← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 33

Sashe 11

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Naji sai anjima habbi,
'ki koreni ynxu tunda na gaya miki gasky, ta tashi sabe da jakarta ta fice bako sallama, salima na bita da kallo,

Duk Mgnr da suke akan kunnuwan Sa'eed, yasan halin salima baxata taba canxawa ba yana mamakin xuciya irin tata, yasan inda xai kamata,

Yana xaune mai aikin ta shigo da kaya a hannunta ta ajiye a gabansa ta fita, bata jima ba sai gata ďauke da ruwa da lemu, ta xauna haďe da tankwashe qafafuwanta tana xuba masa abinci a plate, shiru yayi kawai yana kallon yarinya aikin da take yafi albashin da ake bata, dole xai qara mata kuďi, ya ďauko Mai aiki saboda wanke wanke, mopping da kula da yara, sai gashi mai aikin ita ke kula da komai tun daga gidan, yaran har Mai gidan komai itace,

Tana gama xuba masa ta tashi ta fice da sauri batare da ta kallesa ba Kamar yanda matar gidan ta gargaďeta.

2day~

Tun daga ranar fauxie bata qara xuwa gurin baba ba hassalima muryarshi idan taji guduwa take ta boye bayanda Iman batayi da Ita ba, ta riga ta sanya tsoronsa a xuciyarta,

Shima baba yana tsananin nadamar Marin da yayi mata dan gashi fatyma tana xarginsa da wani abu akai, baya manta sanda taxo ta sameshi da Mgnr dan me xai Mari fauxie akan magani,

'saboda tayi min asara,
'wannan wace irin asara ce da tafi lafiyar fauxie baba?
'banason Mgnr banxa fatyma, Fauxiya ya'ta ce I have the right in mata duk abinda naga dama a duniyar nan bamai cewa dan mi saboda ni na haifeta,

'Ni xn tambayeka dan mi saboda qanwatace, ita kaďai nake da a duniyarnan, amana ce a gurina idan na Bari aka cutar da Ita gobe Allah xai iya kamani, Inaso na bata farin cikin da bata samu a gurin UWA ba, fauxie na min kallon wani bangare na rayuwarta jin daďin ta da komai,

'Ashe baki da tarbiya Iman, ni xaki xauna kina gayawa mgn haka, kina nufin bana baku farin cikin da mahaifiyarku xata baku idan tana raye ko me? Kije gaki gata indai nine sai naga bayanku...... Sosai ta buďe ido tana masa kallon mamaki da jin furucinsa shi kansa baisan ya furta ba sai a ynxu sai yayi Saurin gyara mgnrsa,

'Ina nufin kije gaki ga Fauxiya ki xame mata uwa duk abinda takeso ki mata,ki ďauki duk wani responsibility nata, na yafe maki ita kome xai same ku daga ke har ita baruwana da lamarinku,

Batare da tayi mgn ba ta fice tana kuka sosai, Kukan maraici da rashin gata a ynxu....

Tun daga lokacin ta daina xuwa gaidasa kamar yanda Yace ba ruwansa dasu haka suma ba ruwansu dashi, sai dai kallo daga nesa ko idan sun jiyo jiniyar motocinsa,

Tana xaune a falo taga jini na bin qafafunta, ba ciwon mara ba komai jini ya soma fito mata, da sauri ta nufi toilet ta duba, bleeding takeyi sosai kenan cikin xubewa xaiyi ta faďa a xuciyarta sai ga hawaye na bin kuncinta ta fito da sauri jikinta har rawa yake, tun daga Sama har qasa duk inda tabi jini ne, tana kuka ta Kira adama ta gyara gidan xataje asibiti,

Sosai masu aikin sun tausayamata, abinda suka lura da rayuwarta akwai kuďi a tare dasu amma ba kwanciyar hankali.

