← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 31

Sashe 7

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anan Safna ke ce mata suna asibiti Alhaji Nazir ya kaisu jijjiga kanta kawai tayi ta mik'e aka hau tambayarta ina zata je

Cikin muryarta da bata fita tace zata je asibitin ta gano halin da suke ciki dan tamkar yanzu Hajiya Nafeesa ke ce mata ta kwantarwa da Daddynsu Hankali da kanenta

Fawazz Saurayinta da sauri ya mik'e yace zai kaita asibitin

Saiam ko kallonsa bata yi ba tayi waje kamar iska zai d'auketa ....

Nikam sai dai kuyi maneji Allah dak'yar nayi wanan

Mutuwa rigar kowa wacce ba cirewa ta d'auki Hajiya Nafeesa jikanta sarki buwayi Hajiya Nafeesa Allah ya jikanki rabbi shi yayi kiranki kullum muna ta tunaninki muna yabon halayarki

Ya Allah ya Allah ya gufuru ya Allah ya Allah Ya Allah gafarta mata ya
Allah ya Allah馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶馃槶 Allah kasa mucika da kyau da imani
[2:34PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫

*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝

*A heart touching story*

庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*sadaukarwa ga dukanin masoyana na zahiri da badini da wayanda na sani da wayanda bansani ba Sadnaf na kaunarku kamar yanda kuke kaunarta ana tare insha Allahu*馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹馃檹

Page 5

Ogansu Sai daya gama shek'a ayarsa da linder ya fito ya shirya a cikin manyan kaya kai ahaka idan ka ganshi zaka d'auka mutumin arziki ne Dan har da su hula yasa

Yana fitowa daga d'akin su Lion suka mimmik'e har da Akram da kansa ke balain ciwo Hannunsa a sak'ale yake a k'ugun Linder ya sakar musu wani jairin murmushi yana

"Killer lion scorpion black Akram Ni zan tafi Port Harcourt wajen iyalina zan dan huta haka kamar na 3weeks kafin mu kuma fita wani operation d'in inda nake tunanin wanan karon kano muka nufa dan akwai wani Alhaji Buba mai gwala gwalai yana da balain kudi ina nan ina monitoring d'insa akwai wata servant d'insu Habiba ita nakeso na jawo jikina in sakar mata kud'i ta bani details d'insu sosai da yanayin gidan immediately ina gama samun Duk wani information akansu zan kiraku Ku fara shirye shiryen daya kamata"

"Sanan kafin lokacin idan kuna da wani uzuri zaku iya zuwa kuyi amma kwana uku kawai na Baku dukanku Ku dawo do I make my self clear"?

Da sauri dukansu suka gyad'a Kansu suna yes boss

Daga haka ogansu yasa kai ya fice daga palon suna take mishi baya still yana rik'e da kugun Linder dan shi zaiyi dropping d'inta a hanya

Sai da Killer yasaka mishi brief case d'in kud'inshi abayan boot kafin ya ja da baya Ogansu kuwa yaja katon jeep d'in yabar harabar gidan

Ciki suka koma gabad'aya kowanensu yafara shirin tafiya uzurinsa akwai masu zuwa su duba iyayensu irin su Lion da sukayi wa iyayensu karya akan aiki suke a Abuja akwai irinsu black dake da iyali da suma suka shirgawa iyalinsu karya akan suna aiki a abuja

Akram ya rigasu shiryawa gabad'aya dan ji yake kamar akan k'aya yake

Kallonsu Lion yayi fuskarsa d'auke da murmushi adai dai lokacin da yake rataya jakarsa a kafad'arsa yace

" to ni kunga tafiyata zanje naga parent d'ina da siblings d'ina zan kai musu d'an abunda muka samu insha Allahu bazan wuce 3days da boss ya d'ibar mana ba"

Dukansu murmushi sukayi dan haka kawai Allah ya had'a jininsu da Akram shiyasa ma koda an fita operation dashi baiyi komai ba basa damuwa

