Sashe 13
Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*HEA MASOYANA FANS D'INA INA FARINCIKIN SANAR DAKU INA UPDATING NOVEL D'IN BAK'IN DARE A WATTPAD ACAN ZAN RINGA POSTING KAFIN WATSAPP SO PLS IF U ARE REALLY I DIE FAN DONT FORGET TO SEARCH FOR SADNAF FOLLOW AND VOTE ME THERE I WOULD B GREATFUL WEN I START COUNTING YOUR VOTES*馃檹馃檹馃檹
*Page 8*
Wasa wasa sati biyu kenan da Alhaji Bala yaje wajen Mai gida abunda ake cewa kwanciyar hankali Sam Alhaji Bala bashi dashi dan Duk abinda Mai gida yace yayi ya yi amma Kullum sai Hajiya Nafeesa tazo mishi a cikin mafarki ko a zahiri yabi ya zama kamar mai k'aramin tab'in hankali Dan ko yaya yaji motsi sai ya firgita ya zunduma Ihu
Hajiya Lubna da Naila kuwa hankalinsu yayi masifar tashi da halin da suka ga Alhaji Bala a ciki Dan tunda ya fara shafa wani magani mai Warin kashi a jiki ga jajayen candles da yake kunawa duk dare suka fara tsorata da lamarin Alhaji Bala Naila b'uya ma take a d'aki dan ta fara zargin Daddynta yafara samun tab'in hankali kowane lokaci zai iya rufesu da duka dan abun nashi ya kai yanzu har da rana Ihu yake shi kad'ai idan yana zaune a cikin Palo ya kuma k'i gayawa Hajiya Lubna abinda ke faruwa idan ta matsa mishi da tambayoyi sai ya rufeta da fad'a tamkar zai daketa
A haka suka zuba mishi ido suna mishi addu'a samun sauki
B'angaren su Saiam kuwa Addu'a suke babu dare babu rana akan Allah yayi wa Hajiya Nafeesa Rahama ya kuma toni asirin Alhaji Bala har akayi sadakan bakwai bakinsu na d'auke da azumi idan kagansu sai sun masifar baka tausayi dan kowacensu kalar idonta ya koma ja sunyi shak'uwa da mahaifiyarsu fiye da tunanin mai tunani ko abinci basa iya ci ballantana akai ga cikakken bacci ahaka nasu nafila ne akan Alhaji Nazifi tunda danginsu dake tayasu zaman makoki suna dan kwantar musu da hankali sabanin Alhaji Nazifi da ke wuni a d'aki baya fitowa ba um bare uhum uhum haka zai yi tagumi yana kallon Hoton Hajiya Nafeesa lokaci lokaci yana share hawayen dake zubo mishi duk Wanda yazo mishi gaisuwa sai dai ya hakura ya tafi dan Alhaji Nazifi baya ko motsawa daga inda yake kiran Sallah kawai ke sa ya tashi Sallar ma a d'aki yake yinta a k'arshen sujadarsa kuwa kuka yake fashewa dashi yayi ta yiwa Hajiya Nafeesa Addu'ar Rahamar Allah
Sai da akayi Sati biyu da Rasuwar Hajiya Nafeesa Alhaji Nazifi ya d'an fara dawo wa dai-dai a inda ya nemo wani babban Mallami mai tarin ilimi yace ya taya shi da addu'ar Allah ya tonawa azzalumin da ya kashe Hajiya Nafeesa Asiri shi da zaman lafiya har Abada
Mallamin kuwa yace ya kawo kud'in Sadaka ya had'a kan Almajirai ya raba musu ayoyi da addu'oi insha Allahu asirinsa na dab da tonuwa
Makud'an kud'i Alhaji Nazifi ya bashi tare da yi mishi godiya
A Daren ranar suna zaune a Palo gabad'aya kowanensu hannunsa d'auke da carbi yayan Hajiya Nafeesa Alhaji Musa da tun magriba yana gidan kallon Alhaji Nazifi yayi dayake Jan counter kansa a sunkuye yayi yace mishi yanzu sai dai a d'aga Auren Safna da Saiam idan Hajiya Nafeesa tayi Arba'in sai a d'aura musu Auren dan ba dan rasuwarta ba da gobene d'aurin Auren
