← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 31

Sashe 9

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Bala ganin mutane sun sanshi da yawa ciki kuwa har da manyan mutane yasa ya fara tunanin bad'a kama sabida kar wayanda yake yiwa fashi su gane shi

Anan ya fita can k'asar waje yaje ya samu Mask mai irin fatar mutum sak aka mishi bak'in fenti ya koma yake Sawa idan zai fita fashi acikin irin wanan yanayin ya had'u da wata lubna 'yar Ethiopia suka kula soyayya acikin kankanin lokaci ya Aureta abunka da akwai masu gidan rana

Shekararsu biyu da Aure ta haifo mishi wata tsalleliyar 'ya mai mugun kama da ita dan ta ma fi Mahaifiyarta kyau nesa ba kusa ba kai kana ganinta tunani zakayi ta had'a jinsi da larabawa ga gashi

Alhajj Bala tunda yake bai tab'a San wani Abu arayuwarsa ba sama da 'yarsa Naila yana bala'in ji da ita Wanda yake ganin ko ruhinsa zai iya cirewa ya bata gatan da yakewa Naila ya wuce tunanin mai tunani Dan dai dai da makaranta daya saka ta sai da yaja wa masu makarantar warning sosai akan ta ko kud'a baya so ya tab'ata ballantana akai ga duka musamman ya samu Nanny da bata da aikin da ya wuce ta ringa kula da ita har su taso

Kowane lungu da sak'o na gidan shi mak'ale yake da hoton Naila sai data shekara bakwai ya daina kwana da ita burinsa bai wuce yaga duk abinda yagani ya siyo mata ba abunda dai ake cewa gata Naila ta same shi

Mahaifiyarta kuwa tunda ta haifi Naila bata k'ara b'atan wata ba hakan kuwa ba k'aramin damunta yake ba Alhaji Bala ke kwantar mata da hankali akan karta damu Naila kawai ma ta ishesu rayuwa

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Alhaji Bala yake k'ara samun dabaru da k'warewa na fashi sosai Dan har 'yan siyasa yake robbing abun shi abun yana ciwa mutane tuwo a kwarya amma an rasa Wanda yake wanan aika aikan

Watarana Alhaji Bala yaje gidan wani attajiri shi da yaransa Dan suyi fashi bayan sun gama kwashe uban kudade da gwala gwalai anan yace zai keta had'in matar Attajirin ai fa nan gizo ke sak'ar dan Attajirin fir yak'i yarda a tab'a mishi mata yace sai dai idan bayan ranshi

Da yake doka Mai gida ya basu akan idan zasuyi wa mace fyad'e kar su sake su kashe mutum sai sun gama biyan bukatarsu agaban kowa sanan idan zasu kashe mutum sai su kashe

Aifa nan Alhaji Bala yafara k'ok'awa da Attajirin da yak'i bari yaje kusa da matarshi duk gindin bindigar da ya ringa buga mishi akai jini na wanke masa fuska hakan bai sa ya hakura ya bashi hanya ba k'okawa suke sosai inda Attajirin ya kai hannunsa fuskar Alhaji Bala dan ya yak'uso mishi fuska aikuwa sai gashi ya Ciro mask d'in fuskarshi anan yayi tozali da fuskar Alhaji Bala

Ya gwallo ido cikin kinkina yana nuna shi da hannu dan shima kansa Yasan Alhaji Bala awajen taimakon talakawa

Alhaji Bala kuwa k'arasa cire Mask d'in fuskarshi yayi ya ce ya daina mamaki shine nan anan ya hau gaya mishi mugayen halayenshi da Sana'arsa inda a k'arshe ya sa su Lion suka rik'e mishi Attajirin ya ketawa matarsa haddi agabanshi

Ya harbe matarsa ya harbe mutumin sau biyu daga nan suka saka kai suka fice

Suna fita mak'ota suka shiga gidan dan duk abunda ke faruwa suna ji har 'yan sanda sun kira amma shiru basu k'araso ba har b'arayin suka tafi

