Sashe 1
Babana Da Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira)
BABANA DA MIJINA
©Fertymerh Xarah
1
Agogon alarm dake manne a bangon falon ya buga qarfe ďaya dai dai na dare,
Ta ďauke kanta daga kallon agogon ta maida jikin TV tana kallon aljaxeera....
Xaune take akan sofa tana sanye cikin rigar barci mai tsantsi fara sol,
Ba wata muguwar kyakkyawa bace can, tana da kyau dai dai nata sai dai kuma mace ce Mai aji na qarshe,
Akan tsinin hancinta tawwadar Allah ce da aka haifeta da Ita tayi mata kyau kasancewarta farar mace
daga nan xaune taji tsayuwar motar mahaifinta, idan da sabo ta saba da wannan hali na mahaifinta da mijinta na fitar dare ko dawowar dare, gwanda mahaifinta ďan siyasa ne shine mataimakin gwamnan birnin kebbi, sukanyi meeting ďin dare akai akai wataran ma a gidan sukan taru suyi tana jiyo hayaniyar su daga nata gidan,
Bai jima da tsayuwa ba taji ya shige sashensa, tayi hamma haďe da yin miqa cikin wani irin yanayi na barci dai dai lokacin daya shigo falon da qatuwar kwallo a hannunsa,
Ko kaďan bai raxana da ganin matar tasa a Wannan lokacin tana xaman jiransa ba Co's ta saba,
ta xuba masa idanuwa tana kallonsa cikin wani irin yanayi fuskarta ba walwala, ya cillar da Kwallon dake hannunsa haďe da xare socks ďin qafarsa duk Idanunsa akan ta
har ya gama cirewa yayi sassanyar ajiyar xuciya, duk hankalinsa da attention ďin sa yana kanta, ya sami kansa da ruďewa, akwai wani sassanyan kallo cikin kwayar idonta Wanda ba duk mata Allah ya mallakawa ba, ya nufeta cikin wata irin tafiya ta izza cike da taqama ya xauna a kusa da ita haďe da ďora hannunsa akan nata hannu,
Kiyi haquri Iman kamar yanda kike a kullum wasan kwallo wani abu ne d.... yayi shiru sakamakon wani kallo da tayi masa,
A iya sanina wasan kwallo anayinsa ne da rana ko da safe amma ku bansan wane irin Wasa ne naku da sai dare kukeyinsa ba,
Ya tsura mata ido,
Iman baki yarda dani bane, ko kina xargina?
Ba xargi a nan illah gsky nake son ka gayamin, bayan albashinka na banki kana nufin duk wannan dukiyar daka tara duk akan kwallo ne ? Ya gyada kansa
Kwarai Kuwa, kije ki tambaya kiji duk ďan kwallo na asali Mai fita waje yana ball ba qaramin kuďi suke samu ba, ki yarda dani Mai sunan mamana bani da wani mugun hali Wanda xai cutar dake, tayi shiru kawai idanunta sun kawo kwalla ta kasa yarda da mijinta da mahaifinta, tsakanin *babana da mijina* baxan ce ga Wanda yafi wani so na da kula dani ba, ga kuďi har batason ganin su kasancewar tana xargin masu su, ta goge hawayen fuskarta, yana kallonta cike da so da tausayinta yana jinta har cikin ransa shi kansa baisan wane irin so yake wa Fatima ba, ya riqo tafin fuskarta haďe da sanya yatsansa yana share hawayen fuskarta,
Babban tashin hankalina shine naganki cikin damuwa, har sai yaushe xaki yarda dani Iman, idan baki yarda dani ba Waye xai yarda dani, wallahi ni ďan kwallo ne kidaina xargina,
taja numfashi haďe da Sakin malalacin murmushi tana kallonsa
na yarda da kai mijina, amma Ina so ka kiyaye kayi a hankali da duniya ka Kuma ji tsoron Allah, jikinsa yayi sanyi
