← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 31

Sashe 14

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Bala sai da ya bar wajen mai gida yafara tunanin wajen wa zai nemi taimako wane mallami zai samu ya iya mishi aiki Hajiya Nafeesa ta rabu dashi yana cikin wanan tunanin wani tsohon Mallaminsa Mallam na maliya ya fad'o masa arai shima wani hatsabibin Mallami ne dan shi akan ruwa yake zama a dalilin Mai gida ya watsar dashi

Bai tsaya wani dogon tunani ba ya d'auki hanyar Sokoto bashi ya isa kungurmin dajin ba sai Tara na dare

Sai daya sha bak'ar wahala ya iya gane wajen

Tunda ga nesa ya faro jiyo muryar Mallam na Maliya na mishi maraba tun bai k'arasa ba ya hau fad'a mishi abubuwan dake tafe dashi

Alhaji Bala kuwa da hanzarinsa ya k'arasa wajen da yaji muryarsa na fitowa

Sai da yayi kamar zai yi mishi sujadda kafin ya d'ago ya kalli Mallam Na Maliya dake ta juyi asaman ruwa a zaune shi ba a k'asa ba shi ba a sama ba

Sai da ya fara kwashewa da wani mahaukacin dariya yace "Kura matar nan da ka kashe tana da k'arfi rabaku sai an sha wahala amma awajena Abu mai sauki ne zan baka wani ruwa ayanzu kayi wanka da shi zaka daina ganinta na 'yan kwanaki kafin ta cigaba da zuwar maka kafin lokacin kasan yanda zaka je kabarinta ka haka rami agefen kabarin nata kasa wanan wuk'a da layan ka binne idan dai kayi haka ta rabu dakai kenan har abada"

Jikin Alhaji Bala ne ya hau rawa yace "Na Maliya ai bansan a inda aka binneta ba"

"Wanan yafi komai Sauki kaje unguwarsu idan kaje ka samu wani Mara k'arfi kace ya raka ka makabarta zaka je kayiwa mammata addu'a daga nan zaka iya bugar cikinsa kaji a inda aka binneta tunda sunan mijinta ba b'oyayye bane kana cewa Ashe matar Alhaji wane ta rasu ni kuwa ina kabarinta yake da haka zaka bugi cikinsa bayan kayi mishi alheri ni nasan zai nuna maka daga nan sai ka aiwatar da kudurinka indai ka samu ka binne ni nasan zata rabu dakai har Abada"

Wani nanauyan ajiyar zuciya Alhaji Bala ya sauke Dan gani yake abin da kamar wuya kansa ya k'ara sadawa k'asa kamar zai mishi sujadda kafin yace "Godiya nake Na Maliya menene ladan aikina"

Wani Mahaukacin dariya Na Maliya ya kwashe dashi kafin yace " kai ma kasan bana fad'a sai komai ya kammalla kuma duk abinda nace ayimin idan ba'ayi min ba kasan mai zai biyo baya dan ba iya fatalwar matar zan sa ya ringa bibiyarka ba har da sauran mutanen daka kashe"

Alhaji Bala girgiza kansa yayi yace angama indai Hajiya Nafeesa zata daina bibiyarsa da haka yayi mishi sallama da zumar sai ya dawo ya mik'e a gajiye yaje ya hau motarsa ya kuma d'aukar hanya.......
[2:37PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫

*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝

*A heart touching story*

庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Follow me on Wattpad@Sadnaf*

*Page 9*

Alhaji Bala ba k'aramin farinciki yayi ba a lokacin da yaga ya kwana biyu Hajiya Nafeesa bata zo mishi a amafarki ko a zahiri ba

Tuni yafara dawowa dai-dai hankalinsa ya fara kwanciya sai a lokacin yaje ya samu Naila har cikin d'akinta sabida ta daina fitowa gabad'aya sabida tsoronsa da take ji

Hajiya Lubna kuwa ido kawai ta zuba mishi bata k'ara bi ta Kansa ba tunda taga alamar baya so ya fad'a mata abinda yake damun shi

Naila da sauri ta mik'e a lokacin da taga ya shigo

Alhaji Bala ya sakar mata murmushi yana "zo nan babyna kar dai kice gudun daddynki kike"?

Naila itama murmushin ta sakar masa da ta Gan shi a nutse ta tafi da gudu ta rungume shi tana "Daddy what happened to you"

Murmushi Alhaji Bala yayi a lokacin dayake kwantar mata da dogon gashinta San tilon 'yarsa na ratsa mishi zuciya yanda yake jin San Naila he can do anything bcos of her

Zame ta yayi daga jikinsa ya rik'e hannyenta ya nufi dogon kujerar dake d'akin ya zaunar da ita ya zauna a gefen ta tare da kuma rik'e hannayenta yace " am so sorry dear Some thing came up that Daddy could not handle but now am fine u should not be scared again"

Naila murmushin farinciki ta saki tace "Daddy yanzu ka warke babu abinda yake damunka"

Alhaji Bala cikin farinciki ya gyad'a mata kai

Naila kuwa ta tashi ta fara tsallen murna kamar wata yarinya dama yarinyar ce ma tunda she is 14yrs

