← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 31

Sashe 26

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru su Akram sukayi suna Sauraren Alhaji Nazifi dake cewa Akram ya hakura da Samha ya zabi a cikin Suhaima da Saheeba tunda Samha tak'i ta aminta dashi yasan Suhaima da Saheeba bazasu bashi Matsala ba sun d'an fi Samha saukin Kai duk da itama Samhar ba fin k'arfinsa tayi ba zai iya tilasta mata amma baya so ya tilasta mata d'in dan yiwa yaro Aure dole baya cikin tsarinsa baya kuma so ya takura mata dan yarinya ce sosai kuma shi har ga Allah yana so ya had'a zuria dashi sabida nagartattun halayenshi dafatan zai amshi tayinsa ya zabi Suhaima ko Saheeba tunda duk d'aya suke da Samha

Tunda ya fara magana Akram ya jike da Gumi yaji kamar guduma yake kwad'a mishi dan San da yake yiwa Samha bayajin zai iya hakura da ita sai dai idan Aure aka d'aura mata da wani batun su Suhiama kuwa bai ma San kamaninsu ba ballantana har d'aya daga cikinsu ta kwanta mishi aransa gashi yana jin nauyin Alhaji Nazifi baya jin zai iya duba tsabar idonsa ya watsa mishi k'asa a ido

Yazeed shima tuni hankalinsa ya tashi daya ji abinda Alhaji Nazifi yace dan ya kamu da San Saheeba yana tsoron Akram yace Saheeba yakeso

Alhaji Nazifi kuwa kamar yasan tunanin da Akram yake yace mishi kar ya damu yaje yayi tunani bazai mishi dole ba idan dai babu wacce ta mishi a cikinsu kar yaji nauyinsa ya fad'a mishi

Wani d'an ajiyar zuciya Akram ya saki dayaji abinda yace dan hanya kawai yake nema da zai zille

Godiya ya hau yiwa Alhaji Nazifi

Alhaji Nazifi yayi murmushi yace ba komai su tsaya suci abinci sai su tafi

A tare suka mik'e suna ce mishi sun koshi sun gode

Babu yanda Alhaji bai yi da su ba akan su tsaya a kawo musu abinci dan so yake yayi amfani da wanan damar yasa su Suhaima su kawo musu abinci daga nan yaga wacce ta kwanta mishi amma fir suka k'i ahaka suka mishi Sallama suka tafi suna mishi godiya.

Suna fita waje Yazeed ya cakumi wuyan rigar Akram yana kar ya sake ya zabi Saheeba dan ita yake so

Akram doke hannunsa yayi ya buga tsaki tare da shigewa cikin mota dan shi ya ma manta kamanin Saheeba ai baya jin ko sarauniyar Indiya za'a mishi tallarta zai so ta kamar yanda yake San Samha

Yazeed ne ya ringa surutansa shi kad'ai yana ya hakura kawai da Samha tunda bata San shi ya zabi d'aya yar uwarta ta kawai tunda yaga alamar dukansu kyawawa ne Akram shi dai bai ce uffan ba har suka isa gida yana tunanin hanyar da zai bi ya shawo kan Samha ta so shi gashi bashida lambar wayarta ballantana ya ringa communicating da ita ko ya samu ta saurare shi

Aranar Akram kwana yayi yana addu'ar Allah ya mallaka mishi Samha amatsayin matar Aurensa indai Alheri ce agare shi idan kuma ba Alheri bace a gare shi Allah ya cire mishi Santa a zuciyarsa

B'angarensu Samha kuwa bayan sallar ishai Suhaima ta zubo musu abinci a faranti suna ci har da Alhaji Nazifi dan tunda Hajiya Nafeesa ta rasu ya maye gurbinta suke cin abinci tare

Alhaji Nazifi kallon Samha yayi dake ta juya cokali tana cakalar abincin haka ta koma shiru shiru tunda Akram yace yana Santa tunani yayi watak'ila sabida K'in da takewa Akram ta koma haka

Murmushi yayi yace "Baby meyesa bakya cin abincin?

