← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 33

Sashe 9

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari sun gama shirinsu tsaf na fita aiki, a tare suka sauko inda suka sami Dijeh na rigima da fauxie harda kukanta fafur taqi ta sanya uniform,

'barka da safiya hajiya... ta faďa tana kallonta cikin girmamawa,

'barka... Kukan me kike yi Kuma,

'taqi ta sanya uniform hajiya...
'why fauxie? ke meyasa kullum akaxo shirinki sai anyi rigima dake, cikin kuka ta soma mgn,
'Anty ni baxan je Skul ba xan biki asibiti...

Deedah yace amma baby jiya fa naji kina Mgnr xakije da kifi Skul har anty ta hanaki, tor ynxu me xai hana miki xuwa Skul,

'yaya ni baxan je ba kace sister taje dani hospital, Iman taja tsaki ta fice tana fadin

'ba inda xanje dake... Ahmed ya karbi uniform hannun dijeh da socks ďin ta da takalmi kana ya ďauke ta yafita harabar gidan da Ita,

Akan Mota ya ďora ta har lokacin kuka take hrda kiran baba,

Deedah ya Kira driver,
'idan sun tashi Skul by one ka kaita asibiti inda Iman xasu dawo tare,

'shikenan yallabai.... Ya dubeta,
'idan Kuma bakiyi shiru ba xnce ya dawo dake Kada yaje dake inda sister, tayi shiru tana ajiyar xuciya, ya Sanya mata uniform ďin harda socks and sandals ďinta ya sauko da Ita daga motar,

'jira inxo, tana tsaye gurin yaje ya karbo abincinta da skulbag ďinta....

Yana tsaye gurin har suka fice tana yimasa bye bye, ya sauke ajiyar xuciya haďe da girgixa kansa yana faďin Fauxiya rigima.

1:00pm

Ta fito daga labour room, tana tafe da waya a hannunta tana amsa Kira harta iso consultant,

'likita bokan turai acewar Dr Fulani,

Dr Umayma tace daga ina kike haka kina xufa , Iman ta xauna tana share gumi,

'daga Gynaec nake labour room, wata yarinyace qarama ga dukkan alamu bata isa aure suka yi mata, she is too young,

Allah ya taimakesu sunxo asibiti da wuri da Babu mamaki sai VVF ya sameta,

Fulani ta dubeta tana faďin,
'uwar na raye,

'tana raye har yaron amma kam tasha da kyar dan dai da sauran kwanaki a gaba ne, inkin ganta gwani tausayi early marriage,

'Umayma tace mutumin qauye kenan, ga maxan ba haquri,

Iman tace dan ma bakiga mijin ba babban mutum ne Wai shine Mai gari yana da ďan iliminsa shiyasa Wai suka xo da Ita asibiti,

'ai Kuwa da ta mutu a banxa cewar Fulani dake cin samosa, Iman ta ďan dubeta,

'sister xn sami sobo.....

'yau Kuma sobo xakisha cewar Dr Umayma,

'Kinsan Mai ciki da Kwaďayi inji Fulani bayan ta miqa mata robar sobo, sukayi dariya dai dai lokacin fauxie ta shigo da gudu ta faďa jikinta ta baya,

'miss you sister,

'Kada kisa na faďi bakiga mutane bane kin shigo ba Sallama, ta koma da sauri tana dariya,

Sallama tayi ta shigo tana faďin, gud afternoon anty Fulani & anty Umayma,

Suka amsa mata, fauxie rigima, taje ta xauna kusa da Iman tana faďin,

'Anty xn sha sobo...
'Fulani ta bata wani sobo tana faďin gashi fauxie kibar anty tasha nata, tana dariya ta karba,

'Tnkuuuu anty, ta juya tana kallon Iman,

'Anty shi baba baya shan sobo a battle ko cup yafisha a kwarya naganshi ranar yana sha ya ce na fita d......

Nan take Iman ta kware saboda ruďewa ta shiga tari sosai ba kakkautawa.....

My wattpad Phertymerh1

Babana da mijina......

