← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 31

Sashe 6

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukansu ne ya d'auke gabad'aya a lokacin da Saiam ta aza d'aya hannun ta abakin ta alamar suyi shiru ssshshhssh tace cikin whisper kamar bata San aji mai take cewa "kuyi shiru karku tashi mummy daga bacci bacci take yi ba mutuwa tayi ba uban waye yace mummy ta mutu to duk Wanda yake wa mummy fatan mutuwa shi zai mutu ba mummy ba dan haka Ku matsa karku tasheta
Mummy ai baki mutu ba ko? ni nasan bacci kike yi ba gobe kika ce zamuje gidan Aunty khadija ba Ni nasan bazaki mutu ba lah mummy kinga wai kuka suke kin mutu"

Wani mugun ihu Safna ta fasa tana tashiga uku ta lalace Aunty Saiam ta haukace su Sahiba kuwa jikinsu ya d'auki rawa suka zubawa Saiam ido dake kwantar da gashin Hajiya Nafeesa

'Yan sandan kuwa hankalinsu ne ya tashi suka hau yimata video still lokacin tana surutu ita kad'ai Samha kuwa zub'ewa tayi ak'asa Dan k'ok'awa take da numfashinta

Ahankali aka fara rarrashin Saiam data k'ara rungume kan Hajiya Nafeesa kamar wacce za'a k'wace ta sai surutu take ita kadai tana yiwa Hajiya Nafeesa rad'a a kunne ganin bama tasan suna yi ba yasa suka fara k'ok'arin b'anb'are hannun Saiam daga kan Hajiya Nafeesa data rungume

Wani mugun ihu ta ringa yi tana kar su tashi mummynta bacci take ba mutuwa tayi ba su rabu da ita kar su tasar mata mummynta..........

I really felt it wlh Allah ka biya mahaifinmu bukatunsu ka ara musu tsawon rai wayanda suka rasa nasu iyayen Allah ka kai haske kabarinsu alfarmar annabi Muhammad Saw

Ina masoyan Sadnaf masu nemanta ido rufe ga contact din Sadnaf nan da Alphabet 0H0CCGCABCE

Karku manta ishashen lokacin danake dashi shine Friday Saturday Sunday sauran ranakun sai ahankali amma bance bazaku jini ba incase idan ban poster ba working days sai kumin uziri
[2:33PM, 4/7/2018] 鈥�+234 806 462 6766鈥�: 馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫

*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝

*A heart touching story*

庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Page 4*

Ihu Saiam ke yi sosai ta kankame kan Hajiya Nafeesa akan kar atasheta bacci take ba mutuwa tayi ba

Dak'yar matan suka banbare hannunta daga kan gawan Hajiya Nafeesa Saiam kuwa ta hau birgima a k'asa gwanin ban tausayi

Matar Alhaji Nazir mak'ocinsu Alhaji Nazifi ce tafara ankara da halin da Samha take ciki dan kirjinta sama yake sosai

Salatin da tayi da k'arfi ne yasa suka juya suka kalli inda Samha ke kwance cikin mawuyacin hali Sahiba hannu ta d'ora aka tana ta shiga ta uku ta lalace

Da sauri 'yan sandan suka umarci matan da a saka Samha a mota itama tana buk'atar taimakon gaggawa

Mata biyune suka kinkimi Samha sukayi waje da ita inda d'aya daga cikin 'yan sandan ya d'auko wani zani daya gani akan k'ofa ya rufe Hajiya Nafeesa

Kafin ya maida hankalinsa kan Safna da Suhaima dake zaune a kusa da gawan Hajiya Nafeesa sai sheshek'a suke suna jiyo muryar Saiam da aka kulle a dressing room tana su bud'e mata ita mummynta bata mutu ba

Da k'yar Suhaima ta iya basu labarin duk abinda yafaru d'aya d'an sandan yana recording d'ayan kuma yana rubuta statement d'in bayanan ta

K'arfe takwas dai-dai yan uwa da abokanan arziki suka ringa tururuwa cikin gidan suna koke koke familyn Hajiya Nafeesa gabad'aya sai da suka zo ciki kuwa har da mahaifinta da mahaifiyarta

