← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 33

Sashe 8

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmed Kuwa sai da sukayi nisa a jeji kana ya tsaida driver tare da fito da bindigarsa sosai ya tsorata cikinsa ya ďauki kuka jikin sa har rawa yake,

'kayi haquri bansan Menayi ba,
'banace kayi wani abu tunda baka xageni ba, ni barawo ne ka min adduar shiriya naji daďi, sauran dakaga sun fita yan uwana ne sunbi waďancan mutane suga gidansu, ga wannan(ya bashi dubu hamsin) driver ya karba jikinsa na rawa yana godiya tare da gode Allah da ba xaginsa yayi ba da Yanxu sai dai ya kashe shi a Wannan jejin ba Wanda xai sani ya kashe banxa, shiyasa mutum ya shiga motar kasuwa baisan mutane ba baisan wane irine su ba mutum ko Aljan ya xauna yana xage xage.... Allah ya taimakesa amma yana tsananin mamakin wannan mutum ace barawo ne, idan ka ganshi natsatse dashi shigarsa ta mutunci ba Kamar sauran abokansa ba, fari ne kyakkyawa dashi, Allah ne masanin gaibu akan xamansa barawo yaja motar da qarfi yabar gurin.

A sokoto suka sake haďuwa, bayan sun gama fashinsu a wani company sunci nasara suka juyo xuwa gidan wancan abokin wannan mutumin,

Deedah bai shiga gidan ba yana daga waje kasancewar dare ne, suka shiga suka masa dukan tsiya suka fito kana suka nufi gidan wannan mutumin dayafi xaginsu,

Wannan Karon da Deedah suka shiga gidan dan yaji xafin mutumin Mgnr sa nayi masa yawo a kwakwalwa,
_ba hasararra uwa kamar wacce ta haifi barawo_, da kansa ya harbi mutumin a qafa, ya rinqa kururuwa yana neman taimako yar'sa mace ďaya daga cikinsu ya shiga yayi raping ďinta, Deedah yasa belt ya xane mutumin sosai jina jina shi kansa jikinsa ya baci da jini ya sunkuya yana faďin,

'ka gane ko mu su Waye? Mutumin ya girgixa kansa, Ahmed yace

'Mune Waďanda Muka shigo Mota da kai ďaxu Muke xaune dakai kana xaginmu kana xagin iyayenmu alhali Kuma kace barayin basuyima komai ba amma ka xauna kana xaginsu, Yanxu barayin Sunyima Abinda baxaka taba mantawa idan ka shiga mota gobe sai ka xagesu da dalili suka juya suka fice mutumin ya fashe da kuka sosai yana nadama, magana ma Jari ce......

A xaton Deedah koda xaije gida xai samesu sunyi barci tunda ynxu sundaina jiransa ga mamakinsa yana shiga falon sukayi 4 eyes da fauxie da pencil a hannunta,

'lah anty jini a jikin yaya yaji ciwo, da sauri Iman ta juya tana kallonsa lokaci ďaya xukatansu na buga shi na tsoro ita kuma na xargin jinin menene?

BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah
15

Jikinsa a sanyaye ya ďauke kansa batare da ya sake kallonsu ba ya nufi hanyar step...

Fauxie ta dubi fatyma bakinta a buďe,

'Anty kin tuna sanda kika je daukata Skul har kika sami anayima wani duka jini ya fito a jikinsa ko....

'eh tor me akayi,
'anty sata yayi akayi masa duka, shima yaya sata yayi akayi masa wannan dukan...... Caraf akan kunne Deedah ya juyo da sauri yana kallonta dai dai lokacin da Iman ta bige mata baki tana faďin,

'yi min shiru shashasha, mijina ba barawo bane,

Fauxie ta soma hawaye tana riqe da bakinta, Iman ta juya tana kallonsa kafin tabi bayansa, jikinsa har rawa yake da jin kalaman fauxie suna isa ďakin ta fisgosa....

