← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 31

Sashe 17

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na Maliya Wani Mahaukacin dariya ya k'ara kwashe wa dashi yace "ko matan duniyan nan zaka bani bana so Naila nakeso ka kawo min idan ba haka ba duk abinda ya biyo baya kai ka siya da kud'inka na baka nan da Sati d'aya ka kawo min ita"

Bat Na Maliya ya b'ace Alhaji Bala ya saki wani gigitaccen k'ara yana "wlh bazan iya ba Na Maliya bazan iya baka tilon 'yata ba gwara ka kasheni Dana baka ita"

A haka Alhaji Bala ya kwanta a k'asa yana ihu da kururuwa akan bazai iya bawa Na Maliya 'yarsa ba sai da yaga wajen ya fara duhu sosai ya mik'e ya bar wajen sai kuka yake kamar wani k'aramin yaro.....馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀

Alhaji Bala yaga ta kansa ooo ni 馃槀馃槀馃槀
[2:38PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫

*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝

*A heart touching story*

庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Follow me on Wattpad@Sadnaf*

*Page 11*

Hajiya Lubna da Naila dake zaune a Palo suna kallo wajen k'arfe goma sha d'aya na dare a firgice suka mik'e a lokacin da suka ga Alhaji Bala ya shigo k'afa babu takalmi yabi ya fita daga hayyacinsa idon nan nasa yayi jazur

Hajiya Lubna sallati kawai ta ringayi har Alhaji Bala ya zube akan kujera yana dafe da kansa

Naila da Sauri ta matsa kusa dashi tana "Daddy mai ya sameka"

Alhaji Bala d'agowa yayi tare da cire hannunsa daga kansa a lokacin da ya k'urawa Naila ido hawaye masu zafi suka hau zubo mishi wai princess d'insa daya ke jinta tamkar ruhinsa ita zai kaiwa Na Maliya a lalata ta har na tsawon wata uku da ace yasan abinda Na Maliya zai nema kenan gwara ace Fatalwar Hajiya Nafeesa tayi ta bibiyarsa har ya mutu bazai tab'a iya kai Nailarsa wajen Na Maliya ba yayi duk abinda zai yi

Naila hankali a tashe ta hau sharewa Alhaji Bala hawaye itama hawayen ya hau zubo mata tana "Daddy mai yasa kake kuka mai ya faru"

Hajiya Lubna sakin baki tayi tana kallon ikon Allah Dan zata iya cewa this is the first time data ga hawaye a fuskar Alhaji Bala ko a lokutan baya da yake cikin tashin hankalin da bata San abinda ya haddasa ma sa shi ba bata ga yana zubar da hawaye ba kamar yanzu

Alhaji Bala hannayen Naila ya ruk'o yana "Angel insha Allahu indai ina rayye babu Wanda ya isa ya cutar dake I would protect you with all I have banida sama dake a rayuwata zan iya yin komai akanki babu wanda ya isa ya keta miki haddi sai dai idan bana numfashi

Hajiya Lubna da sauri ta mik'e jikinta na rawa ta nufi wajen Alhaji Bala tana " Alhaji wai mai yake faruwa ne waye zai tab'a Nailan"?

Alhaji Bala mik'ewa yayi ba tare da ya kalli Hajiya Lubna ba ya nufi b'angarensa

Hajiya Lubna tayi sauri ta sha gabansa tana "Bala magana nake maka kayi min bayani waye zai cutar da Naila"?

