← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 31

Sashe 29

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hamdala Alhaji Nazifi ya runga yi a zuciyarsa Dan Yasan Akram zaiji dadi idan yagaya mishi Samha ta amince girgiza kansa yayi cikin farinciki ya d'aga muryarsa yanda Samha zata jiyo shi yace "ai da kin tsaya girman kai kiga yanda kwad'o zai miki k'afa"

Samha kuwa dafe k'irjinta tayi tana mamakin yanda akayi Kalmar ta fito daga bakinta wani irin kunya da nauyin Alhaji Nazifi da su Saheeba ne ya rufeta ita da ta gama cika baki bata San sa sai gashi babu kunya babu tsoron Allah ta bud'e baki tace tana San sa ahaka ta mak'ale a band'aki ta kasa fitowa

Su Suhaima kuwa sai tsokanarta suke suna kwaikwayar muryarta lokacin da tace bata San shi

Alhaji Nazifi kuwa yana zuwa palon da su Akram suke suka zub'e a k'asa suna gaishe shi wani irin kunya da Nauyin yanda zai ce mishi baya San su Suhaima ne ya rufe shi

Alhaji Nazifi kuwa yana lura da yanda Akram ya takura kansa yak'i d'agowa murmushi yayi ya kira Sunan Akram

Akram ya d'ago yana kallonsa ce mishi yayi kar ya damu yasan yana jin nauyin ya fad'a masa baya San su Suhaima kar ya damu matar mutum kabarinsa Allah ya Riga da ya tsara Samha rabonsa ce dan ta amince zata Aure shi

Akram sakin baki yayi yana kallon Alhaji Nazifi dan badan yasan babu 'yar wasa a tsakaninsu ba da sai yace wasa yake masa

Yazeed cikin tsananin farinciki yace Alhamdulillah amma munji dadi

Akram kuwa fad'ar farincikin daya tsinci kansa a ciki b'ata bakine dan k'asa rufe bakinsa yayi da ace Alhaji Nazifi baya nan babu abinda zai hana shi taka rawa

Alhaji Nazifi kuwa addu'a Ya musu na Allah ya tabbatar musu da Alheri ya mik'e zai tafi Akram yayi sauri ya dakatar dashi yana sunkuyar da kai dan so yake ya mishi maganar Yazeed dan tundazu yake mitsininsa

Farinciki Gaza b'oyuwa yayi a fuskar Alhaji Nazifi bayan Akram ya fad'a mishi Yazeed na San 'yarsa da ta kawo musu ruwa ran nan

Alhaji Nazifi tambayoyi yayi wa Yazeed akan family d'insa da irin aikin da yake yi

Aikuwa ya samu gamshashiyar bayani akan family d'insu Yazeed dan kanin Mahaifin Yazeed abokinsa ne tare sukayi secondary school addu'a ya k'ara musu na fatan Alheri suka ringa mishi godiya ya mik'e yace bari ya turo su Saheeba

Yana fita Akram da Yazeed suka runguma juna suna murna Akram kamar ya jawo Samha gabansa yayi ta kallonta haka yakeji sai kallon bakin k'ofa yake yaga ta inda Samha zata b'ullo

Alhaji Nazifi kuwa d'akinsu Samha ya nufa fuskarsa d'auke da murmushi har a lokacin su Suhaima maganar Samha suke Samha kuwa na mak'ale a band'aki

Alhaji Nazifi tambayarsu yayi inda Samha take suka ce mishi tana band'aki tak'i fitowa

K'walla mata kira ya fara yi Samha kuwa kamar ta nutse dan kunya dak'yar ta bud'e k'ofar band'aki tafito kanta a sunkuye

Alhaji Nazifi murmushi yayi yace "jaira kawai ana so ana kaiwa kasuwa maza shirya kije gashi can a Palon bak'i yana jiranki Saheeba kema kije kina da bak'o idan kin dawo zan miki bayani akan shi"

