← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 31

Sashe 10

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Alhaji Bala yaci abincin dare ya huta suna ta hira da Naila tana bashi labarin School shi kuwa sai biye mata yake yana k'yalk'yala dariya Hajiya Lubna kuwa ganin alamun gajiya a tattare da Alhaji Bala amma yak'i zuwa ya kwanta yasa tacewa Naila ta hakura gobe sai ta cigaba da bashi labari amma a yanzu Daddynta ya gaji

Alhaji Bala da sauri da ya mik'e dan dama ya gaji hanya yake nema

D'akinsa ya nufa direct ya shiga wanka yana fitowa ya fad'a kan gado ko towel d'in jikinsa bai cire ba dan wani mugun bacci yake ji ga gajiya ko minti biyu bai yi da kwanciya ba bacci yayi awon gaba dashi

Kafin Hajiya lubna tayi shafe shafenta tazo wajen shi har yayi nisa a bacci

Girgiza kanta tayi ta gyara mishi kwanciya ta kashe fitilar d'akin ta bar d'akin ta koma Palo dan akwai film d'in da takeso ta kalla

12:30 am dai dai

Alhaji Bala yayi wani irin juyi dan ya gyara kwanciyarsa kamar cewa akayi ya bud'e idonsa ya kalli bakin k'ofa aikuwa ya hango Hajiya Nafeesa a tsaye rigarta gabad'aya a jike da jini har d'iga jinin ke yi ta zuba mishi ido tana kallonshi hawaye sai zuba suke a idonta

Wani irin razananan Ihu Alhaji Bala yayi take fitsari mai zafin gaske ya kubce mishi ihu yake sosai da iya k'arfinsa

Hajiya Lubna da Naila ta Dade da bacci a cinyarta a guje ta mik'e Naila tabi bayanta

Suna shiga d'akin sukaga Alhaji Bala ya rufe idonsa da k'arfi yana "dan Allah kiyi hakuri ki rabu dani"

Karar bud'e k'ofar d'akin ne yasa ya bud'e idonsa da sauri ya duro daga kan gadon jikinsa na wani irin k'yarma yabi ya jike da gumi sai sauke nannauyan ajiyar zuciya yake kamar Wanda yayi gudu.....

B'angaren su Saiam kuwa a lokacin da suka isa asibiti tana had'a ido da Alhaji Nazifi Hawaye ya hau zubo mata dan yabi yafita daga hayyacinsa kamar ba shi ba hawaye kuwa sai zubo wa suke a fuskarshi

A hankali ta kalli gefen gadonshi ta hango Samha itama a kwance idonta a rufe itama hawaye nata zubo mata ahankali ta k'arasa gadon da Samha ke kwance ta rik'o hannayenta adai dai lokacin da Samha ta bud'e jajayen idonta babu ko digon fari ahankali ta fara magana cikin rawar murya tana " Aunty Saiam yanzu Mummy ta tafi ta barmu kenan muma yanzu mun zama marayu bazata sake dawo wa ba"?

Saiam kuka ta fashe dashi ta jawo Samha ta rungumeta tana rarrashinta

Alhaji Nazifi dake kwance a gefe kuwa ya fashe da wani irin kuka.........
[2:35PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫

*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝

*A heart touching story*

庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*ALHAMDULILLAHI ALHAMDULILLAHI MASOYA NA SAMU SAUKI BANSAN TA INA ZAN FARA DA YI MUKU GODIYAR IRIN KAUNAR DA KUKA NUNA MIN BA HAKIKA BAKA SANIN MASOYANKA SAI ABU YA SAMEKA NI KAM SAI DAI NA GODEWA ALLAH DAN MASOYANA BAZASU KIRGU BA NASHA ADDU'OI BANDA KIRA DA TEXT MESSAGES NIDAI BAZAN IYA LISSAFAKU BA SAI DAI KAWAI NAYI MUKU GODIYA A DUNKULLE NGD ALLAH YA BAKU LADA YA SAKA MUKU DA ALHERI DA ZAN IYA LISSAFOKU WLH DANA LISSAFOKU AMMA INA BAZAN IYA BA MARYAM I GITAL BARSMARH YAR LELE MAMAN MANAL HADIZA KADUNA YAR BAIWA PHAUZA NAFEESA I SHEHU BANIDA ABINDA ZAN CE MUKU SAI ADDU'A KAWAI*

