← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 33

Sashe 27

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Xuwa wannan lokacin iman tasan ta rasa Deedah ďinta, ta rasa wanda takeso, farincikinta, a ynxu da ta jima bata ganshi ba bataji ďumin jikinsaba ta yarda ya mutu ya barta har abada, xuciyar musulunci ce kawai ke riqe da Ita a yanxu,

Hankici tasa tana ďauke hawayen fuskarta cikin tausayin kanta,

Tunda ta iya ta karbi rashin Deedah, na wanene baxata iya karba ba a ynxu? But it's still painful.... Yeah so painful!

Bata burin mai kuďi ko wane irin mutum ne shi, tafison talaka xama da Wanda bashi da meyiwuwa hakan xaisa xuciyarta ta xamo so contacted, kuďi basu amfana ta da komai ba illah baqin ciki a rayuwa,

Wannan dalilin ne ma yasa ba abinda ke burgeta a duniya balle ya sanyata nishaďi, haka take xaune ba doguwar magana, babu hope, no future, babu xabi acikin rayuwarta, duk yanda Allah yayi da rayuwarta dai dai ne.

A yau ta tuno da Deedah kan abubuwa da yawa, baxai barta cikin damuwa ba, hawayenta kaďai xai gani gigicewa xaiyi da tarairaya concern da emotional pity amma ynxu babu shi,

Ba Wanda xai rarrasheta, ba wanda xai sanyata a jikinsa ya nuna damuwarsa akanta, babu wannan Deedah dake son farin cikinta Wanda xai iya barin komai na rayuwarsa dan yaga ya faranta tata rayuwar,

Wasu irin hawaye masu ďumi suka barko daga idanunta, a hankali bakinta ya soma motsi,

_"This life has changed... and we go our separate ways Deedah... but you'll still be in my heart till my dying days... my world has never meet a person like you..... I love you Deedah."_

My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina*

©Fertymerh Xarah 💞

37

Bayan wata biyar~~

Abubuwa sun soma daidaituwa a rayuwar Iman, batada sauran damuwa a ynxu bayan ta fauxie da little ynda suke kiransa,

Tana fita aiki a ynxu, komai normal batada matsala a ynxu tanajin daďin rayuwarta ba tunanin da takeyi a da,

Tayi kyau tayi jiki fatar jikinta sai sheqi take haka hasken fatarta ya daďa qaruwa, da kaganta Kaga qasaitacciyar mace mai ji da kuďi tako ina,

Dr Deen da Sa'eed kowa naganin ya cusa soyayyarsa a xuciyarta sai dai batada xabi acikinsu har wannan lokacin tama fi jin Sa'eed a xuciyarta akan Deen bata taba tsayar da tunaninta akan Deen fa, anata ganin Sa'eed yafi dacewa da Ita, shine abokin mijinta shine mutumin da ke xaunawa ya saurari damuwarta lokacin da Deedah na raye, shine mutumin dake share mata hawaye yana kwantar da xuciyarta and still now yana qoqari akanta he still loves her and she do too,

Akwai wani lokaci suna tare da fauxie sai ta tambayeta akan yanda take shiga sashen baba har tasami kwalbar da ta fasa,

Sosai fauxie ta tsorata bata manta dukan da baba yayi mata ba a tunaninta Iman ma dukanta xatayi, sai ta soma yarfe hannuwanta bayan ta ajiye robar ice cream dake hannunta kamar xatayi kuka ta dubeta,

'Anty Kiyi haquri baxan qara ba,
'ba komai xnyi maki ba, I just want to know, saboda me ma xan dake ki fauxie?

