← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 31

Sashe 21

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samha haka kawai fuskar Akram ya k'asa b'acewa a idonta indai ta zauna ita kad'ai sai tunaninsa ya fad'o mata ta ringa jin wani iri a zuciyarta Wanda ta ringa alk'anta haka da kiyayyar da take musu Dan babu wayanda ta tsana kuma bazata manta dasu ba sama dasu Alhaji Bala har gobe tana hango fuskokinsu a idonta Wanda Akram yafi tsaya mata a zuciya ta kuma rasa dalilin haka babu ranar banzan da zata dungura goshinta a k'asa batayi addu'a akan Allah ya tona musu asiri ba

Su Saiam kuwa suma tuni suka fara warware Dan mazajensu na iya bak'in k'ok'arinsu wajen deb'e musu kewa kullum a cikin waya suke dasu Saheeba addu'a suke sosai Akan Allah yayiwa Mahaifiyarsu Rahama duk da wani zubin su kanyi mafarki da ita a cikin kyakyawan yanayi

B'angaren su Akram kuwa tuni sukayi arranging d'in yanda zasu damke Alhaji Bala aranar da zaije operation gidan Alhaji Ghali inda suka jawa su killer kunne sosai akan su basu had'in kai kar Alhaji Bala ya gane wani Abu har suyi arresting d'inshi

Tuni su Akram suka nufi Dajin da suke zama Dan su jira Alhaji Bala

Inda 'yan sanda kuwa suka yi surrounding d'in gidan Alhaji Ghali ba tare da saninsa ba har da masu video coverage da hotuna

Alhaji Bala kuwa a no mercy d'insa ya nufi Abuja da mugun nufi a zuciyarsa dan tunda Naila ta rasu yaji bai k'i duk Wanda yayi tozali dashi ya mutu ba most especially mata Sa'anin Naila Dan aransa ma ya kuduri idan Akram yau ya bijirewa Umarninsa babu abinda zai hana ya harbe shi

K'arfe goma sha d'aya ya isa Dajin fuskar nan tashi a d'aure yana shiga kantamemen palon dukansu suka mik'e tsaye alamar girmamawa dan dama haka suke gaishe shi

Akram kuwa haka kawai gabansa ya yanke ya fad'i da suka had'a ido da Alhaji Bala take ya hau Jan addu'oi aransa akan Allah ya basu Nassara har su damke Alhaji Bala batare da wani failure ba

D'aya bayan d'aya Alhaji Bala ya ringa binsu da kallo wanda da ace da wadatar haske awajen babu abinda zai hana yaga yanda su killer suka fita daga Hayyacinsu gaban Akram kuwa sai fad'uwa yake

A hankali ya sauke idonsa akan Akram dan shine a k'arshe gabansa yaje ya tsaya ya damko kafad'arsa yace " Akram a yau inaso kasani babu tausayi babu imani a cikin al amarina kayi taka tsan tsan karka bijirewa umarni na dan wlh yau slide mistake idan kayi sai ka tafi lahira na d'au alwashin sai na d'au fansar Kisan da aka yiwa 'yata Naila wlh babu Wanda zan ragawa yau Dan haka u guys should be very carefull"

Killer ji yake kamar ya fito yayi magana yace wa Alhaji Bala Akram pretending yake ayau za'a kama shi dan ayanda yake ji aransa gwara a kashe Akram inyaso a kamasu gabad'aya take yayi amana da shawara da ya yanke

Ya bud'e Baki yace "Oga inada Magana"

Gaban Akram ne yayi wani irin Yankewa ya fad'i ya zubawa Killer ido

Killer kuwa ya d'auke kai ya kalli Alhaji Bala ya bud'e baki zai yi magana bud'e bakinsa ke da wuya yaji an d'auke shi da wani bahagon mari daya sa ya kusa kurmancewa

Dafe kumatunsa yayi da hannu biyu ya waiga da sauri Dan yaga Wanda ya zuba mishi wannan Marin

