kuka take harda majina.

Megari yace"Salamatu idan aka barku zaku fasa mata auran dole ko sai kunyi mata din?" Salamatu cikin kuka had'e da tusa tace"na rantse da Allah bazan mata ba na hakura suje su rik'eta, ni daman zumunci zan kara amma na fasa bak'in cikina guda uwar garke na da na siyar Wayyo Allah tinkiyata." Ta karasa maganar tana fashewa da kuka.
Megari yace ikon Allah yanzu idan aka baki tinkiyar shikenan babu wata matsala kin yarda bake ba Ma'azzara?" Salamatu tace"Alqura'an kuwa megari." Haliru yace"Ni bana son komai ma a barni kawai." Adamcy sai da murmushi ya subce masa ya girgiza kai yace"Yallab'ai a sauke su tunda sunyi nadama zaku iya tafiya ngd." Yana fadin haka ya juya yabar gurin direct gurin mota ya nufa ya shige.

Hussaina na ganin haka ta kama hannun Ma'azzara suka nufi gunsu kawu Hashim da Saratu suna tsaye suna kallon ikon Allah.
Salamatu tana dirowa a motar ta kalli d'aid'aikun mutane yan gulma ta gyara daurin zani tace"Allah duk wanda naji zancan nan gobe a kace daga bakinsa ya fito na shiga bak'ar mota, Qura'anin Allah sai yaci mati da yaji kut zaku ga tsiya" shegu yan sa idanu. Ta juyo wajan megari tace"Ran megari ya dade batu na tinkiya uwar garke sai zuwa gobe ko? Wlh na tuba bazan sake shiga sabgarta ba tunda abin ya zama haka." Haliru yace"nima wlh na barta akan wannan abin na shiga bak'ar mota bani ba ita Alqura'an." Megari dariya yay yace "To ni dai na tafi Salamatu dan Allah ki shiryu malam musa Allah ya kara maka hakuri da kwarin ciki." Megari na gama fadin haka ya barsu nan tsaye ya nufi gun Adamcy yay masa sallama ya nufi gidansa. Ai kuwa ba 'bata lokaci suka wuff suka fada cikin gida a guje. Malam musa ya danne dariyarsa yaje yay ma Adamcy godiya shima ya shiga gida yan sandar suka tafi dan daman ance tsorone zasu basu.

Hussaina tace"Kawu moje mana duk an watse fa." Hashim yay dariya yana kallon yan tsegumi. Hashim yace"muje Hussaina ai Al'amarin mutanan sai Addu'a kawai." Saratu tace"wlh fa." Mota suka nufa.
Adamcy har suka shiga ba wanda yay ma magana, su Hussaina na baya yaja motar yabar gurin sai ajiyar zuciya yake sauke wa.

Su Hussaina hirasu suke suna dariya k'asa-k'asa suna maimaita abinda ya faru Ma'azzara tayi shiru bata ce komai ba.

Suna zuwa gida Adamcy ya shige bangaran da suka sauka, su kuma suka shiga gun su Ummee.
Hussaina zaune kusan Ummee tana maimaita mata yadda akayi Ummee sai dariyar Salamatu take, abin ya bata dariya sosai.
Hauwa'u tace da Hussaina "Wai ina 'dan uwana ne kuka shigo ku kadai?" Hussaina tace "ya shiga ciki ko wanka zaiyi nasan" Ummee tayi murmushi ta d'auki wayarta ta kira Adamcy bugu d'aya ya d'aga tace"Bature baka zo ka bamu labarin yadda a kayi ba?" Daga can ya shagwab'e yace "Allah Ummee nah ni na gaji bacci nake ji na kwanta ma kice Hussaina ta biyo min da coffee." Ummee tace"To dan Albarka ga Jiddah na neman ka fa." Yace "Ok bata wayar" ummee taba Hauwa'u wayar ta kara a kunneta tace"Haba Abokina haba rabin jikina shine kaje ka kwanta ko sallama da kanwar ka ba kai ba, bakaji lafiyar babynka ba." Adamcy yay murmushi yace"Wayyo ni Adamun Hauwa'u nayi laifi To yi hakuri bari nazo naji babynmu ya yake." Yana fadin haka ya tsinke kiran yana murmushi ya mik'e ya saka jallabiya kan kayan baccin sa ya fito.

Ummee tace da Hussaina "maza hada masa coffee kafin yazo." Hussaina ta mik'e ta nufi kitchen.
Ma'azzara dai ta sadda kanta k'asa tana wasa da yatsotsin hannunta, Ummee tace" Ma'azzara tashi mana idan bacci kikeji Adiya har tayi bacci." Ma'azzara batayi magana ba dan so take taga uncle dinta kafin ta kwanta ta rok'eshi ya bata zobe guda...
Sallamar sa ce ta katse mata tunanita d'ago tai da sauri ta kalli kofar shigowa yana sanye da jallabiya ruwan toka tayi masa kyau kamshinsa ya cika parlon.
Chapter 10 · 0% Book details