Abunka da babban mutum tuni aka kaisu asibiti acikin daren duk da basu da tabbacin suna rayye

Suna zuwa aka k'arbesu Matarsa kuwa dama ta Dade da rasuwa Mijin ne dai ake ganin da alamar yana numfashi

A lokacin da likitoci suka dukufa akan shi dan ceto ransa bud'e idonsa yayi a cikin mayuwacin hali ya yafito d'aya daga cikinsu

Yana isa inda yake yayi Sauri yace ya k'ira mishi d'aya daga cikin 'yan sanda dake waje

Da sauri suka kira d'aya daga cikin 'yan sandan yana zuwa Attajirin yace da k'arfi "ba kowane ke robbering mutane ba sama da " ALHAJI BALA MAI KUD'I WANDA KE TAIMAKON TALAKAWAN NAN SHINE YAZO YAMIN FASHI YAYI WA MATATA FYAD'E YA HARBETA YA HARBENI"

Cikin sauri sauri Attajirin ya gaya musu yanda sukayi da Alhaji Bala inda mamaki ya hana d'an sandan motsawa yana k'ok'arin ya tambayeshi ko dai mai kama dashi ne rai yayi halinsa

Tofa anan yan sanda suka fara bincike a b'oye dan su San sana'ar da Alhaji Bala keyi inda suka saka mishi ido sosai a lokacin suna zaune a garin kano

Mai gida ne yafara gaya mishi yayi taka tsantsan an fara sa mishi ido asirinsa ya kusa tonuwa idan da hali ya bar garin kano

Aikuwa a cikin kankanin lokaci Alhaji Bala ya koma port Harcourt da zama shi da iyalansa

Inda 'yan sandan suka tabbatar da zargin da suke mishi anan suka samo Akram dan ya k'ware a binciko sirrin mutum dan har pretending ya tab'a yi akan shi mahaukacine sabida kawai su kamo wani dan yankan kai

Tuni Akram shima ya koma portharcourt da zama ya samu wani dan benci ya baza sweet alewa har dasu sigari yafara siyarwa a opposite gidan Alhaji Bala yana ganin duk wani shige da ficen Alhaji Bala da iyalinshi har da 'yar tilon 'yarsa dayake bala'in ji da ita kamar ransa

Sai da ya samu wata shidda yana lura da duk wani movement d'in Alhaji Bala inda watarana da yamma Bayan akram ya gama had'a wani plan

Alhaji Bala na dawowa gida tunda ga nesa Alhaji Bala yaga antaru a opposite d'in gidansa ana alamar akwai abunda ke faruwa

Parking yayi ya nufi wajen da saurinsa dak'yar ya kukutsa cikin mutane anan yaga Akram na dambe da wani akan sai ya biyashi kud'insa daya siyi sigari da sweet Akram har dasu kuka yasaka yagaggun kaya

Tsawa ya daka musu suka rabu da juna suna sauke ajiyar zuciya Akram kuwa har da guntun hawayensa da majina

Anan Alhaji Bala ya tambayesu mai ke faruwa suka fad'a mishi yayi wani tsaki ya Ciro sabbabin Dari bibiyu masu yawa ya mik'awa Akram

Akram kuwa ya tsuguna har k'asa ya fara yiwa Alhaji Bala godiya

Ko tsayawa bai yi ba ya nufi wajen motarsa

Daddare bayan su Alhaji Bala sun gama cin abinci haka kawai Akram ya ringa fad'o mishi a zuciya haka kawai yaji yaron ya kwanta mishi bai tsaya wani dogon tunani ba ya mik'e yayi waje

Direct wajen Akram ya nufa daya buga tagumi yana kallon waje d'aya har ya zauna agefenshi Akram bai sani ba sai da ya dafashi

Ya juyo a firgice suna had'a ido yayi sauri ya sauka daga kan bencin zai tsuguna Alhaji Bala yayi sauri ya maidashi ya zauna

