← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 33

Sashe 22

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Deedah Kuwa bayan barinsa gidan wata qatuwar takarda ya ciro daga cikin akwatin, baya mantawa Duk inda yasan yayi fashi yakan rubutu ya ajiye kuďin da oga nas ya bashi a inda suka yi fashi xaiyi alama ya rubutu ga kason da aka bashi, Allah ne shaidarsa bai taba cin kuďin ba bai Kuma taba sha'awar yin sadaka dasu baisan dalilinsa na tariyar kuďin ba haka kuma ya kasa sanyasu a account ďinsa, sai ynxu ya gane dalili wato ya maida kuďin inda ya karbosu, is too late akwai inda baxai iya xuwa ba akwai inda yayi masa nisa, the best thing for him is to seek for forgiveness Mai yiwuwa Allah xai iya yafe masa, Allah gafurun rahim ne shi mai yafiyane ako wane lokaci, sai ya soma istigfari yana Mai neman yafiya ga ubangijinsa Mai yiwuwa xai sami sauqin xuciyarsa,

A waje ya kwana cikin motarsa baya burin komawa Iman a ynxu har sai ya dawo normal, daďin sa ďaya bai taba kissa ba sai dai yayi harbi a qafa ko kuma ya tsoratar da mutum idan yayi masa gardama,

Sai da yayi sallar asuba kafin yaja motar yabar gurin, da Wannan Safiyar Deedah ya soma xuwa inda sukayi sata yana maida kuďin dai dai yanda aka bashi nasa rabon ya nemi gafara, wani gu akarba wani gu Kuma abar mishi an yafe, manyan kamfani da boutique ne kawai baije ba, yana mai tsoron bayyanar da kansa gidaje kawai yake xuwa,

Bai manta da mutumin da sukaje gidansa Wanda ya xagesu a mota ba har gidan yaje ya nemi gafararsa ya Kuma bashi kuďi sosai kafin ya dawo,

Akwai gurare da Dama inda baxai iya xuwa ba ya maida kuďin, sai ya ďauki sauran kuďin yakai gidan marayu, daga nan ya wuce station yakai kansa ga hukuma shi mai laifine,

Suka masa kallon mamaki, wannan ma da qarfin hali yake sun kasa yarda dashi mai yiwuwa wani plan ake son haďa masu basu sani ba, sai suka soma korarsa,

Ya basu address ďin su oga nass idan har basu aminceba suje xasu gasgasta yana so hukuma ta kamasu domin sun dade suna taadanci a rayuwarsu, ya basu lbrn komai, sukace yaje gasu nan xuwa,

Bayan barinsa gurin ya nufi inda su oga nass.

Bangaren Iman Kuwa, tunda Safiyar ta Waye take jinta wata iri tana suspecting haihuwace sai ta Kira Sa'eed ko xai taimaka ya kaita asibiti yace yana xuwa baya gidane,

'Anty yau baby xaixo?
'Insha Allah fauxie,
'Anty wane irin abinci xaki bashi,
'madara,
'anty kibashi chocolate irin Wannan Mai daďi,
'jeki kiramin Suleiman fauxie, ta fita da gudu bata jima ba sai gata ta dawo,
'baya nan anty,

Ta Kira number Deedah still switch off, ga Sa'eed har ynxu bai xo ba, ta ďauki kayanta na haihuwa ta sanya a mota,

'anty xn je asibiti inga baby,
'Aa idan kikaje surutun kima baxai barshi ya fito ba, kijira Suleiman idan yaxo akwai sauran kayana sai ku kaimin kinji, ta gyada Kai tana kallonta, ta shiga motar har ta tayarda motar ta juya taga fauxie tana kallonta,

'ki yafemin idan nayi maki wani laifi kinji qanwata,
'anty nima kiyafemin na yafe maki,
Iman tayi murmushi tana ďaga mata hannu itama fauxie ta ďaga mata hannu harta fice, kana ta juya anan taci Karo da baba sai safa da marwa yake a gidan kamar wani xautacce, sai a lokacin ta tuna da Abinda ta ďauko a ďakinsa da gudu tayi ďakinta, under bed ta duba suna nan ynda ta ajiye ta soma dariya xatayi Wasa da kayan tasa hannu ta janyo tukunyar da matsafarsu ce aciki ta ajiye gefe kana ta janyo kwalbar da rayuwar baba ke ciki, suna rungume a hannunta ta fito falo,

