← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 33

Sashe 2

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Xaka sami kuďi sosai indai xaka iya shiga cikinmu, ni babban ďan ta'adda ne nayi irin Wannan rayuwar taka ta talauci da haka hr na rasa iyayena, saboda rashin kuďi gurin haihuwa matata ta rasa ranta, bansan wace irin rayuwa muke ciki a ynxu ba da masu kuďi basa taimako dan Allah, Mai kuďi daga shi sai xuri'arsa, ďan siyasa ma haka, neman aiki ynxu baxaka samu ba sai dai su bawa yan uwansu, shugabannin mu na Yanxu basa aiki kamar na da, shin miye laifin talaka? da haka na nemawa kaina aiki nakewa masu kuďi fashi, inada yara biyar duk aka sami kuďi kowa Ina bashi kason sa da haka nake gayyatar ka kashigo cikin xaka sami kuďi Kuma xakaji daďi....

da'ace mutumin ya lura da yaga xufar dake ambaliya a fuska da jikin Ahmed, yayin da gudun jini ya Katse a jikinsa, hanjin cikinsa ya dunqule guri ďaya

ďan fashi kenan xai xama, barawo Mai daukar haqqin mutane haqqin da ba nasa ba, duk wahalar nan da yayi wajen neman ilimi da kwalinsa sai ya qare a sata.... tor miye amfanin karatun da yayi? Wata xuciyar tace rayuwar mahaifiyar ka fa, kana nufin karatun yafi tane?

BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

3

Shiru yayi yana kallon mutumin sosai xuciyar sa sai bugawa take yayinda take ingixa sa akan ya amincewa mutumin ya sami kudin da xai Kula da Inna, tunda yan uwansu ma sun gujesu basa taimaka masu da komai tunda ba su da,

Baya manta sanda mahaifinsa na da rai yan uwansa kamar xasu haďiye su saboda kulawa Kuma saboda mahaifinsa mutum ne dayasan haqqin ďan uwa yake biya masu buqatocinsu, yau gashi babu ran mahaifinsa sun gujesu saboda basu da komai, mahaifiyarsa na kwance ba kuďi Kuma ba Wanda xai iya xuwa ya xauna da Ita asibitin sai shi.....

Wannan dalilin ne ya Sanya Ahmed amincewa ya karbi tayin oga nas Wanda yayi matuqar jin daďi da ya amince kai tsaye ya bashi dubu goma da address ďin inda xai same sa....

Bayan ya karbi kudin jikinsa na rawa yaje pharmacy dake nan asibitin ya siyo magani ya nufi inda mahaifiyarsa take,

Yanda ya sameta hankalinsa yayi matuqar tashi ya juya xaije ya Kira likita ta riqo rigarsa, da kyar take iya mgn

Baxan tashi ba Ahmed, buri na bai cika ba inganka yau ka xama wani mutum da duniya xata so kuma tayi alfahari dashi, kayi haquri da duk yanda rayuwa ta xoma, ka nemi halal, ka Kula da kyau kada kabari ruďin duniya da abinda ke cikinta ya ci galabarka,

Hawaye yake sosai, jikinsa na rawa hankalinsa yayi matuqar tashi da maganganun mahaifiyarsa,

Baxaki mutu ynxu ba Inna sai nayi maki gata, ya banbare hannunta da kyar ya fita da gudu neman likita,

Ko kafin su xo rai yayi halinsa, Allah ya gafartawa Inna......
*

Alhaji Abdallah mutumin xuru ne qaramar hukumar Birnin kebbi,

Babban mutum ne mai ji da kansa Wanda duniya ke damawa dashi a siyasa, shine mataimakin gwamna a Yanxu kafin ya sami matsayin da yake a yanxu sai da yayi fafatukar duniya da shige shige Wanda Dama a Yanxu idan mutum na neman cimma wani buri nasa yakan manta Allah ya kauce hanya, a taqaice sai da ya bada jinin ďaya daga cikin yaransa kafin ya sami kujerar da yake Kai a yanxu,

Ya'yan shi biyar mata biyu maxa uku sai matarsa Mami, mace mai kirki da mutunta ďan Adam..

