← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 33

Sashe 16

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karka damu, ynxu da ya hau sosai yanada nasaba da halin da fauxie take ciki....

'fauxie xata sami sauqi ki kwantar da hankalinki.

Pherty novels.....

[08/03, 8:14 p.m.] Pherty🎤👯: *Babana da mijina*

©Fertymerh Xarah 💞

25

Da tunani iri iri Deedah ya kwanta a ranar, barci ya kasa daukarsa har lokacin da Iman tayi barci sai ya gyara mata kwanciyarta ya lullubeta kana ya sauko daga Saman gadon ya fito,

Da sanďa ya fice daga nasu gidan ya nufi gidan baba, ba kowa ko Motsin mutum babu sai na kukan tsuntsaye,

Batare da tunanin komai ba kai tsaye ya shiga falonsa dai dai lokacin da baba ya fito daga ďakin bautarsa da kayansa jajjaye na tsafi hannunsa ďauke da kwarya jinine aciki,

Ganin Deedah na qaramin tsoratashi yayi saura qiris kwaryar dake hannunsa ta faďi a qasa, Karo na biyu Deedah ya kamasa dumu dumu sai ya take fuskarsa bayan ya ajiye kwaryar a gefe ya juyo yana kallonsa,

'Waye ya Baka ixinin shigo min gida a Wannan lokacin har cikin falo na,

'ba neman kai nake da kaya ba ballantana na nemi ixinin shigowa wannan falon, baba ya buďe ido sosai yana kallon Deedah da mamaki, me yaron ke nufi kada dai ya rena sa ne yana son ya manta shi surukinsa ne,

Deedah yacigaba da faďin,
'naxo kan mgnr qanwata fauxiya, nasan ciwon ta baxai rasa nasaba dasa hannunka aciki ba, idan baka kyaleta ba wani abu ya sameta kasani tamkar a idon duniya ne,

'abin kunya, abin takaici da haushi yarinyar cikinka kake neman salwantar wa saboda neman duniya, har akwai abinda xaka nema a duniya najin daďi kamar kasancewarka da Iyalanka, ko kamanta haqqinsu dake kanka, idan yau ka faďi ka mutu gobe kacewa Allah me? Kana tunanin haqqinsu ma xai barka, meyasa kake son kashe su, kaji daďi har Allah yayi ma kyauta da yaran, ni shekarata uku da aure matata na samun ciki yana xubewa, ina son yara Kuma still nake xaune da Ita cikin qauna da aminci,

Baba ya nuna sa da yatsa,
'kashiga taitayinka Ahmed, kafita daga idona ba ruwanka da iyalina,

'inada ruwa dasu kasancewar nike riqonsu suna min kallon miji, yaya kuma uba, wallahi idan baka cire muguntarka akan su ba, *Ni Ahmed Deedah xan xama ajalinka*, I will not care da kai ko waye, you are nothing to me, idan har fauxie da fatyma ba ya'yan ka bane don't ever call me your inlaw ko kuma kariqa min kallon suruki,am not...... ya faďa cikin tsawa yana nunasa da yatsa daga yanayinsa xaka karanci bacin rai sosai a fuskarsa,

'kafin ka xama ajalina ni xn xama ajalinka Deedah, kana raye kana gani xn kashe matarka da qanwarka kafin na kasheka Kuma kafin nan sai na wulaqantaku a duniya na toxartaku yanda kowa xai tsaneku, na rasa matata da Ya'ya na maxa ballantana waďanna mata, *Ni na kashe su da hannuna*,ya faďa cikin tsawa cikin subutal baki,

'kai ka kashe su Alhaji Abdallah, har kake ikirari da wannan, Subhanallah....jikinsa na soma rawa,

'na rasa matata na haqura ballantana su, tunda kayi gigin shigo rayuwata sai na kashe ka na kashe fauxie na kashe fatyma......... kai yaji muryar Deedah tare da Kukan harbin bindiga,

Deedah ne riqe da bindiga ya harba kwaryar dake ajiye a gefe kana ya nuna sa da Ita Idanunsa jawur,