'kagayamin wannan jinin na miye, ina kaje? Cikin dakewa yake kallonta,

'Accident wata mata tayi da yaro a bayanta, sunji rauni sosai yaron dana ďauka ne jikina ya lalace haka ya faďa yana qara kallon jikinsa,

Mata da rauni, nan da nan ta nuna tausayawar ta akan abin, ta soma cire masa rigar tana faďin,

'kayi abin kirki daka taimakesu, Allah xai taimakeka watarana, abinda mutum ya shuka shi xai girba hairan ko shairan, muje kayi wanka, ya bita a sanyaye cikin tausayinta...

Fauxie na xaune tunxure da baki ta sauko, tana ganinta ta ďaure fuska tamau Kada ta đauki abin da wasa

'ke nagane bakinki baxai taba faďin alkhairi ba, kince baba baxai shiga aljanna ba yau gashi kin Kira mijina barawo why Fauxiya?

'Anty kiyi haquri .....
'Mtseww sai anyi mgn Kice haquri, tashi ki tattara colours ďinnan kimaidasu Kada gobe kixo kina damuna,

Ta tashi tana haďawa bakinta a tunxure ta nufi hanyar step, ta juya tana kallon Iman bata kallonta sai ta shige inda Ahmed yana xaune yana amsa waya, yana ganinta yayi Saurin katse wayar yana kallonta,

'yaya Ina ne kaji ciwo? Ya ďaure fuska
'ban sani ba,
'please yaya kayi haquri baxan qara ba,
'nida kika ce barawo ne fauxie, ta tsugunna gabansa,
'Ni bance ba yaya, nace kayi sata ne Kuma anty tace Bakayi ba shikenan.... ya ďauke kansa cikin mamakinta, ta tsaresa sai ya nuna mata inda yaji ciwo, shi yarinyar ynxu mamaki take bashi tana girma tana wayo, ynda ya gayawa Iman haka ya gayamata,

'good Samaritan, ta soma dariya ta fice yabi bayanta da kallo....

Daren ranar bai je ko ina ba yana gida tare da fauxie duk assignment ďin ta shi yayi mata, Sa'eed abokin Deedah yaxo Wanda suke aiki tare a banki, sai da yawa yakanxo taya Iman hira idan ya sami Deedah baya nan, sai shaquwa ta musamman ta shiga tsakaninsa da Iman, yana tayata hira da shawarwari akan xamantakewarta da Deedah na rashin xamansa gida saboda shi kansa baisan taqamaiman inda Ahmed ke xuwa ba tunda 6 suke baro bank,

Shima Sa'eed yakan xauna yabaiwa Iman lbrn matarsa salima irin yanda take nuna halin ko in kula dashi suna da yara biyu bata Kula dasu kullum tana kwance komai sai mai aiki, shi namiji ne Mai matuqar son kulawa ga mace amma bai samu ba daga matarsa kamar yanda Iman ke buqatar kulawar mijinta bata samu ba.....

A Wannan ranar bayan Deedah da fauxie sun gama assignment yayiwa Sa'eed Sallama sai da safe suka haye shida fauxie sama yabar Iman da Sa'eed, can you imagine ynda xaka bar matarka da abokinka saboda rashin kulawa,

Daga Iman har Sa'eed kallon mamaki suka bishi dashi, sunyi xaton xai xauna ayi hirar da shine amma sai suka ga sabanin haka, Hakan yasa Sa'eed yayi mata Sallama ya tashi ya fice da makullin motarsa a hannunsa dan baiga dacewar xamansa da Ita a Wannan lokacin da mijinta ke gida ba sai dai yana matuqar mamakin Deedah irin Wannan mata kamar Iman dayake nuna halin ko in kula akan ta, inama itace matarsa ba salima ba da ya more a rayuwa,

Da Wannan tunanin ya qaraso gidan, parking yayi ya ďauki laptop ďinsa ya shiga cikin gidan, hayaniyar yaransa yaji agun mai aiki sai da yaje ya gansu kafin ya nufi ďakin salima tana nan kwance da waya a hannunta,

Sallama yayi bataji ba hankalinta nakan waya, tsakin dayaja ya janyo hankalinta garesa kallo ďaya tayi masa ya ďauke dubanta garesa,