Alhaji Bala sai da ya gama kare mishi kallo yace "kabani takaitaccen tarihinka"

Wani irin farinciki ne ya rufe Akram amma a zahiri kuwa k'walla suka hau zubo mishi

Anan Akram ya karkata kai ya fara zuba mishi mugun karyar irin talaucin da suke ciki shi da iyayensa shine babba a familynsu su wajen goma sha biyu babansa makaho ne haka ma mamansa sanadiyar accident da sukayi yanzu shine komai nasu

Wani irin tausayin Akram ne ya rufe Alhaji Bala ya tambayeshi yana so yayi bankwana da talauci da sauri Akram ya zube a k'asa yace mishi ee
Alhaji Bala k'ara tambayarshi yayi kowane irin aikine zai iya?

Bud'ar bakin Akram sai yace koda yankan kai ne zai iya

Wani irin murmushi Alhaji Bala yayi yace kar ya damu zasu had'u gobe ya shirya zasuje wani wajen

Aranar Akram kwanan farinciki yayi ya kira manyansa akan su taya shi da add'ua su kuma sa ayi mishi sauk'ar Qurani akan Allah ya kareshi daga wani mugun Abu

Washegari da sassafe Alhaji Bala ya d'auki Akram suka d'auki hanyar Maiduguri inda Mai gida yake sai daddare suka isa wajen Mai gida idan banda adduoi babu abunda Akram keyi a zuciyarsa

Abun mamaki mai gida shima yana ganin Akram yaji San shi har a zuciyarsa

Anan Alhaji Bala ya gabatar mishi da Akram akan yanaso ya zama yaronsa shima ya duba akwai alheri atattare da Akram ko dai babu

Abun mamaki Har Mai gida ya gama dube dubensa haske da alheri kawai yake hangowa attatare da Akram

Cikin farinciki mai gida ya fara gayawa Alhaji Bala irin Al khairan dake tattare da Akram akan zai ringa samun mahaukatan kud'i dan haka ya ringa lallab'a Akram ya ringa binshi a hankali kar ya ringa matsa mishi akan yayi Abu

Take Alhaji Bala ya amince bakinsa har kunne anan suka kwana mai gida ya ringa musu tsubuce tsubuce Akram kuwa ya ringa zuba addu'a a zuciyarsa

Washegari suka koma port Harcourt da Akram da shirin shima next operation dashi zasu tafi

Duk abunda ke faruwa Akram na sanar da manyansa halin da ake ciki

Ahaka suka fara fita first operation inda suka nufi garin bauchi sukayi wa wani hamshakin mai kud'i sata sukayi wa yaransa biyu fyad' duk abunda ake yi Akram na mak'ale da secret camera d'inshi a lokacin babu yanda Alhaji Bala bai yi da akram akan shima yayi wa d'aya daga cikin 'yan matan fyad'e yak'i next operation ma ya kuma yiwa Alhaji Bala gardama akan shi zai ringa rakasu amma bazai iya kashe mutum ba bakuma zai iya yiwa kowa fyad'e ba tun a lokacin Alhaji Bala yaso ya fasa kwakwalwar Akram amma mai gida na hana shi ........

Wanan shine takaitaccen tarihin Alhaji Bala

Cigaban labarin

Alhaji Bala sai da yayi wa Naila yar shekara goma sha hud'u uban siyayya na wajen dubu d'ari hud'u sanan ya k'arasa gida

Inda yana isa gida Naila ta fara tsalle tana mishi oyoyo

Duk girmanta kuwa sai daya d'aga ta sama ya yi juyi da ita kafin ya sauketa k'asa yana tambayarta ya gida Hajiya Lubna kuwa tana daga gefe tana ta murmushi tana jinjina irin soyayyar da Alhaji Bala ke nunawa Naila

3hrs ltr
Chapter 9 · 0% Book details