Kukan Harbin bindigar ya tayar da Iman daga barcin da take, ta duba gefe ba Deedah gabanta yayi matuqar faďuwa ta sauko da sauri tana kiran sunansa a hankali,

'shoot me Deedah idan kana tunanin bullet xai iya shiga jikina, ko kana xaton a banxa nake xaune, you can't kill me sai dai ni na kashe ka, get out of my house,

'I promise you ni Deedah na ďauki alqawarin baxaka iya cutar da kowane daga cikin mu, kana nan xaka ga qarshenka haqqin Waďanda ka kashe ma baxai barka ba nima baxan Barka ba, for now danasan kowaye nasan mugun abun da ka aikata sai kayi danasanin sanina a rayuwarka, ta cikin ruwan sanyi slow poison xn xamema Kuma batare da fatyma ta sani ba,

'ka iya bakinka Deedah akaina, a ynxu xn iya nakasaka kaxama abin kwatance a gurin su....

Hankalin fatyma tayi matuqar tashi, tana sanye da hijab ta fito daga gidan, taji Kukan bindiga a Ina ne, ina Deedah ya shiga a Wannan daren bayan yayi mata alqawari baxai qara fitar dare ba,

Tana tsaye gurin taganshi ya fito gidan baba, a yanda ta lura kuka yakeyi taga yana share hawayen fuskarsa har kamar baya kallon gabansa, ta maida kallonta gidan baban tana ganin inuwarsa a tsaye ta window tor meya hadasa da Deedah, yaushe ma Deedah yaje can kuma Kukan miye Deedah keyi, ta juya tana kallon inda Deedah yake wayam babusa babu alamarsa ya fice daga gidan, ina ya nufa?

Da sauri taje bakin gate tana dubawa ko inuwarsa babu hankalinta yayi matuqar tashi, kada dai baba ya kori Deedah ne daga gidan, har xataje inda baban sai ta fasa ta fito nan bakin gate ta xauna tana jiran Deedah acikin wannan daren babu tsoro a xuciyarta burinta taga mijinta taji dalilin kukansa.
[08/03, 10:01 p.m.] Pherty🎤👯: *

Deedah Kuwa tafiya yake yana tunanin maganganun baba, kuka yake sosai bai damu da inda xaije a wannan daren da nisan tfyr da xaiyiba,

Sai ynxu yake regretting rayuwarsa kasancewarsa ďan fashi, he loves fatyma, yana qaunarta komai xai iya akanta,yana son kareta da qanwarta ga hannun axxalumin mahaifinsu, yana son basu kulawa da farin cikin da suka rasa gun uwa da uba, yana son xame masu uwa ba uba ba......

Tafiya yayi sosai acikin wannan daren kafin ya iso gidan oga nas, qofar ya soma bugawa ahankali, duk yaran dake gidan suka tashi da sauri kowane da bindiga a hannunsa haka shima oga nas xaune da qatuwar bindiga a hannunsa yana kallon qofar da Deedah ke bugawa a tunaninsu hari aka kawo masu,

Mutum ďaya ya buďe qofar tare da nuna Deedah, suna ganinsa suka ajiye bindigoginsu suka koma suka xauna,

Kai tsaye inda oga nas ya nufa suka sami guri suka kebe dan yayi mamakin xuwan Deedah haka,

'kayi haquri idan na batama a tsawon xaman da mukayi da kai, daga yau nadaina fashi...... Dariya sosai oga nas keyi har yaransa na jiyosa yana kallon Deedah,

'ta yaro mai take bata qarko, ai baka isaba, idan kaga kabar wannan sana'a to ka mutu acikintane, inaaaa waye kai,

Deedah ya murtuqe fuska,
'na kasance da kai tsawon shekara uku ina yima aiki, bn taba nuna gaxawata akan kaba, ina shiga haqqin matata, idan bata yafemin ba Allah baxai barni da haqqinta ba, nagane wannan sana'a bamai kyau bace agareni da kai Ina roqonka kaima ka shiryu kamar yanda Allah ya shiryani kadawo hanya kadaina fashi,

