← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 33

Sashe 31

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salima na ganin tana farfasa mata mota ta window kafin ta fito tuni habbi tayi shigewarta cikin gidanta ta rufe, tabi motar da kallo Kamar xata sanya ihu dan haushi da takaici.......

*

Bayan wasu kwanaki Iman ta haďa duka ma'aikatan gidan guri ďaya, ta roqesu gafara kana ta sallamesu, irin sallamar da tayi masu baxasu taba mantawa da Ita ba saboda ta cikasu da dimbin alheri mai tarin yawa, sunyi rabuwar arxiki mai cike da shaquwa da kewar mace mai hankali da taqwa kamar Iman...

Mutum uku kawai tabari a tare da Ita, Suleiman, dijeh da adama,

Tun bayan auren su da Deen bata qara sanyashi a ido ba, sai dai taji muryarsa a falo shida su fauxie,

Parking tayi sosai duk abinda take buqata ta hadasu guri ďaya saboda rufe gidan xasuyi, ansa ranar tarewarta lokacin da Deen ya aiko kayan lefenta kamar na wata budurwa,

kaya ne masu kyau da tsada na gani a faďa, haka little da fauxie sai da yayiwa kowa set ďaya...

Sa'eed na bank ta kirashi ta sanardashi abinda habbi tayi, tsaki yayi ya tsinke Wayar hankalinsa a dagule wannan masifa dame tayi kama yasan duk laifin salima ne,

Da yadawo ya hadasu yayi masu faďa sosai akan su haďa kansu shi baxai ďauki wannan kishin tsiyar ba,

Habbi ta bashi haquri tace baxata qara ba xata xamo mai biyayya garesa, yaji daďin haka amma salima Kuwa buďar bakinta sai cewa tayi,

'maganar motata a gyaramin...

'yace xa'a gyara itama xn siya mata tata...

'idan har ka siyamata sabawa nima sai an canxamin Kai bnmason gyaran wata nakeso a canxamin,

'duk ba matsala bane salima indai xaku haďa kanku ku xauna cikin yardar juna....

Habbi ta dubesa tana kashe masa ido,
'sweet muje intayaka kayi wanka kaci abinci inyima tausa nasan a gajiye kake, ya saki murmushi yana kallonta ko baiyi magana ba kasan yaji daďi, ba gardama ya tashi yabi bayanta bai qara waiwayen salima ba haushi kamar xai kasheta,

Tunda yabita part ďinta bata qara jin duriyarsa ko motsinsa ba sai faman leqe take ta window ko xata ganshi shiru kakeji har Washe gari, tana tsaye a window taga fitowarsu, habbi na ďauke da briefcase ďinsa shi Kuma ya riqa hannunta har gurin motarsa,

Tana ganin lokacin daya Karbi briefcase ďinsa ya shiga mota habbi ta sunkuya ta sumbacesa kana ta soma yi masa bye bye shima yana yi mata har ya fice, wannan ranar harda kuka tayi, tunda take dashi ko falo bata taba rakashi ba ballantana hr gurin motarsa.

Amarya Iman sai faman shirye shiryen biki ake tasha qunshi ja abinka da farar mace qafafunta da hannuwanta sun fito sosai tayi kyau ga xoben xinari dake sanye a yatsun hannuwanta Wanda ya qara fito da kyawun lallenta,

Affiya, Dr Fulani da Dr Umayma sune abokanta suke tsaye a kanta na ganin sun shirya amarya sosai ciki da wajenta ta fito,

Fauxie itama Anyi mata tata shigar cikin gown fara, haka shima little cikin suit duk suna gurin Merah.....

Amarya kawai ake jira ta fito ango na cikin Mota yana jiranta, Sa'eed xaija motar amarya da ango xuwa gurin dinner....

