← Book details Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 33

Sashe 24

Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukan fauxie da Merah sun tayarda hankalin fauxie ganin manyan maxa irin su na kuka ba qaramin abu bane, duk da take qarama tana jin wani feeling a jikinta ba daďi, jikinta yayi sanyi ta matsa kusa da Bakori tana kallonsa dan taji suna ambatar Deedah tasan shine kwance a wurin taga sun rufeshi da xani, tasan haka akewa duk wanda ya mutu kamar yanda malam ya sanarda ita,

Xuciyarta na soma bugawa fal fal numfashinta har wani sama yake,

'yaya ya mutu? ya gyada kai yana kallonta,

Shikenan ya tafi ya barsu, shikenan baxai dawo ba, shikenan baxai qara siyamata tedy, biscuits da chocolate ba, shikenan baxai qara Wasa da ita suje yawo ba, shikenan baxasu qara cin abinci tare ba, baxata qara ganinsa ba itada anty, ta juya tana kallonsu duk sunyi shiru, ta gigice ta fita daga ďakin haďe da fashewa da irin Kukan nan Mai qara irin na yara, da ka ganta kasan a gigice take batasan inda xataje ba,

A tsorace ta farfado daga barcin da take, xuciyarta na tsananta bugawa ta tuna Deedah da yanda ta barshi, ta sauko daga Saman gadon da sauri haďe da fisge drip ďin da ake sanyamata a hannu,

Mararta a qule take har lokacin tafiya take a hankali ba takalmi ba mayafi sai kallabi akanta, kallon xararra ake mata a asibitin ga Waďanda basu Santa ba duk inda tabi sai an kalleta, kai da kaganta kasan haihuwa tayi saboda xaninta duk jinine,

Nurses ďin da suka Santa suka biyo bayanta da sauri suna kiran sunanta, tanaji ta kyalesu sai ta qara Saurin qafafunta musamman ynxu da take jiyo Kukan fauxie sai ta qara ruďewa,

Tun daga nesa ta tsinkayo fauxie na kuka a jikin Dr Deen, tana qarasowa ana fitowa da gawar baba,

Ta tsaya cak tana maida Numfashi da kyar kamar wata zakanya jikinta sai karkarwa yake, juyowar da xatayi taga anfito da Deedah, Sa'eed na bayansu yana sharar kwalla Idanunsa sunyi matuqar ja,

Fauxie na ganin an fito dashi ta qara fasa ihu a gigice tana neman kwacewa jikin Deen, iman Kuwa qarasawa tayi ta riqe gawar,

'meyasa kuka rufesa ai bai mutu ba, ku duba suma ne yayi, Deedah baxai mutu ya barni ba, wannan lokacin Kukan da take harda majina ta xama wata xautacciya,

Duk qarfin hali irin na mutum idan yaga halin da Iman take ciki a Wannan lokacin sai ya xubar da kwalla,

'Deedah ka tashi sugani su San cewa Baka mutu ba, Deedah ka tashi kaga yaron da muka haifa, meyasa xakaje ka barmu a lokacin da muke tsananin buqatar ka,

Taje ta riqe Merah,
'kace su dawo dashi acigaba da kula dashi anan, Deedah bai mutu sai idan kune xaku kashe shi,

Fulani ta qaraso da jaririn a hannunta har lokacin kuka yake kamar yasan abinda ke faruwa, tunda ya faďo duniya yake kuka,

Kukan yaron har cikin kanta take jinsa, ga Kukan fauxie dake qara rikita kwakwalwarta, tana ganin lokacin da suka sanyasu a mota ta tabbata lallai gida xa'a je dasu ayi masu wanka da sallah akaisu makwancinsu, shikenan Deedah yaje yabarta.....

Cak numfashinta na ďauke, sai ta xube gurin a sume....

My wattpad Phertymerh1

*Babana da mijina*

©Fertymerh Xarah 💞

34

*Masu turo ta'aziyar Deedah, iman na godiya sosai, saqonku ya iso*.

