← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 33

Sashe 4

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harta iso gida bata da sukuni muryarsa ke mata yawo akai, ki aureni, ki aure ni....

Da kyar ta fito daga motarta, ta juya tana kallon harabar gidan birjik da securities, ina little sister ta shiga.. Oh Allah ta tuna ita Mai laifi ce a gareta yau baxata xo yimata oyoyo ba tana fushi da Ita,

Da sauri ta qarasa cikin gidan tana kiran fauxie, shiru bata amsa ba harta iso qaton falon su ga mamakinta sai ta sameta xaune akan sofa da skulbag ďinta tana ciro littafanta da alama assignment xatayi,

Ta ajiye kayanta ta qaraso inda take,
Kinaji Ina kiranki kika min banxa, is not the right thing fauxie,

Ta tunxure bakinta ta maida kanta gefe, ta xauna kusa da ita tace da kika je Skul are you not happy, kinga friends ďin ki, you play and eat together,

Ni banyi wasa ba,
Tor meyasa? Ta nuna ta da yatsa idanunta sun kawo kwalla, ta rungumeta don't cry, gobe dake xanje, kinci abinci,

Yes sister, dijeh tayi min wanka,
Yayi kyau, ta buďe littafinta tana duba class work ďinta,

Subhanallah Fauxiya me kikeyi a class har kika faďi haka, 2/5
Tayi shiru tana kallonta, sosai ta ďaure mata fuska,
Xamu bata dake, silly girl, simple questions baxaki iya amsawa ba,

Tace Anty ni ban iya ba ku.... ta katseta cikin fushi,

Shut up, ta tashi a harxuqe itama Fauxiya tabi bayanta,
'Anty kiyi haquri, koda naje nayi kuka shine banyi ba,

Har suka iso ďaki tana roqarta,
Anty kiyi haquri karki gayawa baba, ta juyo tana kallonta
Baba kike tsoro kenan, ai Kuwa xn gaya masa,

Ta soma bubbuga qafafuwanta,
Dan Allah anty baxan qara ba, I promise you.....

Da dare ta kasa barci sai juye juye take, idan ta rumtse idanuwanta kyakkyawar fuskarshi take gani, maganarsa nayi mata kururuwa a kunne.....

NI MARAYA NE KI AURENI.....

BABANA DA MIJINA

©fertymerh Xarah 💞

7

Ta rumtse idanuwanta,
Yh is true as her age ya kamata ace tana da aure yanxu, baba will be happy duk da baya mata Mgnr auren tasan yana so ne,

Duk Acikin likitocin ita kaďai ce budurwa bayan nurses da yawa sun girmeta wasu Kuma age mate ďin tane, tana da maneman aure da yawa but she don't have interest on them, ta kunna fitilar ďakin tana kallon fauxie,

Abubuwa da yawa take tunawa game da rayuwarta da qanwarta, komai suke so suna samu kuďi da jin daďi, haka komai yi masu akeyi, tun daga kan girki, wanki, shara, kula da gidan da komai ma baba ya Sanya masu yi masu, sai dai sun rasa kulawarsa basu samun Isashen lokaci daga garesa, kullum yana hanyar tafiya baya ďebe masu kewar UWA, hawaye suka sumulyo mata, ta qanqame qanwarta dole tayi aure kodan farin cikinta da qanwarta, dole tayi aure ko damuwarta xata ragu ta sami soyayyar miji tunda bata sami ta iyaye ba.......

Washe gari tare da Fauxiya suka nufi asibiti, sai tsalle take tana jin daďi, nurses ďin dana Santa suka soma murmushi,

Yau Fauxiya a asibiti, Ashe akwai rigima..
Fatyma murmushi kawai take hr suka iso office ďinta, ta ajiye Jakarta juyowar da xatayi ba Fauxiya ba dalilinta, dama tasan a rina,

Ta xauna tana duba files ďin patient ďin da xata duba na ranar, sosai ta dade akansu kafin ta gama, shiru ba alamar fauxie, ta tashi tabi bayanta inda take xato nan ta sameta office ďin Dr Merah tana xaune a gefensa da sweet a hannunta sai surutu take masa yana duba patient ďinsa, sai kayi xaton yar sa ce ta cikinsa