Sai ta kasa yarda da Iman tayi cikin gida da gudu inda masu aikin gidan tabar Iman, dariya kawai tayi tabi yarinyar da kallo, lallai fauxie ta tsorata ba qaramin bugu baba yayi mata ba da alama,

A daren ranar ta kasance da Sa'eed a farfajiyar gidan, yana tsaye bakin motarsa yayin da ta jingina a motar tasa, duk yanda yayi ya shawo kanta akan ta amince da soyayyarsa taqi amincewa anata tunanin duka duka wata nawa da rasuwar Deedah da har xata maimaita wani aure a ynxu,

'ko xnyi aure baxan auri mai kuďi ba Sa'eed, talaka nakeso mai wadatar xuciya wanda bashida burin kuďi ballantana ya nemesu ta kowacce hanya, banason miji Mai irin ra'ayin *Babana da mijina*, inason mijin da xai soni ya nunamin soyayya har qarshen rayuwata,

'har sai yaushe xaki gane ba kowane namiji suka taru suka xama ďaya ba, kinsan ni Kinsan aikina Kinsan kowaye Sa'eed idan kina tantama akaina ne then you can ask salima ta gayamiki koni waye,

Tayi sama da idanunta tana kallon sararin samaniya idanunta fuskarta ďauke da murmushi tana son wannan yanayin da iska mai daďin gaske ke kada jikinta, ta lumshe idanuwanta dai dai lokacin da motar Dr Deen ta kunno kai a gidan,

Daga ita har Sa'eed suka juya suna kallon motar ko ba'a faďa ba sunsan kowaye, Sa'eed ya bata fuskarsa yana kallonta,

'waishi wannan likitan me yake xuwa yi gidan nan ne miye alaqarki dashi,

'abokin takarar ka ne idan baka gamsu ba xaka iya tunkararsa kaji qarin bayani, ta juya tana kallonsa,

'duk Mgnr da xamuyi dakai bana son kana sako min matarka aciki,

'kigayamin matsayina fatyma, Inaso mufara shirye shiryen auren mu,

Dariya tayi mai fitar da sauti tana kallonsa, Deen dake cikin motarsa yana kallonsu yaga tayi masa kyau a yau, wannan tawwadar Allah dake fuskarta tana birgeshi, sai dai akwai bacin rai sosai a xuciyarsa na ganinta da wani Kuma tana dariya a gabansa,

Yana ganin sanďa Sa'eed ya shiga motarsa ya bar gidan ta qaraso garesa, cikin sanyin muryarta take gaidashi bayan ya fito a motarsa, batasan meyasa takejin nauyin Deen fiye da Sa'eed ba, bata iya haďa ido sosai dashi saboda kwarjini da yayi mata a fuska,

'ya little da fauxie,
'suna lafia inaji a ynxu sunyi barci,

Yayi shiru Kamar baxaiyi mgn ba sai Kuma ya dubeta,

'naxo ne kan mgnr mu, baffa yana so yaji hukuncin da kika yanke idan ba damuwa Inaso manya su shigo Mgnr mu,

Wannan Karon ba walwala a fuskarta kowa damuwarsa yasani banda tata, gani take kamar taci amanar Deedah idan har tayi aure ynxu, tana yawan mafarki da Deedah shiyasa har ynxu take ganin kamar xai dawo gareta bai mutu ba,

'Tace kayi haquri Dr Deen har ynxu ba kowa a xuciyata sai mijina shi nakeso banajin inda wata sauran dama da xn bawa wani a ynxu,

'hakane baxan takura rayuwarki akaina ba, I also feel the pain you feel, Sanda na rasa matata banyi tunanin akwai wata mace da xn nema har na so ta ba sai lokacin dana tsinci kaina a sonki, Wanda ya mutu baya dawowa Iman, forget about the fast and face the future, inada haufi akanki,

Kada kayi haufi akaina Zaharadeen soyayyata da Deedah haďin Allah ce badan wasu kyale kyale na rayuwa ba, continue to be your natural self Dr Deen ka xamo yayana I like it and I respect your values too much...... Deedah nake so ta yanda har bana iya waiwayawa in hangi hierarchy ďin da shi yake gani Wanda so baya laakari dasu...