Suna shigowa su Suhaima suka fashe da mugun kuka Safna ta mik'e da gudu taje ta rungume hajiyar su Nafeesa Dan tamkar an tsaga k'ara sabida kamaninsu da Hajiya Nafeesa banbanci kawai ita hajiyar su Nafeesa ta tsufa

Agaban gawan Hajiya Nafeesa ta tsugunna ahankali ta yaye zanin da aka rufe mata fuska dashi

Runtse idonta tayi da k'arfi data ga yanda jini ya wanke fuskarta

Fuskarta ta kumbura tayi suntum

Girgiza kai kawai take hawaye na gudu a fuskarta ahankali ta maida Zanin ta rufe

Ta fara magana cikin wani irin yanayi tana "Nafeesa bazan tab'a yafe wa Wanda ya kasheki ba amatsayina na mahaifiyarki zanta addu'a Allah ya tarwatsa rayuwar Wanda ya kashe ki shi da kwanciyar hankali a duniya sai dai alahira"

Kuka take sosai Wanda yasa duk wayanda ke palon kuka

Mahaifin Hajiya Nafeesa kuwa yana daga nesa ya kurawa Gawan Hajiya Nafeesa ido jikinsa sai rawa yake yana tuno shekaranjiya da ta zo gida tana ta abubuwa haka kamar na bankwana sau uku ta na fita ta dawo idan suka tambayeta mai ta dawo yi sai tayi murmushi tace ta dawo ne tayi musu Sallama Ashe sallamar k'arshe take musu Ashe tafiyar da ba'a dawowa zatayi

Alhaji Mamman fashewa yayi da kuka yana "Ya Allah ka tonawa wadanan azzuluman asiri Allah ka hanasu zaman lafiya a gidan duniya Allah ka wulak'antasu Allah ka dai-daitasu"

Kuka Alhaji mamman keyi sosai

Ahankali mazan suka fara mik'ewa suna Barin palon dan za'ayiwa Hajiya Nafeesa wanka a suturceta akai ta gidanta na gaskiya

Ciki kuwa Saiam gajiya tayi da buga k'ofar ta sulale k'asa tana "Mummy ki tashi kice baki mutu ba baccine ya d'aukeki"

Ahaka tayi ta sumbatu tana kuka ak'arshe ta koma tana sauke ajiyar zuciya ahankali wani irin bacci ne yayi awon gaba da ita ko minti biyar batayi da bacci ba tayi mafarki yanda take kwance Hajiya Nafeesa ta bud'e k'ofar d'akin ta shigo fuskarta d'auke da wani irin murmushi exactly kayan data sa ne ajikinta har da hular net d'in

Zumbur Saiam ta mik'e tana nunata da hannu tare da cewa "Mummy dama baki mutu ba ni nasan mafarki nake yi ba mutuwa kikayi ba"

Murmushin da Hajiya Nafeesa ke yine ya juye zuwa b'acin rai tafara magana tana

"Haba Saiam Akan me zaki ringa Min kuka alkawarin da kika d'aukar min kenan kada ki sake ki k'ara zubar min da hawaye mutuwa Riga ce a Wuyan kowa idan lokacin tafiyarka yayi babu makawa sai ka tafi Dan haka nima lokacin tafiyata ne yayi addu'arku kawai nake bukata

" Haba Saiam karfa ki manta kece babba ke ya kamata ki ringa kwantar wa da kanenki hankali ki zame musu tamkar uwa Daddynku na cikin wani hali kiringa kwantar masa da hankali ki zama jajirtaciya Dan Allah Saiam idan kun tuna ni kuyimin addu'a kawai karku manta azumin danace Ku rama min"

Saiam da sauri tace "to mummy wai yaushe zaki dawo muna bukatarki mummy"

Wani murmushi Hajiya Nafeesa tayi daya sata masifar kyau da haske tace "Saiam da kunsan inda zanje ayanzu da baki ce na dawo ba da Baku wahalar da kanku kun zubar da hawayenku ba inda zanje yafiye min inda na Bari sau dubu dan haka kucigaba da min addu'a Saiam kina so inyi fushi dake"?

