← Book details Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 40

Sashe 21

Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yar dariya ya subucewa Ammi tana fadin yaron nan karka kashe ni mana

Ya zauna gefen Aisha yana fadin haba Ammi taya zan kashe ki

Kallan Aisha ya yi sai tai murmushi ta kawar da kanta

"Yen mata babu gaisuwa yau"

"Ina kwana"

"Sai dana roka"

Ammi ta mike "muje mu yi breakfast ko"

Duk suka tashi suka wuce Dining suka zauna, Ammi ta shiga serving Aisha bayan ta gama, ta shiga kokarin serving din Don, Don ya dakatar da ita

"Ammi ki huta abinki, ki bar Aisha ta yi serving dina"

Ta harareshi cikin wasa "wai kai meyasa ka cika son bata wahala ne, baka tunanin ba ita kadai bane"

Ammi ta cigaba da serving dinshi bayan ta gama ta yi serving din kanta

Ta bangaran su Haseena kuwa sun dawo gida, Feedo ta hada musu shisha suka zauna falo suna sha suna hira

Haseena ta ce Feedo akwai wani cin amana da yaudarar da aka yi min, ba zan taba yafewa ba

"Fada min su waye suka miki?"

"Wata Kawata ce sunanta Balkisu, ta ci amanata, ta damfare ni kudi har naira million uku"

"Garin yaya?"

Nan take Haseena ta bata labarin abin daya faru, Feedo dariya ta yi ta ce amma ke shashasha ce, wallahi da nine ke batar da ita zan yi

Haseena ta ce to yanzu miye abin yi?

"Kawai zan sa yarana ne suje su kama min ita su kawo ta har gabanki ta nemi gafarar ki, ko hakan bai yi miki ba"

"Eh hakanma ya yi, to yaushe za'a dakko min ita?"

"Ko yau idan kina bukata za'a dakko ta, kawai bani hotonta da address dinta"

Haseena ta dauki wayarta ta nemo hoton Bilkisu ta mikawa Feedo wayar

"Ga hotonta"

Feedo ta amsa wayar tana kallo

"Wannan ai nasanta, ba a Gwarimpa take ba"

"tabbas anan take, to ai shikenan wannan mai sauki ne, bari na tura musu hotonta da address dinta"

"Dakyau my Feedo Allah yabar zumuncin mugunta"

"Amin"

Haseena ta mike "to ni bari naje can gidan naji da Aisha"

"To sai kin dawo"

Haseena ta fita Feedo ta cigaba da zukar shishan ta

Bayan su Ammi sun kammala yin breakfast suka dawo falo Ammi da Aisha suka zauna, Don ya ce bari ya je ya dawo

Ammi ta kira Sunanshi ya juyo yana kallanta "ma'am Ammi"

"Yaushe zaka yiwa kanka fada ka fara neman na kanka"

Don ya yi murmushi ya kalli Aisha "sai ranar da dana yazo duniya, kinga lokacin ai girma ya zo ko Ammi"

"Umar Allah ya shirye ka"

"Amin mamana na kaina"

Ya fita Ammi ta bishi da kallo, Aisha ta shafa cikinta

"Baby babanka na birge ni, ka fito kamarshi"

Ammi ta juyo ta kalli Aisha

"Me kika fada?"

Aisha ta dukar da kanta cike da kunya ashe maganarta ya fito har Ammi ta ji

"Nafi so Baby ya fito kamarki, da tarbiyar ki da kyawawan dabi'unki, idan ya fito kamar babanshi zaki sha wahala"

Aisha murmushi kawai ta yi

Feedo ta gama shan shisha, ta tashi ta shiga bayi tai wanka ta sauya kaya, da alamu fita zata yi, tana shigowa falo ta ci karo da Don, tsorata ta yi sosai zata yi magana ya dakatar da ita

"Wato Feedo ni zaki ciwa mutunci, ki je har gidanmu gaban mahaifiyata, gaban mata ta, shegiya yaushe mahaifarki keda guarantyn daukar ciki, Feedo sai na gwada miki ni nafi ki bariki"

"Ni dai ka yi hakuri, na yi kuskure"

"Na yi hakuri fa kika ce, ashe ma bansan me nake yi ba"

"Don karka yi min wani abu, ko kashe ni ka yi aikin banza ka yi tunda kudi aka biya akan naje gidanku na yi karyar ka yi min ciki"

A rikice ya kalleta "waya saki?"