Naxir shine babban yaron sa, sai fatyma(iman), Musa, Ismail da qaramar su Fauxiya,

Acikin yaran kaf ya fison Fatima da Fauxiya ko kaďan baya son Abinda xai tabasu, soyayyar da yake nuna masu daban ce da ta sauran yaransa.......

Kuďin sa Kuwa baa magana, yana da dimbin tarin dukiyar da yabayarda ya'yan sa uku duka maxa,

Mutuwar su tana xowa Mami a baxata, babu ciwo babu komai xaka ga kumfa na fita bakin su daga nan Kuma rai yayi halinsa, da haka ta fara rasa yaron ta Naxir...

Naxir ba qaramin mutum bane, a shekaru yabawa 26 har an nema masa mata, fatyma Kuwa a lokacin ba Mgnr aure a gabanta she is 24 karatunta ta sanyawa gaba, she want to achieve the goal, bata da buri a duniya kamar ta wayi gari yau ta ganta cikakkiyar likitar mata tana jin haushin yanda mata ke Kai matsalolinsu da sirrin jikinsu ga likita namiji,

Sanda babansu ya fara siyasa a lokacin komai ya soma sauyawa daga rayuwar gidan na rasa babban ďan gidan, sosai Mami ta shiga damuwa shi kansa Baban ya nuna damuwarsa duk da shine sila akan komai,

Sai wani lokaci da matsafin nasu ya nemi ya bada ďaya daga cikin ya'yan sa mata, sosai hankalinsa ya tashi domin a duniya ba abinda yake so kamar Fatima da Fauxiya komai xai iya akansu,

Ya qara russunawa haďe da gyara hannu jar rigar dake jikinsa ta tsafi,

Kiyi haquri shugabata xan bada yarana biyu maxa a maimakon matan Ina matuqar sonsu musamman ma Fatima Iman.......

Ta kece da wata dariya mai raxanarwa sai da gurin ya ďauka kafin tace

Sima ta amince yau da dare nake buqatar jinin Ya'ya ka,

An gama ya shugabata ya faďa yana russunawa,

Ta qara wata dariyar kafin ta juya Kan amininsa Wanda shine sanadin kawo sa gurin,

Me xaka bawa Sima gobe tayi Kari dashi labaran? Ya sunkuyar da kai cikin girmamawa...

Babu ya shugabata sai abinda kika yanke min, banda kowa ynxu a duniya duk na bayar matatace kawai ta rage...

Bana son matar ka, bana son jininta tuntuni na gayama dan haka ka nemomin jinin wani mutum ko wane irine ka kawo min a gobe,

Shikenan ya shugabata.... ta qara yin wata dariyar bayan ta nuna na kusa dashi,

Kai kuma munada labarin anyi haihuwa a gidanka jinjirin mukeso kafin ayi suna......

Da haka kowa Sima ta gaya mashi Abinda xai kawo ta Kuma cikasu da kuďi iya adadin da suke so....

Dama hakane idan har xaka shiga wannan har ka xaka wayi gari baka da kowa a duniya duk ka bayar saboda neman haram da son abin duniya ka sami kuďi, mecece ribar wannan sana'a?

Da dare duka yaran na tare da Mami, sai Kai da komawa yake naganin yanda xai ďauki rayuwar yaran biyu.....

BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah

4

Already Fauxiya tayi barci, Fatima Kuwa tana study room ta matsawa kwakwalwarta da karatu,

Musa ne da Ismail ke tare da Mami, sun jima sosai tare da Ita kafin suyi mata Sallama suka fice...

Yana xaune a falo suka fito, fridge suka buďa kowane ya ďauki yoghurt Wanda dama al'adar su ce basa kwanciya sai sun sha,

Baba Xamuje barci kayi mana addua, ya ďago yana kallon yaran bawai bayason yaransa bane son xuciya da neman duniya suka rufe masa ido, yayi matuqar tausayawa yaran,

Shikenan musa ka Kula da qaninka, Allah ya tashe ku lfy ya raba ku da sharrin mutum....