Samha d'agowa tayi tana murmushin yak'e tace " Babu komai daddy"

Girgiza kai Alhaji Nazifi yayi still da murmushi a fuskarsa yace "Baby kenan ai nasan meye yake damunki tunda yaron nan yace yana sanki kika bi kika takura kanki kina tunanin zan tilasta miki ki so shi to ki kwantar da hankalinki bazan miki dole ba yau yaron yazo ya sameni nace ya hakura dake zan bashi Suhaima ko Saheeba dan nasan su bazasu k'i shi ba"

Alhaji Nazifi da zai lura da ya hango tsantsar tashin hankalin dake kwance a saman fuskar Samha da ya jiyo irin bugu da tsallen da zuciyarta yake yi kamar ya fad'o k'asa

Alhaji Nazifi kuwa bai lura da halin da take ciki ba ya maida kallonsa kan su Suhaima dake cin abincin su hankalinsu kwance da alama basu damu ma da maganar da Alhaji Nazifi ya fad'a ba hasali ma kowace a cikinsu fata take ace Akram ita ya zab'a dan duk wace ta amsa sunanta mace mai aji da kyau bata da burin da ya wuce ace Akram ya zamo mallakinta

Alhaji Nazifi cewa yayi "Suhaima Saheeba nagayawa Akram ya zabi d'aya a cikinku tunda 'yar uwarku bata San shi kunga kuma babu yanda za'ayi na tilasta mata dafatan duk wacce ya zab'a a cikinku bazata watsa min k'asa a ido ba"

Murmushi kawai sukayi suka sunkuyar da kai alamar dukansu sun amince

Alhaji Nazifi kuwa murmushin jin dadi yayi dan yasan mai murmushinsu ke nufi

Samha kuwa wani irin jiri ta ringa ji yana Neman kayar da ita sabida tashin hankali murmushin data hango kwance a saman fuskar su Suhaima ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba

Babu Wanda ya lura da halin da take ciki har suka kamalla cin abincinsu suka mik'e dan dama idan suna cin abinci itace take tashi a karshe

A daddafe ta mik'e ta kai farantin kitchen ta wuce d'aki tana zuwa ta zube a k'asa wani zazzafan zazzabi ya rufeta atakaice aranar da mugun zazzabi ta kwana da mafarkan Akram

Suhaima da Saheeba ganin Asuba tayi bata tashi dan tayi sallahr asuba ba yasa suka nufi kan gadonta dan su tasheta

Sallati sukayi gabad'aya da suka ga halin da take ciki a rude suka d'agata suna tab'a jikinta dake tururin zafi

atakaice sai da Samha tayi kwana uku a asibiti kafin a sallameta tabi ta rame sabida tunanin Akram haka kawai take jin haushinsu Suhaima

Alhaji Nazifi kuwa sai lallab'ata yake yi shi da su Suhaima abunka da yar Auta

Bayan kwana biyu da aka sallamota daddare wajen k'arfe biyu tana kwance tana tunanin Akram sai juyi take sirarran hawayen nadama na bin kuncinta sai yanzu take data sani k'in amincewa Akram sai yanzu take data sani data d'orawa kanta girman kai tak'i k'arbar soyayyar Akram yanzu gashi Akram ya hakura da ita zai zabi d'aya daga cikin 'ya'yyenta ya Aura

Juyawa tayi ta kalli su Suhaima dake baccinsu peacefully duk abinda take yi Saheeba na kallonta dan juyawa tayi da zumar gyara kwanciyarta ta hango samha na Jan majina tana sharar k'walla mamaki ne ya rufeta tayi kamar bacci take yi

Samha kuwa durowa tayi daga kan gadon ta nufi Palo dan ta sha kukanta ta gode Allah

