← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 31

Sashe 28

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samha kuwa ta k'asa magana sai hawaye dan kamar a faifai take hango duk abinda ya faru a ranar take wani mugun tsanar Alhaji Bala ya k'ara darsuwa a ranta

D'aga idanuwanta da suka rine suka koma tamkar garwashi tayi ta zubawa Akram da jikinsa ya fara rawa yana tunanin abinda ya sata kuka

Murya a dak'ushe tace "Akram Mummy na tuna Kissar gillar da Alhaji Bala yayi wa mahaifiyata a wannan Bak'in Daren na tuna da ace Mahaifiyata na Rayye babu Wanda zai kai ta farincikin Aurenmu bata da burin daya wuce taga ranar da Autarta zatayi Aure sai gashi yanzu bata rayye zanyi Aure Akram na tsani Alhaji Bala da ace zan samu bindiga babu abinda zai hana ni harbeshi na k'ona shi a wuta na tsane shi Akram na tsane shi wlh"

Ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka

Akram da shima hawaye suka fara k'ok'arin zubo mishi sabida tsanin tausayin Samha murya na rawa ya durk'usa a gabanta ya Ciro handkerchief daga aljihunsa yace "Soulmate I know how you feel wlh har gobe idan na tuna ta ina zubar da hawaye Samun irin Mummynku a ayanzu sai an tona tunda Alhaji Bala ya kashe mummynku ya rasa kwanciyar hankali tun ba'aje ko'ina ba Allah ya saka muku zaluncin da ya muku Soul mate ko da baki harbeshi ba halin da yake ciki kawai yanzu ya ishe shi dan har rok'o yake a harbeshi dan yanzu shi ba mutum ba haka zalika shi ba Dabba ba shi ba rayayye ba shi ba matacce ba Soul mate addu'a kawai zamu ringa bin mommy dashi dan nasha mafarki da ita tana ce min na kula daku and I promise insha Allah zan zame muku tamkar yaya pls stop crying ki daina zubar min da wannan hawayen naki mai tsada"

Akram yace yana share mata hawaye da handkerchief d'in hannunsa mai kamshi

Samha janye fuskarta tayi tace "I want to see him Akram inaso naga Alhaji Bala da idanuna inaso naga halin da yake ciki ganinsa ne kawai zai kwantar min da hankali in daina jin rad'ad'in danake ji a zuciyata"

Murmushi Akram yayi yace "Anything for you my princess your wish is my command"

Samha murmushi itama ta sakar mishi Akram ya koma ya zauna yafara janta da hira sai data fara kyalkyale dariya hankalinsa ya kwanta

As promise Akram yazo bayan kwana dan ya kaisu Samha su gano Alhaji Bala dan su Suhaima ma sun dage sai sunje sun gano shi su Saiam da Safna ma ba a barsu a baya ba dan burinsu suma suga yanda Alhaji Bala ya koma su cigaba da la'antar shi

Har suka je inda aka ajiye Alhaji Balan dake kwance jikinsa na fitar tsutsosi basu gane shi ba sai toshe hanci suke suna waige waige dan su gano inda Alhaji Bala yake

Akram murmushi yayi dan yasan bama su San mutum bane a kwance Samha juyowa tayi tace "wai yana ina ne"?

Murmushi Akram ya k'ara yi yace " Gashi nan a kwance a gabanku"

Direction d'in hannunsa suka bi da kallo idonsu ya sauka akan Alhaji Bala da babu ko fata a jikinsa sai kasusuwa da tsutsosi dake fita a jikinsa in badan yana numfashi ba tunani zakayi wani dabbar ne Rabin fuskarsa a kwailiye

A razane suka ja da baya suna gwallo ido suka kurawa Alhaji Bala ido

Saiam ce tayi k'arfin halin magana cikin inina tace "kana so kace mana wannan abun dake kwance Alhaji Bala ne"?