Hajiya Nafeesa ya gani a gefensa ta gwallo ido tana kallonsa sai huci take

Wani razannan ihu yasa ya kankame Black yana nuna hajiya Nafeesa da Hannu

Su Alhaji Bala kuwa suka bi inda yake nunawa da kallo basu ga komai ba

Wani ihun ya k'ara sawa A lokacin da Hajiya Nafeesa ta ringa doso shi yaje ya kankame Alhaji Bala yana k'ok'arin magana

Amma ina amadadin yayi magana sai gwaranci yake yi kamar mai koyon magana

A zuciye Alhaji Bala ya ture shi daga jikinsa ya d'auke shi da mari yana "wanan wane irin iskanci ne zaka ishe mu da ihu menene yake tsorata ka wani sabon iskancin ne haka"?

Killer zaro ido kawai yake yana gwaranci yana nuna Hajiya Nafeesa da hannu sai k'ok'arin kankame Alhaji Bala yake

Ihu kawai yake yana zagaya wajen yana gwaranci Dan Hajiya Nafeesa tsorata shi take sosai

Akram kuwa mamaki ya ringa yi na abinda yake tsorata killer haka har maganarsa ta koma ta yara

Alhaji Bala a zuciye ya damko killer ya wulashi d'aki ya kulle ya dawo cikin palon ya kalli agogon hannunsa yaga k'arfe sha biyu da minti ashirin

Bak'ak'en kayansa ya d'auko ya sa ya d'auko mask d'insa ya saka a fuskar shi with Command yace su wuce su tafi is time

Da sauri suka ringa ficewa jikinsu na d'an rawa Alhaji Bala ya ringa mamakin yanda akayi basu da kuzari kwata kwata sai da ya koma d'akin daya sa killer ya saka seletep ya rufe mishi baki sabida ihun da ya ringa yi Dan har fitsari ya saki a wando

Sannan ya fito suka d'auki hanyar gidan Alhaji Ghali yana ta sake saken irin muguntar da zai yi

Basu sha wahalar shiga cikin gidan ba dan Alhaji Bala sai da ya shirya sosai kafin su taho mai gadi ma gindin bindiga ya buga mishi ya zube awajen a sume

Da zuwansu da shigarsu cikin gidan 'yan sandan dake kewaye da gidan duk suna Sane tuni suka k'ara gyara tsayuwarsu suna jiran abasu Umarni banda masu video coverage da hotuna da suma suka zama ready suna jiran su fara aikinsu duk da wasu sun fara d'aukansu video a lokacin da suka shigo

Alhaji Bala k'afa d'aya akan d'aya ya d'ora a center table d'in dake cikin palon yana girgiza k'afa a lokacin da su Black suka raba Kansu suna fito da mutanen dake cikin gidan ciki kuwa har da Akram da wani irin farinciki yake ratsa shi na cikar burinsa finally Alhaji Bala yau asirinsa zai tonu

Alhaji Bala kuwa wani irin dariyar mugunta yake a lokacin da yaga ana hankad'o keyar 'ya'yan Alhaji Ghali Dan dukansu sun zo Hutu su wajen Uku had'add'un yan mata kyawawa dasu

Alhaji Bala sai Lashe lebb'e yake yana matsa cinya yana hararo yanda zai musu fata fata har sai sun koma ga mahallicinsu

Alhaji Ghali kuwa da matansa biyu jikinsu rawa kawai yake

Sai da ya gama karewa 'yan matan kallo ya maida kallonsa kan Alhaji Ghali yace "kasan abunda ya kawo mu ba sai ka b'ata mana lokaci ba"

Alhaji Ghali jiki na rawa ya shiga gyad'a masa kai

Alhaji Bala kuwa ya kalli Lion da black sukayi sauri suka tisa keyar Alhaji Ghali suka shiga ciki suka hau fito da kud'add'e a brief case suka hau ajiyewa agaban Alhaji Balan daya tsurawa 'ya'yan Alhaji Ghali ido da suka cure waje d'aya jikinsu na rawa

Sai da suka gama ajiye kud'in agabansa ya kalli Alhaji Ghali da jikinsa ke rawa yace

"Ka tabbata duk kud'in dake cikin gidanan kenan"?