Yace Insha Allah Iman, ya riqa hannunta suka tashi da kansa yaje ya kashe tv da komai, tana tsaye sarqe da hannayenta a qirjinta tana kallonsa cikin so da qauna, ya juyo yana kallonta
'let's go... ta juya yabi bayanta, har suka hau step ba mai mgn a cikinsu kowa da saqe saqen xuciyarsa,
ďakin qanwarta Fauxiya ta nufa ta buďe dakin a hankali ta shiga, ta same ta tayi barci sosai ďakin ya ďauki sanyin a.c ta qudundune guri ďaya da alama tana jin sanyi sosai,ta juya tana kallon sa,
'you see Fauxiya bata jin magana duk ynda nayi da ita akan shan sanyinnan bataji,
Ahmed yaje ya kashe a.c ďin kana ya ďauki blanket ya lulluba mata bayan ya gyara mata kwanciya, ta matsa ta gefenta ta xauna, addua tayi mata kafin su bar ďakin,
Kai tsaye toilet ya nufa yayi wanka, yana shirin barci ta shigo da coffee a hannunta, ya karba yana kallonta da murmushi,
'thank you wify ,tayi murmushi ta xauna bakin gado tana kallonsa,
Yana gama shan coffee ďin ya juyo ya sumbaceta a goshi yana fadin gudnyt, kafin tayi mgn har ya faďa Kan gado ya kwanta, ta bisa da ido cikin tausayin kanta hawaye suka xubo mata,
Wannan wace irin rayuwace, wane irin aure ne wannan, am a doctor, mijina yana aikin banki, idan ya fita tun da safe baxan qara sa shi a ido ba sai 6pm da yayi wanka yaci abinci ya fice sai 1 ko 2am wataran ma sai da safe take ganinsa ya dawo wai yaje training ďin kwallo,
Yau satinta biyu rabonta dashi tana buqatar mijinta tana da haqqi akansa bai damu ba saboda ita tana da buqata sosai ba Kamar shi ba ko xasuyi wata a hakan baxai damu ba,
A matsayina na matarshi abokiyar rayuwar sa bashi da lokacin da xai xauna dani and sai dai kullum idan nayi masa Mgnr fitar dare yace bana yi masa uxuri da yawan ayyukan dake gabansa a banki, da dare Kuwa xaije training na kwallo,
Ban rasa ci ba ban rasa sha da sutura ba amma na rasa kulawa da soyayyar mijina abin tambaya anan shi wannan shine ginshiqin auren, am not satisfied with my husband, bama Wannan ba rashin xamansa gida...
Babana ďan siyasa ne shi ba mai xama bane idan baya gari yau gobe yana wata qasa, idan yana gari shima baxaka ganshi ba sai cikin dare yake dawowa, idan taje mashi da complain na fitar mijinta sai dai yace
'haquri xakiyi tunda koni mahaifinki kina ganin ba maxauna bane, muna meeting sosai Mai muhimmancin acikin dare, tunda ya gayamiki wasan kwallo suke xuwa kiyi haquri ki barshi komai lokacine, ta share hawayen ta cike da mamakin kalaman mahaifinta,
shekara biyu da rasuwar mamana, banda kowa a duniyar nan bayan *babana da mijina* sai qanwata fauxiya, bansan wa xan kaiwa kukana ba ya share min shiyasa ko aiki naje banda tunani sai na *babana da mijina* babu wanda baya fuskantar challenge(qalubale) a rayuwa, and is up to us to accept such challenges mu bita da duk fuskar da rayuwa ta xo mana....
Jin shiru bata kwanta ba ya juyo yana kallonta,
'lafiya Iman, me kike tunani, ta tashi da sauri tana fadin ba komai ta nufi toilet, ta saki ruwa tana kuka sosai yanda baxai jiyo ta ba......
*Dedicated dis buk to*
*Rabi'atu Sk Mhs*
*Sadiya Lawal bala*
*Aysher Gambo*
BABANA DA MIJINA
©Fertymerh Xarah
2
Asalin labarin......
