← Book details Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 40

Sashe 39

Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu ta ce ke me Haseena yai miki da zaki sani na manna mata cutar HIV, me Aisha ta yi miki da kike son fitar da ita daga gidan mijinta, ke azzaluma ce

Aisha kasa jurewa tai daukar Leemat tai tabar falon da ita gudun kada ta dauki cuta tsabar warin dake fita

Haseena ta kalli Feedo "Feedo nagode da kika gwada min karatun duniya, kinsa na fahimci duniya, ba don ke ba da har yanzu ina cikin duhu"

Feedo kan Bilkisu ta yi ta jata da dambe, ganin haka yasa Don ya kira police, bada dadewa ba sai ga polisawa sun karaso, dakyar suka iya jure tafiya da Feedo tsabar warin dake fita daga jikinta, wani dan sanda ma sai da ya yi amai, koda aka iso dasu police station hankalinsu tashi ya yi, a tarihi basu taba jin wari irin wannan ba, wani daki aka kebewa Feedo aka kalleta ita kadai a ciki, sai ihu take yi tana kuka tana sumbatu "Bilkisu saina kashe ki, kema Haseena saina kashe ka, harda kaima Don duk saina kashe ku" sai ta fashe da dariya, da alamu dai hauka ya fara kama Feedo

Don ya shigo daki ya samu Aisha na bawa Leemat nono, yazo ya zauna gefenta yana fadin "dafatan dai lafiyarta kalau don wannan warin zai iya kashe mutum"

Aisha ta ce lafiyarta lau

"Kin tabbata?"

"Eh na tabbata"

Aisha ta mayar da nononta ta mike "bari na je wurin Aunty Haseena"

Don ya mike "to muje, ina ga jikin nata ma sai mun je asibity"

"Nima haka muke gani"

Fita suka yi, bangaren Haseena suka wuce, suka shiga bedroom dinta suka sameta kwance kan sallaya, sanye take da hijabi, tana rike da carbi, a hankali take furta "astagfirullah wa atubu ilaika"

Don ya kada kai cike da Tausayinta, Aista ta duka kusa da ita "Aunty Haseena Sannu, ki tashi muje asibity"

Haseena muryarta na rawa "ba zan je asibity ba, a kira min mahaifina da mahaifiyata"

Don ya bata rai "Haseena me kike fada haka, bana so"

Cincibota yai kamar jaririya, yai mamakin yadda jikinta yai zafi, sai rawar dari take yi, rufe idanunta tai hawaye na fita "ka taimaka ka kira min iyayena"

Don ya ce Haseena babu abinda zai faru, zaki sami lafiya

Ya kalli Aisha jeki dakko min makullin motana

Aisha ta ce to sannan ta fita da sauri, shi kuwa ya fita da Haseena, yana isowa harabar gida jini ya fara fita ta hancin Haseena da bakinta, Don ya rikice gabadaya a take ya fara furta "Inna lillahi wa Inna ilaihir raji un" Aisha ta karaso da makullin mota, suka shiga mota suka wuce

Suna isa asibity aka shiga da Haseena Emergency, tuni Don ya kira iyayen Haseena, sannan ya kira Ammi da Abba ya sanar musu, cikin kankanin lokaci kowa ya karaso asibity

Likitane ya fito ya same su, suka tunkarosa suna tambayar jikin Haseena "jikinta alhamdulillah, zaku iya shiga ku ganta" Mahaifin Haseena Alh Aminu da mahaifiyarta hankalinsu ya tashi matuka ganin halin da Haseena take ciki, da kuma suka kara samin labarin an rabata da mahaifarta, suka kara shiga wani sabon tashin hankali, Alh Aminu ya yi alkawarin ba zai bar Feedo ba

Haseena kwance, bata motsi, hawaye kawai ke fita daga idanunta, mahaifiyarta zaune gefenta tana shafa kanta tana kuka, Aisha rike da Leemat itama kuka take yi, hatta Ammi ta yi matukar tausayawa Haseena

