← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 33

Sashe 30

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'why did you hate me Sa'eed?
'saboda me, meyasa kike wannan mgnr iman, duk duniya akwai wanda ya kaini sonki ne, you hate me shiyasa na barki da Wanda kike so, naga kamar Ina takuraki shiyasa na barki,

'ba haka bane, har ynxu xuciyata ta kasa tantance min xabina, idan nace bana son ka ko bana son Deen nayi ma qarya, amma fushinka akaina K.... ya katseta,

'ki auri Dr Deen....itace kalma dana fito bakin Sa'eed ta ďago tana kallonsa cike da mamaki,

'I know Kinason Dr Deen, he loves you too, na taba gayamiki ya sameni nan saboda ke, bawai ya roqeni na barmashi ke ba ya roqeni akan idan na aure ki na kula da ke da yaranki, na baki farinciki har a qarshen rayuwarki, ba abinda na fahimta a idanuwansa sai xallar soyayyarki, bai fito ya faďa a baki ba amma idanunsa sun nuna, ina sonki Iman, dole ta sanya xn haqura dake ki auri Dr Deen domin yafini buqatarki, bashida kowa bayan mahaifinsa, nikuma I have family matsalar bnda kwanciyar hankali akansu,

Tunda yake magana tayi shiru tana kallonsa ta kasa fahimtar komai a kalamansa Illa na ta auri Dr Deen, yes xata iya haqura da Sa'eed cos xuciyarta tafi rinjaya kan Deen and she accept it, ta amince xata auresa ko dan kwanciyar hankalinta dana yaranta,

'but Sa'eed...... Shishshsh ya katseta, kada kidamu dani, Allah is with me idan salima mai shiriyace Allah ya shiryata ya ganar da Ita, ban kullace kiba, idan kin amince I will be your brother na har abada kamar mun fito ciki ďaya dake....

Ta gyada kai tana murmushi mai tare da hawaye, farin cikinta a yau, ta rasa yayyunta biyu da suka rasu yau ga madadinsu, Dr Merah da Sa'eed, kyautace daga Allah Kuma ta karba da hannu biyu, ta rasa mahaifi ta sami baffa a hannu sai dai fatan miji na gari wannan shi kaďai ne burinta a Yanxu.

Tare da Sa'eed sukaje suka sami baffa da Mgnr kan ta amince da auren Deen, sosai baffa yayi farinciki kamar xai haďiye Iman haka yakeji,

Koda baffa ya gayawa Deen Mgnr bai nuna masa farinciki ba amma har a xuciyarsa yaji daďi, duk da hakan ya basar bai nemeta ba kamar baisan da Mgnr ba,

Dr Merah, Sa'eed da wani kawunta su suka karbi sadakinta, sune waliyyanta,

Sai dai ba yanxu xata tare ba sai tagama shirye shiryen ta kamar yanda Dr Deen shima yana buqatar lokaci har ya haďa kayan aurenta.

Salima na xaune a falo tare da yaranta taga mutane na shigowa gidan,

'waďannan su Waye ta faďa bayan ta tashi, ga mamakinta sai taga qatuwar Mota da kaya ana saukewa irin kayan amare ďinnan, maxa ke shigowa da kayan yayin da matan suka nufi ďayan part ďin da ke rufe, tana gani suka buďe suka shiga,

'no she can't believe it Sa'eed baxai mata haka, tor kodai haya yabada gurin, inajin haya ya bada gidan, let me confirm it,

Ta sanya hijab ďinta ta fita, cikin maxan masu sauke kaya ta nufa,

'sannu malam,
'sannu hajiya,
'wancan part ďin haya aka ďauke sa kome?
'A'a amaryar mai gidan ce gobe xa'a ďaura aure ta tare,

Batace komai ba amma jikinta har rawa yake saboda tashin hankali,

Koda taje ďakinta kasa xama tayi sai safa da marwa take, ganin ba mafita ta dauki hijab ďinta ta fice kai tsaye gidan Iman ta nufa ta Kuwa yi Sa'a ta sameta,

Ba Sallama ba komai ta faďa gidan suna haďa ido da fatyma ta soma faďa da xage xage ta inda take shiga batanan take fita ba,

Iman na xaune da adama tana yanka mata fruits, idan ke mai karatu kin tanka tor Iman ta tanka, tunda ta maida kanta ga cin fruit bata qara waiwayarta ba, dama iman ga haquri da sanyin hali.