Killer ne yace " same here muma zamuje muga namu iyayen akwai kanwata ma da za'ayi bikinta nasan suna nan suna zuba ido dan dani suka dogara Nima zan kai musu abunda ya samu"

Murmushi kawai Akram yayi a zuciyarsa yana tausayin halin da suka jefa Kansu sabida talauci yana tausayinsu ranar da asirinsu zai tonu asaka musu ankwa a hannu all they are a doing is for d sake of their family

Duk rashin aikin yi ne ya janyo musu fad'awa halaka ciki kuwa har da rasa imaninsu tunda basu d'auki kisan kai abakin komai ba

D'aya bayan d'aya ya bisu ya rungume yana ce musu sai sun dawo nan da kwana uku daga haka yasaka kai ya fice daga gidan dayake ji tamkar prison bai zame ko ina ba sai head quarter d'insu na Ss

Agajiye ya k'arasa office d'inshi ya dafe kansa dake Sara mishi har yanzu yana jin ihunsu Samha a kunensa ko yaya ya runtse idonsa sai ya hango abubuwan da suka faru a Daren jiya

Haka kawai yaji ya tsani kansa yana tuhumar kansa shima da laifin shi awajen kisan Hajiya Nafeesa sai yanzu yake mugun daya sani da ya d'auki mataki tun a lokacin daya sani ya harbesu duka dayaga yanda Hajiya Nafeesa ke fad'i tashi akan ta kare martabar 'ya'yanta idan kuma ya tuna kwanan ta ne ya kare sai ya rage ganin laifinsa ahaka ya zauna wajen minti ashirin kafin ya iya mik'ewa ya Shiga band'akin dake cikin office d'in ya d'aura alwala yazo yayi sallar Azahar yana idarwa ba tare da b'ata lokaci ba ya nufi office d'in ogansu

Bayan sun gaigaisa kamar yanda suka saba da tambaye tambaye ogansu ya tambayeshi abubuwa daya k'ara samo musu akan Alhaji Bala

Akram jiki Asanyaye ya mik'a masa 'yar k'aramar Camerar dake hannunsa ogansa kuwa ya k'arba a dokance

Cikin minti biyar ya had'a camerar da system d'in dake gaban table d'insa

Tun daga yanda suka shirya da zasu tafi operation har zuwa yanda suka d'aure mai gadin gidansu Hajiya Nafeesa daya bud'e musu k'ofa tagumi ogansu yayi yana kallon system d'in dake gabanshi jikinsa sai rawa yake yabi ya jike da gumi duk da sanyin Ac dake ratsa office d'ind'in

Wani irin kad'awa idonsa yayi ya mik'e jikinsa na wani irin k'yarma "innalillahi wa inna ilaihi rajiun" kawai yake maimaitawa ahankali ya kalli Akram daya dafe kansa da hannu biyu k'walla na zuba a idonsa dan wani irin zafi yake ji a zuciyarsa dayake jiyo sautin kukan Hajiya Nafeesa da su Saiam magana ya fara yi yana

"Akram meyesa baka ceci rayuwar matan nan ba meyesa bakayi wani Abu dan kar Alhaji Bala ya harbeta ba tunda nake ganin abubuwa ban tab'a ganin abun tausayi irin wanan ba matan nan tabani tausayi fiye da tunanin mai tunani Alhaji Bala ya Dade yana abubuwa amma this time around his cup is full bama bukatar wani prove ko evidence wayanda muke dasu kawai sun ishemu enough is enough lokaci yayi da ya kamata mutane su San waye Alhaji Bala lokaci yayi daya kamata ace mutane su San irin sana'ar da yake yi"