Sai bayan ta furta hakan kunya ta lullubeta don ganin irin yanda ya saki jiki sharaf ya xubawa fatar bakinta dake motsi, sai take ganin kamar ta zarme tayi subutal baki sai tayi Saurin gyara xancenta da cewa,

'nidai fatana da burina shine nasami soyayyar wanda nakeso, ya yarda dani nima in yarda dashi Allah ya yarda damu baki ďaya, nayi alqawarin xama dashi acikin kowane hali, akwai ko babu, daďi ko akasinsa ma'ana talaka nake so......

'idan wannan ne kin samu nima talaka ne mai nema a gurin Allah akoda yaushe,

Batasan sanda dariya na subulce mata ba, hakan ya sanyashi nishaďi,

Unconditionally ya miqa mata hannu,

'shakes my hand Iman, na gode da kulawarki koda bakyasona, Ina roqon Allah ya fiddani a kunyar soyayyarki ya bani ikon fita haqqoqinki, yabani ikon shiga xuciyarki ya Kuma bani ikon muhimmantata fiye da duk wani al'amari da ďan Adam ke burin samu....

Suka haďe hannunsu wuri guda kamar masu qulla alqawari kana ya janye hannunsa ya juya ya shiga motarsa tana tsaye tana kallonsa har yabar harabar gidan.

Tunda yaje gida yakasa kwanciya, sonta yake har cikin ransa amma ya fahimci bata sonsa ko kaďan,

Gashi yau ya tsinci kansa cikin wani al'amari Mai girma akan Iman, duk da ba sonsa take ba, sai ya soma yaqi da xuciyarsa,

Sai dai duk iya qoqarinsa a Wannan daren ya gaza rintsawa ko ya runtsan surar Iman yake gani cikin murmushi, abin kamar azal.

Don haka da yayi sallar asuba ya dade yana roqon Allah sauqi cikin al'amarin, Iman ta kankane ko ina na xuciya da kwakwalwar shi, ta kassara gangar jikinsa bata barshi da ko saqo ďaya da xai sanya tunanin kansa ba.

Don haka a Washe gari shine mutum na farko daya danna masu kararrawar falonsu yana cikin shirinsa na xuwa asibiti,

Adama taxo ta buďe, ya umurceta da ta kwaso kaya a boot ďinsa kana ya Sanya kai cikin falon bakinsa ďauke da Sallama,

Tana xaune da fauxie a dinning suna kalaci yayin da little ke tsakiyar falon yana Jan rarrafe,

Iman ta ďaga fararen idanuwanta tana kallonsa Waďanda a take ya gano sun qanqance sun ďan tasa sunyi ja kaďan alamun rashin wadataccen barci kamar nasa,

Kada yayi haufi inji xuciyarsa, itama ta kwana cikin kwatankwancin irin situation ďin daya kwana jiya,

Gabaki ďaya jiya tunaninsa dana Sa'eed sun hana mata barci da sukuni batada choice a cikinsu kowane danashi matsayi a xuciyarta dama xasu haqura da ita datafi kowa farin ciki domin babu maganar aure a xuciyarta Yanxu.

My wattpad Phertymerh1

*Babana da Mijina*

©Fertymerh Xarah 💞

38

_dis page is for you Faxyfashion_

Ta ďauke kanta daga kallonsa ta maida hankalinta kacokan Kan abincin da take ci,

Fauxie taxo da gudu ta rungumesa tana dariya,

'Mrng yaya...
'Mrng little angel, bakije Skul ba,
'ina jiran driver bai xo ba,

Ya ďauki little yana yi masa wasa, yaron sai dariya yake daka ganshi kaga Deedah photocopy sak....

Adama ta shigo da kayan kai tsaye ďakin Iman ta nufa dasu duk da batasan ko menene acikiba amma bata ďebe tsammani ga kayan Iman ne,

Driver yaxo fauxie ta fice tana yi masu bye bye,

Iman ma Acikin shirin fita aiki take tana gama kalaci ta taso ta karbi little yaqi xuwa ya liqewa Deen,

Ta rataya Jakarta tana faďin,
'xan barka anan kuwa inda adama tunda yau ni kakewa quya,

Dr Deen ya juya dashi tabi bayansa, motarta ta shiga shima ya shiga tasa tare da little,
Chapter 27 · 0% Book details