Don zuwa ya yi dayan gefenta ya tsaya, Haseena ta juya kwayar idonta kan Don, ta lumshe idanunta sai wasu sabbin hawaye suka shiga fitowa, kama hannunta yai yana dan murzawa a hankali

Sai yanzu Haseena ta bude baki dakyar ta shiga yin magana bakinta na rawa "mijina ina sonka har bayan rayuwata, ina fatan yin rayuwa tare da kai da yar uwata Aisha a aljannah, ku kula min da Leemat, Allah ya raya mana ita ta zama abin alfahari"

Don bai san lokacin da hawaye ya ciko a idanunsa, baya son a gano halin da yake ciki yasa ya fita da sauri,

Alh Aminu ya kasa dakatar da hawayen dake masa zarya, mahaifiyarta ta ce "Haseena maganganunki na kashe min jiki, don Allah ki daina"

Haseena ta girgiza kai tana kallan mahaifiyarta, sai numfashi ta ya fara yin sama, Ammi karasowa tai ta zauna gefen Haseena, a hankali ta shiga fadin "la'ilaha illallahu Muhammadar rasulullahi sallallahu alaihi wa salam" a hankali Ammi ta cigaba da maimaitawa

Alh Aminu da Mahaifiyar Haseena ganin abin dake shirin faruwa yasa suka rikice gabadaya, hankalinsu ya tashi

Cikin sa'a Haseena ta furta kalmar da Ammi take ta faman maimaita mata, Haseena gabobi ya tsaya daga aiki cak, ruhi ya fita, gangar jiki ya rage

Ammi ta furta "Inna lillahi wa Inna ilaihir raji un" sannan tasa hannu ta shafa fuskarta, ta rufe mata idanu

Wani kara mahaifiyar Haseena tai sai ta yanke jiki ta fadi, Aisha kukanta ya tsananta sai fadin Innalillahi wa Inna ilaihir raji un take yi

Don ya shigo da sauri, ganin halin da ake ciki yasa ya tsaya cak yana kallan Haseena, tabbas babu rai a jikinta "Inna lillahi wa Inna ilaihir raji un" ya karasa wurinta da sauri, sai dai wannan karan ya kasa dakatar da hawayen da suka taru a idanunsa
"Ubangijin daya halicceki ya fimu sonki"

Likita ya shigo ya kara duba Haseena, tabbas rai ya yi halinsa

A motar Asibity aka dauki Haseena aka kawota gidan mijinta, Don da mahaifiyar Haseena suka yi mata wanka sannan suka suturta ta cikin suturarta na karshe, bayan anyi mata sallah aka wuce da ita kushewarta 😭😭😭😭

Hmmmm rayuwa kenan, yau kaine gobe ba kai bane, komai kake yi ka dinga tuna mutuwa, a kowani lokaci dake tafiya kara kusanto kushewarka kake yi, tarin arziki ko karfin mulki da sarauta ba zasu amfanar da kai komai ba, wallahi mu ji tsoron Allah, karmu yarda zuciya ta rudemu

bayan sarakan uku Alh Aminu ya je police station din da Feedo take, yasa aka fito da ita, warin dake fita daga jikinta yasa ya tsorata, tsoron Allah ya kamashi, yana mamakin wai mutum ne yake wari haka ba wai mutuwa ya yi ba, Feedo surrutai take yi barkatai alamun dai ta zare "sai na kashe kowa, waye zaiyi soyayya dani ya bani kudi, yunwa nake yi, niko kwanciya idan mutum zaiyi dani na yarda" sai ta fashe da dariya "ho ni Feedo"

Alh Aminu ba zai iya cigaba da shakar warin dake fita daga jikin Feedo ba ya kalli DPO

"Ni ina ganin zan wuce tunda Allah ya nuna mata iyakarta, ga wari kuma da alamu ta haukace, wannan kadai ya isheta ishara"