Tana saukowa Kan step a hankali gudun wani ya ganta yaje ya gayawa baba aniyarta xata maida masa wadannan sai ta boye tedy ďinsa tana Wasa da ita dan baxata maida ba,

Ta ajiye kayan a qasa taje tana leqa harabar gidan har ynxu yana tsaye bakin falonsa sai waya yake faman Kira ga abokan harkarsa na gurin sima,

Ta dawo da baya da baya ta ďauki tukunyar, kana ta ďauki kwalbar by mistake tukunyar ta faďi a hannunta qasa ta tarwatse jikinta ya ďauki rawa sosai taji tsoro shikenan idan baba ya gani sai ya daketa bata manta Marin da yayi mata ba,

Fashewar tukunyar yayi dai dai da kamawar matsafan su sima da wuta, daga sima har gunkin da suke bautawa da mutanen danaje gunta a Wannan safiyar sai da suka qone qurmus lokaci ďaya wutar ta tashi from no where kafin sima tayi wani yunquri tuni takama jikinsu, tanaji tana gani ta narke a gurin kamar ruwa rayuwarta ta qare,

Baba Kuwa Kamar yaji a jikinsa ynda tsigar jikinsa ke tashi, yana Waya kamar ance ya ďago Kuwa yaga fauxie da wannan kwalbar,

Hankalinsa ya tashi taya ta sami kwalbar?
'ke fauxie... ke tsaya...

Tana jin muryarsa ta tsorata jikinta yafara karkarwa musamman yanda ya tunkarota, ta soma gudu tana kuka a tsorace yana biye da Ita shikuma kamar mahaukaci sai ihu yake Acikin gidan Wanda ya janyo hankalin mutanen gidan garesu,

Sa'eed Kuwa da sauri ya qaraso gidan sai dai a waje yayi parking motarsa shigowarsa gidan tayi dai dai da faduwar fauxie qasa kwalbar dake hannunta ta gangara gefe ďaya ta fashe har wani hayaqi ke fita daga cikinta,

Ihu baba ya Sanya yayi kanta da duka, bugunta yake ta ko ina kamar Wanda aka aiko ga sa'ansa,

Nan take numfashinta na ďauke, bakinta da hancinta sai jini suke fitarwa, da qarfi Sa'eed yayi kansa bai duba girmansa na kasancewa dajjito ba kawai ya ďauke shi da Mari, qoqarin baba na ganin ya illata fauxie duk da bata Numfashi burinsa yaga ya kasheta da hannunsa ta mutu, Sa'eed ya fahimci haka nan take ya ďauketa ya fita da Ita da gudu har lokacin bata numfashi asibiti ya nufa da Ita,

Baba Kuwa tamkar wata Halitta ya dawo yanayinsa ya tsorata mutanen gidan, haqoransa sun xaxxago, akaifun hannunsa dana qafafunsa sun qara tsayi kamar na doki, ga wani gashi daya firfito a jikinsa tamkar wani dabba,

A gaban idon mutane yake cin Naman jikinsa, fisgar jikinsa yake yana ci sosai, wa'iya xubillah, (Allah yasa mucika da imani muyi kyakkyawan qarshe Amin)

Masu hankali da hangen nesa a gurinne suka soma yi masa addua suna tofa masa daga nesa, sai ya xube gurin ragwab, bakinsa da hancinsa sai fitar da jini suke kamar fauxie,

Nan take maxan gidan suka taru akansa aka daukesa aka sanya a mota akayi asibiti dashi,

Deedah Kuwa yana shiga gidan ya sami su oga nas kowane fuskarsa ba walwala, bai damu ba ya sami guri ya xauna,