Bata Bari ta ganta ba ta juya da sauri ta nufi a&e,

Su biyu ne aciki shida abokinsa Sa'eed gurin aikin su ďaya a bank,

Da Sallama ta shiga idanunta sanye cikin farin glass, hannuwanta a aljihun Labcoat ďinta, sosai tayi kyau,

Suka amsa sallamar suna kallonta, bata yarda sun haďa ido ba, drip ta xubawa idanu tana tambayar ya Mai jiki,

Sa'eed ya amsa da jiki Alhamdulillah, ta maida hankalinta kan haďa masa magani,

Sa'eed ya tashi yana fadin,
Aboki is olmost tym, by 8 xn dawo, ya gyada Kai yana kallonsa kafin ya fice,

Dr. Save a life.... taji ya faďa daga inda yake kwance, kusan faďuwa ta tashi yi, batasan meke damun patient ďin ta ba, hr lokacin bata tanka ba sai ma qoqarin yaqi da xuciyarta takeyi, ta juyo haďe da miqa masa magani ya karba, ta ďauko masa swan ta bashi hr lokacin bata kallesa ba shikuma Idanunsa akanta, bayan ya gama sha, ta duba file ďin sa yana da sauran allura uku, ta dafe goshinta da hannunta.....

A duniya idan akwai abinda Deedah ya tsana allura, indai akan allura ne yana da rakin wannan, bai tsoron bindiga kamar yanda yake tsoronta..

Yana Ganin ta ďauko allura ya tashi xaune, wannan Karon fuskarsa a yamutse,

Ummi bana son allura, na roqeki karki min, ta juyo da mamaki tana kallonsa Abinda ta gani a idanuwansa ya nuna mata yes he mean it, baya son allura, batayi mamaki ba cos tasha samun case irin Wannan, tayi far da ido bayan ta cire glass ďin idonta,

Ni Kuma sai nayi ma allura, Iman not Ummi pls.... dai dai lokacin Merah ya shigo tare da Fauxiya a bayansa,

Ta juya tana kallonsa bayan ta sanardashi abinda ke faruwa, Merah ya karbi allura,

Haka mukayi fama dashi jiya, gashi namiji har namiji amma yana tsoron allura kibari xnyi masa....

So funny, ta soma dariya sosai ba kakkautawa Wanda rabonta da irin dariyar tun Mami na da rai, shi kansa Merah ta bashi mamaki bai taba xaton tana dariya haka ba, taja hannun Fauxiya suka fita,

Daga inda take xaune take jiyo rigimarsu da Ahmed Wanda da kyar da suďin goshi yayi masa suna xaune Merah ya fito,

Kinyi laifi likita, yiwa patient dariya,
Am sorry bansan yanda xnyi bane.....ya fice ta tashi ta shiga ďakin, suna haďa ido ta ďauki wata dariya harda sa hannu tana rufe bakinta, Fauxiya bata San komai ba amma sai ta taya yayarta dariya Wanda ya janyo hankalin Deedah xuwa gareta

Itama farace kamar fatyma sai dai tafi fatyma kyau sosai, ita yarinyar wacece ko yar'ta ce,nooo ai yaji jiya tace ita da qanwart..... tunaninsa ya Katse lokacin da yaji fauxie na faďin

Anty meyasa kike dariya, tayi shiru tana faďin ba komai,

Please tell me sister.... ta juyo tana kallonta cikin xare ido
Nace babu menene...
Fauxie tayi shiru tana kallonta ta juya tana faďin ki jirani Ina xuwa idan naxo ban same ki ba sai na dake ki Kuma baxan qara xuwa dake ba,

Tana jin haka ta nemi guri ta xauna,ta juya ta fice, Idanunsa akan su suna haďa ido da ita tayi Saurin ďauke kanta cikin jin tsoronsa saboda raunin dake goshinsa,