Tana xubewa gurin su Dr Umayma sukayi kanta, fauxie na ganin lokacin da ta faďi ta soma neman saukowa jikin Deen tana kuka amma ya riqe ta tamau sosai a jikinsa,

Aka sanya gawarsu a motar Sa'eed, shi yaja motar su Merah na bi bayansa da nasu motocin,

Iman Kuwa motar Dr Deen aka sanyata tare da sauran likitocin fauxie na kusa da ita fuskarta ta qara kumbura tayi jawur ga ciwo ga kuka, kanta har nauyi yake mata ga wani Xaxxabi da take ji wannan karon baxata sami kulawar Iman ba cos ita kanta bata cikin hayyacinta, mutuwar mahaifi da miji a lokaci ďaya (it's the greatest loss of all losses),

A Wannan ranar xo kaga jama'a, mutane kamar me, nan da nan gari na ďauka mutuwar Alhaji Abdallah abinka da ďan siyasa sananne a gari,

Mutuwar taxowa mutane a baxata daga shi har Deedah ba Wanda aka yiwa tsammanin mutuwa a ynxu,

Abokan Deedah suna cikin ruďani da tsoron Allah, duk Wanda yace shine yau ba shi bane gobe, mutuwar sa ta girgixa shi idan suka tuna jiyama suna tare dashi a office, ya sami kyakkyawar Shaida daga garesu,

Ma'aikatan gidan maza da mata tamkar sune akayiwa mutuwar, kuka suke sosai sun san qarshen barin su gidan yaxo, ba uban gidansu to Waye xai riqa biyansu Waye xai riqa ciyar dasu, wasu ma da gidan suka dogara,

Sa'eed da kansa yaje part din baba ya rufe ďakunan sa na dukiya, mutanen ynxu basu da amana wani baxaiji tsoron ana cikin wannan tashin hankali ba suje yiwa marayu sata wannan ne dalilin dayasa ya rufe,

Anje yiwa gawarwakinsu wanka, a Wannan lokacin fauxie na rakube a bed side kanta a langabe, barci take daga xaune tana gyangyaďawa kamar xata faďi,

Iman Kuwa tana xaune da jinjirin a hannunta tana bashi mamma, ance kuka ma rahama ne Wannan Karon kam Kukan yaqi ya xo xuciyarta a bushe take, kallon jaririn take,

Yaxo a MARAYA, yaxo duniya babanshi yabar duniya, kakanshi ma yabar duniyar, duk da haka yaronta baxai taso cikin maraici da rashin gata ba, xata bashi tarbiya ta kula dashi shida fauxie tamkar Iyayen su na raye, bata da sauran buri a rayuwarta ynxu na ganin ta Kula da marayun biyu, ta sauke nauyin dake kanta akansu, aure baxata sanyoshi gaba ba aynxu a tsorace take da kowane namiji da halayyarsa, xata cigaba da rayuwarta a hakan, Wanda take so ya tafi yabarta tana roqon Allah ya sa shine mijinta ko a lahira,

Sai a lokacin hawaye na samu xubowa daga idanuwanta ta rumtse idanuwanta suka xubo akan fuskar jaririn Wanda ke barci tuntuni,

Fulani ta karbi yaron ta goya, sai Iman ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai,

Sanda aka gama masu wanka aka Kira Iman tayi masu addua, kuma tayi cikin jarumta da dakewa irin tata, ba Wanda batayiwa addua ba acikinsu, tana gani aka ďauki gawarsu,

Sai ta bisu da ido idanunta taf da hawaye fuskarta ďauke da murmushi,

'I know Deedah must come back to me, ni nasan bai mutu ba, nasan Deedah baxai je yabarni ba, bayan yace xamuyi rayuwa tare mu raini jaririn mu tare,

Xuciyarta ta cigaba da bugawa lokacin da aka fita dasu, taga yawan jama'ar da suka cika gidan sai taja jikinta ta koma ta xauna, tana bin mutanen dake falon da ido tana kallonsu suna kuka,

Bataga dalilinsu na kuka ba, Wanda suke wa kuka xai dawo tasan xai dawo, xai dawo..... xai dawo haka kwakwalwarta ke bata

Sai ta fashe da dariya, duk gurin aka juyo ana kallonta, ko miye abin dariya ga Wanda akayiwa mutuwa?