Alhaji Bala matsawar da Hajiya Lubna yayi ya nufi d'akinsa Dan a halin da yake ciki baya jin zai iya wani dogon magana

Hajiya Lubna bin bayansa tayi da kallo har ya shige d'akinsa

Juyawa tayi ta kalli inda Naila ke zaune ta had'a tagumi da hannu biyu hawaye na ta zubo mata Dan Sam bata gane mai Alhaji Bala yake nufi ba

Aranar Alhaji Bala ko runtsuwa bai yi ba yana saman gado a zaune yana ta tunanin yanda zai biyowa Na Maliya Dan Sam ba zai iya kai tilon 'yarsa ba

A takaice sai da Alhaji Bala ya zama tamkar wani zararre sabida fargaba da tsoro dan gani yake Tamkar Na Maliya zai iya zuwa ya d'auke Naila

Hajiya Lubna ta k'asa gane kansa tambayar duniya tayi mishi akan ya gaya mata abinda ke faruwa yak'i ya gaya mata

Aranar da aka samu kwana uku da dawowarsa daga wajen Na Maliya yana zaune a d'akinsa ya buga tagumi yana tunanin yanda rayuwa take juyawa dashi sai ayanzu yake daya sani bai kashe Mai gida ba Dan yasan mai Gida bazai tab'a masa haka ba yana ganin shima Kashe Na Maliya kawai zai yi ya huta inya so idan ya gama dashi sai ya San abun yi akan operation da yake fita babu Nassara

Da wanan tunanin ya samu hankalinsa ya d'an kwanta washegari ya d'auki Hanyar sokoto da sassafe da zumar zuwa ya kashe Na Maliya

B'angarensu Akram kuwa sun gama shirya yanda zasu damke Alhaji Bala Dan sunga alamar ya fara d'ago Akram sabida mugun sa mishi ido da Alhaji Bala yayi Dan a ranar da zai tafi sai da yace mishi idan suka kuma fita wani operation d'in Akram bai tab'uka abin arziki ba babu abinda zai hana ya kashe Akram

Kwana biyu da tafiyar Alhaji Bala ogan Akram Abdullahi yayi arranging d'in motocin 'yan sanda aka je akayi arresting d'insu Lion gabad'aya

Akram dake cikinsu a hankali ya fita daga tsakiyarsu yayi joining d'in yan sandan ya zaro I D card d'inshi ya nuna musu yana Murmushi

Mamaki ne ya hana su motsawa sakin baki kawai suka yi suna kallon Akram kamar wani sabon hallita

Akram d'aya bayan d'aya ya bisu ya kwace wayoyin hannunsu da bindigogi aka tasa keyarsu aka yi waje dasu

Killer k'asa hakuri yayi sai da yace "Ak meyesa ka yi mana haka Ashe shigowa kayi cikinmu Dan ka San sirrinmu you are not part of us y Akram y"?

Akram murmushi yayi yace " am Neva part of you guys nayi pretending Na zauna a cikinku Dan nasamu enough evidence akan Ku da Mai gidanku Alhaji Bala Alhamdulillah Na samu more than enough evidences"

"Yaro take them away"

Da sauri d'an Sandan da aka kira da Yaro ya tasa keyarsu Killer suka shige motar

Su Akram suka bisu a baya

Alhaji Bala kuwa b'oye bindigarsa yayi a wandonsa gabansa Na fad'uwa ya nufi inda Na Maliya ke zama Dan ya yanke a ransa zai yaudari Na Maliya ne akan ya amince idan ya sakankance sai ya zuba mishi Harbi

Tun kafin ya k'arasa Ya fara jiyo dariyar Na Maliya mai barazanar toshewa mutum kunne
jiki na d'an rawa Alhaji Bala ya k'arasa yana nan a zaune a saman ruwa sai yawo yake yi

Zubewa yayi agabansa kamar zai yi mishi Sujadda Na Maliya kuwa ya cigaba da kyalkyala dariya

Alhaji Bala ganin yak'i ya mishi umarni daya d'ago ne ya sa ya d'ago Dan Ya Kalleshi ga mamakinsa sai ganin bindigarsa daya b'oye a wandonsa yayi akan ruwa a gefen Na Maliya