Daga haka ya sa kai ya fice daga d'akin

Yana fita Suhaima ta rangad'a gud'a tana sun kusa shan biki Saheeba kuwa tunda yace taje tayi bak'o jikinta ya hau rawa dan bata tab'a tsayawa da Saurayi ba da taimakon Suhaima suka shirya duk da Samha nonok'ewa take yi Suhaima kuwa sai tsiya take mata har bak'in k'ofar palon ta rakasu ta juya

Dukansu sanye suke da dogwayen riguna iri d'aya sai dai bambamcin kala na Samha bak'ine na Saheeba kuma Pink

Samha kuwa sai da ta rufe fuskarta ruf jikinta na d'an rawa har suka isa palon da su Akram suke

A tare suka amsa sallamar da sukayi musu Akram kuwa ya zubawa Samha ido da ta rakub'e a bakin k'ofa kanta a sunkuye

Wani wawan ajiyan zuciya ya sauke daya sa sai da Yazeed ya d'ago ya kalleshi

Saheeba ce tayi k'arfin halin gaishe su dan Samha sabida rawar da jikinta yake yi ta k'asa bud'a bakinta

Yazeed ne ya amsa sabida hankalin Akram na kan Samha dake neman shigewa k'asa

Sai a lokacin Saheeba ta d'aga kanta suka had'a ido da Yazeed gabanta ne ya yanke ya fad'i take itama jikinta ya hau rawa

A takaice aranar zancen kurame akayi su Akram ne kawai suka ringa kid'ansu suna rawarsu dan su Samha basu tab'a tsayawa da namiji da sunan zance ba

K'asan zuciyar Samha kuwa duk fitar maganar Akram sai taji kamar k'ara rura mata wutan San shi ake a zuciyarta

Saheeba itama tunda ta had'a ido da Yazeed taji ya kwanta mata aranta

Akram babu yanda baiyi ba dan yaga fuskar Samha amma fir Samha tak'i bud'a mayafin data rufe fuskarta dashi akan dole ya hakura dan ko magana tak'i tayi mishi

Sai wayarsa ya mik'a mata ta ta sa mishi number ta ta mik'e da sauri tabar palon

Yazeed shima lambar Saheebar ya k'arba dan itama kunya ya hana ta saki jiki suyi hira

Tunda ga lokacin soyayya mai zafi ya shiga tsakanin wannan masoya kowace kullum tana mak'ale da waya a kunne idan kuwa basa waya to suna musayar messages

Suhaima itama tuni ta fara kula wani Saurayinta Khaleed da bata bashi fuska ada itama ta shiga sahun su Samha

A cikin kankanin lokaci manya suka shiga maganar kafin kace me ankawo kud'in Aure da sa rana lokaci guda aka sa ranarsu Suhaima nan da wata uku masu zuwa Wanda yayi dai dai da gama exams d'in Samha

Akram da Samha kamar su had'iye juna sabida so duk da a filli idan yazo bata wani nuna mishi so sabida kunyar shi da take ji amma idan a waya ne ko a chatt tayi ta nuna mishi irin San da take mishi

Watarana yazo zance shi da Yazeed yana tayiwa Samha hirar bikinsu da yanda zai kasance Samha kuwa murmushi kawai take mishi bata cewa komai aranar kasancewar bak'in kaya ne ajikinsa haka kawai bak'in Daren da suka zo gidansu da Alhaji Bala ya fad'o mata Wanda hakan ya d'an sa gabanta fad'uwa tare da kura mishi ido

Akram tsayar da maganar da yake yi yayi dayaga yanda ta kura ya mishi ido ya kirata da Sunan da yake kiranta dashi yace "Soulmate lafiya kuwa kike kallona haka"?