©Fertymerh xarah💞

17

Da kyar ta iya tsaida tarin da take bayan Dr Umayma ta miqa mata ruwa tasha,

Batare da tunanin komai ba tana juyawa takaiwa fauxie duka a baya, ta saki qara bayan ta saki sobo ta riqe bayanta tana kuka sosai,

'Haba likita saboda me xaki daketa cewar Dr Fulani dake kallon fauxie,

'surutun banxane banaso, ina ruwanta da baba mai gadi ynxu da har take sanyo xancensa anan, why can't she control her mouth ace yarinya duk inda taje surutu... Yanayin da take mgn xaka karanci bacin rai sosai a fuskarta,

Dr Umayma tace gaskiyane fatyma, yaro mai surutu baiyiba ballantana irin na fauxie da ba control, baba masu gadi Kinsan basu fiye shan kayan bottle sunfi gane su xube a wani guri su sha, ruwa ma sai kiga a kwarya suna sha, ita kuma yace sobo yake sha a kwarya ai is nothing tunda har ansan me yake sha,

Fauxie najin suna Mgnr baba mai gadi, ita kuma bashi take nufi ba amma taji Iman tace shi, cikin kuka ta dubi Iman,

'Anty bafa........Shut up! ta faďa cikin tsawa haďe da jefa mata empty bottle dake gurin,

Fulani ta riqo fauxie xuwa jikinta a yanda ta lura Iman xata iya jimata ciwo,

'kiyi shiru fauxie, kidaina fadar abinda baa tambayeki ba, baba mai gadi ko a kwarya xai iya cin abincinsa bai damu ba, bakiga daga qauye yaxo ba, yawancinsu acan da fulanin daji duk akwarya suke cin abinci so ba wani abin damuwa bane, ta dubi Iman,

'kiyi haquri Dr fatyma karki sake dukanta, inkin lura abinda kike xato bashi fauxie ke nufi ba, beside ma fauxie batasan ire iren waďannan abubuwan ba,

Fatyma ta sa tissue ta gyara bakinta kana ta soma harhaďa kayanta tana faďin,

'surutun tane bana so baida amfani ballantana mai gadin mu salihin mutum ne, idan bana hana mata surutu wataran xata ďauko min abinda yafi qarfina,

'hakane acewar Dr Umayma, Iman ta haďa kayanta tayi masu Sallama ta fice, fauxie na kuka tabi bayanta,

Fulani ta dubi Umayma tana faďin ni naga hankalin fatyma ya tashi sosai kuma ta hana Fauxiya magana,

Umayma tace masu gadin nan bawai mutum xai basu yarda bane, tadai bi ahankali ta saurari Fauxiya ďin, ai wani surutu yana da amfani,

Hakane cewar Fulani tana jinjina kanta,

Sun fito harabar asibitin fauxie taga mai siyarda agwaluma, da sauri ta share hawayen fuskarta tana faďin,

'Anty ga mai agwaluma ki siya min, Iman tayi mata banxa

'kinji anty.... Nan ma ta kyaleta, nan da nan ta soma hawaye tana sheshsheka,

A hanya suka haďu da Dr Merah suka tsaya gaisawa da Iman, ya dubi yanda fauxie ke kuka sosai, da alama ta jima da Kukan yanda yaga sautin ma baya fita,

Ya riqo ta yana tambayar waya tabamin suruka matar prince?

Iman tasa kai tafice batare da tayi mgn ba, ya sunkuya yana tambayar fauxie,

Ta kasa magana da hannu ta nuna masa mai agwaluma, ya tashi yana kallon Iman da har ta shiga motar ta,

'kai fauxie duk Wannan Kukan na agwaluma ne, yayi shiru yana tunani shi aganshi yaje siyen agwaluma ynxu girma ya faďi, a matsayin mulkinsa a asibitin da kuma sarautar dayake taqama da Ita, har ynxu yana taqama da *mulki ko sarauta* abin a jininsa yake,

Hannu yayi wa ďaya daga cikin fadawansa dake tsaye a gefe, yaxo da sauri haďe da sunkuyawa cikin girmamawa irinta sarauta,

'kaje da Ita ka siyamata agwaluma kana ka kaita gurin yayarta,

'angama yallabai, yaja hannunta shi Kuma Merah yayi shigewarsa asibiti.