Tana ficewa Saheeba tayi sadaf sadaf tabi bayanta

A 3 seater Samha ta kwanta ta bud'e wayarta ta shiga Zgallery ta bud'o hotunan Akram tana kallo tana shafa kan wayarta hawaye sai zubowa suke a idonta

Saheeba dake jikin labule ta d'an bud'e dan ta ringa hango abinda Samha ke yi mamakine ya k'ara rufeta data hango tana kuka tana shafa hotunan Akram

Samha kuwa magana ta fara yi ahankali Saheeba ta k'asa kunnenta dan ta jiyo ta

"Ina San ka Akram ina Kaunarka Girman kai da taurin zuciya zai sa na rasa ka bansan yanda zanyi rayuwa babu kai ba ina kunyar na koma wajen Daddy ince inasanka yanzu ya zanyi Akram"?

Kuka take sosai har da sheshek'a

Saheeba kuwa ahankali tayi baya ta koma d'akinsu jikinta a sanyaye bata tsaya b'ata lokaci ba ta tashi Suhaima ta rik'e hannyenta sukayi wajen palon suka kuma lab'ewa

Samha kuwa surutanta take ita kad'ai tana shafa screen d'in wayarta sai da suka ji duk abinda take cewa a k'arshe ta rungume wayarta a kirjinta tana sauke ajiyar zuciya

Suhaima tsaki tayi lokacin da suka koma ciki tacewa Saheeba "Kece fa baki sani ba wlh na dade da sanin tana San sa tsabar munafirce da taurin zuciya yasa ta Dage bata San shi aikuwa sai na wanata na wajigata zan gayawa Daddy gaskiyar tana San shi ni gobe ma hirarsa zan tayi zance ina sansa sai zuciyarta ta kusa bindiga zan kyalleta"

Murmushi Saheeba tayi tace "kai Aunty Suhaima Auta ce fa"

Tsaki Suhaima ta k'arayi tace "Autar fa dalla jekiyi kwanciyarki Ashe shiyasa ta ringa ma rashin lafiya takaicina ma Daddy yaringa lallab'ata akan ta so Akram Ashe ta dade tana sansa"

Takun da suka jiyo ne ya sa suka hau gadonsu da sauri suka rufe ido kamar masu bacci

Samha kuwa sai da ta lelek'a fuskarsu taga bacci suke ta hau kan gadonta ta kwanta ta na sauke ajiyar zuciya sabida kukan da tayi........
[8:15PM, 4/22/2018] ‪+234 813 272 6929‬: 🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑

*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅

*A heart touching story*

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Follow me on Wattpad@Sadnaf*

*Page 20*
*FINALE*

B'angaren Akram kuwa yana ta tunanin yanda zai fuskanci Alhaji Nazifi yace mishi babu wacce tayi mishi a cikinsu so d'aya tak Samha yake yiwa Yazeed babu yanda bai yi dashi ba akan ya hakura da Samha yace Sam idan ba Aure ko mutuwa tayi ba babu abinda zai sa ya hakura da ita dan duk addu'oi da istahara da yake yi akan Allah ya mishi zabin da yafi Alheri Samha yake gani a matsayin matarsa kuma yana ji a jikinsa Samha matarsa ce ahaka dai ya d'aure akan zaije ya samu Alhaji Nazifi ya gaya mishi halin da yake ciki Dan kar yaji shi shiru

B'angaren su Samha kuwa washegari Alhaji Nazifi na fita Suhaima ta hau tambayar Samhar da ta tasa breakfast d'inta agaba ta kasa ci sabida tunanin Akram akan me yake damunta haka take tunani kwana biyu bata gane mata

Samha d'aurewa tayi ta saisaita kanta Dan kar su d'agota tace musu babu komai kawai Mummy ce ta fad'o mata abunka da Wanda yake jiran kiris take hawaye ya hau zubo mata

Saheeba ta guntsa dariyar da ta taho mata dan tasan karya Samha take yi San Akram ke dawainiya da ita
Chapter 26 · 0% Book details