← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 31

Sashe 22

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Lion ajiye bindigogin hannunsu sukayi amadadin su bi umarninsa

Alhaji Bala ya saki baki yana kallonsu cikin tsananin mamaki Akram kuwa ya saki murmushi yana girgiza kai

A tsawace Alhaji Bala yace "kanku d'aya kuwa ko Baku ji mai nace ba shoot this fool before counting of 2"

Lion a hankali ya girgiza kansa yana "oga bazamu iya ba"

Alhaji Bala jikinsa ne ya fara rawa for the first time yaji gabansa ya fad'i

Shammatar Akram yayi ya d'auki bindigarsa da ya ajiye a k'asa.

A tare sukayi pointing juna da bindigar

Alhaji Bala kyalkyalewa yayi da dariya yace "Akram you are such a big fool wlh babu abinda zai hana yau na kasheka Sai a yau nake dana sani Dana taimake ka Mai gida ya yaudareni da ya bari na jawo ka jikina tayaya mutane zasu San abunda nake aikatawa tayaya dubuna ya cika Do u have any prove against me no u don't have now drop your gun or I else"

"Or else what Alhaji Bala wat can you do"? Yaji an fad'i daga bakin k'ofa

Da sauri ya waiga Dan yaga Wanda yake magana

Abdullahi ne ya shigo 'yan sanda suna take mishi baya tare da pointing d'inshi da bindiga

Alhaji Bala Ido ya waro sosai a lokacin da 'yan sanda suka zagaye shi 'yan jarida da video coverage suma suka hau haska su da cemarorinsu

Bindigar Hannun Alhaji Bala subucewa yayi daga hannunsa cikin tashin hankali yafara binsu da kallo d'aya bayan d'aya jikinsa na rawa

Akram kuwa ya k'ara sakin murmushi yace " yadai oga y are u speechless da ka gansu I thought ai zaka bud'e musu wuta ne da suka shigo"

Juyawa yayi ya kalli masu video coverage da hotuna yace "Ku d'an Matso kad'an kuga Wanda ke mana wannan aika aika kuga Wanda ke farautar dukiyoyin jama'a da yiwa yaran mutane fyad'e"

Da sauri suka matsa kusa da Akram Dan burin kowa yaga shi ya fara d'aukan wanan mugun Dan fashi da ya addabi jama'a

Alhaji Bala jikinsa in banda rawa babu abinda yake yi gani yake kamar mafarki yake yi wai shi yau 'yan sanda suka zagaye da 'yan jaridu

Akram kuwa a hankali ya matsa kusa da Alhaji Bala 'yan sanda kuwa suka k'ara saita shi da bindigoginsu in case in zai yi gardama

Akram da murmushi ya kai hannunsa fuskar Alhaji Bala dan ya Ciro mask d'in fuskarsa

Alhaji Bala yayi sauri ya rik'e mishi hannu yana "Akram Dan Allah karka min haka ka rufa min asiri kar ka kunyatani"

Wani irin murmushi Akram yayi ta gefen baki yace "kunya kuma Alhaji Bala kunya fa kace ai babu batun kuma jin kunya a yau babu batun rufin asiri ayau a yanzu zan cire wanan Mask d'in fuskar taka kowa yasan kai waye"

Alhaji Ghali da sauri yaje ya tsaya a gefensu Akram dan ya matsu yaga waye

Alhaji Bala runtse idonsa yayi da k'arfi jikinsa na masifar rawa a lokacin da Akram yafara k'ok'arin cire Mask d'in fuskarsa

"Alhaji Balaaaaaaaaaaaa" Alhaji Ghali yace cikin shock tare da nuna shi da hannu

Wayanda kuwa basu San Alhaji Bala ke wannan ta'asar ba suma jikinsu ya hau rawa suka k'ura mishi ido har da masu k'ara Murza idonsu dan su tabbatar da shine ko ba shi bane.

Alhaji Bala kuwa runtse idonsa yayi gam yak'i ya bud'e idonsa dan flash d'in camerori ke haska shi ko ta ina

D'aya daga cikin 'yan sandan ne ya matsa kusa dashi ya kamo hannayensa ya saka mishi ankwa

Alhaji Bala da sauri ya bud'e idonsa sakamakon wani mahaukacin dariya dayaji a gefensa

Na Maliya ya hango akan ruwa sai yawo yake asaman ruwa yana kyakyata dariya

Alhaji Bala kuwa hawaye ya hau zubo mishi a idonsa

Na Maliya yace "Alhaji Bala mai akayi da maza ai baka ga komai ba tukuna sai na taso maka wayanda zasu na d'ebe maka kewa a kurkuku sai ka rok'i mutuwa ta d'auke ka da rayuwar tashin hankalin da zaka ringa yi"

Wani Mahaukacin dariyar ya kara kecewa dashi ya b'ace

Alhaji Bala hawaye kawai yake a lokacin da 'yan sanda biyu suka fara tura keyarsa suna nufar waje dashi

Su Lion ma tuni aka saka musu ankwa a hannu akayi waje dasu

Alhaji Ghali dake daskare awaje d'aya dan tsabar mamaki binsu yayi da sauri wani d'an sanda ya dakatar dashi akan kar ya bisu

Masu hotuna da video coverage sai turereniya suke wajen d'aukan Alhaji Bala har aka sa su a Black Mariya suka fara tafiya babu abinda kake ji sai jiniya

Masu video coverage da hotuna tuni suka koma kan Akram dake Rik'e da Mask d'in Alhaji Bala suka fara d'aukansa 'yan jarida kuwa suka fara jera mishi tambayoyi

