← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 31

Sashe 24

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Bala kuwa wani wawan ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da suka b'ace take Na Maliya ya bayyana saman kansa yana kyakyata dariya sai yawo yake a saman ruwa babu Wanda ke ganinsa sai Alhaji Bala

Sai da na Maliya yayi dariya mai isarsa yace "Bala kad'an kagani sai na k'ara taso wayanda suka fi wanan yawa wlh sai ka rok'i mutuwa ta d'auke tsabar masifa da azabar da kake ciki"

Alhaji Bala kuka ya fashe dashi yana "Na maliya ka rufamin asiri na tuba wlh iya masifar da nake ciki ma ya isheni"

Dariya Na Maliya ya k'ara kyakyalewa dashi ya b'ace

Duk mutanen dake cikin kotun zubawa Alhaji Bala ido kawai sukayi suna mamakin surutun da yake yi shi kadai

Alhaji Bala bin jikinsa dake masifar rad'ad'i dan azaba ya ringa yi da kallo dan ji yake kamar an hura mishi wuta nan da nan wasu kuraje masu masifar kaikayi suka feso mishi wani razanan ihu ya saka ya fara Sosa ko ina kamar sabon mahaukaci

Tuni mutanen dake kotun suka k'aure da hayaniya suna Alhaji Bala ya haukace tun ba a je ko ina ba

Duk abinda akeyi Akram na daga gefe ya zubawa saurautar Allah ido dan ya d'an girgiza da lamarin Alhaji Bala tunda gashi dai sautukan bulalai kawai suka ringa ji basu ga kowa ba

Dak'yar aka samu mutanen kotun sukayi shiru sabida Alkali dake San magana

Alkali sai da ya gyara zaman glass d'in fuskarsa ya k'ara karewa Alhaji Bala dake Sosa jikinsa a haukace kallo yayi gyaran murya yana tunda Wanda ake case dashi ba'aji ta bakinsa ba sabida halin da yake ciki za'a d'age kara zuwa sati biyu masu zuwa aranar kuma za'a yanke mishi hukuncin daya dace da laifin da ya aikata su kuma su killer tunda sun amsa laifinsu batare da sun wahalar da sharia ba zasuyi life imprisonment with hard labour daga haka Alkali ya buga guduma tare da mik'ewa

'Yan sanda hud'u ne suka rik'e Alhaji Bala sakamakon fifizgewar da yake yana ihu dan tsabar Susa da yakeyi har jini jikinsa ke yi

Ahaka suka jashi sukayi mota dashi yana zunduma ihu

Ahankali mutanen kotun suka fara fitowa data kotun suna mai Al ajabin abunda ke faruwa

Hajiya Lubna kuwa ko ajikinta Dan Sam Alhaji Bala bai bata tausayi ba tunda lokacin daya ke tapka rashin Imaninsa shima babu digon tausayin wayanda yake zalunta aransa

Hajiya Saude Mahaifiya Alhaji Bala kuwa kuka ta ringa rizga hannunta aka dan ita kad'ai tasan irin masifar da take ciki bata jin zata iya komawa kauyensu dan tunda 'yan garinsu sukaji labarin Bala dan fashine sukayi zuga suka tafi gidajen kannensa suka ringa jifansu suna asirin yayansu ya tonu Ashe d'an fashi da makamine

Ita kuwa sai a makota ta b'uya Dan petur suka zazzagawa gidanta suka cinna mishi wuta suna munafika ce ita

tasan irin sana'ar da Alhaji Bala yake yi ita take d'aure mishi gindi

Magana take so tayiwa hajiya Lubna akan ko zata taimaka ta tafi da ita gidansu Dan bata da wurin zuwa Dan ko k'annen Alhaji Bala sun bar garin sabida tsabar tashin hankali amma ga mamakinta wani mugun harara Hajiya Lubna ta watsa mata tare da Jan tsaki tayi shigewarta mota Baki a sake Hajiya
Saude ta bita da kallo har sai data daina hangota