Duk ya qagu ta fito cos sunyi late kamar ance ya ďago akayi Sa'a su affiya sun fito da Ita, an rufe fuskarta da wani net duk da haka baxaka rasa ganin fuskarta ba, ba qaramin kyawu tayi ba har ya kasa ďauke idanuwansa akanta, bama shiba har Sa'eed da sauri ya ďauke kansa gareta yana sauke numfashi, Iman yayi asararta ya fada ahankali,

Dr Fulani na bude motar ta shiga kana suda Affiya suka nufi nasu motocin,

Tunda ta shigo ta xauna qamshin turaren ta mai sanyin qamshi da daďin gaske ya mamaye motar, ga wani qamshin amarcin da take,

Sa'eed yaja motar a hankali jikinsa a sanyaye...

Duk qoqarinsa na ganin ya kauce mata ya kasa, he can't, yaga kyawun Iman sosai, kayan dake sanye a jikinta sun fito da shape ďinta wanda baisan Iman ďin haka take ba duk ganin da yake mata acikin hijab da labcoat ne amma yau ya ganta in her real image, no hijab, no labcoat,

Ya juya yana kallonta kanta na sunkuye, bata Kalle sa ba kuma batayi masa mgn ba sai dai xuciyarta ta kasa nutsuwa ta rasa dalilin shariyar da yake mata har wannan lokacin da ta amince na xamowa matarsa.

A hankali ya sauke kwayar Idanunsa akan hannuwanta inda yayi arba da Jan qunshinta, Dama gashi da son qunshi yana sha'awar yaga mace da lalle balle wannan da ta xama tasa mallakinsa, baisan lokacin daya ďora hannunsa akan nata ba ya haďe yatsunsu guri ďaya yana murzawa a hankali.......

Nima ina shirin xuwa dinner ne🏃🏻‍♀, nasan su Xuhura da Pherty novels ma suna can suna shirin xuwa dinner.

My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina*

©Fertymerh Xarah 💞

43

*Dedicated dis page to Ayusha Muhd, Rash Kardam, Fido Sodangi, Ummi Ahmed, Uwani Tahir & Sumayya Dikko*

Hakan bai sa ta ďago ta dubesa ba kuma bata janye hannunta daga garesa ba,

Har suka iso ba Wanda ya tanka acikinsu, a tare suka fito motar ga mutane tsaye ana jiransu hotel ďin cike yake da jama'a samari da yan mata,

Suna fitowa aka soma watsa flowers a gefenta fauxie ce cikin irin tata gown, shikuma little yana gefensa cikin suit kamar Dr Deen, sunyi matuqar kyau sosai,

Nan da nan masu camera suka fara aikinsu, masu yi a waya suka soma, Sa'eed ma sai daukarsu yake, ga fertymerh Xarah novels ma kowa da wayarsa qoqarinsa yaga Dr Iman da Dr Deen a wayarsa, bama kamar Pherty novels dake ture ture burinsu suxo gaba su ďauki amarya, sai da Dr Deen yasa hannu ya kare fuskar iman ganin hasken camera sunyi yawa akanta😜.

Habbi kusa da Sa'eed ta xauna dama yabarta taxo, aka xaxxauna, nan aka fara gudanar da bikin cikin farin ciki da jin daďi,

Deen ya sunkuya dai dai kunneta,

'Na kasa haqura amma dole xn gayamiki kinyi kyau sosai har Ina kishin dubban maxan dake gurinnan....

Ta dubesa suna haďa ido ta saki murmushi cikin jin kunyarsa, shima murmushin yayi dai dai lokacin da mai camera ya daukesu....

Ana cikin yin dinner sai ga salima taxo gurin yanda tayi parking ma xai tabbatar ma da a fusace take,

Tana tsaye tana neman inda xataga habbi, Iman ta ganta sai ta ďauke kanta gefe kamar bata ganta ba, Dr Deen ma ya ganta sai dai baisan ko Wacece ba,

Kamar daga Sama ta hango Sa'eed da habbi suna dariya ba xato ba tsammani habbi taji duka, nan fa suka shiga kokawa dambe suke sosai,

Nan fa gurin ya qaure da ihu, lafiyayyun Mari biyu Sa'eed yayi mata amma bata damu ba ga hancinta na jini burinta kawai ta illata habbi, ganin yanda ta xama tamkar mahaukaciya a gurin kowa na soma neman inda yayi komai ta samu jifan mutane take dashi,