Akram girgiza mata kai yayi yace " kwarai shine ya koma haka bamu San mai yake damunsa ba zakiga yana ta ihu yana cizge fatar jikinsa yana fad'ar abubuwan da ya aikata yana ya tuba ya daina kullum sai ya rok'i a harbeshi ya mutu akan azabar da yake ciki"

Girgiza Kansu kawai suke yi suna mamakin halin da suka ganshi a ciki dan ko iya manya manya tsutsosin dake crawling a jikinsa ya ishe shi azaba

Samha na k'ok'arin magana Na Maliya ya bayyana yana kyalkyale dariya babu Wanda yake ganinsa sai Alhaji Bala

Alhaji Bala da muryarsa bata fita yana daga kwance ya fara ihu yana Na Maliya ya kashe shi ya huta

Aikuwa na Maliya na watsa mishi ruwan kaikayi ya mik'e da skeleton d'in jikinsa ya fara cizge Sauran fatar dake jikinsa yana ihu har Dana fuskarsa

A tsorace su Suhaima suka ja da baya suna kallon ikon Allah Alhaji Bala kuwa sai cizge cizge yake yi

Yafi k'arfin minti Ashirin ahaka kafin ya zub'e a k'asa yana kuka yana rok'on mutuwa tazo ta d'aukeshi

Girgiza kai su Samha kawai suke suna Al ajabin halin da suka ga Alhaji Bala a ciki Saiam kuwa cewa take lallai Allah ba azzalumin bawa bane tun a gidan duniya yake Hisabi ko ahaka aka bar Alhaji Bala ya girbi abinda ya shuka

Ahaka Akram ya maidasu gida suna Al ajabin halin da suka ga Alhaji Bala

Dangin Alhaji Nazifi kuwa ganin suna tayiwa Alhaji Bala zancen Aure yak'i basu had'in kai ne yasa suka sa ranar da za'a d'aurawa su Suhaima Aure shima zasu d'aura mishi da Nazifa Cousin d'insa🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑

*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅

*A heart touching story*

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Follow me on Wattpad@Sadnaf*

*Page 20*
*FINALE*

B'angaren Akram kuwa yana ta tunanin yanda zai fuskanci Alhaji Nazifi yace mishi babu wacce tayi mishi a cikinsu so d'aya tak Samha yake yiwa Yazeed babu yanda bai yi dashi ba akan ya hakura da Samha yace Sam idan ba Aure ko mutuwa tayi ba babu abinda zai sa ya hakura da ita dan duk addu'oi da istahara da yake yi akan Allah ya mishi zabin da yafi Alheri Samha yake gani a matsayin matarsa kuma yana ji a jikinsa Samha matarsa ce ahaka dai ya d'aure akan zaije ya samu Alhaji Nazifi ya gaya mishi halin da yake ciki Dan kar yaji shi shiru

B'angaren su Samha kuwa washegari Alhaji Nazifi na fita Suhaima ta hau tambayar Samhar da ta tasa breakfast d'inta agaba ta kasa ci sabida tunanin Akram akan me yake damunta haka take tunani kwana biyu bata gane mata

Samha d'aurewa tayi ta saisaita kanta Dan kar su d'agota tace musu babu komai kawai Mummy ce ta fad'o mata abunka da Wanda yake jiran kiris take hawaye ya hau zubo mata

Saheeba ta guntsa dariyar da ta taho mata dan tasan karya Samha take yi San Akram ke dawainiya da ita

Suhaima kuwa tab'e baki tayi tace ta dai fad'i gaskiya ba abinda ke damunta ba kenan akwai dai wani Abu da take b'oyewa yake nukurkusarta a zuciyarta

Samha kuka ta fashe dashi tana ita babu abinda take b'oyewa daga haka ta mik'e da gudu tabar palon ta nufi d'akinsu

Suhaima harara ta bita dashi tana ce mata munafika Saheeba kuwa sai Dariya take dan tasan zallar yarinta ke damun Samha