Suka ce Amin,

Ismail yace baba ni gobe baxan tsaya lesson ba ka gayawa driver yaje ya ďauke ni da sauri,

Meyasa Ismail...
Mami tace xataje dani da Fauxiya unguwa banda musa,

Yace tor shikenan xanyi masa magana, musa yace
Baba baka cika min alqawari na ba, kace xakaje dani waje nayi karatu irin anty Iman

Fatyma ai tagama karatun kaima xakaje ni xan kaika da kaina,

Yaron yayi tsalle ya rungumeshi, thank you father Ina sonka..... Jikin Baban yayi sanyi sosai da kyar ya iya rungume yaron a jikinsa kafin ya rakasu har dakinsu da kanshi, yana labe yana kallon sanda suke game suna shan yoghurt Wanda a ciki yayi siddabarun sa, basu jima ba Kuwa suka xube gurin suna kakaki kumfa na soma Fita bakinsu, yaje da sauri ya ďauke yoghurt ďin ya musanya shi da Wanda baida komai ya fice, idan xakayi masa kallon natsuwa a Wannan lokacin xaka fahimci baya cikin hayyacinsa ko kaďan....

Mami ta fito daga ďakinta Kai tsaye study room ta nufa ta sami fatyma da tulin takardu a gabanta, gefenta kofin coffee ne da take korawa akai akai...

Iman ya kamata ki riqa bawa kanki hutu ki samawa xuciyarki sauqi, wannan karatun yayi yawa haka ke kullum akan takarda....

ta ďago idanunta da kyar tana kallon mahaifiyarta idanunta sunyi jawur sosai sun nuna kalar barci,

Mami you won't understand,karatun likita is quite different da sauran karatun, kibari nan da shekara ďaya na kammala karatuna na xama cikakkiyar likita xn fara maki surgery..

Surgery? ta tambaya da mamaki tana kallonta, surgery akan me?

Tayi far da ido tana kallon ta cikin shigar wasa irin ta ya'da uwa,
Tace Mami har ma sai na gaya miki kibari lokacin yaxo xaki sani...

Mami tayi dariya tana tattara littafan dake gabanta,
Ko Alhuda huda yana samawa xuciyarsa sauqi Iman, ki tashi kije ki kwanta,

Ta tashi tana miqa, a tare suka fito suna tafe suna hira, baba na ďakinsa yana jinsu hr lokacin da yaji Faty na fadin,

Mami Ina ya'yanki ko sunyi barci bnji hayaniyar game ba,

Me yiwuwa haka ne, amma bara na dubasu, ta nufi ďakin Faty na bayanta, yana daga window yana kallonsu har suka shiga, basu jima ba ya jiyo qarar fatyma tana kiran baba... ya koma yayi kwanciyarsa kamar mai barcin gaske,

Iya ruďewa sun ruďe bama kamar Mami da ta xama mutum mutum, batasan meke faruwa akan ya'yan taba, suna haka baba ya shigo cikin yanayin barci sosai ya nuna damuwarsa hrda kuka yayi.....

Tun daga lokacin abubuwa sun soma faruwa, walwala da jin daďi sun rageshi a gidan, ga kuďi kamar me, basu taba xargin sa akan Kuďin da yanda yake kashe dukiya ba saboda sun San dan siyasa ne,

Iman da Fauxiya ne kaďai suka rage masu a ynxu duniya, yana son su fiye da xaton mai karatu haka yake ji komai xai iya dan ganin farin cikinsu....

2 years later

Siyasa ta tashi sai faman xabe ake ana campaign, baba yaje wa Sima da buqatar Wannan Karon yana son matsayinsa na mataimakin gwamna kowane mutum ne yaci gwamna a birnin kebbi yana so yaxama mataimakinsa, wani xabe mai xuwa yana so ya fito takarar shugaban qasa....

Sosai sima tayi dariya wadda tayi matuqar raxana su,

Buqatar ka xata biya Abdallah, xakaci siyasa idan har xaka bada jinin matar ka......
Chapter 2 · 0% Book details