*KUNGIYATA REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS NGD DA KAUNA DA KULAWA DA KU KA NUNA MIN ALLAH YA BIYA MUKU BUKATUNKU NA ALHERI*

*INA GODIYA AUNTYNA AUNTY SIS ALLAH YA RAYA MIKI ZURIA*

*INA MIK'A GODIYATA GA GRPS GRPS DA SUKA RINGA MIN ADD'UA ALLAH YA SAKA MUKU DA ALHERI*

*WANAN SHAFIN NAKU NE YAN GIDAN MIEMIE B DA ZAUREN BIEBIE ISAH THANKS FOR D LOVE AND SUPPORT*馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹

*Page 7*

Saiam da Sauri ta Saki Samha dake sheshek'ar kuka ta nufi wajen Alhaji Nazifi dake kuka kamar k'aramin yaro

A gefen gadon ta zauna tare da Ruk'o hannun Alhaji Nazifi ta saka d'aya hannun nata ta goge hawayen dake ta zubo mata tace muryarta na rawa

"Daddy dan Allah kayi hakuri ka daina kuka haka Allahn da ya bamu ita shi ya k'arbeta Dan yafi mu San ta hakuri ,zamuyi mu ringa mata addu'a Mummy tace kar mu sake zubar mata da hawaye addu'ar mu kawai take bukata Daddy a matsayinka na Mijinta addu'a kawai ya kamata ka ringa binta dashi idan kai kana kuka mu mai zamuyi Daddy Dan Allah Daddy kayi hakuri ka share hawayenka kukanka na k'ara tunzura Samha kukanka na k'ara karya mata zuciya kai ya kamata ace ka rarrasheta"

Alhaji Nazifi kamar k'aramin yaro ya ringa gyad'a kai da sauri yana goge hawayen da suke k'ara tultulowa

A hankali yafara magana cikin rawar murya

"ALLAH YA JIKANKI NAFEESA ALLAH YA KAI HASKE KABARINKI TUNDA NA AUREKI BAKI TAB'A YARDA NA KWANA DA FUSHINKI BA BAKIDA BURIN DA WUCE KI FARANTA MIN RAI KINYI MIN BIYAYYA NAFEESA KIN BINI SAU DA K'AFA KIN BAWA YARANA TARBIYYA INGANTACIYA KO DAN WANAN INSHA ALLAHU ALJANA CE MAKOMARKI BAZAN TAB'A SAMUN MACE IRIN KI BA NAFEESA NAYI RASHIN DA HAR NA KOMA GA MAHALLICINA BAZAN SAMU WACCE ZATA MAYE GURBINKI BA ALLAH SARKI NAFEESA INA MA ACE NASAN DAREN JIYA ZAKI TAFI KI BARNI INA MA ACE NASAN GANIN K'ARSHE NAKE MIKI DA WLH BAN KWANTA BA DA NA ZAUNA NA NEMI YAFIYARKI NAFEESA ALLAH YA JIKANKI NAFEESA"

Duk inda Alhaji Nazifi yakai Dan ya danne kukan daya taho mishi kasawa yayi sai daya k'wace mishi

Saiam da Samha kuwa mutuwarta ya dawo musu sabo fil aransu suka hau kuka

Kamar Wanda aka mitsina suka ga Alhaji Nazifi ya mik'e yana "Saiam an binneta ne"?

Saiam kanta kawai ta iya gyad'awa

Alhaji Nazifi kuwa yayi sauri ya tuje Karin ruwan da ake mishi a hannun bai damu da jinin dake zuba a hannun shi ba

Yayi hanyar k'ofa da sauri

Saiam da sauri itama tabi bayan shi tare da shan gabansa tana

" Daddy ina zaka je ahaka ?kaga jinin da ke ta zuba a hannunka?