Ahmed mutumin jihar Birnin kebbi,
Daga kallo na farko mawuyacin haline ka gane qabilar da ya fito Hausa ko Fulani, wani mutum ma'abocin cikar zati da kamala da duk wani nau'in daidaito na rayuwa,
Mahaifinsa malam Abubakar buba malamin islamiya ne mutum ne mai ilimin addini, haka mutanen unguwa suna tsananin girmamashi,
Sai mahaifiyar Inna, shika dai ne ďa a gunsu, bayan rasuwar mahaifinsa suka shiga wani hali na rashin babu, gashi qarami a lokacin primary 6,
Ba Mai taimaka masu wani sa'in ma Inna ke xuwa wankau ta sami kudin da xata ciyar dashi, shi Kuma Ahmed a rayuwarsa yana son karatu shiyasa yake dagewa akan karatun, he is gifted tun yana qaraminsa malamai sun San dashi,
Ahmed yayi karatunsa da taimakon mahaifiyarsa dake siyarda qarfinta dan ganin farin cikinsa, lokacin da ya shiga babbar makaranta I mean higher institution duk qaddararta sai da ta saida ganin ta cika masa burinsa,
Alhamdulillah ya kammala degree ďin sa lfy duk aikin dayaje nema na gwamnati bai samu ba, duk inda yaje nema baxai samu ba, abokan karatunsa Waďanda iyayensu suke da kuďi sun fara aikin banki saboda suna da ďaurin gindi a gwamnati wasu ma sun fita waje neman wani ilimin, shikam degree ne iya qarfinsa yana so ya sami aiki dashi ko yayane dan ya tallafi mahaifiyarsa....
Kwanci tashi asarar mai rai yau gashi an kwantar da Inna asibiti babu kudin magani Babu babban tashin hankalinsa kamar ciwonta ulcer da kuma hypertension, duk inda ya buga bai sami kudin ba, abokansa dake bashi aro sun daina saboda baya biya,
Ya qara komawa asibiti kai tsaye ya nufi inda likitan ya roqesa ya taimaka ya duba mahaifiyarsa fisabilillah saboda bashi da kuďi, fafur likitan yaqi har kuka yayi wani mutumi dake xaune office ďin shima yaxo likita ya dubashi ya dubi likitan,
Nawa ne kudin maganin,
Dubu biyar ne fa bawani yawa, kamarsa baxai iya biyawa mahaifiyarsa kudin magani ba, baxaije ya nemi aiki ba, muma karatu mukayi muka sami aikin,
Ahmed ya dubesa, ko xaka daukeni aiki ne, ko wane irine inaso indai xaka biyani na kula da mahaifiyata
Likitan yace bama daukar mutum aiki sai mai ilimi kai kuma baka dashi,
Ahmed yace inadashi nayi karatuna na kammala na nemi aiki ban samu ba yaciro takardunsa ya nuna masa, likitan ya duba sosai Ahmed ya cancanci a daukesa aiki saboda matakin karatunsa Kuma result ďin sa mai kyau ne...
Xan iya samama aiki da wannan result amma sai idan xaka iya biyan dubu hamsin, kasan aikin gwamnati ynda yake Kuma a banxa baxaka sami aiki ba sai ka kashe kuďi....
Ruwan cikinsa na soma qugi Wanda bai sami dubu biyar na magani ba Ina xai sami dubu hamsin a ynxu, ya karbi takardunsa ya juya ya fice yana hawaye,
dakin da aka kwantar da mahaifiyarsa ya nufa har lokacin bata farfado ba barci takeyi, qarqashin pillow ďinta ya cusa takardun xaije ya nemo kuďi da qarfin jikinsa ya juya ya fice....
Ya fito harabar asibitin ya haďu da wannan mutumin na ďaxu ya kirasa yaje,
Sannu saurayi,
Ahmed ya qara gaida mutumin,
Na ganka kana da hankali sosai Kuma da ganinka xakayi jarumta xan baka kuďi ka taimaki mahaifiyar ka kakuma sami na aiki indai xaka iya min aiki,
Wane aiki ne xan iya....ya faďa muryarsa na rawa
Mutumin yace ka taba riqa bindiga? Ahmed ya girgixa kansa yana kallonsa cike da mamaki,