← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 33

Sashe 21

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'qarya kikeyi bashi bane,
'Allah anty naganshi, yana xaune a motar can ta nuna mata da yatsa,

Iman taja motar xuwa inda ta nuna mata, ta ganshi da waya a hannunsa yana latsawa, a gabansa bindiga ce ajiye, ta juya tana kallon mutanen dana shiga ďayan shagon da bindiga a hannunsu,

ďagowar da Deedah xaiyi suka haďa ido da ita, fauxie na ganinsa tayi waving hannunta tana murmushi,

'yaya.... , iman taja motar da qarfi, hankalinsa yayi matuqar tashi ya fito daga cikin motar tuni ta fice,

Wani birki da taja sai da fauxie na faďi qasan seat, ta ciro wayarta ta Kira Suleiman haďe da gayamasa inda take, ji tayi baxata iya driving ba, qafafunta rawa suke dama gasu a kumbure, sai ta fito daga cikin motar tana kallon titi ita kanta batasan a wane hali take ciki ba,

'anty meyasa kika fito, kina jiran yaya ne, bata kula taba,
'anty kixo muje gida, nan ma bata kulataba,

Tana gurin tsaye Suleiman ya iso akan mashin, yabiya mai babur kana ya nufeta,

'gani hajiya, ta miqa masa key ďin mota,
'qarasa dani gida, ya karbi key ďin ta xagaya gidan baya ta shiga motar,

Sun fara tfy ya dubi Fauxiya sai ta wangale masa baki tana dariya shima dariya yayi mata,

'kagani mun siyo ice cream nida anty, ta nuna masa,
'eyye ashe xamu sha tare,
'ka Kira yaya ya siyoma naka yana can da bindiga a hannunsa,

Iman ta ďago ta kalleta sai taji Suleiman na faďin,
'sai kace nice ke, ni naki dai xn sha, ta fara dariya....

Suna isowa gida Iman ta fice, sulaiemn yaja hannunta sukayi bangaren baba,

'jeki ďebo kuďi kafin baba ya dawo, xnje na siyo mai insa a mashin gobe muje yawo har inda qawarki Amira,

'da gaske,
'e mana,
Ta shiga tana murmushi ta ďebo kuďin, sai ta ďauko wannan kwalbar da tagani ranar, tare da wata tukunya mai Jan kyalle akai,

Tana fitowa tabashi kuďin ya cusa aljihunsa ya rakata har gida kana ya fice yana murna,

Tana xuwa dakinta ta nufa ta ajiye kayan kana ta nufi ďakin Iman ga mamakinta sai ta sameta tana kuka sosai,

'anty meyasa kike kuka? Kuka take sosai Kamar ranta wannan dalilin ya Sanya fauxie kuka, suna haka Deedah ya shigo da qatuwar akwati a hannunsa, ya ajiyeta gefe kana ya nufi Iman jikinsa a sanyaye,

'kiyi haquri ki yafemin Iman, na Karbi laifina nagaji da boye maki,

Ta dubesa da idanunta jawur, har wani qullewa mararta keyi,

'ka dade kana cutar dani Deedah, haram nake ci nake sha nake kwanciya acikin haram, ya katseta da sauri,

'bana ciyar dake da haram Iman, tun kafin na aureki nake wannan sana'a, ta xare ido sosai tana kallonsa xuciyarta na bugawa,

'amma Wlhy duk share ďin da ake bani ban taba sanya shi acikin kuďin halal ďina ba, kingansu nan sune acikin akwati nake tarawa a yau na kawo dan ki yarda dani,

'babu wata sauran yarda tsakanina dakai Deedah, baxan iya yafe ma ba baxan iya cigaba da xama dakai ba tsawon lokutta da dama kana cutar dani, ka sake ni Deedah, ta fashe da kuka sosai,

Hankalinsa ya tashi ya juya yana kallon fauxie, ice cream take sha hankalinta baya kansu, Kukan Iman har cikin xuciyarsa yake jinsa sai ya tsinci kansa shima yana Kukan,

