← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 33

Sashe 5

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'na fahimceka babana, abinda kake so Inaso dan na farantama kamar ynda kake min, nayi ma alqawari xn fitar da miji Acikin kwanankinan, ya faďaďa murmushinsa cikin jin daďi ya soma sanya mata albarka....

Bayan tafiyarta ya faďa cikin tunani, shikenan rayuwar yar'sa ta shiga cikin hatsari kenan, ita baxata taba haihuwa ba Kamar ynda sima ta faďa duk tayi ciki xasu ďauke yaron da haka xai cimma burinsa na xama shugaban qasa, hawaye suka xubo wannan wace irin rayuwace.....

Bayan barinta gurin ya shiga cikin tsananin tashin hankali, batasan wa xata fitar ba tsakanin manemanta, gwargwado kowa nayi mata soyayyar gsky sai dai batasan meyasa xuciyarta tafi karkata da Ahmed ba, a kullum sai yaje asibiti ya ganta kafin yaje gun aiki, har nan gida yake xuwa su dade tare da Fauxiya, akwai abubuwa da yawa data duba Wanda yasa ta xabi Ahmed a matsayin mijin aurenta,

He is happy too sanda yaji umminsa ta amince xata aure sa,

Cikin qanqanin lokaci soyayyarsu tayi nisa sukayi matuqar shaquwa da juna, baba ya aminta dashi bayan dogon bincike da akayi akansa wurin aiki, basu gane komai ba kasancewar abokansa na hulda daban, na gurin aiki daban sai suka bashi shaidar gsky....

Bayan auren su ne abubuwa suka soma yi mata yawa tun daga kan mahaifinta da mijinta,

Mahaifinta baxata Kai Kukan mijinta ya duba mata ba saboda ba maxauna bane, idan ma yana gari tor baxata ganshi ba sai cikin dare akwai wani ďakinsa da yake shiga Wanda ba Wanda ya taba shiga acikinsa, idan yana ciki ba Wanda ya isa ya shiga haka ma baxai fito daga ciki ba sai cikin dare da jajjayen kaya wani sa'in ma da abokansa suke shiga,

Mijinta Kuma idan ya fita aiki tun safe baya dawowa sai marece, daga nan xaisa kai ya fice baxai dawo ba sai cikin dare Wai yaje training ďin kwallo, can you imagine?

Sau biyu Ina samun ciki yana xubewa Wanda na rasa dalilin haka a matsayina na likita, nayi bincike iya bincike na kasa samun dalili komai nawa normal, Inaso na sami babana Kan Mgnr koxai taimakamin da wani abu amma baxai saurareni ba cos he is busy, mijina ma yakan nuna damuwarsa idan ya xube bayan kwana biyu kuma shikenan xai bar mgnr,ban San waxan kaiwa kukana ba,waxan gayawa damuwata ya taimakeni da shawara kodan mijina...

Na kasa samun soyayyar mijina, ba kulawa kullum busy busy shine maganarsa a duk lokacin danayi masa qorafi, na kasa sabawa da wannan hali na *babana da mijina* Kuma ban taba xarginsu ba ko bincike akansu, duk da Allah s.w.a yace LA TAJASSASU
WALA YAGTABBA ADUKUM BAADAD kada kuyi
bincike kuma kada sashenku yariqa cin wani
sashe ma'ana kada wasu mutane su xauna
gulmar wasu mutane.....

Shine Asalin labarin.........

BABANA DA MIJINA

©Fertymerh Xarah 💞

9

Dawowa daga labari ~~~

Tafito daga toilet bayan ta ďauro arwalla, inda yake ma bata kalla ba ta sanya hijab ďinta ta fara sallah,

Deedah na daga kwance yana kallonta sai ya sami kansa da saukowa ya shiga toilet yayi arwalla ya bi ta...

Bayan wani lokaci sun gama ta tashi batare da ta cire hijab ďin ba taje ta kwanta haďe da juya masa baya, jikinsa a sanyaye ya tashi yayi light off yabi bayanta ya kwanta haďe da juyo da Ita, she is crying....