'saboda matarka xaka bar wannan aikin, to ai kamar baraxanace ga rayuwarta, nasan ta nasan asibitin da take aiki acan ma xn iya samunta na ďauke ranta da alburushi Kaga idan ta mutu ai ba batun haqqinta dake kanka,

Sosai Deedah ya tsorata da Kalaman oga nas, yasan wayeshi yasan abinda xai iya da Wanda baxai iyaba, wannan qaramin aikinsane dole ta ruwan sanyi xai biyo masa idan yana son suyi rabuwar arxiki sai yayi shiru yana kallonsa,

'idan kanason kasancewa da matarka lfy ka xauna dani, shekarun baya musu bai taba hadani dakaiba karka Bari mu somayi dakai Deedah,

Deedah ya tashi ya fice ransa a bace batare da yayi mgn ba, oga ya bisa da kallo Deedah nason Wasa dani idan yayi sake sai in kashe sa dashi har matar tasa....

Koda Deedah ya dawo yasami Iman xaune bakin gate tana jiransa, tambayar duniya tayi masa yaqi ya gayamata komai sai kuka da yake har wannan lokacin, ynxu shida iyalinsa suna tsaka mai wuya,

Kukansa ya daďa tayar da Nata hankalin itama sai ta tsinci kanta cikin tayasa Kukan, a Wannan ranar daga shi har ita bawanda ya rumtsa sai juye juye da suke faman yi,

Washe gari har sukayi shirinsu bamai walwala a fuska breakfast ma basuyi ba suka fice kowa ya nufi gurin aikinsa,

Tana office ďinta xaune tana tunanin idan ta tashi xataje ta duba fauxie sai ga Deedah ya shigo jikinsa a sanyaye,

Ta dubi agogo to ten ynxu, ta maida dubanta garesa bayan ya xauna farar takarda ya miqa mata idanunsa jawur kamar xaiyi kuka,

Jikinta na rawa ta karba kada Deedah ya saketa ne, da kyar ta warware tana dubawa, ta barin aiki ce.. ...ta ďago da sauri tana kallonsa,

Wane aiki Deedah?

'farin cikin ki shine nawa Iman, I promise to change, inason kasancewa dake kamar yanda kike so nabaki farin ciki irin wace mata ke buqata a gurin mijinta shiyasa na bar aikina na banki a yau, are you happy Iman?

'happy with what Deedah? Ta faďa da tsananin mamaki tana kallonsa ido a buďe,

'why xaka bar aikinka saboda ni, ni nace kabar aikinka, tell me Deedah idan Baka aiki what did you want to do? Gida xaka xauna ni nafito aiki or what, akwai abinda ke faruwa tun jiya kaqi ka sanardani, pls tell me miye damuwarka Deedah?

Ya xare baqin glass ďin idonsa, sai a lokacin ta lura da yanda idanunsa sukayi jawur da alama yasha kuka, nan da nan hankalinta na tashi idanunta suka kawo kwallah,

'ba haka nake nufi ba Deedah, bnce kabar aikin ka saboda ni ba, training dakace na dare kanayi nace Kabari, fitar dare nace kadaina Deedah ba aikinka ba.....

Pherty novels

*Babana da mijina.....*

©Fertymerh Xarah 💞

26

Yayi shiru kawai yana kallonta, baisan yanda xai gayamata fitar dare baxata yiwu ya daina ba saboda abinda oga nas ya faďa masa a daren jiya,

'Naga you have not sign it, so baxaka bar aikin ba, ta yage paper into pieces kana ta xuba a dustbin, ta dubesa,

'kaje gurin aikinka tunda bnda muhimmanci da xaka gayamin damuwar ka, jiya naganka ka fito gidan baba kana kuka, meyasa? Meya haďa ka dashi? Me ya kaika gidanshi bayan na gayama abinda ke faruwa ynxu, kai tsaye ya bata amsa,

'saboda lfyr fauxie naje, tayi masa wani irin kallo,

'ban fahimceka ba, miye hadinsa da lfyrta mutumin da bai damu da Ita ba,
Chapter 16 · 0% Book details