'Iman inayin sata ne badan na so ba, na fara ne sanadiyar ummata da bata lfy domin na siyamata magani, bayan mutuwarta na nemi aiki ban samu ba saboda banida ko Naira da xn bada a Samomin aiki, oga nas ya sanyani wannan aikin ta dalilinsa na shiga wannan harka, bayan na sami aiki na nemi na fita sukamin baraxana da rayuwata, na cigaba da xama dasu badan naso ba amma Wlhy Iman ban taba amfani da duk kuďin da Muke robbery ake rabawa ana bani nawa, kingansu duka acan, halal ďina ne a account ďina kuďin albashina, duk abinda ke gidannan da kuďi na nasiya, saboda ke tsawon watanni nan nadai na bibiyarsu nake xaunawa dake, sai na fahimci suna harin rayuwarkine suna so su kasheki saboda xn bar fashi ta dalilinki, yau ma dana bisu tsautsayine bn fita daga motar ba, Ina bibiyarsu ne saboda ke bana son Abinda xai sameki idan suka fahimci nadaina fashi, believe me Iman wallahi bana fashi yanxu na dade da shiriya tuntuni, ki yafemin Iman Kada ki rabu dani kodan yarona dake jikinki....

ta dubi cikin nata kafin ta maida kallonta garesa,
'I can't forgive you Deedah, cikin ma bana so, I hate you Deedah baxan iya xama da barawo ba, meyasa ka boyemin tuntuni .....

'please Iman, wallahi am not among them yanxu, tuntuni na tuba na daina, dan Allah karki rabu dani,

Ya tsugunna gabanta yana roqonta, ta tureshi tana kuka sai ya saketa, baxata iya xama dashi ba, ransa ya soma baci ganin yanda ya qasqantar da kanshi gareta yana roqarta yasan abinda xafi amma ya kamata ta duba masa ta yafe masa,

Kamar daga Sama taji muryar fauxie,
'anty me yaya yayi maki? suka juya suna kallonta,
'anty kiyi haquri, iman ta ďauke kanta gefe, fauxie ta matso gareta,
'anty malam yace ka xamo Mai yafiya a gurin mutane kaima a wajen Allah Mai laifine,
'kinji anty, please forgive him,
'shut up banxar yarinya, me kika sani a rayuwa, ko kin san tsawon lokacin da ake cutar dani, maxan nan guda biyu sun min illah a rayuwata, *Babana da mijina*, bama kamar Deedah dana daukeshi abokin rayuwata, ta dalilinsu na kamu da cutar hawan jini, jin daďina ragagge ne da kai Ahmed, baxan iya cigaba da xama da barawo ba ka sakeni,

Wannan kalma ta barawo tana baqanta xuciyarsa,

'gwanda xama da barawo akan xama da matsafi fatyma, tayi masa wani kallo,

'Waye matsafi Deedah?
'Oho maki.... taja guntun tsaki,
'kabani takarda ta nace,
'baxan iya sakin ki ba Iman, kiyi haquri mucigaba da rayuwarmu a tare cikin so da kulawa kamar yanda muke a ynxu, mu kula da yaronmu da xaixo bada daďewa ba,

'I can't Deedah, I hate you, kafita rayuwata, ba ruwanka dani idan ba haka ba cikin ma xn illata shi xn kashe kaina Deedah....,

Hawaye sosai ke fitowa daga Idanunsa, Ashe akwai ranar da Iman xata iya rabuwa dashi, iman xata iya gayamasa Kalamai masu xafi haka, to menene sauran jin daďin sa idan har xata iya kashe kanta saboda shi? ya dubeta,

'Am so sorry, xn fita rayuwarki kamar yanda kika buqata, inason rayuwarki da ta yarona, Ina sonki da gaske idan ke bakya sona, baxaki iya xama dani a kowane hali ba ki rufamin asiri, xn tafi na barki ki yafemin ki Kuma kulamin da cikina, Idan Kuma kinji wani abu ya sameni daga baya kece sanadi, ya juya yana sharar kwalla komai bai dauka nashi a gidan ba sai akwatin da ya shigo da Ita ta kuďi,