'why Iman, meke faruwa? Ko motsi batayi ba illa hawaye dake qara xuba a idanuwanta... Ya cire mata hijabin haďe da qanqameta,

'I hurt my Iman, kiyi haquri akan Wanda kike,i hurt you and I will change, I promise to change Iman ya qara matseta jikinsa, har lokacin bata tanka ba illa qoqarin kwace jikinta da take yi,

Ya tashi xaune yana kallonta,
'why ol dis...., me Kuma nayi Yanxu, nayi tunanin mun gama mgn dake tun a falo, ta tashi tana kallonsa sai Kuma taji ta kasa furta masa komai saboda bacin rai da damuwa, he knows it yasan damuwarta duk baxai wuce fitar dare da rashin bata haqqinta ba, tor ya xaiyi shi kansa a ynxu baya so yana nadamar xama barawo bayan ga aikinsa, idan yayi yunqurin barin aikin oga nas xai ďauki mummunan mataki akansa kamar yanda ya faďa,

Kallonta yake yana observing da ido da xuciya, gaba ďaya yanayinta ya sauya ya nuna wata mace dake axabtuwa da soyayya da sha'awa Mai yawa,

Amma kawaicinta da kau da kai ya rinjayi komai, tana haquri dashi shi kansa ya Shaida, ba kowace mace xata xauna da miji haka ba shiyasa yake qara son ta, ya riqo hannunta Idanunsa cikin nata,

Baxan gaji da baki haquri ba, ki yafemin Iman, xnyi qoqari na rage fitar I promise you.....

*

Washe gari bayan ta tashi daga barci tayi miqa a hankali tare da koro addua,
_Alhamdulillahil lazee ahyana ba'adama amatana wa ilaihir nushour,_ ta miqa hannu side ďin Ahmed taji sa wayam, ta buďe idanuwanta,
She is late, da sauri ta diro ta faďa toilet inda ta same sa ciki yana wanka,

A tare suka fito kowane ďaure da towel, ita iya cinyoyinta shi Kuma iya qugunsa, jikine dashi na Manya Kuma qasaitattun maza,

dogo ne sosai Mai kyau sura ta ko'ina, a tare suke shirinsu, qoqarinsu kada suyi lattin fita,

Wardrobe ta buďe ta ďauko mashi baqaqen Spanish suit Mai haďe da farin tie, ta ajiye masa akan gado kana ta soma shirinta cikin riga da zani na Atampha ta ďora labcoat akai da ďan qaramin gyale tayi rolling, idanunta sanye da farin glass, lokaci ďaya suka gama shirinsu, yaja dogon hancinta in appreciation ďin irin kulawar da take mishi,

'kinyi kyau dear Allah ya barmin ke, murmushi tayi haďe da manna mishi kyakkyawar sumba a qirji ya qara rungumeta,

Yana riqe da hannunta suka sauko step dai dai lokacin da Fauxiya da mai Kula da Ita suka fito tana ďauke da qatuwar school bag ďin ta, murmushi tayi lokacin da suka haďa ido da Ahmed,

'morning sister...
taje da gudu ta rungumeshi tana fadin
'morning yaya... ya ďauke ta yana murmushi haďe da Jan hancinta,
'morning my baby....

Dijeh ta gaidasu kana tayi waje da jakar Fauxiya,

A tare suka xauna akan dining table, Fauxiya baxata tsaya guri ďaya ba, idan taci na wannan ta dawo taci na wannan da haka hr suka kammala suka fito su uku a tare,

Driver na jiran Fauxiya kai tsaye ta shiga motar tana ďaga masu hannu suma suna mata bye bye, suka kalli juna haďe da yin murmushi ta shiga motar ta shima ya shiga tasa,

Tana gaba yana biye da Ita hr suka xo FMC birnin kebbi, sai da yaga shigarta kana ya juya tasa motar xuwa first bank dama kullum sai ya rakata yaga shigarta asibiti yake tafiyarshi.