Shuru Feedo ta yi tana tunani, tambayarta ya yi a karo na biyu "na ce miki waye ne?"

"Wasu ne, ban san su ba, ban san ya suke da kai ba, amma kamar akwai wani abu tsakaninka dasu"

Don ya ce karki raina min hankali mana, karki mayar dani karamin yaro

"Wallahi dagaske nake fada maka, sanyani aka yi, kuma bansan su ba"

"Ok, na ji, yanzu taya zanyi na gansu"

"Nima ban sani ba amma ka bani lokaci zan yi bincike na gano su"

"Baki da numbansu"

"A'a banda shi, basu bani numbansu ba, amma akwai ta hanyar da zan gano su"

Don ya ce to na baki lokacin kadan ki gano su idan ba haka ba sai na kashe ki

Yana gama fada ya juya ya fice, tai yar dariya "shashasha kawai, kafin ka kashe ni, ni zan kashe ka"

Ta ja karamin tsaki ta dau wayarta da makullin motanta ta fita

Ammi da Aisha zaune a falo suna hira sama sama, sallama suka ji hade da bude kofar falon, suka mai da kallansu kofar falo

Haseena ce ta shugo fuskarta dauke da annuri

Ammi ta ce "yau Haseena ce a gidan"

Haseena tai murmushi "Ammi ni ce, ina wuni"

"Lafiya laiu, ya kwana biyu"

"Ammi ai kwana biyun nan bana jin dadi"

"Ayya kuma Umar bai fada min ba"

Haseena ta zauna kusa da Aisha

Aisha ta ce ina wuni Aunty

Haseena ba yabo babu fallasa ta ce lafiya lau yar uwata ina ta missing dinki, na kosa ki haihu ki dawo gida, gidan babu dadi da babu ke

Aisha ta danyi murmushin karfin hali ta kawar da kanta daga kallan Haseena

"Abba fa"

"Ai Abbanku kwana biyu ayyuka sunyi masa yawa, babu shi a wannan kasar baya wachcan kasar"

"To Allah dai ya bashi nasara"

"Amin"

Haka Haseena ta wuni a gidan har wurin karfe biyu na rana tana neman hanyar da zata bawa Aisha magani

Abincin rana ya kammala Ammi ta ce su tashi suje Dining, Haseena ta dauki Jakarta ta cusa hannu, kwayar maganin ta ciro daga cikin gidanshi guda biyu, ta makale a hannunta

Duk suka tashi suka wuce Dining suka zauna, Haseena ta shiga serving Ammi

Ammi ta ce ai dakin huta ranki Haseena

"A'a Ammi karki damu"

Aisha ta fara serving kanta, sai Haseena ta dawo kanta

"Har kin yi serving kanki ashe baki jira ni ba"

Aisha tai murmushi "nagode tunda kin yi niyya"

Itama Haseena murmushi tai "to bari na zuba miki juice, kinsan a halin da kike ciki yanzu kina bukatar fruit"

Haseena ta dauki glass cup sannan ta jawo jug din juice, ta tsiyaya juice a cikin glass cup sannan ta jefa kwayoyin Cytotec, kawo glass cup din ta yi gaban Aisha ta aje

"Yauwa yar uwa gashi"

Aisha tai murmushi "nagode"

