← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 33

Sashe 20

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'anty tace kaxo ka siyomin ice cream,
'tor xo kigani, sirri xamuyi karki gayawa kowa kullum xn riqa goyaki muje yawo a Roba Roba ďina kina so? ta gyada Kai tana kallonsa da murmushi, ya riqa hannunta yana waiwaye Kada a ganshi,

'je ďakin baba ki ďibomin kuďi, kiyi sauri Kada wani yazo yagani, batare da tunanin komai ba ta faďa ďakin tsafinsa, kuďi ne birjik a qasa ta ko ina, Akan gado a qasa sai faďowa suke ďaya ďaya kamar yanda leaves ke faďowa a itaciya,

Ta kwashi kuďin tana kallon ďakin, har xata fita sai idanunta na sauka akan tedy ďinnan ta tsafi, ta ďauka, sai taga wata kwalba da ruwa acikinta ga wani abu ja aciki yana yawo aciki (rayuwarsa ce aciki cewar Sima) sai abin ya birgeta, ta duqa xata ďauka Suleiman ya soma mgn,

'me kike jirane, ko kaďan ne ki fito Kada wani yagani, buqatata nasami na cnxa waya na kaiwa ummata sauran, dan ma Ina sata Ina haďa kayan aure ynxu,

Ta juya ta fice tana waiwayen kwalbar Abinda ke ciki yana yawo ke birgeta ta qudira aranta xata dawo ta ďauka,

Tana fitowa ya ďauketa cike da farinciki cos ta ďebo da yawa suka fito yana faďin,

'wannan kuďin haka kikace anjima naje xnce da baqar Leda, ya karbi kuďin ya cusa aljihunsa kwata kwata hankalinsa bai kai ga tedy dake hannunta ba azatonsa tatace,

'Kada ki gayawa kowa kinji,
'tor xakaje dani yawo,
'kwarai ma kuwa baby, kina gaban mashin ďina, aike abinso ce gareni, gaki yar fara kyakkyawa matar Manya ko? tayi murmushi tana kallonsa,

'muje anty tana kiranka,

Tana xuwa takai tedy ďakinta ta boye qarqashin gadonta bataso Iman tagani tayi mata faďa,

Ranar Deedah ya dawo suna xaune ďaki dashi take bashi lbrn abinda ya faru a asibiti,

'Allah yaji qanta amma Waye Dr Deen kamar nasanshi,

'kasanshi mana wannan na paediatric wanda muka taba kai fauxie gurinsa sanda tana Mura,

'na mantashi amma na tausayamishi kodan jaririn,

'idan ka ganshi xaka tuna, wani fari kyakkyawa haka, yanada fara'a sosai,

'kinaso kice yafini kyau kenan?

'chab ni na isa, akwai namijin da yafi mijina kyawu ne, kawai Ina misalta ma shine, yayi murmushi ya ja dogon hancinta

'you are the best my only wife, Ina sonki Iman, itama murmushin tayi haďe da kwantawa a qirjinsa,

Bayan sati ďaya tana shiga asibitin kayanta kawai ta ajiye a office ta nufi labour room tun kafin ta shiga take jiyo kururuwar wata mata, da sauri ta qarasa tana tmbyr meya sameta,

'yauwa Dr help us, tana labour Kuma aljannunta suka tashi,

Iman ta matsa tana kallon matar a bakinta addua take, matar mai aljannu tana juyowa taga Iman sai taga baba tsaye a gabanta, ita kaďai ke ganinsa saboda aljannunta, ta taso xata capki Iman a xuwan shi xata riqa akayi Saurin riqata dai dai lokacin haihuwa na xomata,

Kwata kwata Iman ta manta bata hayyacinta saboda tausayin matar, sai kawai ta karbi haihuwar, yaron na hannunta baba ya soma tsafin,

Idanun matar suka jujjuye, wani qarfi yaxo mata ta xabura da qarfi ta capko wuyan Iman ta shaqureta iya qarfinta.