Saiam juyar da kanta tayi dan ita yanzu Sam Auren bama ya gabanta bata jin zata iya Aure ta rabu dasu Sahiba gwara ta zauna ta kula da kanenta tunda itace Babba
Alhaji Nazifi sai da yafara Sauke ajiyar zuciya kafin ya d'ago yace " A goben za'a d'aura musu Aure insha Allahu babu abinda za'a fasa dan Nafeesa ta rasu bashi zai sa a d'aga daurin Auren ba dan ko an d'aga ba dawowa zatayi ba ni nasan burinta bai wuce taga ranar d'aurin Auren Su ba kuma insha Allahu zan cika mata wanan burin nata dazu na yiwa iyayen mazajen waya akan su zo da shirinsu gobe k'arfe goma sha d'aya za'ayi D'aurin Auren in yaso sa tare idan an kwana biyu"
Tunda Ya fara magana Saiam da Safna suka d'ago arazane suna kallon shi kuka suka fashe dashi kamar had'in baki Saiam tace"Daddy dan Allah kar a d'aura mana Aure gobe mummy satinta biyu da rasuwa yau ya za'ayi a d'aura mana Aure gobe ni wlh na hakura da Auren zan zauna na kula da kanena idan mukayi Aure waye zai kula dasu Daddy Dan Allah mun fasa bama San Auren" Saiam ta karashe maganarta cikin matsanacin kuka
Alhaji Nazifi Da ji yake kamar shima ya fashe da kuka girgiza kai yayi ya mik'e daga kan kujera ya nufi inda suke a zaune
Zama yayi agabansu ya tank'washe k'afafunsa ya kira sunan Saiam da Safna yace "Karku manta ni ina rayye ban mutu ba ni zan kula dasu har zuwa lokacin da suma zan Aurar dasu burin Mahaifiyarku Kullum bai wuce taga ranar Aurenku ba kuma ni nasan a yanzu idan aka d'aga d'aurin Auren nan sabida ita bazata ji dadi ba gwara in cika mata burinta duk da bata Raye idan ta kanenku ne insha Allahu ni zan kula dasu ba wai ana d'aura Auren gobe a goben zaku tare ba sai an d'an kwana biyu haka mun d'an k'ara samun nutsuwa mun k'arasa sauran shirin namu sai Ku tare"
A takaice da k'yar Alhaji Nazifi da Alhaji Musa suka shawo kansu Saiam suka yarda za'a d'aura musu Aure a gobe Su Suhaima kuwa tausayin Kansu ne ya k'ara lullub'esu dan ahaka da suke d'an ganin juna hankalinsu ke kwanciya ayanzu kuma idan Saiam da Safna suka yi Aure gidan girma zai k'ara yi musu
B'angaren Akram kuwa suna nan suna shirye shiryen yanda zasu kama Alhaji Bala cikin Sauki shi da yaransa inda Akram ke kiran su Lion da suka Dade da komawa gidansu dake Daji dan cika Umarnin Alhaji Bala
Akram kuwa karya ya ringa musu da Mahaifiyarshi ce ba lafiya shi yasa bai dawo ba amma kafin ogansu ya dawo zai dawo
Akram ganin anyi sati Biyu Alhaji Bala bai kira shi ba yasa yafara shan jinin jikinsa yana tunanin ko dai Alhaji Bala ya gano cewa shi Ss ne
Lambar Alhaji Bala ya gwada kira bai d'aga ba sai da ya mishi miss call biyar bai d'aga ba take hankalin Akram ya tashi oganshi ya kwantar masa da hankali yace ya kira su Killer ya bugi cikinsu yaji idan kuwa suma basu d'aga ba to tabbas sun gano shi
Yana kiran Killer ya d'aga wayar Akram yace mishi a cikinsu akwai Wanda sukayi waya da oga kuwa dan yana ta kira bai d'auka ba