Akram kuwa sai da 'yan jarida suka kara tsayar dashi suna jera mishi tambayoyi dak'yar ya yak'ice ya gudu ya barsu dan ya gaji da wanan tambayoyin da suke mishi dan Sam shi ba gwanin magana bane yanzu nan zaiji kansa na ciwo

Alhaji Bala kuwa tukuru ya zama k'aramin Mahaukaci yana surutai tare da so she soshe cikin k'ank'anin lokaci hallitar jikinsa ya fara sauyawa yana komawa wani irin hallita cisge gashin kansa kawai yake yana buge buge jikinsa sai jini yake yana fad'ar abubuwan da ya aikata Lokaci lokaci Na Maliya ke bayyana ya ringa shek'a mishi dariya yana zuba mishi wani ruwa dake sa ya k'ara haukacewa wajen Sosa jikinsa

Bayan sati d'aya da zaman da akayi a kotu aka k'arawa Akram S Adam mukami ya zama babba banda uban kyaututukan da manyan masu kud'i suka ringa bashi gida ne mota kudi banda uban kyautar da Governor ya mishi har da su hutun wata uku Dan ya zagaya kasashen ketare yaje ya huta Akram kuwa godiya kawai yake yiwa Allah akan d'aukakar da ya mishi dan yasan duk abinda ya samu yin Allah ne ba nashi ba

Duk inda ka zagaya gidajen television gidan jaridu duk wata media hirar Akram s Adam kawai ake yi na irin namijin k'ok'arin da yayi na chapke Gagarumun dan fashi Alhaji Bala

'Yan mata kuwa tuni suka haukace burin kowace ace tazama buduruwar Akram s Adam ga kyau ga kud'i

Samha kuwa bak'on al amarin data tsinci kanta a ciki ne ya sa ta fara rama dan idan dare yayi Sam bata iya bacci Haka kawai take tunani na babu gaira babu dalili babu dama ta hau wani net sai taci karo da hoton Akram da labarinsa ita dai tasan babu Wanda ta tsana sama da shi amma ga mamakinta bata iya bacci sai ta bud'o hotonsa ta kalla bacci kuwa idan ya d'auketa sai tayi mafarkinsa ta kuma rasa Wanda zata samu ta gayawa halin da take ciki

Alhaji Bala kuwa lamarinsa yayi tsamari duk dare sai 'yan sanda sunji saukar bulalai amma sun rasa wayanda ke dukan Alhaji bala

Haka zai kwana yana ihu yana sosa jiki fatar jikinsa duk ta kwaye har wani wari yake yi sabida bayan ya sha bulala Sai Na Maliya ya watsa mishi ruwan da zai ringa cisgo fatar jikinsa

Rok'on 'yan sanda kawai yake akan su harbeshi da wanan azaba da yake ciki

Akram kuwa tunda aka bashi Hutu yafara shirye shiryen zuwa gidansu Samha duk da yasan by now ta riga da tasan ko shi waye amma still wani fargaba da rashin kwarin gwiwa yake ji dan yasan sun Riga da sun tsane shi tunda yana tsaye aka kashe mahaifiyarsu bai ma San ta ina zai fara tunkurar gidansu ba har ya kai shi da sanar da su abinda ke tafe dashi nasan Auren Samha dan ranaku daidayane bai yi mafarki da ita ba tunda yake bai tab'a jin San wata 'ya mace kamar yanda yake San Samha ba

Ahaka Akram ya ringa saka rana rashin kwarin gwiwa da fargaba na hana shi zuwa sai da ya samu sati d'aya ahaka kafin ya iya d'aure yaje tare da Amininsa Yazeed da yaringa karfafa mishi gwiwa.....

