Sashe 16
Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Bala ya tsaya daga bakin k'ofa yana bin Sharon da wani mugun kallo jijjiyoyin kansa a tatashe
Sharon kuwa ganin Alhaji Bala ne da yaransa yasa ya sauke ajiyar zuciya yana dafe k'irjinsa yana "Oga Ashe kai ne ai da ka kirani awaya wlh ka tsorata mu"
Wani mugun tsawa Alhaji Bala ya daka mishi yana "Ni zaka Yaudara Sani ni zaka ciwa amana nasaka ka aiki na biyaka kud'inka a karshe ka zagaye kaje ka fad'awa Alhaji Buba akan ya gudu yabar gidan za'a zo ayi mishi sata ko"
Sharon jikinsa ne ya hau rawa cikin in ina ya fara girgiza kai yana "wlh tallahi ban gaya mishi komai ba karka manta Oga ba yau na fara maka irin wanan aikin ba"
Alhaji Bala ransa a b'ace ya nufi wajen Sharon a tunzure ya shak'o vest d'in jikinsa ya had'a shi da bango yana "u would pay for all I loss babu Wanda ya isa yaci amanata na kyalle shi"
Akram Sallati kawai yake a cikin ransa dan yasan sai Alhaji Bala ya kashe Sharon
Alhaji Bala a tsawace ya kira sunan Akram yana "Shoot him"
Sharon kuwa ya zube a k'asa ya rik'e k'afar Alhaji Bala yana rok'on shi
Akram kuwa jikinsa ne ya d'auki mugun rawa Dan bazai iya kissan kai ba shima yasan rashin Harbin zai sa asirinsa ya tonu Dan Alhaji Bala yace indai suka k'ara fita operation sai yayi kisan kai idan yak'i kuma Alhaji Bala zai d'ago shi
Wani tsawan Alhaji Bala ya k'ara buga mishi yana "ka Harbeshi nace kana b'ata min lokacin "
Akram d'aga bindigar yayi duk da yasan ba iya Harbin zai yi ba Hannunsa sai masifar rawa yake adai-dai lokacin da buduruwar Sharon ta tafi da gudu ta fad'a jikin Sharon tana "please don't kill him he is the only one i have pls I beg of you sir"
Da yake buduruwarsa Yoruba ce kuka take sosai tana rungume da Sharon da jikinsa ke rawa gumi na keto mishi ko ta ina
Wani irin bak'in ciki ne ya rufe Alhaji Bala yace a tsawace "Akram shoot the both of them before counting of two"
Akram jikinsa ne ya cigaba da Rawa shima take ya jike da Gumi
Alhaji Bala kuwa ya nufi wajen Akram yana "zan harbeka wlh ka Harbesu Nace"
Alhaji Bala yace yana buga k'afarsa da k'asa
Buduruwar Sharon kuwa sai ihu take
Tsabar rawar da jikin Akram keyi bindigar sub'alewa yayi daga hannunsa
Alhaji Bala ya d'auki bindigar hannunsa ya bugawa Akram akai sau biyu
Akram ya saki wani gigitacen k'ara a lokacin da jini ya wanke mishi fuska tare da fad'uwa k'asa
Alhaji Bala ya juya a fusace ya sakarwa Sharon bullet akai sau biyu ya sakarwa buduruwarsa a kirji
Wurgar da bindigar yayi ya cakumo Akram da hannu biyu yafara jijjigashi yana "mai kake nufi Kana cikinmu bazaka iya kashe mutum ba sau nawa zan gaya maka aikinmu babu imani babu imani sau nawa kake so na gaya maka this would be the first and last da zan saka ka kayi Abu ka k'i yi wlh if u try it again I would kill you".