Alhaji Bala mik'ewa yayi yace ta shirya anjima zasu tafi shopping ta zabi duk abinda take so

Naila wani tsallen murnar ta k'arayi tare da rungumeshi tana " I love u daddy you are d best dad eva "

"I love you to Darling"

Alhaji Bala yace adai dai lokacin da yake barin d'akin fuskarsa d'auke da tsantsar farincikin yayewar matsalarsa

D'akin hajiya Lubna ya nufa dan ya rarrasota dan yasan fushi take dashi

Bai sha wahala wajen rarrashinta ba abunka da mata da miji sai gashi sun bige da soyayya dan dama tunda ya dawo basu had'u ba sabida rashin kwanciyar hankali sai da komai ya wakana Hajiya Lubna ta hau bashi shawarwari akan ya daina wasa da Sallah dan ita tasan aljanu ne suka ringa tsorata shi sabida babu wani kariya a jikinshi

Murmushi kawai Alhaji Bala yayi yace mata to zai gyara daga haka ya mik'e ya fad'a band'aki

Siyayya yayi wa Naila na fitar hankali Hajiya Lubna sakin baki kawai tayi tana kallon shi dan siyayyar ma har Dana banza bata kuma isa ta hana shi ba idan ma tayi magana cewa zai yi ita kad'ai ce dashi gwara ya kashe mata

Sai da magriba suka dawo gida bayan ya kaisu wajen shakatawa aka ringa jido musu siyayyar da sukayi ana shiga dashi cikin gida

Alhaji Bala yana tsaye aka gama shiga da kayayyakin Hajiya Lubna da Naila kuwa dama sun Dade da shiga ciki

Wajen motarsa ya koma ya shige ciki tare dasa lock

Wayarsa dayake communicating dasu killer ya d'auko daga bayan seat d'in motarsa dan baya shiga da wayar cikin gida sabida tsaro

Bai yi mamakin ganin miss call d'insu ba dan yasan Dole dama su neme shi

Layin Killer ya fara kira bugu d'aya ya d'auka

Yana amsa gaisuwar da Killer ya mishi yace "karku damu oll is fine na d'an shiga rububi ne hope duk kuna villa( sunan da yake cewa gidansu dake daji)

Killer ce mishi yayi " eee oga duka muna nan AKram ne kawai har yanzu bai zo ba sakamakon mom d'insa bata da lafiya yama ce zai kiraka ya fad'a maka"

"Zancen banza zancen wofi ina ruwanmu da wani Mom d'insa bata da lafiya who even cares ko mutuwa tayi dole ya dawo bakin aikinsa bansan mai yasa yake so ya ringa take umarnina ba amma babu komai zanyi wa tufkar hanci tunda mai hanani is gone let me call the fool"

Bai bari Killer yayi magana ba ya kashe wayar yana huci tare da dialling number Akram

Adai-dai lokacin da Akram ke kan Sallaya yana Jan carbi idonsa a lumshe fuskar Samha nata mishi yawo a ido dan kwanaki nan shi kad'ai yasan mai yake ji akan Samha duk fitar numfashinsa sai ya tuna ta bai tab'a jin San 'ya mace a zuciyarsa kamar yanda yake jin San Samha duk da Sau d'aya ya tab'a ganinta

Ringing d'in wayarsa ne yasa ya bud'e idonsa tare da d'aukar wayar ganin mai Kiran ne yasa ya mik'e da sauri tare da gyara zamansa ya d'aga wayar

Alhaji Bala fad'a ya rufeshi dashi yana "wai meyesa kake so kaga kana bijirewa umarni na ne?

Yanzu kawai Dan uwarka bata da lafiya shiyasa Baka koma Villa ba tuntuni yo ko mutuwa tayi na baka umarni kak'i bi Akram abubuwan da kake min ya isa haka not any more yanzu ba zanyi tolerating wanan nonsense d'in naka ba idan muka fita operation dole ka ringa participating idan na saka doka dole kuma ka bi baka isa kuma ka bar cikin mu ba Dan idan kayi joining d'inmu ba fita idan kuwa ka dage zaka fita sai na kasheka na kashe family d'inka gudun tonuwar asirinmu yanzu ba anjima ba ka shirya ka tafi Villa jibi muna da operation and kai zakayi leading d'inmu ranar kaji mai nace ko baka ji"

Da k'yar Akram ya iya cewa naji sabida tsananin mamakin Yanda Alhaji Bala ya canza take ya fara tunanin ko dai Mai gida ya fara ganowa shi d'an lek'an asiri ne

Jikinsa na rawa yafara Neman oganshi Abdullahi dan ya gaya mishi halin da ake ciki

Shima mamaki ne ya rufe shi daya gama jin abinda Akram yace ajiyar zuciya ya sauke yacewa Akram "tabbas Alhaji Bala is up to some thing tunda kaji yace yanzu kai ma dole ka ringa participating idan ya fita operation"

Akram hankali a tashe yace "oga yanzu ya za'ayi nifa bazan tab'a iya wani Abu ba idan ya fita rashin imaninsa har fyad'e fa yake sawa ayiwa yaran mutane da matan su ni aganina kawai tunda mun Riga da mun samu evidences kawai gobe aje har gida ayi arresting d'in shi"
Chapter 14 · 0% Book details