BABANA DA MIJINA

©fertymerh Xarah 💞

10

Alhaji Abdallah xaune a qasaitaccen falon sa duk abin duniya ya dame sa ya rasa inda xai tsoma ransa yaji daďi,

Sau biyu yana ďaukar cikinta yana bayarwa ga matsafarsu Gashi wani bincike ya nuna Iman tana ďauke da wani cikin Wanda daga ita hr Ahmed basu San dashi ba,

Sima ta nuna tana son cikin, tabbas Wannan ma sai ya xube, shin haka rayuwar yar'sa xata kasance bata haihuwa da tasami ciki ya xubar? Yayi wa kansa wannan tambayar,

'Nooooooo ya faďa a hankali gudun securities ďinsa su jiyosa, Idanunsa sunyi jawur har jijiyoyin kansa sun fito goshinsa raďau raďau,

Yana son Fatyma yana tsoron wani abu ya sameta musamman a mahaifarta amma ya xaiyi mecece mafita?

Yayi shiru Idanunsa suna fitar da kwalla lokacin dayaji muryar sima na faďin,
'cikin mukeso Kuma dole abamu idan ba haka xamu ďauki rayuwarta gaba ki ďaya mu baka dukiya da Abinda kake so na duniya..... Aka kyalkyace da dariya, yayi firgigit daga tunanin da yake yana kallon falon dariyarta ce kawai yakeji ta ko ina......,

*

Fitowar ta kenan daga ďakin haihuwa, yau a gajiye take sosai tunda taxo bata xauna ba, ga Jiri da Xaxxabi da take ji Wanda baida nasaba da yunwa anata tunanin kenan,

Ta sami gu ta xauna inda ta sami Dr Fulani, ta dafe goshinta da hannuwanta biyu,

Successful doctor..... yanda suke kiranta idan suna tsokanarta cos da wuya ta karbi haihuwa da hannunta yaron ya mutu ko uwar sabanin wasu likitocin da har jima yaro sukeyi gurin haihuwa, a yanda take a natse haka ma take aikinta a natse shiyasa nurses da yawa suke son aiki da Ita, ba ďaure fuska ko Wulaqanci kowa faram faram take dashi bama kamar patient ďin,

'ya akayi Dr fatyma...cewar Fulani tana kallonta,

Ta ďan ja guntun tsaki kafin ta janye hannunta a goshinta,
'bansan meke damuna ba yunwa ko gajiya... Fulani tace
'harda damuwa fatyma, tor ya xakiyi da yanda Allah ya tsara miki rayuwarki idan lokaci yayi xaki ganki kin haihuwa kidaina sa damuwa a xuciyarki, Iman ta girgixa kanta kafin kace me hawaye sun soma xubo mata Wanda hankalin Fulani ya tashi...

'ba haihuwa bace damuwa ta Fulani, damuwata *babana da mijina*, bansan ya xanyi da rayuwata ba, ta fashe da kuka mai tsanani haďe da maida kanta jikin table tana kuka sosai Mai tsuma xuciya,

'innalillahi wa inna ilaihir raji'un shine Abinda Fulani ke furtawa jikinta na soma rawa tunda suke da Iman bata taba ganin hawayen ta ba ballantana irin Wannan Kukan tabbas ko menene babban al'amari ne....

Ta dawo kusa da ita ta xauna haďe da dafata,
'meyasa fatyma, wannan kuka haka komai yayi tsanani maganinsa Allah,

Ta tsaida Kukan da take ta hanyar goge hawayen fuskarta, ta buďe Jakarta ta ciro hijabinta ta warware ta sanya kana ta cire labcoat ďinta da gyalenta ta maida a jaka ta tashi tana kallon Fulani,
'xanje gida likita sai Kuma gobe idan Allah yasa muna da rabon gani. Fulani ta tashi tana kallonta,

'baxaki gayamin damuwar ki ba? Fatyma tayi murmushi sosai tana kallonta Kamar wacce bata da damuwa,

'ba komai Fulani, idan ma da akwai xn sanardake, ta juya ta fice Fulani ta bita da ido tasan ta da Xurfin ciki Dama baxata gayamata damuwarta ba amma meyasa babanta da mijinta ne damuwarta,
Chapter 5 · 0% Book details