Samha kuwa take hawaye suka hau tsare a kumatunta data tuna Hajiya Nafeesa da jajircewar da tayi dan kar a keta musu haddi

Kau da kanta tayi daga kallonsa ta cigaba da zubar hawaye

Hankalin Akram kuwa idan yayi dubu ya tashi a gigice ya hau tambayarta abinda ya faru

Samha kuwa ta k'asa magana sai hawaye dan kamar a faifai take hango duk abinda ya faru a ranar take wani mugun tsanar Alhaji Bala ya k'ara darsuwa a ranta

D'aga idanuwanta da suka rine suka koma tamkar garwashi tayi ta zubawa Akram da jikinsa ya fara rawa yana tunanin abinda ya sata kuka

Murya a dak'ushe tace "Akram Mummy na tuna Kissar gillar da Alhaji Bala yayi wa mahaifiyata a wannan Bak'in Daren na tuna da ace Mahaifiyata na Rayye babu Wanda zai kai ta farincikin Aurenmu bata da burin daya wuce taga ranar da Autarta zatayi Aure sai gashi yanzu bata rayye zanyi Aure Akram na tsani Alhaji Bala da ace zan samu bindiga babu abinda zai hana ni harbeshi na k'ona shi a wuta na tsane shi Akram na tsane shi wlh"

Ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka

Akram da shima hawaye suka fara k'ok'arin zubo mishi sabida tsanin tausayin Samha murya na rawa ya durk'usa a gabanta ya Ciro handkerchief daga aljihunsa yace "Soulmate I know how you feel wlh har gobe idan na tuna ta ina zubar da hawaye Samun irin Mummynku a ayanzu sai an tona tunda Alhaji Bala ya kashe mummynku ya rasa kwanciyar hankali tun ba'aje ko'ina ba Allah ya saka muku zaluncin da ya muku Soul mate ko da baki harbeshi ba halin da yake ciki kawai yanzu ya ishe shi dan har rok'o yake a harbeshi dan yanzu shi ba mutum ba haka zalika shi ba Dabba ba shi ba rayayye ba shi ba matacce ba Soul mate addu'a kawai zamu ringa bin mommy dashi dan nasha mafarki da ita tana ce min na kula daku and I promise insha Allah zan zame muku tamkar yaya pls stop crying ki daina zubar min da wannan hawayen naki mai tsada"

Akram yace yana share mata hawaye da handkerchief d'in hannunsa mai kamshi

Samha janye fuskarta tayi tace "I want to see him Akram inaso naga Alhaji Bala da idanuna inaso naga halin da yake ciki ganinsa ne kawai zai kwantar min da hankali in daina jin rad'ad'in danake ji a zuciyata"

Murmushi Akram yayi yace "Anything for you my princess your wish is my command"

Samha murmushi itama ta sakar mishi Akram ya koma ya zauna yafara janta da hira sai data fara kyalkyale dariya hankalinsa ya kwanta

As promise bayan kwana biyu Akram yaje gidansu Samha Dan ya kaisu su gano Alhaji Bala dan su Suhaima ma sun dage sai sunje sun gano shi su Saiam da Safna ma ba a barsu a baya ba dan burinsu suma suga yanda Alhaji Bala ya koma su cigaba da la'antar shi

Har suka je inda aka ajiye Alhaji Balan dake kwance jikinsa na fitar tsutsosi basu gane shi ba sai toshe hanci suke suna waige waige dan su gano inda Alhaji Bala yake

Akram murmushi yayi dan yasan bama su San mutum bane a kwance Samha juyowa tayi tace "wai yana ina ne"?

Murmushi Akram ya k'ara yi yace " Gashi nan a kwance a gabanku"

Direction d'in hannunsa suka bi da kallo idonsu ya sauka akan Alhaji Bala da babu ko fata a jikinsa sai kasusuwa da tsutsosi dake fita a jikinsa in badan yana numfashi ba tunani zakayi wani dabbar ne Rabin fuskarsa a kwailiye

A razane suka ja da baya suna gwallo ido suka kurawa Alhaji Bala ido

Saiam ce tayi k'arfin halin magana cikin inina tace "kana so kace mana wannan abun dake kwance Alhaji Bala ne"?
Chapter 29 · 0% Book details