Sashe 17
Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani bakin ciki ya dabaibaye zuciyar Don, ya banbareta daga jikinsa ya juyo da sauri yana kallanta
"Kina fada min cikina dake jikin Aisha shine bakya so? Ko kunyar idona baki ji ba"
Ware ido ta shiga yi "to ba kaima na ga baka son cikin ba, so fa kake a zubar"
Ya watsa mata wani mugun kallo "Nina fada miki bana son cikin?
"Ka fada a gabana naji"
"To ki sani ba wai cikin ne bana so ba, haihuwar ce ban shirya yi ba yanzu, kuma naga alamar kamar akwai mugunta a zuciyar ki, karki kuskura na kamaki da laifin cutar da Aisha"
Ya shiga bayi bai jira ya ji me zata ce ba, ta bishi da kallo, idonta ya ciko da ruwa, zube gwiwowinta ta yi a kasa tana mamakin yadda komai ya juye kanta, ta fara tunanin wani hanya kuma zata bi yanzu don ganin burinta ya cika
Haka rayuwa ya kasance har tsawon wata uku, lokacin cikin Aisha na neman wata hudu, har wannan lokacin Don bai kara zuwa gidansu Ammi ba, Aisha ta yi kyau sosai tsabar kulawar da Ammi take bata amma fa tana kewar mijinta, tana son ganinshi, haka dai take zaman kadaici
Haseena kuwa yanzu ta canza takunta, zuwa tai ta yi odan kayan mata tana amfani dasu, sannan ta koyo wasu salo da dibaru kala kala duk akan Don, hakan da ta yi a tunanin ta shine mafita agareta, kuma hakan ya kasance don a kowani lokaci yana gindinta, ko'ina ya je zai dawo ya nema ta bashi, yana yin yadda yake so, amma fa ya yi kewar Aisha, ya rasa dalilin daya sa karamar yarinya take jagula masa lissafi, gashi yana son zuwa wurinta amma yana tunanin Ammi, daga karshe dai ya yanke shawarar zai je kome zai faru ya faru
Ammi tana mamakin har tsawon wannan lokacin Haseena bata kara zuwa ganin jikin Aisha ba kamar yadda a baya take nuna damuwa a kanta, kuma kota waya bata kira ba, har yanzu abin na bawa Ammi mamaki
Ammi da Aisha zaune a falo suna hira sama sama, Ammi ta ce nafara odan kayan Baby fa'
"Me da me kika yi oda?"
"Durowa, keke, bath da sauransu" Ammi ta mike "bari naje na dakko dayar wayata na nuna miki"
"Ok"
Ammi ta wuce Aisha zaune tabi Ammi da kallo tana murmushi tana yaba yadda sirikarta take kulawa da ita, jin motsin an shugo yasa ta juya da sauri, Don ta gani, wani farin ciki ta ji a ranta, ya karaso da sauri ya zauna gefenta ya rungumeta
"Haba matata meyasa zaki guje ni, ni ina can ina ta kewarki, ke kuma kina nan kina ta jin dadin ki kin manta dani"
Marairaicewa ta yi ta yi dai dai da ido "ba kai ka ce baka son Babyna ba"
Yadda ta yi maganar ya bashi sha', awa, manna mata kiss ya yi a bakinta "taya zan ce bana son Babynki, bayan Babyna ne nima, kawai dai ki fahimce ni ban shirya zuwan Baby ba yanzu, ki bani hadin kai mu zubar dashi, kinga nan da shekara uku zuwa biyar saina kara yi miki wani cikin
Da sauri Aisha ta janye jikinta daga nashi "ka wuce bana son ganinka, ni nafi son Babyna akan kowa, ba zan taba baka hadin kai ba a kashe dana" hawaye ya ciko idanunta
"Yakamata ki fahimce ni, Aisha ke kadai ce macen da nake tunani a duniya kuma kona shirya haihuwar Baby kece nake so ki zama mahaifiyarsa, ke nake sha'awar ki zama uwar yayana, na yaba da tarbiyyar ki"
Ammi ce ta shugo rike da waya, tana ganin Don ta hada rai "Me kuma ya kawoka?"
"Haba Ammi bamu gaisa ba kuma naga nan ai gidanmu ne bai kamata ki tambayeni meya kawo ni ba"
Ta galla masa harara "naji nan gidanku ne daga yau na koreka, karka kara zuwa"
Ya kalleta cike da mamaki "Ammi me na yi haka da zaki yanke min wannan hukuncin?"
"Au bakama san me ka yi ba, a gabana, a gaban Mahaifinka a gaban kowa ka ce baka son jikana har kana fada mana a zubar, au kai bakama dauke shi wani abu ba, ya yi kyau, to sai ka fita"
"Ammi naji zan fita amma da matata zan fita, gaskiya na gaji"
"Au jarabar taka ce ta motso ka shine ka lallabo ka zo, to babu inda zaka je da Aisha tana nan gidan"
"Gaskiya ni dai a bani mata ta, kuma ni bada izinina aka dakko min mata ba, a karkashina take, ni nake da iko da ita"
Ammi ta tsaya tana kallanshi cike da mamaki "to shikenan zan gani yau ni ce na haife ka ko kaine ka haife ni"
Ta samu wuri ta zauna tana kallanshi, kallan Aisha ya yi "tashi mu tafi" Aisha ta kalleshi ta kalli Ammi, Ammi dai nata faman kallan ikon Allah
"Ke na ce ki tashi mu tafi ko?"