Alhaji Nazifi da sauri yace " Saiam zanje kabarinta nayi mata addu'a tunda badani aka binneta ba tana bukatar addu'ata"

Daga haka ya ratsa ta gefen Saiam yayi waje da Sauri

Samha itama Saukowa tayi daga kan gadon tacewa Saiam itama zata tafi gida zaman asibitin ya isheta haka

Babu yanda Saiam ba tayi da Samha akan ta bari ruwan da aka sa mata ya kare ba fir tak'i akan dole Saiam ta kira likita ya Sallamesu

Naila da sauri ta juya tayi waje sakamakon ganin towel d'in da Alhaji Bala ke d'aure dashi a kugunsa ya fad'o k'asa

Alhaji Bala sabida tashin hankali da tsoratar da yayi bai ma San a tsirara yake ba

Hajiya Lubna kuwa itama cikin rawar jiki ta nufi wajen Alhaji Balan daya jike da gumi ta d'auki towel d'insa dake k'asa tace

"Alhaji lafiya kuwa mai ya firgita ka haka da har towel d'inka ya bar jikinka Baka sani ba"?

Alhaji Bala sai a lokacin yasan a tsirara yake hannuwansa na rawa ya k'arbi towel d'in daga hannun Hajiya Lubna ya d'aura tare da zama a gefen gado still yana hango Hajiya Nafeesa a tsaye a idonsa

Numfashinsa sai fita yake da Sauri sauri

Hajiya lubna itama zama tayi agefensa Dan tunda take dashi bata tab'a ganinsa acikin irin wanan halin ba

A hankali tace "Alhaji Lafiya mai ya tsorata ka haka ko dai mafarki kayi"?

Alhaji Bala bai ce mata komai ba har lokacin jikinsa bai bar rawa ba

Magana Hajiya Lubna ta k'ara yi

Alhaji Bala ya daka mata wani mugun tsawa yana "dala ki rabu dani Wai meyesa bakida hankaline dolene sai na gaya miki abinda yake damuna"?

Hajiya Lubna da sauri ta mik'e tayi waje ba tare da ta tsaya bashi hakuri ko taji mai zai cigaba da cewa ba

dan haka take idan taga ransa a b'ace bata tsayawa a wajen barin gurin shi zai fiye mata alheri dan itama akwai zuciya

Naila data yi jingum a Palo tana ganin Hajiya Lubna ta fito ta tareta da sauri tare da tambayarta abinda ya samu Abbanta

Hajiya Lubna da itama ranta ya b'aci bata cewa Naila komai ba illa ma hannunta da ta rik'e sukayi hanyar d'akinta

Naila kuwa ganin babu fuska yasa bata k'ara tambayarta ba ta kwanta kamar yanda Hajiya Lubna ta kwanta

Alhaji Bala aranar kwanan zaune yayi a tsorace gani yake ko yaya ya runtse idonsa Zai iya ganin Hajiya Nafeesa

Rayuka nawa ya kashe amma babu wacce ta tab'a masa fatalwa sai Hajiya Nafeesa tunda yake ko mafarkin wayanda ya kakashe bai tab'a yi ba sai Hajiya Nafeesa me hakan ke nufi agaskiya bai ga ta zama ba dole da asuba ya d'au hanyar Maiduguri yaje ya nemi taimakon mai gida

Allah Allah kawai yake gari ya waye

Wajen k'arfe 3:40 yafara gyangyad'i a zaune sai baccin ya kusa sace shi sai yayi firgigit ya zauna ahaka ya ringayi har sai da baccin yaci k'arfin idonsa ya kwanta bacci yayi awon gaba dashi

Mafarki ya fara yi da Hajiya Nafeesa tana ta kuka ga kirjinta na ta zubar da jini sai binshi take da gudu shima yana ta gudu da iya k'arfinsa sai ihu yake yana azo a taimaka mishi amma ina gani yake kamar ba gudu yake ba sabida Hajiya Nafeesa tana dab da k'arasowa inda yake
Hannu ta mik'a da niyyar damk'o shi ya mik'e a firgice yana ihu sabida ba ilimin islama ballantana yayi sallati

Yana zama ya kuma hango hajiya Nafeesa abakin k'ofa atsaye kamar dai yanda ya ganta a mafarki

Wani razannan ihu ya saki da iya k'arfinsa

Hajiya Lubna da Naila suka kwasa aguje sukayi d'akin

Suna bud'e k'ofa Hajiya Nafeesa ta b'ace

Alhaji Bala kuwa ya ringa wani irin k'yarma kamar mai jin sanyi ga wani uban gumi kamar Wanda aka kwarawa ruwa

Naila a bakin k'ofa ta tsaya dan towel d'insa ya kuma yin wani wajen
Chapter 10 · 0% Book details