Tana fitowa Sa'eed na shigowa, yanda ya ganta ya sanyashi fitowa ba shiri,

Key ďin motar ta ta bashi dan batason ta bata motarsa,

'muje asibiti Sa'eed, bleeding nakeyi ka taimaka ka kaini Kada cikin ya xube Ina matuqar son sa,

Yakai Idanunsa qafafuwanta sosai ya rikice yace ta shiga tashi motar,

FMC suka nufa suna isowa ko parking bai gama ba ta fita da sauri, sai ynxu takejin ciwon mara amma bata damu ba, Sa'eed na bayanta shima hankalinsa a tashe suka nufi Gynaec,

Tayi Sa'a Dr Fulani na gurin ita ta dubata ta gaya mata cikin ya lalace ya riga ya xube wata biyu,

Wani irin kuka ta soma yi gwani ban tausayi Fulani na rarrashinta da bata baki sai dai tana mamakin yanda cikin fatyma ke xubewa akai akai bayan ko ynxu ta dubata batada matsalar komai a tare da Ita,

A Wannan lokacin sai fatyma ta yanke hukuncin xata soma planning meyiwuwa bata da rabo a duniya sai ta huta da wannan wahala da take taji da wahalar dake damunta, itama Fulani sai tabata kwarin gwiwa akan haka,

Sa'eed ya Kira Deedah ya gaya masa halin da ake ciki,

Sanda ya xo sosai xaka ga damuwa a fuskarshi, yana tsananin tausayin matarshi musamman irin kukan da take mai ratsa xuciya, daga shi har Sa'eed sai suka fice daga ďakin dan baxasu iya jure jin kukanta ba.

Dariya suke ba kakkautawa, irin dariyar da ko ina ke amsawa idan anayinta, sima da mutanenta kenan,

Burin ka ya kusa cika Abdallah idan kaci gaba da bamu jinin fatyma muna sha, muna jin daďin sa kaima kana jin daďin mu, akwai kuďi na can na jiranka a ďakin ka, ya sunkuya

Godiya nake ya shugabata, suka ďauki wata dariya....

Bayan sun dawo asibiti suna xaune a falo har salima matar Sa'eed da ya'yan su Adnan da Khadija,

Fauxie suna gefe suna Wasa da Adnan abinka da yaro bata damu ba sai dariya take tana xagaye falon ita da Adnan,

Deedah ya shigo da sallama a bayansa wata kyakyawar budurwace ta shigo,

Kallo ďaya Iman tayi masa xuciyarta na soma bugawa fal fal ko sallamar bata amsa ba ganin ynda Deedah ke rawar jiki akan yarinyar ita kuma Wacece,

Budurwar ta xauna tana gaidasu duk cikin su salima kawai na amsa, Sa'eed ma kallon mamaki yake masu, Deedah ya soma mgn

Uhm....uhm... Iman ga saudah ta xo ta gaidaki ta miki ya jiki, mgnr da ta fito bakinta da wadda yaji fauxie nayi nayi matuqar ruďashi,

'ita wacece, daga ina.... dai dai lokacin da yaji fauxie na cewa,

'Adnan ina bindigar ka muyi wasa?

'yace ni banda bindiga daddy bai siya min ba,

' Qarya kakeyi kana da Ita, wacce kaba yaya ya ajiye ma rannan.... ka tuna? kaje kace yaya yabaka bindigarka muyi Wasa.

Pherty🎤👯

Babana da mijina.....

©fertymerh Xarah 💞

20

Da kyar ya iya saita numfashin sa gurin Iman ya kawar da jinsa gurin su fauxie amma hankalinsa a matuqar tashe,

Ya kasa furta mata ko wace irin kalma, baisan yanda xai bayyanata a cikin mutane cewar wadda xai aura ce,

Ganin haka Iman ta ďauke idanuwanta akansu ta maida kallonta ga su fauxie dan samawa xuciyarta sassauci kuka ma xata iya a Wannan lokacin, mijinta ya kawo mata wata mace a gida shiyasa bai damu da bata haqqintaba saboda yana da wasu matan a waje ta sauke ajiyar xuciya, salima ta kasa haquri cos Macece Mai xafin kishin tsiya,

'ita Kuma Wannan Wacece Ahmed, dai dai lokacin fauxie ta qaraso tana faďin,

'yaya wai Adnan ka bashi bindigarsa xamuyi wasa,

'Kuje ina tashi xn ďauko masa,

'wace bindiga kuma? Cewar salima tana kallonsu,

'toy gun ce na siyo masa ranar ita take mgn cewar Deedah cikin dakewa?