My wattpad Phertymerh1

[22/03, 4:45 p.m.] Pherty🎤👯:

*Babana da mijina....*

©Fertymerh Xarah 💞

31

....Sai na kasheka, sai na kasheka matsiyacin banxa, baka isa ka kashemin yaro ba, idan ya mutu kaima sai ka mutu,

Idanun iman sun juye, sai kakarin mutuwa takeyi, nurses ďin sai bugun matar suke yayin da wasu suka fita da gudu kiran masu taimako,

Da gudu Dr Bakori da Dr Deen, da Dr Chris suka shiga ďakin,

Sosai ta galabaita kafin su banbareta daga jikinta, ragwab ta xube gurin a sume, Dr Deen ya ďauke ta da sauri ya fice da Ita Dr Fulani na bayansa yayinda sauran likitocin suka rufawa marar lfy suna dubata sai fisge fisge take shi kansa baba tuni yabar ďakin ya bata tun lokacin da yayi arba da matar yaji hankalinsa ya tashi,

Ba Wanda yayi xargin wani abu inda Iman ta sami sauqi kenan, kuma jaririn ya rayu sai dai har lokacin Iman bata farfado ba ta jigata sosai,

'ko akira mijintane a sanardashi cewar Fulani,

'A'a kibarta xata farfado, wuyanta yayi ja sosai wannan ba qaramin riqo tayi mata ba cewar Bakori,

'Fulani tace boyar Allah tabani tausayi Wlhy, fatyma batada matsala a rayuwarta Duk Wanda ya xauna da Ita xaiji daďi,

Dr Deen na tsaye hannuwansa sarqe a qirjinsa yana saurarensu, idanuwansa xube akan fuskarta, komai bai ce ba,

Fiye da minti talatin kafin ta farfado, da addua a bakinta tana buďe idanuwanta hawaye na soma xubo mata,

Sai suka taru akanta dukkansu suna bata baki, rarrashinta suke tare da fahimtar da Ita wasu abubuwa game da irin Wannan dake faruwa,

Sai taji xuciyarta tayi sanyi ita matsalarta Kada a xargeta akan wani abu amma tayi alqawari a xuciyarta kome xai faru a asibitin baxata qara leqa labour room ba, baxata qara taimako ba iyakarta duba patient,

Bayan kowa ya fice ďakin ya rage ita da Dr Deen, sai ta dafe kanta da hannunta duka biyu tana tuna abinda ya faru a ďaxu, ďagowar da xatayi suka haďa ido dashi yana kallonta sai da gabanta na faďi, tayi qarfin halin mgn,

'Likita ya haquri? Ya sauke numfashi bayan ya ďauke idonsa akanta,

'haquri mun gode Allah fatyma, shima yaron ya koma ai, ta dubesa a razane,

'shima ya rasu? ya gyada Kai yana kallonta,

'Subhanallah, Wayyo Allah, Allah ya gafarta masu ya baka haqurin rashinsu ya musanyama da mafi alheri,

Yasa yatsa ya ďauke guntuwar kwallah yana kallonta,

'I have no one in my life, babana kawai, no mother, no wife, no child, no brothers an sister, only my father and family,

Ta sauke ajiyar xuciya kanta a qasa batasan dalilinsa na gayamata wannan ba sai dai a xuciyarta tana tausayamasa,

Daga wannan bai qara cewa komai ba ya fice daga ďakin, itama fitowa tayi ta nufi office ďinta kayanta ta ďauka ta fice daga asibitin gaba ki ďaya,

Ranar Sa'eed ya xo gidan, sun jima suna hira haďe da gayamasa matsalolin da take fuskanta a ynxu asibiti, yace xai tayata addua itama ta dage.....

Baba yayi neman tedy bai gantaba hankalinsa yayi matuqar tashi domin matsafarsa ce aciki wacce da Ita yake bata ba'a ganinsa a duk sanda xaiyi wani sharri, ba shiri ya jewa sima da bayanin batan tedy ďinsa, ta ďauki wata ta basa,

Tun daga lokacin yasa ido sosai akan gidansa dan ganin mai masa shige da fice a ďakinsa,

Fauxie Kuwa kwata kwata ta manta da tedy da ta boye a under bed ďinta bata qara bi ta kanta ba,

Some months.....