Da sauri Saiam ta girgiza kanta

Hajiya Nafeesa tace " to karki k'ara zubar da hawayenki karki k'ara bari kannenki suyi kuka ko daddynku maza tashi ki tafi d'akinku kije kiyimin addu'a kafin akaini makwancina"

Duk mafarkin da Saiam tayi baifi cikin minti biyu ba da sallati ta mik'e zumbur tana bin ko ina na d'akin da kallo gani take kamar ma ido biyu Hajiya Nafeesa tazo mata ba mafarki take ba maganganun da Hajiya Nafeesa tayi mata sai amsa kuwaa yake a kunenta

Da sauri ta nufi k'ofar ta fara jijjigawa tana cewa a bud'e mata

Adai-dai lokacin da aka gama yiwa Hajiya Nafeesa sutura aka sata a tsakiyar d'akin

Ganin bugun k'ofar da Saiam take yayi yawa ne yasa

Aka je aka bud'e mata k'ofar da sauri ta fito daga d'akin har tana tuntub'e

Cak ta tsaya ta kurawa makarar dake tsakiyar d'akin ido an lullub'e Hajiya Nafeesa da farin likkafani

Ahankali ta ringa tafiya har sai data k'araso gaban makarar ta tsuguna ahankali wasu siraran hawaye suka zubo mata

Da sauri ta d'auke hawayen da bayan hannunta ta runtse idonta cikin dakewa da karyayar zuciya tafara karanta suratul Rahman cikin wani irin rawar murya mai d'auke da kuka aya goma kawai ta iya karantawa tafara jero addu'oi tana yiwa Hajiya Nafeesa Addu'a 'yan d'akin kuwa sai ameen suke cewa

Ganin maza sun fara shigowa zasu zo su d'auki gawar Hajiya Nafeesa ne yasa hajiyar su Nafeesa zuwa ta janye Saiam

Aikuwa kamar ta zuga su Saiam dasu Safna tuni suka fashe da wani irin kuka suna kallon makarar Hajiya Nafeesa da akayi sama dashi kuka suke sosai suna shikenan mummy ta tafi

Duk inda ka kai da taurin zuciya sai ka zubar da hawaye

Saiam kamar d'aukewar ruwan Sama tayi sauri ta tsayar da kukan da take ta kamo hannun su Safna gabad'aya tafara goge musu hawaye tana "mummy tace kar mu sake mu zubar mata da hawaye idan ba so muke tayi fushi damu ba tace muringa mata addu'a kawai"

Tausayin Saiam ne ya k'ara rufe duk wayanda ke d'akin dan sun d'auka duk zafin mutuwar Hajiya Nafeesa yasa Saiam ta fita hayyacinta bata San mai take cewa ba

Fad'ar mutanen da suka sallaci gawan Hajiya Nafeesa b'ata bakine dan sai da aka kashe hanyar da motoci suke wucewa dan inda makabartar yake da dan tazara sosai daga gidansu Hajiya Nafeesa ahaka aka kai Hajiya Nafeesa dubanin mutane na yabon hallayenta na gari banda kananan yara da har dasu aka je binneta suna ta kuka Hajiya mai raba musu alewa duk ranar juma'a ta mutu

Idan ka kalli yanda su Saiam suke zaune waje d'aya suna Jan carbi hawaye da majina na zubo musu lokacin da zaka fara hawaye ba sani zakayi ba

Bama sa iya amsa gaisuwar da ake musu ciki kuwa har da saurayin Saiam da Safna da zasu Aura suna ganin halin da su Saiam suke ciki sai gashi hawaye ya hau zubo musu sabida adaren da Hajiya Nafeesa zata rasu da suka zo zance suka je suka gaisheta haka kawai ta hau yi musu wa'azi da nasiha tana kan kujera sanye da hijabi da fararen hakoran maccanta sai murmushi take she is very social and civilized dan har ga Allah har suka je gida suna yabon halayenta ashe mutuwa na nan tafe

Saiam cikin dakushashiyar muryarta ta kalli Suhaima tana tambayarta inda Samha take da Daddy dan duk abinda akayi basani tayi ba
Chapter 6 · 0% Book details