Wannan ne yafi komai baqin ciki da haushi kana faďa ayima shiru amaidaka banxa Hakan ya qara kufular da salima ta soma ball da duk abinda ke falon,

Iman ta tashi ta dubi adama, ki shiga ki qarasa aikinki adama, idan wannan mahaukaciyar ta gama haukarta ta bata gurinnan kiyiwa securities magana a fitar min da Ita daga gidan kana a gyara falon tasa kai ta fice haďe da rufe ďakinta,

Kamar ta sanya ihu haka takeji angama cin amanarta a ganinta, qawarta xata aure mata miji wallahi bata isa ba, Gashi ta kirata mahaukaciya, kamar daga Sama sai ga Sa'eed a gidan abinda idanuwansa na gani ya tsoratashi, meya fito da salima da ixinin wa ta fito meyasa tayiwa falon kaca kaca haka, nan take ya ďauketa da wani Mari sai data ga gilmawar taurari, hancinta ya fara jini,

Basai na gayamaku irin Faďan da sukayi a ranar ba kamar xasu haďe junansu a haka ya fisgeta suka bar gidan......

Daren ranar basu kwantaba kwana sukayi bala'i haka ta xamar masa tamkar wata xararriya sai daya sanyata a ďaki ya rufeta kafin ya sami sa'ida.

Washe gari aka ďaura auren Dr Iman da Dr Deen...

Kana aka ďaura auren Sa'eed da Habbi qawar salima,

Koya xamansu xai kasance da salima, ya salima xata kasance idan ta wayi gari ta sami habbi a matsayin abokiyar xamanta, qawar dake bata shawara akan yanda xata Kula da mijinta, wani abin qarin haushi habbi budurwace bata taba aure ba.

My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina*

©Fertymerh Xarah 💞

42

Har ynxu ban fahimce ka ba, idan ba Iman ka aura ba to Waye ka aura, ko kana tunanin bansan cewa yau aka ďaura aurenka da Iman ba,

'bani ke auren Iman ba, Wanda take aure daban wadda nake aure daban, idan Kina tunanin saboda haukarki naqi auren Iman tor kina tunanin banxa ne, anjima da dare matata xata tare koma wacece xaki ganta,

Hankalinta ya qara tashi numfashinta har fita yake da sauri da sauri, qaryane Iman yake aure idan ba shiba to wake aurenta?

'kagayamin Iman *Matar Waye?* idan har bakai ke aurentaba,

'wannan ne baxakiji a bakina ba, inaji kin saba xuwa gidanta ki sameta ki nuna mata rashin mutuncinki ynxu ma you are free... ya cigaba da haďa kayansa,

'kayan me kake haďawa Sa'eed, har ynxu ban fahimceka ba me kake nufi ne,

'kayana nake haďawa na maidasu inda amaryata inda xa'a kula dasu da darajasu.... Kafin tayi magana ya fice,

Kuka take tana haďa kayanta tayi yaji gida xataje, yana ganin lokacin da ta fita da kayan bai hanata ba, kai tsaye gidansu ta nufa, Ummanta na jin dalilin dawowarta ta rufeta da duka kamar xata cinyeta,

'ai Sa'eed yamin dai dai wallahi, kinci amanar tarbiyar danayi maki dan ba haka kika taso kika samu inayi da mahaifinki ba, kina gani da tsufana a ynxu nake kula da mijina, sau nawa yake kawo qararki gidannan in xaunar dake inyi faďa inyi rarrashi duk bakiji ba,