Cikin Iman ya shiga watan haihuwa, duk wani so, kulawa da gata ba Wanda bata samu daga Deedah, yadaina fitar dare kullum yana tare da Ita komai shi ke mata, shi ke kaita asibiti kuma shi ke daukota,

Soyayya suke mai cike da kulawa a tsakaninsu,duk burinsa na kan cikin a ynxu ita kanta Iman tasan Deedah yafi ta son cikin,

Duk wannan abin da ake ciki baba bai taba sanin Iman Nada ciki ba, shi rabonsa da Ita har ya manta, saboda sun daina bincike akan ta ynxu qananan yara yake satowa yana kawowa sima tun lokacin da matar ta ganesa a asibiti bai qara shiga ba,

Da dare ta fito kitchen ďauke da plate na nama, fauxie na bayanta da tedy a hannunta, ta xauna itama ta xauna kusa da ita,

'anty shi baby kullum sai yaci nama ne?
'Tace eh,
'tor anty ki sammin,
'a'a na baby ne kaďai wannan, ba kinci naki ďaxu tare da yaya ba, ta tunxure baki idanunta sunyi rau rau kamar xatayi kuka, iman ta ďan dubeta ta gefen idanunta,

'crying baby, kina taba jin baby yayi kuka Kuwa ? ta girgixa kanta tana kallonta,

'idan kikayi kuka ma baxai fito ba, shikenan bakida jariri, tayi Saurin goge fuskarta,

'anty yaushe xai fito? Iman ta miqa mata sauran Naman tana faďin,
'ya kusa fitowa ai,
'anty idan na mutu kiyimin sadaka, wai inji malam ana yiwa Wanda ya mutu sadaka,
'tor idan ni na rigaki mutuwa fa?
'nima xn miki sadaka anty,
'ai nafiso ki mutu kibarni dan Idan na mutu bansan ya rayuwarki xata kasance ba, bnsan inda xaki xauna ba,
'anty inda yaya xan xauna ko inda Amira,
'oh oh mutuwa ba ynxu ba fauxie, fata ta gari sai naga aurenki da sultan,
'anty ni bana sonsa yaya nakeso, iman ta dubeta,
'da gaske fauxie, ta gyada Kai tana kallonta,
'kinga shi yaya yana siyamin ice cream, chocolate, biscuits, tedy, yana daukana,
'tor shima sultan xai maki haka fauxie in banda abinki me xakiyi da mijina ai ya maki tsufa,
'anty ni banason sa yaya nakeso,
'ke Kinsan miye so ne? tayi shiru tana kallonta,
'kinga kin tadamin Kwaďayin ice cream ďauko min a fridge,
'babu shi na shinye,
'kiramin Suleiman yaxo ya siyomin, fauxie ta fice da gudu bata jima ba sai gata ta dawo,
'anty bayanan..
'ďan lami fa?
'duk ba kowa a gidan baba, ta duba agogon hannunta 9pm,
'ďauko min hijab ďina da makullin mota kixo muje...

Da gudu ta haura Sama taje ta ďauko sai tsalle takeyi,
'anty kema kina shan ice cream ashe,
'bani xnsha ba baby xai sha,
'baby ya iya sha ne anty,
'sosai ma.... ta buďe motar ta shiga itama fauxie ta shiga,
[22/03, 7:05 p.m.] Pherty🎤👯: Sanda suka isa gurin siyarda ice cream ďin, tana daga cikin Mota ta baiwa fauxy kuďin taje ta siyo, tana kallonta daga cikin motar sai tsalle take Acikin shagon, ta sauke ajiyar xuciya dai dai lokacin da sukaji Kukan harbin bindiga, ta soma waige waige kamar mai neman wani abu, ta juya tana kallon fauxy dake tahowa da baqar Leda a hannunta sai Kuma taga ta tsaya tana kallon wani gu, ta sauke glass ďin motar da sauri tana mata mgn,

'what are you waiting for Fauxy?
'lah anty... ta juyo tana kallon Iman, ta daka mata tsawa,
'kixo mubar gurinnan, da gudu fauxie taje ta shiga motar ta rufe ta juyo tana kallon Iman dai dai lokacin da take tayar da mota,

'anty naga yaya da bindiga tare da wasu mutane, taja wani uban birki tana kallonta xuciyarta na bugawa,
Chapter 20 · 0% Book details