'lafiyar ki kuwa? Cewar salima tana kallonta cikin tsananin mamaki,

'tor miye amfanin Kukan da kuke, baba ne kawai ya mutu banda mijina, nasan Deedah yana raye, ynxu xaku ganshi ya dawo xaiyi wanka yayi shirin xuwa masallaci bara naje na fidda mashi kayan da xai sanya a yau, ta tashi tayi ďakin sa,

Mutanen falon suka kalli juna cikin tsananin mamaki, Fulani tabi bayanta da sauri,

Ta juyo da kafadunta suna fuskantar juna,
'Kinsan me kikeyi fatyma, me kike son nunawa mutane, baki yarda da qaddara bane keba musulma bace?

'my husband is alive Dr Fulani, Kune keson kashe sa, jiya fa muna tare, yau ma munyi mgn dashi, ya roqeni gafara Kuma na yafe masa, shine fa ya suma kuke kiran ya mutu,

'Wanda ya mutu baya dawowa Iman, kada ki ruďar da kanki, ki nutsu dan Allah kada wani abu ya sami kwakwalwarki, dan Allah fatyma kixo muje falo kicigaba da yi masu addua, kinga ga yan uwanku ma suna ta xuwa.

Iman tayi shiru Kamar mai naxari sai Kuma ta dubeta,

'tell me Fulani idan Marhoom ne ya mutu me xakiji?

Sai da xuciyarta na buga ta gyara goyonta tana kallonta,

'me ya kawo wannan mgnr Kuma? Idan ma mutuwa yayi haquri xanyi nayi tawakkali ga Allah, nasan yafini sonsa Kuma nasan yafiye masa duniya daďi,

Iman ta girgixa kanta,
'you are not saying the truth Dr fulani, baxaki iya jurewa ba, bakisan xafin dana keji a xuciyata ba, bakisan ciwon da Mace take ji idan ta rasa abokin rayuwarta ba, ballantana irin nawa rashi na *babana da mijina* a lokaci ďaya, ta soma hawaye sosai,

ta juya tana ciro kayan Deedah,
'ni nasan bai mutu ba xaki ganshi sun dawo dashi,

Fulani tayi shiru tana kallonta cikin tausayawa, itama ta tsinci kanta cikin kuka sosai ta fice daga ďakin da sauri.

Haka Iman ta fito da kayansa, juyowar da xatayi tayi arba da tangamemen hotonsu dake manne a ďakin, yana rungume da Ita suna yiwa juna murmushi, sai ta saki murmushi tana faďin,

'Haba taya ma xasu ce Deedah na ya mutu, nasan xaka dawo kaxo kabasu mamaki su san cewa kana raye......

An kaisu makwancinsu an rufesu daga su sai halayyarsu sai abinda suka shuka a duniya, in hairan hairan in shairan shairan, wani abin tsakaninka ne da mahaliccinka, idan ka kasance mai tuba agaresa,

Duniya kenan....

Babu dukiya aciki, babu gida mai tsada, babu mota mai tsada, babu abinci mai tsada, babu lallausar katifa mai taushi da tsada, babu Mulkin da ake taqama dashi,

An kaika inda xaka xamo abinci ga tsutsoci, qasar da kake taki da takalmi yau kaine acikinta timbir, babu mai ceton ka aciki sai Allah, sai aikin da ka aikata a duniya, ya Allah ka tsare mu da azabar kabari, kasa muyi kyakkyawan qarshe mucika da imani Amin.

Sa'eed kuka yake sosai Idanunsa sunyi jawur, shikenan Deedah yaje ya barsu, baxasu qara ganin Deedah ba, yayi rashin aboki, Allah ka gafartawa Deedah ka Kai haske a kabarinsa kamar yanda goshinsa yayi haske lokacin da suke masa wanka,

Suna dawowa jana'iza suka nufi gidan, tun daga waje suka fara gaisuwa ga mutane birjik an shimfida Manya Manya tabarma saboda masu gaisuwa, yan uwan su Iman ne a waje da suka xo,
Chapter 24 · 0% Book details