Tashi Aisha tai da sauri ta koma wurin Ammi ta rungume ta
"Ammi ni bana so na tafi, zan zauna anan"
Ammi ta rungumeta tana shafar bayanta "kina nan gidan babu inda zaki je"
Cikin tsananin fushi Don ya tsaya yana kallan Aisha
Don ya kulu sosai, ganin rashin hakurinsa ba zai yi amfani ba yasa ya saukar da kai
"Ammi nifa danki ne, ki tausayawa min ki bani Aisha, ita ce kawai jin dadi na"
Ammi ta galla masa harara "me zaka yi da ita?"
Shuru ya yi yana dan sosa kai "nidai Ammi ki taimaka min, idan ba haka ba zan dawo gidan nan na tare"
"Wallahi ka dame ni harka fara saukar min da ciwon kai, don Allah ka tafi"
Wani bakin ciki ya tsayawa Don a rai, ya fice bai ce komai ba, Aisha tabi Don da kallo, tausayinsa ya dabaibaye mata Zuciya kamar ta tashi ta bishi amma babu dama, sai kuma ta tuna yana son ya rabata da Bebinta ne, sai haushinsa ya kamata, Ammi ce ta kalli yanayin fuskarta
"Ko so kike ki bishi"
Ta girgiza kai da sauri alamun a'a, nan take Ammi ta shiga nuna mata kayayyakin Baby da ta fara oda, aikuwa kayan sunyi matukar kyau sosai, Aisha ta yi farin ciki da ganin kayan
Don wurin Wizzy ya biya yana masa complain akan abin daya faru
Wizzy ya ce haba Don miye wani abin bata rai anan, ga mata a gari, akwai fara, akwai baka, akwai ja, akwai yaluwa, akwai wankar tarwada, akwai kore duk kallar da kake so babu wachca ba za ka samu ba sai ka tsaya kana bata lokacinka a kan wata Aisha
Don ya girgiza kai "ba za ka gane ba Wizzy, nima narasa ya akayi, ban taba jin mace a zuciyata ba kamar yadda nake jin Aisha, wallahi rashinta a tare dani damuwa ne, Ammi taki ta gane"
"Haba Don yawa ne wannan, da girmanka, ni Aishan nan ma fa ba wani kyau ne da ita ba Haseena ma ta fita kyau"
Haushi Don ya ji a zuciyarsa "matar tawa ce bata da kyau?
Wizzy ya ce tooo Allah ya huci zuciyarka
"Kenan da kaje gidana kalle min mataye ka yi har ka gane daya tafi daya kyau"
"ba kalle su na yi ba da yawa, kawai a baiyana yake, kallo daya nayi musu na gane daya tafi kyau"
Don karamar tsaki ya yi ya fice batare daya kara ce masa koma ba
Don tuka motarsa yake yana tafiya yana tunani "to wai ma meyasa zan batawa kaina lokaci akan ta, duk zuciyata ta damu kamar ita kadai ce mace, to meyasa ta banbanta a cikin mata? Ya tambayi kansa, sai wata zuciyarsa ta ce masa
"saboda ita ce mace na farko daka fara budewa sabuwa tal a leda, kai kadai kawai ka Santa"
Wani farin ciki ya ji ya ziyarce shi gami da yin wani ajiyar zuciya fadi yake a kasar zuciyarsa "ina alfahari dake matata"
Hankalinsa ya kai kiran sallahn Azahar da ake yi, samun wuri ya yi yay parking sannan ya fito ya shiga cikin masallaci
Yau Aisha dambun shinkafa tasa ayi mata, ya ji gyada da zogale, ai kuwa ta ci sosai har tai gyatsa, can kuma ta cewa Ammi tana son shan chocolate, Ammi tasa aka kawo mata gari guda ai kuwa Aisha tayi tasha tana jin dadi
Haseena kwance kan gadon ta tana tunanin meya faru ita har yanzu shuru babu labarin ciki, harta fara tunanin ta je asibity ta bincike kanta ko kalau take, sai kuma ta basar da zancen data tuna mijinta baya son haihuwa yanzu tana cikin wannan tunanin Don ya shugo, tashi ta yi ta je ta rungumeshi
"Sannu da dawowa mijina"
"Tanx" kawai ya ce mata sannan ya banbareta daga jikinsa yaje ya zauna kan kujeran dake dakin yana cire takalminsa, zuwa ta yi ta zauna gefensa
"Baka da lafiya ne?"
Ya juyo ya kalleta "me kika gani?"
"Na ga kamar baka cikin farin ciki, kamar akwai damuwar dake damunka"
Ya busar da wani iska daga bakinsa "babu komai"
Shafa shi ta shiga yi, ya rike hannunta "stop"
Ta tsaya tana kallansa cikin mamaki "na yi maka wani laifi ne?"
"Kawai I am not in d mood"
Ya jingina kansa da jikin kujerar kai hannu ta yi ta taba shi tana kokarin shafa shi
"Wai na tambayeki mana?"
"Ina jinka"
"Dani dake wa yafi wani jaraba?"
Shuru ta yi bata ce komai ba, sai ta janye hannunta daga jikinsa
"In kara tambayarki mana?"
Kallansa kawai ta yi, fasa yin tambayar ya yi ya mike ya shiga bayi ta bishi da kallo, kawai sai tausayin kanta ya kamata, ta fara tunanin kenan duk abinda takewa Don baya gani, duk yadda take kyautata masa da son sashi farin ciki, tuni hawaye ya fara bin kumatunta
Hankalinta ne ya kai kan wayar Don daya manta dashi akan kujerar, daukar wayar ta yi ta shiga dubawa, ai kuwa ta yi sa'a babu security, ta shiga watsapp dinshi tana duba mutanan da yake chat dasu, hankalinta ya kai kan wata yarinya, bude hoton ta yi sai yanzu ta gane hoton Feedo ne, jikinta na rawa ta dakko wayarta ta kwashe numban sannan ta ajje masa wayarsa ta koma kan gado ta kwanta