'little girl..... ta juyo tana kallonsa,
'Your name...da kyar ta iya buďa bakinta
'Fauxiya Abdallah... ya gyada kansa,
'xo kiji Fauxiya, kamar baxata je ba ta matsa kaďan a tsorace,
'how old are you? Idanunta suka yi rau kamar xatayi kuka,
'6yrs...
Ya xare ido yana kallonta da mamaki, yanayin ta ya nuna a tsorace take dashi sai ya janyota xuwa jikinsa ya ďorata akan qafafunsa, da sannu ya riqa janta da Wasa harta saki jiki sosai dashi tana dariya hrda kwantawa a jikinsa,

'Ya sunanka....
'Kice yayaaa,
'yaya xakaje dani inda mamin ka, ya girgixa kansa
'A'ah
'meyasa ?
'mamina tana duka sosai...
'to ni baxan je ba...
'kina so ki xauna dani, mu riqa wasa tare... ta gyada kai da sauri
'idan ummi taxo Kice ta aureni,
'Wacece ummi, yayi shiru kafin
'yace your sister... ta soma dariya tana kallonsa,
'ita ba Ummi sunan taba kace Anty Iman dai dai lokacin ta shigo,idanunta na sauka akansu, ta ďaure fuska tana kallon Fauxiya, yanayinta ya sanyata saukowa a jikinsa da sauri tana faďin,

Anty shine ya ďorani, Wai sunansa yaya..
'kisa takalmi kixo muje inba haka ba xn tafi na barki anan, ta sanya takalmin da sauri tana faďin,

'Anty Wai inji yaya ki aure sa, yace ku..... ta katseta cikin tsawa..
'shut up Fauxiya... tayi shiru tana kallonsa kafin ta maida kallonta gareta, da qarfi ta fisgi hannunta suka fice, tabe bakinsa kawai yayi ya maida Idanunsa ya lumshe...

BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah 💞

8

Tun bayan barin ta asibitin bata qara xiyartar ďakin da aka kwantar da shi ba, sai ma ta damqawa Dr Fulani file ďinsa,

Iya damuwa Ahmed yana ciki, he mean it yana sonta, aurenta yake son yi, duk da baisan ita ko Wacece ba amma ta kwanta masa a xuciya,

Ranar da aka sallamesa yaje nemanta, Dr Ummi.. Dr Ummi nobody knows her... ba Wanda yasan sunan Acikin likitoci, hassalima ko a nurse sai dai ummu an kaishi inda take yace ba Ita ba.....

Real name ďinta ne baxai iya faďi ba saboda nauyin sunan a bakinsa, amma ya kamaninta yake?

'Yace ita farace, doguwa Mai matsaikaicin jiki, tana da tawwadar Allah a fuska Kuma tana da qanwa Fauxiya,

Dr Umayma tayi murmushi sanin ko wacece,
'Sunanta fatyma not Ummi,
'I know doctor, sunan ne baxan iya faďa ba yana da matuqar muhimmanci a guna...
'duk da haka Ahmad, idan xaka shekara anan asibitin kana Ummi baxaka taba samun ta ba, murmushi yayi bayan ya kishingiďa....

Alhaji Abdallah abubuwa sun soma damunsa tun lokacin da matsafarsu ta nemi fatyma tayi aure suna son jariri daga gareta, sosai ya shiga tashin hankali sanin fatyma bata da wani tsayayye a ynxu,

Sanda ya tunkareta da Mgnr ya ga damuwa qarara a fuskarta Wanda ya Sanya baiji daďi ba,

'ba dan komai nakeso kiyi aure ba fatyma sai dan ni babban mutum ne ďan siyasa da mutane suke kallo da daraja, da yawa mutane sun San matata ta mutu bani da aure inada babbar ďiya kamar ki a gida xa'a soma xargin na hana maki aure,

'bayan Wannan fatyma aure daraja ne dashi, ni kaina xanji daďi idan kikayi aure Inaso nasami jikoki daga gareki, ballantana ma baxamu rabu ba xamuyi rayuwa a gida ďaya dake, wancan gidan naki ne halaq malaq aciki xaki xauna da mijinki da yaranki...... ta goge hawayen fuskarta
Chapter 4 · 0% Book details