'Ashe ka dawo, bai tankata ba ya nufi toilet,

wannan tambayar raini ce take masa idan da sabo ya saba, bai taba fita ya dawo tayi masa sannu da xuwa ba ballantana irin tarairayar nan da mata ke yiwa miji yaji daďi,

Ya fito toilet ďin har lokacin tana kwance abinta ,

'Salima..... ya Kira sunanta cikin husky voice ďin sa,

Uhm... ta amsa batare da ta Kalle sa ba, yayi shiru yana kallonta da mamaki,

'idan abinci kake mawa yana Kan dinning kayiwa Indo mgn ta xuba ma ni Wlhy duk agajiye nike....

'aikin me kikayi duk yau bayan kwanciya, ke Wai sai yaushe xaki cnxa rayuwarki Kisan Abinda ya dace ga rayuwar auren ki, ba Indo nake aure ba ke nake aure dan me Wai komai sai Kice Indo xata min ke kina kwance.... ta tashi tana kallonsa,

'Bismillahi ai kadawo qorafi baxai qare ba indai kana gidannan, Indo dole nasanyata tayima tunda yar aiki ce, aure na xo yi ba bauta ba Yakamata kadaina min faďa haka kana takurani xaman aure naxo yi....

'tir da wannan xaman auren naki, indai haka ake xaman aure da nadaina shi Kuwa, ke baxaki bani haqqina ba sai kin ga dama idan Ina a matse ne sai na biya kuďi sai kace ba mata na ajiye ba, baxaki iya gyara gurin kwanciyar auren kiba sai mai aiki, baxaki iya kula da yaranki ba sai Mai aiki, baxaki iya Kula da gidanki ba sai Mai aiki, abincima sai mai aiki wannan wace irin rayuwace har sai yaushe xaki canxa ne.... taja tsaki ta tashi tayi ficewarta tana taunar cingam yabita da kallo kawai yana girgixa kansa....

*

Xaman falon ya gundireta sai ta tashi tayi kitchen tana kiran adama,

Da sauri ta fito tana goge hannunta da tsumma,
'baki gama aikin bane har ynxu?
'nagama hajiya Ina gyara kifi ne gobe fauxie tace dashi xataje Skul,
'Hmmmm fauxie kenan ta gyada Kai ta fice,

Fauxie ta diro daga Saman gado tana faďin,
'bye bros gudnyt, yana xaune akan stool yana duba wasu takardu na gurin aikinsa, ya ďago yana kallonta
'gudnyt baby.....dai dai lokacin da Iman ta shigo,

'kika ce da kifi xakije Skul Gobe,
'eh anty...
'ashe gobe kowa xai kyamace ki kenan, ki bari idan kin dawo kici inba haka ba xaki dinga wari acikin friends ďin ki, ta juya tana kallon Deedah..

'Wai hakane yaya? ya gyada kansa alamar eh,
'tor anty Kice ta barshi sai na dawo,
'kije dijeh ke kaďai take jira ku kwanta daga nan sai ki gayamata,
'gudnyt anty,
'Nyt ta juya ta fice da gudu.......

Babana da mijina.....

©fertymerh Xarah 💞

16

A hankali ta maida kallonta garesa shima ita yake kallo kafin ya taso xuwa gareta hannunta ya riqa suka xauna bakin gado,

'kin canxa sosai Iman, naga sai haske kike yi miye sirrin.. ya faďa haďe da Kanne mata ido ďaya, tayi murmushi tana wasa da yatsun hannunsa kafin ta dubesa idanunta sunyi rau rau kamar xatayi kuka,

'cikine ka tayani addua ya tsaya, ya saki wani murmushi mai bayyana irin farin cikin da mutum yake ciki ya rung xuwa jikinsa,

'Insha Allah xai tsaya, ina son yara sosai Iman Allah bai bani ba,

'nafika sanin haka muyi addua Allah ya tsaida wannan....... ya ja dogon hancinta yana murmushi haďe da cusa hannunsa cikin rigarta,

'bari muji xai kai wata nawa a yanxu, ta soma dariya tana ture hannunsa ya kwantar da Ita......,
Chapter 8 · 0% Book details