← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 33

Sashe 23

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr Merah kansa jikinsa yayi sanyi sai yaji baxai iya taimakawa baba ba, yayi mummunan abu a rayuwarsa Wanda Allah kaďai xai iya yafe masa tabbas baba baida imani da tausayi tunda har xai iya sanya iyalinsa a Wannan hali, xai iya sadaukar da rayuwar iyalinsa saboda dukiya da duniya to ynxu me gari ya waya, mecece ribar da ya samu a duniyar? Ina dukiyar daya tara yake tinqaho da Ita, ina sima da yake alfahari da Ita yake bauta mata Waye xai cecesa a ynxu?

Dr Merah ya girgixa kansa shida sauran likitocin suka rufawa Deedah baya, na ganin sun cire bullet ďin jikinsa sun ceto rayuwarsa,

Hankalinta baya jikinta, fauxie take gani, ga baba ga Deedah, tana ji tana ganin yanda baba ke fisgar Naman jikinsa ci yake kamar wani dabba yana faďin Duk abinda yayi a rayuwarsa,

Tanaji tana ganin yanda yake shure shuren mutuwa, tana ganin lokacin da numfashinsa na tsaya cak ya mutu, tana ganin ynda fatar jikinsa ke fita daga jikinsa tana yin wata Kala baqiqirin,

Ta fashe da wani irin kuka mai tsananin gaske wannan wace irin rayuwace take fuskanta,

Muryar Deedah takeji yana kiran sunanta sai ta nufesa da sauri lokacin an gama cire masa bullet din jikinsa,

Dr Merah da Bakori baxasu jure ganin halin da Salihar mace take ciki ba a ynxu sai suka fice da sauri suna hawaye cikin tausayamata, itama Fulani kuka take sosai ta fita,

Iman ta faďa jikinsa duk jini,
'ni nasa ka a Wannan halin, kafita kana fushi dani dama kace kome ya sameka nice sanadi, ka yafe min Deedah, Ina sonka, baba ya mutu karka mutu ka barni Deedah, fauxie na can itama xata mutu, idan na rasa ka da fauxie my life will be useful please stay with me Ahmed, (muryarta harta dishe saboda kuka, ga jikinta har lokacin bai daina rawa ba, a rude take Kamar wata xautacciya, sai faman rungumarsa take tana sumbatarsa,

Shima qanqameta yayi sosai a jikinsa yana tayata kuka,

'ki yafemin Iman na kasance mai laifi a gareki, na cutar da rayuwarki haqqinki ne ya kamani, ki yafemin,

Ta ďago tana kallonsa tana share hawayen fuskarsa,

'burina a ynxu ka tashi, Dan Allah karka mutu kabarni, karka mutu Deedah, yaron mu xaixo a yau, karka maidashi MARAYA, ka tausayawa rayuwarta, banda kowa bayan kai da fauxie a ynxu.......tayi shiru sakamakon jin ynda numfashinsa ke fita, tanajin bakinsa na motsi da alama kalmar shahada yake, ta tashi a ruďe ta janyo oxygen xata sanya masa, xaninta har ya kwance a gurin under wear ne kawai a jikinta bata damu ba,

'please Deedah, don't..... karka tafi please,

Ta taba shi baya Numfashi,

'No Deedah will not die, Deedah baxai mutu yabarni ba, Deedah I know suma kayi ka tashi please, ta soma jijjigashi ta dubi gawar mahaifinta kafin ta maida kallonta garesa,

*BABANA DA MIJINA* baxasu mutu su barni ba, *babana da mijina* basuxo duniya a tare ba baxasu je su barni ba, *babana da mijina* suka ďai nake da aduniyarnan they can't die at the same time su barni,

Jin abu nabin qafafuwanta yasa tayi Saurin dubawa, jinine ke xubowa daga qasanta, wani irin ciwon mara na taso mata lokaci ďaya, qafafuwanta suka riqe.......