Yace yana wurgar dashi tare da yin waje
Lion yayi sauri ya taro shi Akram ya rik'eshi sukayi waje kansa kamar ya fad'o
A ranar Sam Alhaji Bala bai yi bacci ba bak'in cikin kud'in da bai samu ba da abincin da bai ci ba kawai yake acan k'asan ransa kuma yana mugun jin haushin Akram
A daren ya fara tunanin gidan Wanda zai kuma zuwa acikin garin kano a gobe da zai samu makud'an kud'i
B'angaren su Saiam kuwa tunda aka d'aura Auren Saiam da Fawazz da Safna da Faisal suke iya k'ok'arinsu wajen kwantar musu da hankali da faranta musu rai ta hanyar zuwa gidan su had'u gabad'aya a Palon gidan suyi ta jansu da hira har dasu Samha
Hakan kuwa ba laifi ya taimaka wajen kwantar musu da hankali Dan su Samha gani suke tamkar 'ya'yyensu ne su Fawazz
Hakan kuwa ba k'aramin dadi yayi wa Alhaji Nazifi ba dan yaran nashi sun d'an fara farfadowa ba kamar da ba duk da kullum cikin dare in suka zo kwanciya a cikinsu sai wata ta zubar da hawaye sabida Hajiya Nafeesa lokacin da take raye kafin su yi bacci sai tazo ta tayasu hira idan sunyi bacci ta tofesu da addu'oi takan lekosu sau d'aya biyu kafin gari ya waye basu tunaninta ma su zubar da hawaye sai sun zo kwanciya kullum cikin tsinewa Alhaji Bala suke suna tashin dare akan Allah ya tona mishi asiri
Duk da Nazifa wata cousin d'in Alhaji Nazifi da mijinta ya rasu shekara uku da suka wuce itama tana bakin k'ok'arinta wajen ganin tana d'ebe musu wanan kewa daddare hakan bai sa sun kasa tuna mahaifiyarsu ba
A ranar da akayi sadakar Arbain tamkar aranar akayi rasuwar sabida yanda aka cika gidan Alhaji Nazifi inda mutuwarta ya k'ara dawo musu sabo fil addu'oi kawai ake bin hajiya Nafeesa dashi ana fad'ar kyawawan halayenta Alhaji Nazifi kuwa aranar har da d'an zazzabinsa
Bayan kwana uku da akayi Arbain d'in Hajiya Nafeesa aka fara shirye shiryen tariyar Saiam Safna inda hankalinsu ya tashi gabad'aya in banda kuka babu abinda suke yi Dan basa so su rabu da juna ko kad'an ganin junan da suke yi ya na d'an rage musu kad'aice
Da kuka da k'yar aka banbare su Samha daga Jikinsu Saiam a lokacin da aka zo tafiya dasu gidan mazajensu Alhaji Nazifi ma sai da ya koka sosai aka rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu
Aranar babu Wanda ya runtsa a cikinsu dan gidan wani irin girma da fad'i ya kara yi musu
Inda b'angaren amaren amadadin amarci angwayen kwana sukayi suna aikin rarrashi dan Saiam har da zazzabi
Wasa wasa sau Hud'u Alhaji Bala ya na fita operation inda suka je babu abinda suke samu gidan empty suke samun shi nan kuwa aikin Akram ne dan yana fad'a musu inda zasu je operation zai yiwa Ogansa Abdullahi text message duk da Alhaji Bala ya sa mishi ido sosai dan haka kawai yafara d'orawa Akram karan tsana
Aranar da Alhaji Bala yaje gidan wani Alhaji Tahir Hamshakin mai kud'i da ya tada kai Alhaji Bala baije gidan ba sai daya tabbatar da akwai kud'i a gidan kuma iyalansa na nan da confidence d'insa ya had'a Kansu Killer suka je suna zuwa suka tarar da gidan wayam babu kowa ballantana a samu abun d'auka