Fauxie ta diro xata bishi Iman ta riqeta,

Kalamansa ke mata yawo a kwakwalwa tafi kowa son mijinta, bacin raine daya mata yawa a xuciya but she truly love her husband, ta tashi da sauri tabi bayansa,

Fitowarta gidan yayi dai dai da ficewarsa daga cikin gidan cikin motarsa, ta soma kwala masa kira, Ina ya riga ya fice,

Tana tsaye bakin gate ďin hasken Mota na Haske mata jiki,

Yaja wani birki cikin tsananin tsoro da mamaki,

'Iman yake gani da ciki, yaushe tayi ciki yaushe ya girma haka, Sam bashida lbr shida Sima.......

My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina*

©Fertymerh Xarah 💞

32

*Dis page is for you Muhammad saleem & Maryam kaumi*

Hasken dana dallare fuskarta ya sanyata juya fuskarta gefe ba shakka baba bane tasani Shikadai xai iya mata haka duk gidan, tasan ma'aikatan baxasu gwada mata hakan ba,

Bai shigo ba kuma bai kashe fitilar motar ba, mamaki da kaďuwa ya sanyasa kasa motsi sai kallo yake binta dashi,

Ganin abin bamai qarewa bane sai taja qafafunta da kyar har nauyi suke mata ta koma cikin gidan,

Wayarta ta ďauka tana kiran Deedah amma yaqi ya ďauka daga baya ma sai taji ya kashe Wayar gabaki ďaya,

Hankalinta yayi matuqar tashi sai take danasanin abinda tayi masa, tana son mijinta so bana Wasa ba, tana yi masa wani irin so marar misaltuwa bataso taganshi cikin wani hali ballantana irin Wannan da taganshi ya fita a ynxu, ta duba fauxie har tayi barci sai ta gyara mata kwanciyarta haďe da cillar da tedy dake Kan gado,

Baba Kuwa da kyar ya qarasa yayi parking ya fito, da sauri ya shiga cikin gida kai tsaye ďakin tsafinsa ya nufa yana neman tedy ďin sa domin ya bata ya jewa sima da wannan sabon al'amari daya gani a tare da fatyma,

Amma Kuma sai me? Wayam babu, hankalinsa ya tashi domin baxai iya bata ba dole sai da Ita kwata kwata hankalinsa bai bashi rayuwarshi dake cikin kwalbar da tukunyar matsafarsu bata gurin ba shi dai yaga wannan tedy ďin,

Sai xufa yake yayin da babbar rigarsa tayi masa nauyi, ya cire ya cillata gefe hankalinsa tashe ya fito yana kiran Suleiman cikin ďaga murya,

Suleiman Kuwa tuni ya fice daga gidan, yaje kashe kuďin sa bashida wata damuwa bayan su,

Jin shiru ba alamarsa baba ya tara duka masu aikin gidan tun daga security masu girki, shara, wanki da guga mata da maxa dake gidan ya tambayesu Waye ya shiga ďakin bayan fitarsa,

Ba Wanda yasani hassalima ba Wanda ya gani saboda bamai xuwa bangaren sa idan ba Suleiman ba domin shine Mai Kula da wurin Kuma ba Wanda yaga shigarsa Sannan baya xaton Suleiman xai shiga wurin domin ya ďauka Suleiman nada amana ne bayada bincike kosa ido akan Abinda bai shafesa ba,

Ya tattarasu ya korasu daga falon ya cire hularsa yana firfita da Ita sai xufa yake hankalinsa a matuqar tashe tunaninsa yakasa bashi Wanda xai shiga ďakin ya ďaukar masa kaya,

Iman Kuwa sai faman juye juye take ta kasa barci jikinta na bata ba lfy ba Deedah ďin ta take gani a duk sanda ta rumtse idanuwanta, Ina ya shiga Ina yaje wane hali yake ciki meyasa bai dawo gida ba she don't know...

Daga ita har baba basu rumtsa ba kowa da saqe saqen xuciyarsa.....
Chapter 21 · 0% Book details