My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina*

©Fertymerh Xarah 💞

*Dis page goes to masoyan babana da mijina, tnkuuuu ol for your love and care, Pherty loves you more😘*

33

Har lokacin bakinta yaqi rufuwa, Deedah take kira kamar ranta,

Nan ta durqushe qasa riqe da mararta,
Tana haka sai ga likitocin sun shigo,

Ganin yanayinta sukayo kanta ,numfashinta na fita da sauri da sauri kamar xai ďauke,

Dr Fulani da Dr Merah suka riqata ta tashi, suka ďorata akan sick bed ,

Da sauri Dr Deen yaja gadon sukayi waje da ita,

Fauxie a ruďe ta farfado, sai kuka take sosai tana kiran anty, taqi yarda kowa ya tabata daga cikin nurse ďin saboda a firgice take,

Sa'eed ne a waje tsare da Ita baisan abinda ke faruwa game dasu Deedah ba, yana xaune yajiyo kukan fauxie a inda aka kwantar da ita, ya tashi da sauri ya shiga ďakin,

Tana xaune akan gadon asibiti, idanunta a rufe take Kukan tana weaving hannunta sai faďi take,

'don't touch me..... don't touch me,

Ta soma qoqarin saukowa akan gadon ga drip ana sanya mata,

Da sauri yaje ya riqata, tana ganinsa ta qanqame sa yayi Saurin riqa hannun da ake sanya mata drip,

'yaya ka kaini inda anty, baba ya dakeni ka ramamin,

'ki tsaya da kyau karkiji ciwo, kinga ana qara maki ruwa,

Tabi hannunta da kallo kafin ta maida dubanta garesa,

'yaya ka kaini inda anty, ni ka kaini inda anty... ta cigaba da kuka tana son saukowa Saman gadon,

'Bari acire mata drip ďin tunda qanwar Dr fatyma ce itama xata iya Kula da Ita,

Suka cire mata drip ďin, yana rungume da Ita a qirjinsa suka fito, idanunta sunyi jawur ga fuskar ta kumbura, gefen idanunta yayi ja daga ciki baqaramin duka yayi mata ba, sai jikinta yayi xafi rau, yanda ta qanqameshi ma ajikinsa abin tausayi ne,

Suna xuwa office ďin Iman bata nan ko Jakarta babu aciki,

'fauxie anty batanan Kinsan inda take xuwa,

Ta gyada Kai tana kallonsa, ya rufe office ďin suka fito,

Consultant suka nufa nan ma bata nan ba likita ko ďaya,

Tana ganin haka ta boye fuskarta a qirjinsa tana kuka,

'yaya ka kaini inda anty,
'Ina xnga anty ynxu fauxie, ai bata gida kuma, Ina ne take xuwa karban haihuwa kin sani? Ta gyada Kai da sauri tana goge hawayen fuskarta,

Tana nuna masa suka iso labour room anan suka ci Karo da Dr Deen sai safa da marwa yake a bakin qofar ďakin sai kace matarsace ke labour.

Yana ganinsu ya qaraso cikin mamaki,

'meyasa ka fito da Ita, bakaga halin da take ciki bane?

Fauxie naganinsa ta qanqame Sa'eed bataso ya karbeta,

'Dr fatyma muke nema tana kuka sai ta ganta ne,

'batada lafiya haihuwa xatayi,

Gaban Sa'eed ya faďi, yana sauko da fauxie jikinsa taqi sauka, baisan bata lfy ba sam, meyiwuwa wannan dalilin ne ya sanya ta kirashi ya kaita asibiti,

Sam baiji daďi ba, sai ya ciro wayarsa da ďayan hannunsa a aljihunsa yana dialling number Deedah, is switched off, ya maida wayar aljihun cikin jin haushin rashin samun Deedah,

Ya dubi Dr Deen sai yaga duk ya damu sosai ko miye dalilinsa na damuwa da halin da Iman take ciki, nan take yaji wani abu ya taso ya tokare qirjinsa musamman daya qare masa kallo kyakkyawan gaske ne da alama yana da jini da Shuwa Arab, ko sumar kansa baqa ce wulik a kwance,

Dr Deen ya dubesa yana faďin,
'Waye yayiwa fauxie irin Wannan duka?