'Malama ke wacece wai kinxo kin xauna gidan mutane,

Saudah ta dubeta cikin basarwa,
'ki tambayeshi mana shi da yaxo dani,

Sa'eed yace ba ruwanki salima matarsa bata tambayesa ba sai ke,

'wallahi sai na tambaya ai ni aminiyarta ce dole na tambayar mata, kayi mgn Ahmed,

Deedah ya kasa mgn ganin yanda Iman ta ďauke fuska daga gareshi yanayin fuskarta ma kesa hankalinsa daďa tashi,

Saudah tace tunda kin matsa kiji koni wacece to budurwarsa ce, yace naxo naga matarsa bata lfy,

Sa'eed na jin haka ya tashi yana kiran su Adnan ya dubi salima tashi muje gida, daga kallon yanayin sa xaka karanci bacin rai a tare da fuskarsa yasa kai ya fice,

'Amma ke Anyi wawiyar mace inda xaki biyo namiji har gidan aurensa wai kinxo gaida matarsa, kina budurwa ko kunya bakyaji koda yake ba abin mamaki bane tunda mutuncin ya riga ya xube a titi, ta dubi Iman dake sauke numfashi da kyar,

Fatyma sai kinyi a hankali fa saboda cutar xamani.... tasa kai tafice tana faďa sosai ranta ya baci,

Suna ficewa Iman ta tashi taja hannun fauxie sukayi ďakin ta,

Saman gadon fauxie ta xauna ta saki wani irin kuka mai cike da qunar xucci, fauxie tayi shiru tana kallon yayarta kafin taje ta kwanta a bayanta,

'Anty kiyi haquri, anty kiyi haquri shine kawai abinda take faďa har Deedah na shigo ďakin, yanayin da ya same su yayi matuqar tausaya masu sai yake nadamar xuwa da saudah amma bayajin xai iya fasa aurenta a yanda yake son yara ynxu ballantana saudah tace xata bashi soyayya mai cike da kulawa.....

A wanna lokacin faďa sukayi sosai dashi, borin kunya yakeyi dan me xata wulaqanta baquwarsa, itama rufe idanuwanta tayi ta Hausa da faďa sosai,

Wannan yana ďaya daga cikin tarihinta rayuwar aurensu basu taba faďa ba sai yau Kuma mai tsanani, fauxie na daga gefe tana kallonsu ta tsurawa bakin Deedah ido tana ganin ynda yakewa fatyma faďa sosai sai ta soma jin haushinsa ta qara matsawa jikin yayarta ta kwanta sosai tana kuka domin a ruďe take da sabon canjin da tagani tsakanin yayarta da yayanta, ita kuka Iman kuka ba mai rarrashin wani har ya gama fadansa yasa kai ya fice, ta rungume fauxie sosai a jikinta kamar wani xai kwace mata ita,

Ta karbi wannan jarabawar da Allah ke mata da hannu biyu tasan watarana sai labari amma ta rasa gane kan mahaifinta da mijinta me suke nufi da ita?

Tun daga lokacin daga ita har Deedah suka ďauki fushi mai tsananin gaske da junansu,

Baxai shigo gidan ba sai gab da asuba, wanka kawai xaiyi ya fice daga gidan, abinci ma ya daina ci a gidan tunda yanada saudah a ynxu,

Iman ma bata taba nemansa ba qoqarinta a ynxu na ganin ta Kula da rayuwar qanwarta Sau da ke Dama fauxie kan tambayeta ina yaya.... ina yaya,
Chapter 11 · 0% Book details