Haseena ta je ta zauna ta shiga serving kanta amma hankalinta na kan Aisha

Don tafiya yake yi a mota yana tunani

"Anya Feedo ba karya take min ba, to su waye zasu biyata akan tazo gidanmu ta ce tana da ciki, miye hadina dasu, koma miye ne nan da kwana biyu zan koma saita fada min ko na yi mata duk abinda yazo min zuciya"

Ya cigaba da tafiya

Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Haseena a lokacin da ta ga Aisha ta kafa glass cup na juice a

Murmushi ta yi tana kallan Aisha cikin wani yanayi fadi take a zuciyarta "burina ya cika, dama nayiwa kaina alkawarin ba zaki taba haihuwar cikin nan ba, yanzu dole zai zube, dole nema ya zube"

Aisha duka ta shanye juice din, ta ji dadi sosai saita kara zuba wani tasha

Ammi ta ce da alamu kinji dadin juice din nan

Aisha ta ce eh Ammi, na ji dadinshi sosai da sosai

"Zan sa a rika miki kullum"

Haseena ta mike "bari baje ta falo"

Ammi ta kalleta "baki cinye abincin ba"

"Ammi na koshi, ban cika cin abinci ba sosai"

Haseena ta koma falo ta zauna tana jin wani farin ciki a ranta

Bayan Ammi da Aisha sun kammala cin abinci suka dawo falo suka sami Haseena

"Har kun gama kenan"

"Eh mun gama"

Prof Attahir da Mum da Lastborn suka shigo cikin sallama, Cikin Murna Aisha ta mike taje da sauri ta rungume Prof

Mum ta ce Aisha haka zamu yi dake, murmushi Aisha ta yi ta rungume Mum

"Kema ai zan rungumeki"

Prof ya ce mamana kinyi kyau sosai

Lastborn ya marairaice "Aunty baki ganni ba"

Aisha ta ja kumatunsa tana fadin "I miss u Lastborn, ya kiriniya?"

"Ni bana kiriniya"

Suka zauna suka shiga gaisawa da Ammi

Mum ta ce Hajiya ya kokarin kulawa da Aisha?

Ammi ta cw Habadai wani kokari, ai hakkina ne na kula da ita

Prof ya ce Yayana ya wuce ko?

"Eh ya wuce, wallahi tafiyar yana yawa, na gaji'

Mum ta ce ayi ta hakuri dai, dan kasuwan kenan

Haseena sauka ta yi daga kujera ta duka ta shiga gaida su, suka amsa cikin farin ciki suna yaba hankali da natsuwarta, Allah ya hada yarsu da abokiyar zama ta gari

Suna ta hira a tsakaninsu sai ga Don ya shigo, Prof na ganinshi yai murmushi yana fadin Babana kwana biyu ko zuwa gaishe ni baka yi

Don ya sosa keya "Uncle ayyuka ne suka min yawa"

"Fada min wani ayyuka, Babana wani aiki ka samu kana yi ni ban sani ba"

Shuru Don ya yi Ammi ta ce ka yi masa magana ko kai zai ji maganarka, bai aikin komai

Prof ya ce haba Babana, meyasa kake haka, kanafa shirin zama uba ne, Idan ka gyara rayuwarka yayenka zasu yi alfahari da kai, hakadai Prof ya cigaba da yiwa Don nasiha

Zufa ne ya shiga ketowa Aisha, wani azababben ciwon mara ne ke addabanta, tun tana jurewa harta fara kuka, hankalin kowa ya dawo kanta

Don ne ya fara karasawa wurinta ya rungume ta "Aisha meke faruwa?"

Cikin muryar kuka ta ce marana yana ciwo

Ammi ta karaso ta rike ta, abu sai kara tsananta yake yi, ta fara ihu, kowa ya tsaya a kanta ana mata sannu

Murmushi Haseena ta yi yauwa, wasa ya fara, fashewa ta yi da Kuka tana fadin a kira likita a taimaki yar uwata
Chapter 21 · 0% Book details