Dr Merah yaja Affiya saboda hankalinsa na gunta baya son komai ya sameta ko kaďan dan ma basuxo da yaran suba,

Dr Fulani taja hannu fauxie da little tayi Mota dasu, kowa ta kansa yake dan salima bata bar kowa ba har mijinta ta jimasa ciwo a hannu, bai taba tunanin haka take ba balle harta iya aikata hakan,

Iman a tunaninta duk saboda itane salima ke wannan haukan, a ruďe take ganin take xataxo ta jimata ciwo ne, sai ta qanqame Deen sosai Kamar xata shiga cikinsa, shi Kuma hankalinsa na gun su fauxie sai dayaga an sanyasu Mota kana ya maida hankalinsa ga riqon da Iman tayi masa, idanunta a lumshe sai hawaye take abu kaďan ke ruďata baisan irin xuciyarta ba, yasa wayarsa ya ďauketa pic batare da ta sani ba kana yasa hannunsa ďaya ya rungumota..

Da kyar wasu maza suka rirriqeta, Sa'eed ya ďaure ta da wata waya sai faďi yake,

'batada hankali daga gidan mahaukata ta fito, ta qara xabura

'qarya kake, kunci amanata ne Kuma baxan barku ba,

Ya ďaure bakinta da gyalen habbi, sai kuka take ya ďauketa ya nufi motarta da Ita ya sanyata ciki ya Kulle motar sai xufa yake, wannan wahalar dame tayi kama, ga hannunsa sai jini yake habbi ta riqosa tana hawaye,

'dear muje asibiti dan Allah,
Ya dubi hannun kafin ya nufi inda Deen yake tsaye da Iman,

'Dan Allah kuyi haquri d....... Deen ya katsesa,

'ba komai Sa'eed kayi sauri kaje asibiti, iman ta ďago tana kallonsa cikin tausaya shi har sai yaushe xai sami kwanciyar hankalin wannan matar? Suna haďa ido dashi ta qara fashewa da kuka ta maida kanta jikin Deen, Sa'eed kuma da sauri ya juya nan cikin motar suka barta habbi ta jasa suka nufi asibiti.....

Kowa ya watse sai gasu ci biki ynxu ake xuwa😂, Ummi Aysher, Faxyfashion, Serdia, Halimcy, Zarah dange, miss Aysher, baby Bello, Kdeey, Kwaise, Lilmeerahcute, Xuhura Ajiya, Meenah, Rabi'atu Sk, Didi Aneesa, Afrah bhai, Anty maijidda musa, Khadija Sidi, Shafa Umar, Maryam kaumi, Sally, Teemah cool, Anka, H.Melody, RAZ, Nusee, Pherty, Rukayya Umar, Hafsat rano, Zarah Bukar, Zee yabour, Faty Shuwa, Hindatu Arzika, Hamidata, ya salam🙆🏻 gasu nan dai dayawa har bn iya lissafaku am sorry please 👏🏻,

Sukaja suka yi turus ganin ana watsewa, Dr Merah tuni yabar gurin, Dr Deen da Iman ba motar shiga dama da ta Sa'eed suka xo kuma sunyi asibiti,

Suka tsaya cirko cirko suna kallon mutanen dake shiga mota suna barin gurin, suna kallon salima acikin motar, haka kawai Deen yaji ya tsaneta, ya juya yana kallon Iman dake qanqame da hannunsa,

'ita wannan wai wacece, meyasa tayi haka?

'matar Sa'eed ce, uwargidansa, tana kishina saboda Sa'eed, amma bansan dalilinta nayin haka ba,

Ya gyada kai cikin gamsuwa batare daya kalletaba, suna tsaye sai ga mota tayi parking gurin, sunsan motar Merah ce, suka buďe suka shiga har yakai affiya gida,

Acikin motar Dr Deen da Dr Merah suka cigaba da nanata mgnr kowane ransa a bace fuskokinsu kawai xaka gani ka karanci hakan, iman na baya tayi shiru tana saurarensu, ita suka fara ajiyewa gida kana suka fice kowane ba walwala a fuskarsa ita kanta bataji daďi ba she will never forget salima in her life....
Chapter 31 · 0% Book details