Jikin Alhaji Bala ne ya hau rawa hankalinsa a matuk'ar tashe yana mamakin abinda ke faruwa dashi ji yake kamar ya zauce
Su Killer kuwa tuni hankalinsu ya tashi suka fara zargin duk yanda akayi an fara ganosu idan ba haka ba ya akayi duk inda suka je basa samun kowa
Zaman dirshan Alhaji Bala yayi a k'asa ya d'ora hannu aka yana tunanin abinda ke faruwa dashi take mai gida ya fad'o mishi arai da a lokacin da yake raye ne da yanzu ya fad'a mishi abinda ke faruwa dashi yanzu wa zaije ya samu baya San zuwa wajen Na maliya dan bai San mai zai ce ya bashi ba a ladan aikin da ya mishi Hajiya Nafeesa ta daina zuwar mishi to ya zai yi dolensa dai yaje wajen nasa dan shi kad'ai zai iya gaya mishi abinda ke faruwa dashi da duk inda yaje baya samun abinda yake so
Da wanan tunanin ya shirya da sassafe bayan ya sallami su Killer yace zai musu waya ya d'auki hanyar sokoto
Yana isa wajen Na Maliya yafara arba da ruwa mai yawa yana ambaliya kamar zai yo kansa a tsorace yaja ya tsaya yana ganin yanda ruwan ke yowa kansa baya ya fara yi da sauri adai dai lokacin da ruwan ya b'ace bat sai ga Namaliya agabansa sai yawo yake a saman ruwa fuskar nan tashi a murtuk'e
Gaban Alhaji Bala na fad'uw ya zube a k'asa kamar zai mishi sujadda bai d'ago ba Na maliya ya fara magana cikins wanan irin murya yana "Kura kana wasa dani ya mukayi dakai"
Jikin Alhaji Bala na rawa yace "Kayi hakuri nayi maka laifi Allah ya huci zuciyarka yanzu ka fad'amin ladan aikina ko menene ko nawane zan bayar akwai kuma wani gagarumin matsala dake tafe dani"
Wani Mahaukacin Dariya Na Maliya ya fashe dashi sai da yayi dariyar na wajen minti goma kafin ya tsagaita yace "ya zama dolenka ne ka bayar da ladan aikin da nayi maka idan ba haka ba sai ka gwammaci ace mutuwa kayi da ace kana rayye bazan kuma saurarka ba har sai ka biya ladan aikin Dana maka da farko kafin na Saurareka"
Alhaji Bala jiki na rawa a tsorace yace "menene Ladan aikinka"?
Na Maliya dariya ya k'ara fashewa dashi yace " ladan aikina shine ka kawo min Naila in ba Aljanina dan Saurayi ya huta da ita na wata uku bayan wata uku kazo ka d'auketa"
Alhaji Bala bai San lokacin da ya mik'e tsaye ba yaji kamar guduma ake kwada masa akai kirjinsa kuwa kamar ya fad'o cikin inina yace "Na Maliya bazan tab'a iya baka Naila ba Dana baka ita gwara ni ka kasheni banida sama da ita arayuwata zan iya sadaukar da komai nawa sabida ita Haba Na Maliya ya za kayi min haka dan Allah ka fad'i wani abun na baka ni ko Mahaifiyata ce ma dan Allah banda Naila"
Murya a k'aushashe Na Maliya yace "baka isa ba dan Dana maka aikin sai Dana baka sharad'i ka kuma yarda dan haka dole ka kawo min ita nan da sati d'aya ko kuma duk abinda ya biyo baya kai ka siya da kud'inka dan sai ka nemi mutuwa ma ya d'aukeka sabida tashin hankalin da zan jefaka a ciki
Alhaji Bala zubewa yayi a k'asa take hawaye ya hau wanke mishi fuska yace " Na Maliya ka rufa min asiri karka min haka dan Allah zan kawo maka Mahaifiyarta zan kawo maka Mahaifiyata amma dan Allah banda Naila dan Allah ka taimaka min wlh Naila yarinya ce shekararta goma sha biyar"