← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 31

Sashe 25

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akram kuwa shima jikinsa ne ya d'au rawa hankalinsa a tashe dayaga yanda Saheeba ta razana da ganinsa

Yazeed kuwa tunda tayi sallama ya k'afeta da ido baya ko kiftawa

Dak'yar Saheeba tace cikin inina tana nuna Akram "Daddy yana tsaye fa aka kashe""""

Da Sauri Alhaji Nazifi ya katse ta yana "Sau nawa kukeso na ringa fad'a muku kwanan mahaifiyarku ya Riga da ya kare ko ya hana shi ko bai hana shi ba sai ta amsa kiran mahallici and j told u guys this young guy is doing his job bansan wane irin kunne ne daku maza ki koma ki d'auko musu ruwan sha kafin na sasab'a miki"

Da Sauri Saheeba tayi waje a tsorace Dan wani irin tsoron Akram takeji

Tana ficewa Alhaji Nazifi yace "am so sorry for what happen kasan yarinta ke damunsu tun ranar da asirin Alhaji Bala ya tonu suke ta surutai sun k'asa ganewa akan aikinka kake aikinku ya gaji haka in banda yarinta idan Ajali ya kira ai sai kaje"

Akram jiki a sanyaye ya d'ago yace "Alhaji nasan hakan zai faru Dole yaranka su tsane ni zakayi mamakin abubuwan danayi undergoing kafin nasamu nassarar capke Alhaji Bala wlh I left my family I live a miserable life just to reveal his secret pls tell your children to forgive me wlh ba laifina bane sai kayi pretending you are one of them zaka iya gano irin su Alhaji Bala"

Alhaji Nazifi murmushi yayi yace "haba Akram karka wani damu aikin Alheri kayi Dan ba dan kai d'in ba babu Wanda zai San true colour d'in Alhaji Bala da yana nan yana tapka b'arna a d'oron k'asa karka wani damu yarana basu tsaneka ba kawai wanan bak'in Daren da suka rasa Mahaifiyarsu ne bazasu iya mantawa ba"

Yazeed godiya ya fara yiwa Alhaji Nazifi shi kuwa Akram gabad'aya jikinsa ya k'ara sanyi ya rasa mai ke mishi dadi dan yasan watak'ila haka Samha ta tsane shi idan taganshi zata tsorata kamar yanda Saheeba ta tsorata

Yazeed fad'awa Alhaji Nazifi yayi na abinda ke tafe dasu na Akram yaga d'aya daga cikin 'ya'yansa yana so kuma ba wasa ya kawo shi ba Aurenta yake so yayi

Akram d'agowa yayi ya kalli Alhaji Nazifi dan yaga yanda ya k'arbi zancen aikuwa ya hango tsantsar farinciki a fuskar Alhaji Nazifi dan murmushi kawai yake yi hakan ne yasa yaji sanyi aransa dan yasan koda Samha zata bashi matsala Alhaji Nazifi zai iya shawo kanta

Alhaji Nazifi duk da yaji dadin maganar da suka zo dashi dan babu Wanda zai k'i bawa Akram 'yarsa ya Aura sai da yadan jinjina lamarin aransa duk da baisan wa yake so a cikinsu ba yasan sai an kai ruwa rana koma wacece a cikinsu zata amince ta Aure shi sabida kiyayyar da suke mishi

Alhaji Nazifi ce musu yayi babu Matsala indai ta b'angarensa ne addu'a zai raka su dashi Allah ya musu zabin da yafi Alheri amma Abu d'aya ne zai sa bazai bashi Auren 'yarsa ba idan dai ta nuna bata sansa dan gaskiya babu wacce zai yiwa Auren dole a cikinsu ballantana ya tursasa wacce yake so duk da bai San wa yake so a cikin yaran nasa ba

