← Book details Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 31

Sashe 1

Bakin Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read



DOCUMENT MADE BY
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE

馃寫 馃寫 *B馃叞K'IN D馃叞RE*馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫馃寫

*Written by*
馃拝馃拝 *Sadnaf*馃拝馃拝

*A heart touching story*

庐 *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
_莎蓻 蓶啤艐'脓 啤艐俪醿� 蓻艐脓蓻艡脓膮谋艐 艐蓶 蓻蓶懦膯膮脓蓻, 醿撑� 莎蓻 膮俪艦啤 脓啤懦膯骚 蓶 骚蓻膮艡脓 啤蕜 艡蓻膮蓶蓻'艦_

#[email protected]
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*Bismillahi Rahamanir Rahim am back again with interesting story insha Allah amma banyi muku alkawarin posting ba kullum Indai ina da sarari zaku na ganin post d'ina thanks for reading*

*Page 1*

Hajiya Nafeesa a zaune take atsakiyar 'yay'anta Saiam Safna Suhaima Sahiba da Auta Samha Saiam itace first born sai mai binta Safna sai Suhaima Sahiba da Auta Samha Hajiya Nafeesa yaranta duka mata ne Allah bai bata d'a namiji ba tana bala'in San 'ya'yanta sosai dan bata da burin da ya wuce taga ta faranta musu rai zata iya yin komai akansu Asalinsu 'yan gombe ne ita da mijinta haifaffun can ne Aiki da Alhaji Nazifi ke yi a Abuja ne yasa suke zaune a Abuja acan duk ta haifi su Saiam sun taso cikin rufin asiri da sutura ta ubangiji Dan babu laifi za'a iya saka su asahun masu kud'i akwai soyayya mai tsafta atsakanin iyalan da kaunar junansu most especially yaran Dan Kansu a had'e yake sosai

Dukansu da Hajiya
Nafeesa suke kama dan Hajiya Nafeesa fara CE kyakyawa idan ka ganta bazaka yarda ita ta haifesu ba dan k'aramin jiki ne da ita Samha ce kawai bata d'auko hasken fatar ta ba kamaninta ya fita daban Dana 'ya'yyenta dan ita kalar Alhaji Nazifi ta d'auko ita ba bak'a ba ita ba fara ba abinda ake cewa madarar Kyau Samha Allah ya bata Dan tafi su Saiam kyau sai dai su gaya mata hasken fata da gashi su Kansu wani zubin suna admiring kyawunta ga diri dan ita yar duma duma ce bata fiye tsayi kamar su Saiam ba

Hirar bikin Saiam da Safna da ya rage sati uku sukeyi cikin nishadi inda suke ta tsara abubuwan da zasuyi a bikin Saiam da Safna murmushi kawai suke yi suna kallon Suhaima da Sahiba dake ta tsara yanda bikin zai kasance Hajiya Nafeesa kuwa nata biye musu tana shafa kan Samha da tayi pillo da cinyar ta kananan kalban dake kan Samha take ta shafawa Samha kuwa ta lumshe idonta dan tana jin dadin yanda Hajiya Nafeesa ke wasa da kalaban kanta dan har wani bacci bacci taji yana Neman d'aukanta dukansu sanye suke da kayan bacci dan Sun kwanta Hajiya Nafeesa ce tazo duba su daga nan kuma ta zauna suna hira

Saiam kallon Hajiya Nafeesa tayi tace

"Mummy kije ki kwanta idan kika biyewa su Suhaima tsaf zasu rik'e ki da surutu dan ba gajiya zasuyi ba yanzu fa sha d'aya da minti biyar"

Hajiya Nafeesa d'aga kan ta tayi ta kalli agogon dake cikin bangon d'akin ta dawo da kallonta kan Saiam tace

" Barni musha hira da 'ya'yana sha biyu naje na kwanta"

Safna cewa tayi "Mummy yanzu Daddy kawai kika bari a b'angarenku gaskiya nidai kije ki taya shi hira ko ni naje na taya shi"