Mamaki ne ya rufe Killer yace mishi suma tun jiya suke kiranshi baya d'auka yanzu nan ma fire ya gama kiranshi bai d'auka ba
Hankalin Akram ne ya kwanta da yaji abinda yace sai yace mishi to bari zai cigaba da kiran shi watak'ila yana hutawa ne da haka suka yi Sallama
Oganshi yace ya kwantar da hankalinsa tamkar Alhaji Bala ya gama zuwa hannu ne
B'angaren Alhaji Bala kuwa ayau yafi kowace rana shiga tashin hankali dan Hajiya Nafeesa bata b'acewa idan ta zo mishi a yanayi na ban tsoro take zuwar mishi sosai Hajiya Lubna sallati kawai take yi dan ita bata ganin abinda yake firgita shi yake ihu yana zagaye d'akin abinda Alhaji Bala ya kwana yana yi kenan
Naila kuwa kuka kawai take tana tunanin ko aljanu ne suka sako Alhaji bala agaba
Sai da aka fara kiraye kirayen Salla Alhaji Bala ya daina ganin Hajiya Nafeesa
A guje ya fito daga d'akinsa duk yabi ya firgice kamar bashi ba daga shi sai dogon bak'in jallabiya babu ko dogon wando a ciki yaje ya hau motarsa ya bar gidan
Rabonsa da yaji shi cikin kwanciyar hankali tun kafin yaje gidansu Hajiya Nafeesa a 360 ya ringa fisgar motarsa ikon Allah kawai ne ya kai shi mai duguri wajen mai gida
Yana parking yasa hannu abayan seat d'in motarsa ya zaro k'aramar bindigarsa yasaka a Aljihunsu fuskar nan tashi a turb'une
Sai da mai gida ya gama uzurinsa kafin ya fito daga cikin gidansa
Ya zauna akan buzunsa yana kallon Alhaji Bala daya k'afe shi da ido ya tsaya tamkar wani soja
Murmushi mai gida yayi yace "kura ya dai ko dai fatalwar ce duk ta firgita ka haka dama na gaya maka wanan zabin farkon shi zaka bi ka ta rabu dakai idan ba haka ba wlh sai ta zarar dakai"
Alhaji Bala wani irin kallo yayi wa mai gida yace "mai Mara bata da zararren ai babu dan ta zarrar Dani duk inda nayi sai na ganta yanzu mai gida kana so kace min babu abinda zaka iya yi wanan matar ta rabu dani"?
Mai gida wani kallo ya watsa mishi yace "idan da akwai zan tsaya b'ata wa kaina lokacine babu abinda zan iya yi akai zabin nan dai nafarko shi zaka bi ta rabu dakai"
Dariyar mugunta Alhaji Bala ya kwashe dashi yace " yanzu dai kana so kace min Fatalwa ta fi k'arfinka kana so kace min duk abubuwan nan da ka rataya da aljanun da suke maka aiki bazasu iya min maganin matar nan ba"?
Mai gida zuba mishi ido yayi yana kallonsa a dai dai lokacin da zoben daya saka a hannun shi ya fara mishi zafi
Take Mai gida ya mik'e hankalinsa a tashe yana kallon Alhaji Bala dan yasan ba alheri ne ya kawo shi wajensa ba kafin ya kai ga wani tunani
Alhaji Bala ya zaro bindigarsa daga Alhajinsu ya nuna shi dashi yana "Mai gida banga amfaninka a doron k'asa ba tunda bazaka iya magance min matsala ta ba idan dai k'asar da kake bugawa ta gaske ce bai kamata ace da ka buga bai gaya maka gidan matar nan da zamuje zai zame min masifa ba dan haka gwara na kasheka tunda yanzu ba amfani kake min ba kafin mai gida yayi wani yunkuri
Alhaji Bala ya sakar mishi bullet hud'u
Mai gida take ya zube a k'asa jini na ambaliya wajen yafara dan girgiza
Alhaji Bala dake huci yayi tsaki yajuya ya nufi wajen motarsa