Rawa jikin shi ke yi sosai idonsa jajawur

Akram kuwa ko magana ya k'asa yi dan shi kad'ai yasan halin da yake ciki

Ni kam waye wanan Alhaji Balan ne toh bari muji waye shi

Alhaji Bala haifaffen dan jigawa ne a kauyen kafin Hausa su hud'u iyayensu suka Haifa duka maza sun taso ne a cikin tsananin talauci dak'yar suke cin abincin sau biyu arana tunda Bala ya taso ya taso da masifar San kud'i dan idan ya zauna da mahaifiyarsa Saude haka zai taba ta labarin irin kud'in da zaiyi idan ya girma da abubuwan da zai mata da kanensa sabida mahaifinsu ya Dade da rasuwa ahaka Alhaji Bala ya taso da mugun San kud'i duk da mahaifiyarsu Saude na matuk'ar k'ok'ari dan taga ta sama musu ingantaciyar rayuwa

Alhaji Bala na da shekara goma sha biyu ya fara buga buga shine noma shine aikin gini sharar kwata duk wani Abu daya San zai shigo masa da kud'i yinshi kawai yake ahaka rayuwa tayi ta tafiya dak'yar ya gama primary sch a kauyensu inda daga nan ya tattara karatun ya watsar ya cigaba da Neman kud'i yana kula da mahaifiyarsa da kanensa uku Saidu Abubakar da zaidu ahaka Alhaji Bala ya ringa Tara kudin da yake buga buga inda ya Tara wajen dubu biyar a lokacin kudine masu daraja da yawa shawara yayi da mahaifiyarsa Saude da ta tsufa tukuf wanda a zahiri ba tsufan tayi ba tsabagen talauci ya tsufar da ita

Shawara ta bashi akan yaje birni ya saro shadodi da atamfuna masu kyau na manya da yara yanda basai aringa wahalar zuwa birni siya ba aikuwa take yabi shawararta dan babu inda ake siyarwa a kauyen

Aikuwa cikin sa'a ya saro kayan dan kayan basa sati ake siyesu har da masu kawo mishi kud'i ya hada masu lefe awanan lokacin

Watarana yaje birni zai sari kayan an gama loda mishi kayan a mota kenan zai hau yaji ana ta mishi horn abayansa

Juyawa yayi yaga wata had'adiyar mota ya had'iyi wani irin yawu dan sai ka isa zaka iya siyan motar kafin ya gama karewa motar kallo aka bud'e k'ofar motar aka fito buhun hannunsa ya wurgar ya tafi da gudu ya rungume abokinsa Ukashat da sukayi primary sch tare

Sai da ukashat ya kalleshi daga sama har k'asa kafin yace ya yaganshi haka

Shi dai Alhaji Bala baki a sake kawai yake bin ukashat da kallo da kayan jikinsa da motarsa

Horn mai motar ya ringa yiwa Alhaji Bala dan yazo su tafi

Ukashat kuwa yace yaje ya hau zai biyosu abaya

Aikuwa haka akayi har k'ofar gidansu Alhaji Bala Ukashat ya bisu sai da aka gama sauke kayan gabad'aya Sanan Alhaji Bala ya nufi wajen ukashat dake hakimce a cikin motarsa yana yatsina fuska kamar Wanda yaga kashi d'aya barin Alhaji Bala ya bud'e ya shiga ya zubawa ukasha ido yana mamakin yanda akayi yayi kud'i acikin shekara takwas kawai da sukayi da rabuwa abunda burinsa kenan arayuwa

Agurguje Ukasha ya gayawa Alhaji Bala silar samun kud'insa ta hanyar armroberry inda wani ya mishi hanya shima anan shima yace idan Alhaji Bala yana so yayi bankwana da talauci to shima yazo yayi joining d'insu da farko Alhaji Bala k'i yayi amma da Ukasha ya kwadaita mishi irin kudin da ake samu atake ya amince

Kaninsa Saidu ya d'ora akan kayansa akan ya cigaba siyarwa

ya shirgawa Mahaifiyarsa karya akan ya samu aiki a birni adduoi Saude ta bishi dashi ba tare da b'ata lokaci ba yabi Ukasha suka tafi
Chapter 7 · 0% Book details