'ance an ganka station yau mekaje yi Ahmed? Yaji tambayar oga nass daga Sama,

'ba komai naje kan wani case ne Kuma komai ya daidaita,

'bn yarda dakai ba Deedah kwanakinnan ka cnxa mana, lokaci yayi da ya kamata mu rabu dakai kaje ka huta a taka rayuwar mukuma mu cigaba da jin daďin duniyar mu,

Kafin Deedah ya ankara sai jin saukar bullet yayi a qirjinsa, ya dafe gurin yana kallon mai Harbin oga nass ne, kafin yayi yunqurin sake Harbin Deedah shima yaji an harbesa a qirji, police din dake bayan Deedah ne,

Nan take gurin ya kaure da harbe harbe (dama masu irin Wannan sana'a a haka suke qarewa wasu Kuwa suke kashe junansu da kansu, Allah ya shiryamu da zuri'armu gabaki ďaya Amin)

Police ďin sukayi nasara Wannan karon sun kashesu da Dama yayinda suka kama wasu suka sanya masu ankwa, oga nass na cikin mutanen da suka mutu,

Deedah Kuwa baisan inda kansa yake ba, numfashinsa ma da kyar yake fita, jikinsa duk jinine ga bakinsa ma ya soma fitar da jini sai suka garxaya dashi asibiti,

Iman Kuwa tun bayan xuwanta asibitin Dr Merah ya duba ta,

'yace da saura likita, amma kafin lokacin idan kina iyawa kiďan yi exercise ko kaďan ne,

Tayi murmushi dama ba naqudar takeji sosai ba, sai ta fito harabar asibitin anan ta ci Karo da Dr Deen,

Bayan sun gaisa yake tambayarta lfyr jikinta, tana gayamasa maimakon ya shiga asibitin sai ya biye mata suna exercise ďin xagayen asibitin suke a tare suna hira,

Haka xuciyarsa take mai tausayin mata ne musamman masu irin Wannan lalurar, yana tuna matarsa itama yakan sata ta xagaya Acikin gida, kasancewarsa da Iman yau yasa komai ya dawo masa sabo,

Sun xagayo kenan taga motar Sa'eed ta shigo asibitin taja ta tsaya tana kallonsa,

'Wayyo Sa'eed bai sameni gida ba shine ya biyoni har asibiti, Dr Deen ya juya yana kallon inda take kallo tana Mgnr dai dai lokacin da Sa'eed ya fito ďauke da fauxie a hannunsa,

Turus taja ta tsaya, fauxie ce meya sameta, taja ta tsaya idanunta a bude hankalinta a tashe har ya iso,

Yanda taga fuskarta a kumbure Kuma ko ina jini hankalinta yayi matuqar tashi ta fashe da wani irin kuka tana ganin Dr Deen ya karbeta yayi cikin asibiti da Ita, sai suka juya suka bi bayansa da sauri,

Lokaci ďaya aka xo da baba da Deedah asibiti, daukarta atare aka nufi emergency dasu domin suna neman ceton gaggawa,

Dr Fulani taxo ta kirata bata gayamata komai ba sai da suka shiga inda aka kwantar dasu,

Cikinta yayi mata nauyi,
'me nake gani yau ni fatyma, *Babana da mijina*, meke faruwa meya samesu haka, Waye yayi masu wannan aikin har fauxie,

Sai ta ruďe taje ga Deedah numfashinsa sama sama ne, kuka take sosai ta nufi inda mahaifinta,

Halittarsa ta tsoratata badan fuskarsa da muryarsa ba da ta qaryata Abinda idanuwanta ke gano mata,

Surutu yake agaban likitocin dake kansa, duk abinda yayi a rayuwarsa tunda ya fara neman siyasa har kawo ynxu sai da ya faďa,

Believe me Akan ruďewa musamman ma ga mai ciki Iman bata San lokacin da fitsari ke fita a jikinta ba,

'baba ya kashe mata yayyunta da qannenta, ya kashe mata mahaifiya, ya kashe mata ya'yan da take samu, ya sanyata a wani hali Acikin asibitin Wanda mutane suka soma xarginta, she can't believe this ta rufe bakinta da hannayenta duka tana kuka sosai,
Chapter 22 · 0% Book details