'xaman gidan kikeso kixo ki xauna muna gugar kafada dake, idan nayiwa mijina kwalliya kema kiyi masa gaki ga gidan ki xauna tunda kin xabi hakan a rayuwarki,

Kuka take sosai Kamar ranta,

Mahaifinta ma ya tsoma bakinsa,
'idan har kika bari kika kashe auren ki saboda son xuciya bani bake kuma baxaki xauna min a gida ba, tashi kije kibani guri shashasha kawai,

'na shiga uku *babana da mijina*, babana xai yafeni saboda mijin dayaci amanata, ta tashi tana kuka ta shiga motarta, wayar habbi ta Kira ko xata sami shawara a gurinta,

Tana ringing ba'a ďauka ba har ta tsinke ta qara kira sai data kusa tsinkewa kana ta ďauka,

'kina gida ne habbi?
'a'a Ina saloon,
'naso naxo ne, Sa'eed aure xai qara yau amaryarsa xata tare, ta fara kuka,

'wannan matsalarkice salima, sanda nake baki shawara bakiji ba ynxu ni banda abinda xn maki, bikin dake gabana ma ya isheni,

'bikin waye Kuma,
'au bakida labarin aurena ne?
'Hhhhhh wasa kike, har yaushe xakiyi aure baki sanardani ba gobe xn shigo kibani mafita,
'a'a basai kinxo ba ni xnma xo, ta tsinke wayar....

Da dare aka kawo amarya duk a nata tunanin Iman ce amarya musamman data ga little a sashen Sa'eed yau, tana ji sanda aka shigo da amaryar da guda sai leqe take ta window, bataga fuskarta ba,

ďakin Sa'eed ta nufa suna haďa ido ta fashe da kuka, yasan xafin kishin da takeji a xuciyarta, yana son matarsa bawai baya sonta ba halintane ya sanya yayi mata haka,

Ya taso ya rungumeta, rarrashinta yake cikin Kalamai masu sanyaya xuciya, sai abin na bashi mamaki ganin yau duk inda ya taba a jikinsa bata hanashi, babu harara babu mitar ta gaji sai ma qara narkewa da tayi a jikinsa tana qara kissing ďinsa....

Da kyar ya sami kansa kamar mai son yi masa fyade a Wannan daren, ya ďauki little dake barci ya fice da sauri......

Washe garin ranar ta kasa haqura ta isa sashen amarya, dai dai lokacin habbi ta fito da gudu Sa'eed na biye da Ita daga baya....

Duk suka ja turus ana kallon kallon... Tamkar a mafarki salima ke ganin habbi da mijin da tafi so fiye da komai a rayuwarta,

'barka da safiya anty xo ki xauna, cewar habbi tana kallonta qasa qasa...

tsananin ruďewa yasa tayi kan habbi suka fara kokawa, da kyar Sa'eed ya rabasu,

'munafuka, snatcher, azzaluma macuciya mai kwacewa mutane miji, sai da kika gama jin sirrina xaki aure min miji Wlhy baxan taba yafe maki ba, kaima baxan yafe ma ba Sa'eed ta soma kuka, basu ankaraba sai ganin kawai sukayi ta ďauki kwalbar malt dake ajiye ta jefata ga plasma t.v ,tayi ratsaratsa, duk abinda tasan mai fasuwa ne tabi tana fasawa, Sa'eed na fisgota ya ďauketa da Mari kana yajata ya fiddata gidan suka rufe...

Kamar habbi xatayi kuka haka take tsaye ganin yanda aka farfasa mata kaya, jiya jiya da kawowata,

Haquri ya soma bata anjima xaisa akawo mata duk abinda salima ta fasa, tana jin haka ta saki ranta ta rungume shi tana kissing,

Tare sukayi wanka sukayi breakfast, daďin da Sa'eed keji baya misaltuwa, bai taba samun irin Wannan kulawar ba, ta rakasa har motarsa sai da taga yabar gidan kana ta ďauki qaton icce ta nufi motar salima,
Chapter 30 · 0% Book details