Dariya Hajiya Nafeesa tayi tace " sai kiyi sauri kije ai Daddynku ya Dade da bacci"

Murmushi sukayi su Suhaima kuwa suka cigaba da hira

Hajiya Nafeesa haka kawai taji gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa ahankali ta sunkuyar dakai tana karanta Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin Minha

Sahiba da Suhaima shiru sukayi suna kallon Hajiya Nafeesa

Gabanta cigaba da Fad'uwa yayi tana ta sallati a zuciyarta ahankali taji gabanta ya rage fad'uwa d'agowa tayi ta kalli su Suhaima dan Saiam da Safna sun Dade da bacci Samha ma bacci ya d'auketa

Ce musu tayi 'ina zuwa bari na dubo Daddynku na dawo"

Suhaima Hamma tayi Alamar itama ta fara jin bacci cewa tayi "mummy ba sai kin dawo ba kawai kiyi kwanciyarki gobe ma cigaba da tsare tsaren"

Hajiya Nafeesa girgiza kanta tayi tace "ina zuwa bari naje na dawo"

Ajiye kan Samha tayi akan pillow ahankali ta yi waje gabanta na cigaba da Fad'uwa tana addu'oi a zuciyarta da dan Sauri ta k'arasa b'angarenta Dana Alhaji Nazifi d'akinsa ta wuce direct

Akan gadon da yake kwance ta zauna agefensa ta lek'a fuskarsa bud'e idonsa yayi ahankali suka had'a ido ce mishi tayi

"Daddyn Saiam dama bakayi bacci ba"?

Harara ya wulla mata yace " bansani ba wai Nafeesa na dawo agajiye ko dan Tausa Babu ballantana hira mai dadi kawai kika kwashi jiki kika tafi wajen 'ya'yanki ba komai ki cigaba ina nan ina neman matar da zan Aura da zata ringa kula dani kije can ki karata ke da 'ya'yan naki tunda kinfi sansu akaina"

Murmushi Hajiya Nafeesa tayi tace "Allah ya baka hakuri ranka ya Dade ina can muna tsare tsare da 'ya'yanka bari nazo na maka tausar"

Tace tana k'ok'arin hawa kan gadon

Juya mata baya yayi yace "ai bana so kuma kiyi kwanciyarki bacci zanyi nama fara kika shigo"

Murmush ta k'arayi duk da gabanta bai bar fad'uwa ba

Mik'ewa tayi ta nufi band'aki dan tayi alwala

Abun mamaki tana alwala jikinta na rawa ga fad'uwar gaba ta rasa mai yake damunta

Tana gama alwala tafito ta cire doguwar rigar dake jikinta tasaka wani mai dan kauri dan Wanda ta cire na bacci ne hijabi ta saka tayi waje da sauri b'angaren su Saiam ta koma ta shiga a hankali taga duk sunyi bacci binsu tayi da kallo d'aya bayan d'aya haka kawai hawaye ya hau zubo mata ta kuma rasa dalilin zubarsu takawa tayi taje gaban gadon Saiam da Safna tana kallonsu sai data samu minti biyar tana kallonsu kirjinta na bugawa kafin ta tofesu da addu'ar kariya taje gaban gadon su Suhaima da Sahiba yanda tayiwa su Saiam haka tayi musu still tana zubar da hawaye a k'arshe ta nufi gadon Samha dake kwance ita kad'ai da teddynta ta rungume a kirjinta zama tayi agafen Samha ta zuba mata ido tana kallon kyakyawan fuskarta hawaye sai gudu yake a kumatunta ta rasa mai yake damunta gani take kamar kallon k'arshe take wa yayanta gani take kamar bazata k'ara ganinsu ba ahankali ta gyara mata kwanciyarta taja mata rigar baccinta daya nannad'e yayi sama ajiyar zuciya ta sauke ta fara magana ahankali tare da d'aga hannuwanta sama tana

"Ya Allah gani gareka ya Allah ga baiwarka nan tana rokanka gafararka bansan abinda yake damuna ba ya Allah wanan fad'uwar gaban danake yi bansan na menene ba ya Allah idan wani musiba ce take tunkaro mu Ya Allah ka tsaremin 'ya'yana ka kare minsu da karewarka Allah ina mai rokanka ka albarkaci rayuwarsu"