Girgiza masa kai Alhaji Ghali kawai yayi dan yama k'asa magana kwata kwata

Alhaji Bala murmushi yayi ya mik'e ya nufi wajen 'yan matan yana wani lashe lebb'e

Alhaji Ghali kuwa yayi sauri yasha gabansa cikin rawar murya yace " bawan Allah Dan Allah dan annabi karka tab'a min yarana idan kud'i kake so zan k'ara maka"

Alhaji Bala wani Mahaukacin dariya ya kwashe dashi yace "ko duk kud'in duniyan nan zaka bani wlh babu abinda zai hana ni yaga yaran can"

Gaban Alhaji Ghali ne yayi wani irin fad'uwa ya durk'usa akan gwiwarsa yace "bawan Allah ka rufamin asiri dan Allah karka tab'a min yarana"

Alhaji Bala wani dariyar ya k'ara kecewa dashi yace "ai ba iya yaranka zan tab'a ba har da wadancan guzumayen"

Akram kallonsu kawai yake yana murmushi

A lokacin da 'yan matan suka fashe da kuka suna k'ara kankame juna

Alhaji Bala ture Alhaji Ghali yayi daga gabanshi ya nufi wajensu yana wani dariya

Alhaji Ghali kuwa yabi bayansa da Sauri yana rok'on shi

Fuska a d'aure Alhaji Bala ya juyo ya kalli Akram da still murmushi yake shimfid'e a fuskar shi yace "take care of this fool"

Akram cikin takun kasaita ya nufesu yana wani irin murmushi adai-dai lokacin da Alhaji Bala ya finciko d'ayarsu ta saki wani wawan Ihu

Wani bahagon Mari Alhaji Bala ya shimfid'a mata a fuska ya jawo rigarta zai raba gida biyu yaji an d'ora mishi bindiga a k'eya yaji ana " thousand days for the thiefs one day for the owner Alhaji Bala your cups is full"

Alhaji Bala a hankali ya juyo dan ya gaskata muryar Wanda yaji............ 🧐🧐🧐🧐🧐
🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑

*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅

*A heart touching story*

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Follow me on Wattpad@Sadnaf*

*Page 15*

Da Mad'aukakin mamaki Alhaji Bala ya zubawa Akram ido dake wani irin Murmushi

Akram kuwa yace "Kana mamaki ne Alhaji Bala yau dubunka ya cika asirinka ya tonu yau mutane zasu San wanene kai yau duniya zata San irin mugayen abubuwan da kake aikatawa yau za'a San irin sana'ar da kake yi har kake taimakawa mutane ake maka kallon mutumin kirki nan kuwa babu Wanda ya kai ka zalunci a d'oron k'asa am not who you think am not one of you nashiga cikinku ne Dan na k'ara Sanin kai waye Alhaji Bala despite abinda ya faru da ya kamata ya zame maka ishara na fyaden da aka yiwa 'yar ka har ya kai ta ga rasa ranta wannan bai sa ka saduda ba kayi nadamar abinda kayi kasan cewar abinda kake yiwa yaran wasu ne ya juya kanka amma me a madadin kayi nadama a lokacin ka k'ara shan Alwashin yanda zaka cigaba da farautar dukiyoyin jamaa kana ketawa 'ya'yansu haddi not any more Alhaji Bala a yau"""

Wani mahaukacin Dariya Alhaji Bala ya fashe dashi yace "kayi kuskure Akram da kayi tunanin wannan soki burutsun da kake yi zai tsoratani I thought as much kai ba Alheri bane awajena and ayau zanyi finishing d'inka Lion Black before counting of 3 Ku bud'e mishi wuta"

Alhaji Bala yace yana buga k'afarsa da kasa tare da rik'e hannun Akram dake rik'e da bindiga
Chapter 21 · 0% Book details