Da Sauri ya mik'e tare da kai hannunsa wajen daya b'oye bindigar yaga babu komai

Na maliya kuwa ya cigaba da kyalkyala dariya

Wani irin tsoro ne ya rufe Alhaji Bala Na maliya kuwa ya tsayar da dariyar da yake yi yace "ka bani tausayi ka d'auka k'arfina dana mai gidanka daka kashe d'aya ne to idan kana tunanin zaka iya kasheni karyar ka ta sha karya domin a tafin hanuna kake duk wani motsin ka da shirin da kake yi ina kallonka ba zaka iya kasheni ba dan haka ka juya ka tafi ranakun Dana d'ibar ma idan sun cika baka kawo ta ba zan zo na d'auketa da kaina idan kuma ka d'auka da wasa nake karka kawo ta kagani karbi bindigar ka ka b'ace min da gani"

Alhaji Bala ja da baya yayi da sauri jikinsa na mugun rawa a lokacin dayaji bindigar a wandonsa

Zube wa yayi a k'asa yana "ka rufa min asiri karka min haka ka fadi duk abinda kake so zan kawo maka cikakkun 'yan mata guda goma zan kawo maka kud'i amma Dan Allah ka rabu da 'yata ba zan iya kawo maka ita ba

Na Maliya Dariya ya kwashe dashi ruwan da yake kai yafara iyowa kan Alhaji Bala

Alhaji Bala kuwa ya fara falfala gudu wuf yaga anyi sama dashi an Nana shi da k'asa sai gashi agaban motarsa

Aguje ya mik'e ya hau motarsa yabar wajen

Ikon Allah ne kawai ya kawo shi gida Dan Sam ba'a hayyacinsa yake ba Na maliya ya masifar tsorata shi

Yana isa gida b'angaren Naila yayi a guje dan yaga ko tana nan Dan gani yake kamar Har Na Maliya ya d'auketa

Naila dake kwance da wayarta a hannu tana buga game da sauri ta mik'e a lokacin data ga Alhaji Bala ya fad'o d'akin kamar Wanda aka hankad'o

Alhaji Bala wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da dafe zuciyarsa a lokacin daya ga Naila

Naila a tsorace tace "Daddy Lafiya kuwa"?

Alhaji Bala girgiza mata kai kawai yayi ya juya yayi waje

A tsakiyar d'akinsa ya tsaya tare da d'ora hannunsa aka yana tunanin mafita dan Na Maliya yafi k'arfinsa ahaka ya raba dare yana tunani sai da wani tunani ya fad'o mishi ya saki wani murmushi cike da farinciki dan gani yake idan yayi haka shikenan Babu yanda za'ayi Na Maliya ya d'auke mishi Naila da wanan tunanin ya samu bacci yayi awon gaba dashi rabon da yayi bacci cikin dadin rai irin wanan har ya manta

Bashi ya farka ba sai wajen Tara da rabi na safe yana kuwa tashi ko sallah bai yi ba ya fice daga gidan dan yaje ya sama musu Visa shi da Naila dan barin k'asan shi zai fiye mishi Alheri

Bai dawo gidan ba sai wajen k'arfe hud'u yana zuwa yacewa Hajiya Lubna ta fara had'awa Naila kayanta zasu bar k'asan goben nan

Mamaki ne ya rufe Hajiya Lubna da Naila zasu yi magana Alhaji Bala ya dakatar dasu ta hanyar d'aga musu hannu yace " bana San tambayoyi ki had'a mata kayanta kawai gobe zamu tafi Dubai ke kuma zaki iya tafiya garinku idan na dawo zan biyo na d'auke ki"

Hajiya Lubna wani mamakin ne ya k'ara rufeta tace "mai Naila zata je tayi a Dubai Al halin basuyi hutun makaranta ba wai nikam Alhaji mai ke faruwane da kake b'oye min wlh idan baka fad'amin ba babu inda za'a kai min 'ya dan Sam bana gane maka kwana biyu idan wani abun ne zai samu Naila ka fad'amin mana"
Chapter 17 · 0% Book details