Tana cikin motar a xaune fauxie ta dawo da baqar Leda a hannunta, agwaluma ce aciki ta buďe motar tashiga gidan gaba, Iman taja motar batare da ta kalleta ba

Fauxie ta juya tana kallonta,

'Anty xaki cnxa min kayan ďaki irin na ihsan, ďakin ta blue ni Kuma ki sanyamin komai pink...

Tayi shiru bata tanka ba,

'kinji anty.... Nan ma shiru,

'Pls.... Kallon da Iman nayi mata yasa taja bakinta tayi shiru ba shiri, har suka iso gidan bata qara mgn ba,

Iman na kallonta ta nufi hanyar gidan baba, bata hanata ba tunda tasan baya gari dole xata dawo mata sai tayi shigewarta cikin gidanta,

Fauxie Kuwa kai tsaye gurin Mai yiwa baba wanki ta nufa tace ya Kira mata babanta, ba musu ya Kira mata shi, kusan sau biyar tana ringing kafin ya ďauka, yana jin muryar fauxie na mgn ya gyara xamansa,

'Auta yau da wannan wayar ake kirana, ina antinki, ta tunxure baki kamar yana ganinta,

'baba wai anty baxata canxa min kayan ďaki irin na ihsan ba,

'meyasa baxata cnxa miki ba? tayi shiru ba amsa,

'yace shikenan anjima xn turo a cnxa maki,

'baba pink nake so,

'tor shikenan, sai me kuma?
'yaushe xaka dawo?
'bayan 2 days Auta, kinaso kiganni?
'eh,
'ki gaida Iman ya tsinke Wayar,

Cikin jin daďi ta nufi bangarensu,

5:pm

Iman na xaune a falo taga ana shigowa da kaya fauxie ce a gaba tana nuna masu ďakin ta,

Matuqar mamaki xaka gani bayyane a fuskar Iman, ina tasamu kayan, kai tsaye ta tambayi daya daga cikin mutanen dake shigowa da kaya,

'Alhaji ya Kira aje ta xabi kayan da takeso a sanya mata a ďaki,

Iman tayi shiru tana jinjina abin, daga inda take xaune tana jiyo ynda fauxie ďin ke basu direction yanda xasuyi, ita ynxu yarinyar ta fara bata tsoro,

Tana xaune suka gama haďa ďakin komai pink har tedy ďin ta da komai, sai murna take xata Kira ihsan taxo taga ďakin ta itama yayi kyau,

Masu aiki sai xuwa kallo ake tsofin kayanta ta raba masu, duk Iman na xaune tana jiyo ynda suke mata godiya, wannan idan tayi sake kayan gidan ma xata kyautar duka,

Da gudu ta shigo falon tana kallon Iman cikin murna,
'Anty xo kiga ďakina yafi naki kyau, nan da nan ta ďaure fuska,

'xo nan fauxie, tayi shiru tana kallonta bata je ba
'ko bakya jine,
'Anty kiyi haquri,
'idan kika Bari na tashi daga inda nake xaune sai kin raina wayonki, xo nace... ba musu taje jikinta a sanyaye Iman ta jawo ta, ta xaunar da Ita kusa da ita,

'gayamin yanda akayi baba yace a cnxa miki ďaki,

'a wayar mai wanki nakira na gayamasa,

'tunda ni baxan miki ba sai kika kirasa ko, idan ya dawo xaki barmin gidana kije duk abinda bana miki yayi maki, buďar bakin fauxie sai cewa tayi,

'Anty ai baba yafiki kuďi, yana dasu da yawa a ďakin sa,

Iman tayi shiru tana kallon yarinyar, dole xata kai xuciyarta nesa akan yarinyar saboda qurciya komai sai da rarrashi,
Chapter 9 · 0% Book details