Ahankali ta sauke hannunta ta share hawayen dake ta zuba ta mik'e tayi hanyar waje tana murd'a k'ofar ta k'ara juyowa tana kallonsu tafi minti goma atsaye still hawaye na zuba afuskarta da k'yar taja k'afarta ta fice daga d'akin gabanta na cigaba da fad'uwa ta rasa mai yake damunta haka kawai takeji kamar akwai abinda zai faru dasu amma bata San menene ba.

B'angarensu ta koma tana shiga d'akin ta shimfid'a sallaya ta tada sallah a lokacin sha biyu saura minti biyu

Shafai da wutr ta fara yi kafin ta mik'e taringa nafilolli sai da tayi raka'a goma akarshen sujaddarta ta ringa addu'a ta kusa minti talatin ahaka kafin ta d'ago da hawaye shab'e shab'e a fuskarta Dan hawayen sun k'i tsayawa Sam hasali ma karuwa suke ga matsanacin fad'uwar gaba da jiki hannuwanta ta d'aga sama tana karayi wa 'ya'yanta addu'a da kariyar ubangiji sai wajen k'arfe d'aya ta shafa ta mik'e ahankali ta cire hijabin jikinta ta zura wani hular baccinta mai net ta d'auko counter d'inta agaban mudubi ta kwanta agefen Alhaji Nazifi bayan ta kuma rufeshi da bargo sabida sanyin Ac dake ratsa d'akin ahankali ta ringa Jan istigifari duk da hawaye bai bar zuba a idonta Ba haka ma fad'uwar gaban

Juyi kawai take yi Dan sam bacci yak'i d'aukanta ta ma rasa takaimaiman tunanin da zata yi lumshe idonta kawai tayi

*1:45am*

A lokacin bacci ya fara d'aukan ta Harbin bindiga taji kamar a mafarki suka mik'e ita da Alhaji Nazifi afirgice suna sallati Alhaji Nazifi a gigice ya mik'e yana neman wajen b'uya Hajiya Nafeesa kuwa tayi hanyar k'ofa da gudu cikin zafin nama Alhaji Nazifi ya ruk'ota yana magana k'asa k'asa yana

"Ke bakida hankali ne ina zaki je ba zaki zo mu nemi wajen b'uya ba b'arayi ne fa suka shigo mana gida "

Hajiya Nafeesa da k'arfi ta fusge jikinta daga ruk'on daya mata tace cikin tashin hankali murya na rawa

"Ina zanje fa kace Alhaji yarana fa idan muka b'uya muka San halin da y'ay'anmu suke ciki bazan iya b'uya ba wajen y'ay'ana zanje na b'oyesu Dan nasan suna farkon gate basu kai ga shigowa na biyu ba Alhaji idan dukiya suke so ka basu mu basu kome suke so kar muyi musu gardama dan Allah Ashe abinda ke ta sani fad'uwar gaba kenan"

Da gudu tayi waje bata tsaya jin abinda Alhaji Nazifi zai ce ba adai dai lokacin da aka kuma harbin bindiga

Alhaji Nazifi kuwa toilet yayi da gudu ya kulle k'ofar jikinsa na masifar rawa yabi ya had'a gumi

Hajiya Nafeesa kuwa aguje ta k'arasa b'angarensu Saiam Dan tana jin suna k'ok'awa da gate d'in da zai sada su da cikin gidan

Tana shiga d'akin

su Saiam dake cure a waje d'aya suna kuka suka mik'e aguje suke je suka rungumeta suna kuka

zame jikinta tayi daga ruk'on da suka mata ta rik'e hannayensu cikin Sauri tana nufar band'aki dasu sai da suka shiga band'akin ta rufe k'ofar band'akin tafara magana hawaye na gudu a fuskarta

"Saiam Safna Suhaima Sahiba Baby

(sunan data ke kiran Samha dashi)
Chapter 1 · 0% Book details