Akram kuwa dak'yar ya ratsa su ya shige cikin mota sai hamdala yake a zuciyarsa da Allah ya cika mishi burinsa na damke Alhaji Bala

Sai da suka koma cikin gidan Alhaji Bala dake Cikin daji suka d'auko Killer dake huge buge yana zabga ihu shi kad'ai dan Yanzu kuma ba iya Hajiya Nafeesa yake gani ba har da wasu da ya kashe da hannunsa ahaka aka kwashe shi aka sa a mota suka nufi headquarters d'insu da ake ajiye manya manya masu laifuka

Alhaji Bala kuwa kansa a sunkuye sai addu'a yake Allah yasa Mafarki yake bayajin zai iya jurewa idan mutane suka gano shine yake aikata wannan ta'asa da wane ido zai kalli mutanen garinsu da wane ido zai kalli Mahaifiyarsa da kannensa da wane ido zai kalli mutanen da yake taimakawa a matsayinsa na mutumin kirki mai tausayin Talakawa lallai Akram ya shamace shi daya san cewa Akram dan bincike ne da ya Dade da kashe shi

Kafin kace me labarin Alhaji Bala shahararren mai kudi mai taimakawa talakawa ya karad'e gari da jihohi gabad'aya akan shine shahararren d'an fashi da makami mai farautar dukiyoyin jama'a da yiwa yara fyad'e duk gidan radio ko television daka kuna labaran kawai ake yi hotonsa aka had'a da Wanda yasaka mask da ainihin hotonsa da mutane suka San shi dashi Alhaji Bala

Jama'a gari kuwa sai mamaki suke manyan masu kud'i da suka San shi ta hanyar taimako suka hau bugawa junansu waya wasu ma basu yarda ba sai da suka ringa bugawa shugaban 'yan sanda waya dan su tabbatar da abinda suke ji wayanda kuwa sukayi falling Victim kuwa tuni suka hau sujadda suna godewa Allah wasu kuwa suka ringa shirin zuwa ganin shi

Akram kuwa kansa ya d'au zafi 'yan jarida sun cika bakin office d'in shi suna jiran ya fito ya musu Karin bayani akan yanda yayi nassarar cafe Alhaji Bala da yanda akayi ya gano Alhaji Bala dan fashine

Sai da Akram yayi wanka ya shirya a toilet d'insa dake cikin office d'insa ya d'aura alwala yazo ya ringa jera nafilfili na godiya da Allah daya bashi nassara akan Alhaji Bala bai samu fitowa ya saurari 'yan jaridar ba sai wajen 10am na safe

Farin suit ne a jikinsa da bak'in nectie yayi masifar kyau ai yana fitowa camera ta hau haska shi 'yan jarida sukayi dafifi suka hau yi mishi tambayoyi har suna turereniya

Akram kuwa sai da ya gyara tsayuwarsa yayi godiya ga Allah tare da addu'a kafin ya fara magana cikin had'adden turancinsa inda gidan talabijin na AIT suke haskawa live tare da raba screen d'in gida biyu Akram a d'aya b'angaren yana kwarara jawabi d'aya b'angaren kuma hoton Alhaji Bala ne dan fashi da hoton Alhaji Bala da mutane suka sani a matsayin mai taimakon Talakawa

A dai-dai lokacin iyalan Alhaji Nazifi na zaune a palon gidan suna karyawa Samha mayar kallon Indian series tana aikin nata na kallo ganin sun tafi talla ne yasa ta fara k'ok'arin canza tasha inda kuwa ta kamo tashar AIT adai dai lokacin da aka hasko Akram yana kwarara bayani agefe ga hoton Alhaji Bala mik'ewa sukayi gabad'aya dan bazasu tab'a manta fuskar Alhaji Bala ba

K'ofin shayin dake hannun Samha ya subuce daga hannunta ya fad'i k'asa gabanta na mugun fad'uwa kurawa Akram ido kawai tayi

Adai dai lokacin da Saiam itama take kallon labaran ta latso lambar Alhaji Nazifi dan tace su kamo tashar AIT

Wayar na ringing amma Alhaji Nazifi ya k'asa d'agawa dan mutuwar zaunen da yayi.... ...

🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑

*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅

*A heart touching story*

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Follow me on Wattpad@Sadnaf*

*Page 16*

Saheeba ce tayi k'arfin halin d'aga wayarta dan dukansu sun k'asa d'aga wayar TV kawai suka kurawa ido ko kifta idonsu basa yi

Cikin rawar Murya Saiam ta hau cewa su kunna TV su ga Tsinanne nan da ya kashe musu mommynsu dubunsa ta cika Allah ya tona mishi asiri

Saheeba ce mata tayi yanzu haka shi suke kallo bata Kara tsayawa taji mai Zata ce ba ta kashe wayar

Alhaji Nazifi kuwa ba ganin Alhaji Bala d'an fashine ya girgiza shi ba ganin Alhaji Bala mai taimakon talakawa da suke hirar shi shekaranjiya akan irin ayyukan alherin da yake yiwa Mara sa shi har suna cewa da za'a samu irin shi guda Ashirin da talakawa sun daina k'ok'awa har addu'oi suka runga mishi sai gashi wai Ashe shine wannan gagarumin d'an fashin Da ya addabi manyan masu kud'i

Samha kuwa tana nan a tsaye kamar an dasata waje d'aya Akram kawai ta zubawa ido dake kwarara bayani wani irin strange feelings da bata tab'a ji ba taji yana zagaye kowane sassa na jikinta

Suhaima ce tayi k'arfin halin magana tace "Allah mai Iko yanzu wanan Alhaji Balan mai taimakon talakawa dama shine tsinanne Dan fashin nan daya zo ya kashe mommy"
Chapter 22 · 0% Book details