Sa'eed yaja dogon Numfashi yana faďin mahaifinta ne,

'metayi masa haka?
'shine ban sani ba nima, na sameshi yana dukanta ne,

Dr Deen yaja numfashi wannan mutumin bashida imani, ya tsanesa tun lokacin da yaji yana wannan surutun kan abinda ya aikata a rayuwarsa, Allah wadarai ga mai hali irin nasa,

'amma kai yayan Iman ne?
'no abokin mijinta,
'kasan Baban ya rasu a ynxu, yana emergency aka kawoshi,

Wata irin faďuwar gaba ta riskesa saura qiris fauxie ta faďi hannunsa ai kuwa ta qanqameshi,

'ya mutu fa kace, Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un,

Dai dai lokacin da Dr Fulani ta fito ďauke da jinjiri a hannunta sai kuka yake tsalawa, lafiyayyen yaro dashi sak Deedah, kallo ďaya xakayi masa ka gane yaron Deedah ne ba inda ya barshi ta ko ina,

Da sauri Sa'eed ya ajiye fauxie a tare shida Dr Deen suka nufi Fulani sai dai Deen ya rigashi karban yaron,

Kukan da Fulani keyi shike ďaga hankalinsu, suka dubeta kuka take sosai,

'Ina Iman? Sa'eed ya tambaya Idanunsa akan ta,

Iman jikinta yayi tsanani sai suma takeyi tun ďaxu,

Jikinsu na soma karkarwa, fauxie ta qaraso tana kallon jaririn, farin ciki xaka gani bayyane a fuskarta,

'yaya wannan baby anty ne? ya gyada kai yana kallonta,

Tayi cikin ďakin da sauri, alokacin Iman ta sami barci,

Dr Merah yayi ajiyar xuciya cike da tausayamata yana kallonta, haka shima Dr Bakori halin da Iman take ciki ko kuka xaka iya yi mata,

Tana ganin Merah taje ta riqa hannunsa,

'uncle anty ta haifi baby, yana can inda yaya, Merah ya juyo yana kallonta fuskarta da yagani sai da gabansa nayi tsananin bugawa, ya buďe idanu sosai yana kallonta,

'accident ne kome, me yajimiki ciwo haka a fuska? Tayi rau rau da idanu ta qara riqa hannunsa,

'baba ne ya dakeni, xaka ramamin,

'Ya salam lallai ba axxalumi irin Wannan mutumin, dubi fuskarta Bakori wannan yarinya xaiwa irin wannan duka haka,

'kabari kawai Merah amma yarannan sunga rayuwa bama kamar fatyma dubi ynda ta koma fisabilillah, basuyi dacen uba ba kam,

Suka fito a tare,
'Iman fa?
'ta sami barci,

Suka nufi emergency harda Sa'eed da fauxie, Fulani Kuwa ta wuce da jaririn a hannunta sai kuka yaron yake sosai,

Sa'eed yaga gawar baba harda fauxie Kuma bata raxana ba batama gane baba bane tana dai kallonsa ne kawai,

Dr Bakori ya dubi Merah,
'likita xo kagani kamar Ahmed ďin baya Numfashi,

Sukayi kansa da sauri har Dr Deen sai a lokacin Sa'eed ya lura da Wanda ke kwance,

Deedah, meya sami Deedah ya qarasa da sauri, tabbas shine jikinsa duk jini,

Iya ruďewa Sa'eed ya rude musamman da yaga Merah yaja farin kyalle ya rufe Deedah da shi,

'Deedah is dead Allah ya jiqansa ya gafartamasa shine abinda Merah ke faďi yana sharar kwallah a fakaice, ya tsorata da mutuwar Deedah yana tuna xamansa dashi sanadiyar Iman yasan irin alaqar dake tsakaninsa da Iman, yasan irin son da suke ma juna tabbas Iman tayi babban rashi, ba uba ba miji a irin Wannan lokacin da suke tsananin buqatar taimako tunda basu da uwa,

Inaji tun da Merah ke asibitin bai taba kuka ba sai wannan lokacin, duk dauriyarsa a yau ya kasa yaja da baya yana sharar kwalla baxai iyaba jikinsa har rawa yake tunanin halin da Iman xata kasance yakeyi,

Sa'eed ma baisan sanda kuka ya xo masa ba, abokinsa koma ince amininsa.....
Chapter 23 · 0% Book details