DPO ya ce wannan hakane your excellency

Alh Aminu ya yi wa DPO sallama ya wuce,

Asibitin mahaukata aka wuce da Feedo, amma killaceta aka yi a wani daki me duhu yadda warin da take yi ba zai cutar da Sauran mahaukatan gidan ba

💮💮💮💮💮💮💮💮💮

Don tsaye a can saman bene shi kadai ya yi shuru yana tuna Haseena, yana tuna soyayyar daya shiga tsakaninsu, yana tuna yadda suke fada, yana tuna soyayyar da take nuna masa, yasan tabbas Haseena tana mutuwar sonshi, Aisha ce ta karaso tai hugging dinshi ta baya "mijina me kake tunani?" Don ya juyo ya fuskanceta, yai smile

"Mata ta ina tunanin Haseena ne"

Aisha damuwa ya baiyana a fuskanta "Allah sarki mijina ka yi kewanta ko?"

Lumshe idonsa yai yana smile "hakika na yi missing dinta sosai, fatana Allah ya jikanta, Allah ya hadamu baki daya a aljannah"

Aisha ta rungume shi cikin farin ciki "amin mijina na kaina" ya kara rungumeta sosai kamar zasu hade da junansu

Aisha ta ce kasan me nake tunowa?

"A'a sai kin fada"

"Ina tuna ranar da aka fada min za'a hadamu aure, na yi kuka kamar raina zai fita, ranar da za'a kawo ni gidanka na yi kuka sosai, ina ganin zan bar iyayena da yen uwana, ina kara tuno nasihar mahaifina, tabbas mahaifina ya yi gaskiya rayuwar aure, rayuwace ta farin ciki, me zai rabani da kai yanzu mijina idan ba mutuwa ba, da mutuwar zata nemi shawarata data dauke mu lokaci daya" Aisha ta karashe maganar cikin muryar kuka, Don ya shiga shafa gadon bayanta

"Mu cigaba da addu'ar mata ta, mu yi addu'ar Allah ya dauki rayuwarmu lokaci daya, don nima ba zan jure ranar da zan bude idanuna ba na ga bakya raye uwar yayana, nasan ranar zan yi hauka"

Don ya banbare Aisha daga jikinshi, ya tsurawa fuskarta ido, hawaye na fita daga idanunta, harshensa ya yi amfani dashi cikin salo ya shiga lashe hawayen

"Mata ta karki damu muna tare har muga jikokinmu"

"Nima haka nake fata mijina"

Don ya ce muje mu duba yarinyarmu "to mijina" suna rungume da juna suka fice

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya, Wizzy ya samu ya auri Fa'iza, yarinyar da mahaifiyarsa ta nema masa auranta, anyi bidiri sosai, Amarya ta tare anan Abuja, Wizzy ya yi farin ciki sosai daya sami Fa'iza virgin, har alwala yai ya yi nafila raka'a biyu ya godewa Allah, kara ji yay soyayyarta ta dasu a zuciyarta, har ya kai ga yana ganin babu wata mace a duniya data kaita

Leemat nada wata bakwai Aisha ta samu wani cikin, Don da Aisha sunyi matukar yin farin ciki kuma basu yaye Leemat ba, haka Aisha take shayar da Leemat kuma take rainon ciki har tsawon wata hudu sannan aka yaye Leemat, aka mayar da ita wurin Ammi da zama

Don da Aisha suka cigaba da rainon ciki har Allah ya kawo ranar haihuwa, Aisha ya mace ta kara haihuwa, sunyi farin ciki sosai, anyi bikin suna an kare, Aisha ta roki Don alfarma asa sunan Haseena, ya amince dari bisa dari, ya ta ci suna Haseena

Wannan karanma Haseena nada wata bakwai Aisha ta samu ciki, still ta kara haihuwar ya mace wacca ta ci sunan mahaifiyar Aisha wato Hameeda, ana kiranta da Ummi
Chapter 39 · 0% Book details