Aranar hawan jini ne kawai basu sawa Samha ba Dan har d'aki suka bita suna hirar Akram kowace na cewa Allah yasa ya zab'eta har suna fad'ar irin San da suke mishi Samha kuwa duk inda ta kai ga San ta d'aure sai da ta fashe da kuka Dan ji tayi gwara su rufeta da duka akan maganganun da Sukeyi su kuwa sai dariya suke aransu

Bayan kwana biyu Akram ya shirya shi da Yazeed suka nufi gidansu Samha Dan ya gayawa Alhaji Nazifi gaskiyar abinda ke ransa daga nan kuma ya shigar da maganar yazeed akan San da yake yiwa Saheeba

Har palon Saukan bak'i aka sauke su Akram dan Alhaji Nazifi yasan da zuwansu sai da ya lek'a d'akinsu Suhaima yace su shirya bak'onsu ya zo duk wacce ya zab'a a cikinsu ta k'arbeshi da hannu bibiyu

Samha da bata da aikin Da ya wuce kwanciya da tunani tabi ta rame tayi zuru zuru sabida tunani wani irin mik'ewa tayi kirjinta kamar ya fad'o k'asa dataji abinda Alhaji Nazifi yace

Su Suhaima kuwa da gangan suka nuna farincikinsu a fili Dan so suke Samha tayi admiting tana San Akram da kanta

Alhaji Nazifi halin da yaga Samha a ciki ne yasa ya zuba mata ido yana "Baby Lafiya kuwa mai ya sameki"?

Samha kuka ta fashe dashi Alhaji Nazifi yayi Sallati yana nufar inda take hannyenta ya ruk'o yana tambayarta abinda yake damunta kamar k'ara zugata yayi ta kara volume d'in kukanta Dan agaskiya bata jin zata iya shiru ta cutu gwara ta gayawa Alhaji Nazifi halin da take ciki

Su Suhaima kuwa ido suka zuba mata suna jiran suji mai zatace

Aikuwa Hakan da ta gani yasa ta sadda kanta k'asa tana tunanin yanda zata fito ta gaya musu halin da take ciki

Alhaji Nazifi kuwa ganin tak'i magana ne yasa ya mik'e ya kalli Suhaima yace tazo ta tambayeta abinda yake damunta zaije wajen su Akram kar ya b'ata musu lokaci

Samha tuni hankalinta ya tashi Dan tasan idan ba fitowa tayi ta ajiye kunya da jin nauyinsu a gefe ba zata kwari kanta Akram yayi mata Nisa

Da Sauri ta tsayar da Alhaji Nazifi dake dab da ficewa daga d'akin tace " Daddy"

Alhaji Nazifi juyowa yayi yana kallonta

Samha kuwa tayi sauri ta sunkuyar dakanta haka kawai kuma taji wani irin kunya da nauyinsa ya rufeta

"Ya akayi Baby"?

A hankali ta d'aga kanta ta kalli su Suhaima da suka kura mata ido tayi sauri ta maida kanta ta sunkuyar gabanta na fad'uwa

Alhaji Nazifi kuwa ganin tana b'ata mishi lokaci yasa yayi tunanin shagwabar ta ne ya motsa tsaki yayi ya juya zai bar d'akin yaji siririn muryar Samha na cewa " Daddy wlh ina Sansa ina kaunarsa"?

A mamakince ya juyo Dan ya gaskata abinda tace yana juyawa yaga ta mik'e dagudu ta shige band'aki ta kulle

Suhaima da Saheeba kuwa dariya suka kyalkyale dashi suna tsokanar Samha akan da ta tsaya girman kai taga ikon Allah

Alhaji Nazifi kuwa maida kallonsa kan su Saheeba yayi Dan su mishi Karin bayani aikuwa suka hau bashi labarin irin San da Samha keyi wa Akram
Chapter 28 · 0% Book details