Sai a lokacin Alhaji Nazifi ya tambayeshi wa yake so a cikin 'ya'yansa

Akram da jikinsa ya gama mutuwa gabad'aya da maganar Alhaji Nazifi dak'yar ya bud'e baki yace k'aramar cikinsu yake so"

Ajiyar zuciya Alhaji Nazifi ya sauke yace babu damuwa bari ya fita ya turo musu ita Allah yasa su dai-daita

Godiya suka had'a baki suna mishi har ya fice daga palon

Yana fita Yazeed ya daki kafad'arsa yana mik'ewa tare da tsallen murna yana "Abokina wlh na samu irin matar danake so na Aura gaskiya 'yar nan tasa data fita ta had'u"

Akram tsaki yayi ya buga tagumi yana kallon bakin k'ofa fargaba duk tabi ta cika shi

Yazeed kuwa sai santin kyaun Saheeba yake yana shima ana kwana biyu zai zo ya samu Alhaji Nazifi akan yana Santa

Alhaji Nazifi kuwa a lokacin da ya isa b'angarensu a Palo ya tarar dasu a zaune sunyi jungum jungum kamar wayanda akayi wa rasuwa

Yana shiga palon Suhaima tayi Sauri ta tare shi tana tambayarshi dagaske Akram ne yazo gidansu?

Suhaima kuwa tana rakub'e a gefe kirjinta kamar ya fad'o k'asa tunda Saheeba ta gaya musu Akram yazo taji jikinta na rawa tama rasa wane irin tunani zatayi

Alhaji Nazifi kuwa waje ya samu ya zauna ya kirasu d'aya bayan d'aya suna Amsawa

A hankali ya fara musu Nasiha mai ratsa jiki yana nuna musu su ajiye kiyayyar da suke yiwa Akram bashi da laifi a mutuwar Hajiya Nafeesa akan aikinsa yake koda ma basu zo ba a ranar kwanan Hajiya Nafeesa yariga da ya kare nasiha ya musu sosai sai da ya tabbatar da jikinsu yayi sanyi ya maida kallonsa kan Samha da ta had'a gumin babu gaira babu dalili yace mata sabida ita Akram yazo wajensa yana Santa da Aure

Wani irin mik'ewa Samha tayi hankali a tashe ta nuna kanta tana " Daddy ni yake so da Aure kuma ka amince wlh ni bana sansa na tsane shi bana so na bud'i ido na ganshi bazan iya Aurensa ba"

Tana gama fad'ar haka tayi d'akinsu da gudu Tana kuka

Alhaji Nazifi bayanta yabi da kallo har ta shige dan yasan dama za'a Rina bazata yi accepting Akram cikin Sauki ba

Mik'ewa yayi ya koma palon b'aki ya bawa Akram hakuri akan su dawo wani lokacin insha Allahu zai yi k'ok'arin ya shawo kan Samha idan kuma ta d'age bata San shi sai dai yayi hakuri dan bazai iya tilasta mata ba

Akram ji yayi kamar guduma Alhaji Nazifi ke kwad'a mishi aka sabida yanda yaji nauyin maganar take hankalinsa ya tashi dan agaskiya bazai iya hakura da Samha ba yanda yake jin mugun Santa a zuciyarsa

Alhaji Nazifi kuwa ganin yanda Hankalin Akram ya tashi yasa yafara kwantar masa da hankali yana kar ya damu zai yi k'ok'ari ya shawo kanta

Ahaka suka mishi sallama suna mishi godiya Akram kuwa kamar ya kife sabida tashin hankali.......

🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑

*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅

*A heart touching story*

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Follow me on Wattpad@Sadnaf*

*Am speechless a hak'ik'anin gaskiya banida bakin da zan yiwa dukanin masoyana godiya sai dai nayi muku fatan Alheri Affan na godiya da adduo'in da kuka mishi Allah ya saka da Alheri ya biya muku bukatunku na Alheri*

*Wanan shafin nakune muna mugun tare*

*Nafeesa I shehu*
*yar Baiwa*
*Bilkisu ya'u BK*

*Page 19*

Alhaji Bala kuwa tuni aka jingine case d'insa a gefe guda sabida shi da matacce babu maraba Dan kamar ma ba mutum ba in banda wari da rok'on mutuwa babu abinda yake yi dan Na Maliya bai fasa zuwa ya watsa mishi ruwan kaikai ba duk da yanzu babu fata a jikinsa sabida cizgeshi da yake yi da kansa

Akram kuwa bashida wani Matsala arayuwarsa sai na rashin shawo kan Samha dan zuwansa gidan uku bata yarda ta fito last zuwansu ne ma sukayi kicibus da ita ta dawo daga Islamiyya a lokacin da yayi tozali da ita ji yayi kamar k'ara kwarara mishi wutan Santa ake Ashe kallon tsoro yayi mata daddare Samha ba k'aramar kyakyawa bace

Samha kuwa jikinta ne ya d'au rawa gabanta na Balain fad'uwa ita kad'ai tasan abinda ya ringa mata yawo a kowane sassa na jikinta a lokacin da ta had'a ido dashi amma dan k'arfin hali irin nata da taurin zuciya d'aure fuska tayi ta ratsa ta gefensu ta wuce duk da kiranta da yake yi da husky voice d'insa dake k'ara narkar mata da zuciya a lokacin Alhaji Nazifi baya nan haka su Akram suka zauna a mota suna jiran dawowarsa dan Akram k'asa tafiya yayi dan gani yake idan bai Shawo kan Samha ta aminta dashi ba komai zai iya faruwa dashi dan duk fitar numfashinsa kaunar Samha linkuwa yake aransa fuskatar kawai yake gani a idonsa da sexy eyes d'inta dake sa shi kasala

Samha kuwa aguje ta k'arasa d'akinta sabida bugun da zuciyarta keyi a k'asa ta zub'e tana maida numfashi tare da dafe saitin zuciyarta sabida harbawa dayake dan Kaunar Akram ayau data gan shi wani San sa ne yak'ara bin ko ina na jikinta babu abinda ke amsa kuwaa a kunnenta sama da muryarsa mai dadin gaske sigar ma da ya kira sunanta ya bambamta da yanda ake kiranta babu Wanda ya kai shi iya kiran sunanta

Lumshe idonta tayi ta na jin muryarsa a kunnenta still tana dafe da kirjinta a hankali ta mik'e taje bakin window ta d'aga labule dan ta k'ara kallon sa

Kirjinta ne ya hau bugawa da Sauri a lokacin da ta hango shi a saman motar shi a zaune ya dafe kwantacen suman Kansa daya sha gyara bak'in agogon dake sak'ale a hannunsa sai kyalli yake shigar white and black yayi na kananan kaya fad'ar kyaun da yayi ma b'ata bakine

Samha ko kifta idonta batayi sabida kallonsa da take wani irin Kaunarsa na ratsa ilharin jikinta

Motsin da taji a bakin k'ofa ne yasa tayi sauri ta saki labulen tare da nufar kan gadonta dan bata so 'ya'yyenta su gane halin da take ciki sabida har dasu ake rarrashinta akan ta saurari Akram

Alhaji Nazifi sai da Magriba ya iso gida bai shiga da motarsa ciki ba ya sauko sabida hango su Akram da yayi haka kawai yake tausayin Akram dan yasan yana balain San Samha sai dai har yanzu Samha tak'i ta karbeshi a matsayin mai sonta duk da ban baki da Nasihar da yake mata

Su Akram kuwa suna hango shi suka tareshi tare da zubewa agabansa suna kwasar gaisuwa bayan gaishe gaishe da tambaye tambaye Alhaji Nazifi yace musu su shiga suyi Alwala suyi sallah tunda Magriba tayi inyaso idan sun idar sayi magana
Chapter 25 · 0% Book details