Wlh ba Jan aji bane ke hanani typing wlh abubuwa sun sha min kai amma insha Allah am almost there....kucigaba da hakuri Dani wayanda suka sani a da ai sun San ba haka nake yi ba🤨🤨🤨🤨🤨

🌑 🌑 *B🅰K'IN D🅰RE*🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑

*Written by*
💅💅 *Sadnaf*💅💅

*A heart touching story*

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Follow me on Wattpad@Sadnaf*

🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂

*HAPPY BIRTHDAY IN ADVANCE MY BELOVED SON AFFAN U ARE ONE YEAR OLDER TOMORROW INSHA ALLAH*

*I hope you have a wonderful day and that the year ahead is filled with much love, many wonderful surprises and gives you lasting memories that you will cherish in all the days ahead. Happy Birthday*

*On this special day, i wish you all the very best, all the joy you can ever have and may you be blessed abundantly today, tomorrow and the days to come! May you have a fantastic birthday and many more to come... HAPPY BIRTHDAY*

*ALLAH YA ALBARKACI RAYUWARKA YA RAYAMIN KAI YA KAREKA DA KAREWARSA YASA KAZAMO MAI HIDIMANTAWA MUSULUNCI YA SAKA MAKA TSORANSA A DUK INDA KA TSINCI KANKA ALLAH YASA KAYI RAYUWA MAI AMFANI DA HAR BAYAN MUTUWA TA ZA'A RINGA FAD'AR KYAWAWAN HALINKA ALLAH YA NISANCEKA DA DUK WANI ABU NA ASSHA DA ABINDA ZAI SA KA SABA MISHI SHIRIYA TA ALLAH CE INA MAI ROK'ON ALLAH YA SHIRYAMIN KAI BISA TAFARKIN ADDININ MUSULUNCI ALLAH YASA YANDA MAHAIFIYATA TAGA AURENA TA GOYAKA NIMA ALLAH YA ARA MIN TSAWON RAI NAGA AURENKA NA GOYA ABINDA KA HAIFA AMEEN*🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

*Page 18*

K'arfe hud'u na yamma suka isa gidansu Samha gaban Akram sai fad'uwa yake dan bai San wane irin tarb'a Alhaji Nazifi zai masa ba ballantana uwar gayyar Samha Yazeed ne ya ringa k'arfafa mishi gwiwa

Har suka aika mai gadi yayi musu sallama da Alhaji Nazifi gaban Akram bai daina fad'uwa ba

Mai gadin tare suka fito da Alhaji Nazifi Dan yaga Wanda yake Sallama dashi

Ganin Akram ne yasa mamaki ya rufe Alhaji Nazifi sakin murmushi yayi a lokacin da suka zube a k'asa suna gaishe shi Akram kuwa sai sunkuyar da kansa yake

Palon Saukar bak'i Alhaji Nazifi ya kai su yana ta tunanin mai ya kawo su wajensa

K'ara gaishe shi sukayi Alhaji Nazifi ya amsa tare da k'ara jinjina mishi irin k'ok'arin da yayi wajen kama Alhaji Bala ya k'ara da mishi addu'oin nassara a rayuwarsa

Akram shi dai kansa a sunkuye yake yana D'an samun relief na fad'uwar da gabansa yake yi dan yaga alamar Alhaji Nazifi bazai bashi matsala ba

Alhaji Nazifi wayarsa ya Ciro daga Aljihunsa ya kira Saheeba a waya akan ta kawowa bak'i ruwa da lemo yana katse wayar ya maida hankalinsa kan su Akram Dan yaji abinda ke tafe dasu

Ganin sun k'asa magana sai zungurar juna suke yasa Alhaji Nazifi yayi murmushi yana Allah yasa shima ba laifi yayi ba suka zo bincikarsa

Murmushi sukayi gabad'aya Yazeed yace ba Laifi yayi ba sun dai zo nema ne a gurin shi

Adai-dai lokacin Saheeba ta shigo da faranti a hannunta sanye take da doguwar Riga ta yane kanta da farin mayafi

Sallamar da tayi ne yasa suka d'ago gabad'aya suna amsawa

Saheeba a Razane ta ja da baya tana sallati a lokacin da suka had'a ido da Akram

Tuni ta saki farantin hannunta jikinta na rawa Dan take ta tuna bak'in daren da suka zo gidansu

Stammering ta fara yi tana nuna Akram da Hannu

Alhaji Nazifi kuwa yayi Sauri ya mik'e ya ruk'ota yana "Saheeba mai haka Akram d'in ne bakisani ba"
Chapter 24 · 0% Book details