← Book details Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 40

Sashe 11

Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don zuwa ya yi ya samu Abba akan zai tafi lagos yin wata harka na kasuwanci, farin ciki Abba ya yi don tunda yake Don bai taba tunkararsa da irin wannan maganar ba, Don ya yi karatunsa daga degree zuwa masters dakyar amma baya yin aikin komai, a tunaninsa taya mahaifinsa yana da kudin da zai iya ciyar da gari guda kuma ya yi aiki, ai aiki sai yayen talakwa ko wa'inda arzikimsu bai kai ba, Abba ya goya masa baya dari bisa dari hakama Ammi, tasa masa albarka

Ranar Aisha kulla kanta ta yi a daki, tana tunanin irin zaman da zata yi da Haseena, kuma gashi tana son bawa Don hakuri amma bata da numbansa

Haseena kuma hankalinta ya tashi da ta ga Don bai dawo ba, gashi dare ya yi, yanzu karfe goma, kiransa ta shiga yi yana danna mata user busy daga karshe ya saka numbobinta blacklist, hankalinta ya kara tashi, ta ga har sha biyu yana neman yi

"Na shiga uku, miye nawa a ciki da zai hada dani yana hukintawa"

Ta shiga safa da marwa

Don da Wizzy wurin karfe daya na dare suka tafi Club, kamar kullum matan wurin daga su sai pant da breziya suke rawa, suna ganin Don, suka yo wurinshi, wasu suna shafa shi, wasu suna rawa a gabanshi, sai watsa musu kudi yake yi yana shafa bayansu

Washegari Aisha ta fito ta shiga kitchen domin yau ta tashi tana jin yunwa, tana cikin hada breakfast Haseena ta shugo cikin fushi

"Ina kwana Aunty?"

Ta galla mata harara "ba zan amsa ba, da ban kwana ba zaki ganni, shashasha kawai, kinje kin dafawa mijina abinci kin cika uban gishiri kina son kashe mu, kinsa mijina yaki dawowa gida, to wallahi idan bai dawo ba yau sai kin gane kuranki dani"

Tunda Haseena tazo ta fara magana Aisha ta dukar da kai hawaye na fita daga idanunta, Haseena ta ja tsaki ta fita, dakyar Aisha ta karasa girki ta wuce dakinta ta fada kan gado tana kuka, ta kasa cin komai

Don da Wizzy kuwa sun dade a lagos don jirgin farko suka biyo, Naira marley mawakin kudu da ya yi suna a duniya da kanshi yazo ya dauke su daga Airport ya kawo su gidanshi dake Victoria island, ya yi farin cikin ganinsu, musamman Don da childhood freind dinshi ne kuma abokin cin mushensa ne, yasa aka kawo musu haddan Wiwi da aka nade su da dala, da kuma nau'o'in abinci da tarin wine da drinks

Bayan sun gama shan Wiwi ya rarike musu ciki suka fara cin abinci, sun ci sun koshi sosai sannan Naira Marley ya dauke su ya kaisu wani sabon wurin hutawa da aka bude, kamar ba a Nigeria ba ga tarin yen mata da suke kaiwa da dawowa

Aisha wuni ta yi a daki sai wurin la'asar da ta ji yunwa na neman ya yi mata illa, ta tashi ta je kitchen ta debo breakfast din data yi da safe ta ci ta koshi sannan ta yi sallah ta kai wa Allah kukan damuwarta

Da daddare Aisha ta fito wanka kenan Haseena ta shugo cikin fushi ta shiga masifa

"Ba zai yuhu ba ki yi laifi ya shafe ni, dole ki je ki nemo min mijina, maza fita kije ki nemo shi"

Aisha ta shiga yin kuka "ni bansan inda yake ba"

"Babu ruwana da baki san inda yake ba fita zaki yi kuma karki dawo sai da mijina"

Hankalin Haseena ya kai kan sallamar da ake yi a falo, "karki fito bari naje na duba wake sallama na dawo"

Haseena da fitanta ta ga Prof Attahir da Mum, bata gane Iyayen Aisha bane

"Sannunku"

"Yauwa sannunki"

Duk suka zauna a kujeran falo tana musu kallan rashin sani

Mum ta ce kai ke kadai ce, ina yer uwar taki?

"Babu kowa a gidan, ni kadai ce"

Prof Attahir ya ce to ina suka je?

Da gudu Aisha ta shugo falon saboda jin muryar iyayenta, sai fadawa ta yi jikin Mum tana kuka, Haseena ta zaro ido, Mum ta dago Aisha tana kallanta

"Yata meya faru?"

Hankalin Prof Attahir yana kan Aisha "mamana meke damunki'

Aisha ta kalli Haseena dake tsaye tasha jinin jikinta, Haseena ta yi saurin karbar bakinta

"Tunda me gidanmu ya yi tafiya jiya take ta kuka, tun dazu nake dakinta ina rarrashinta, zuwanku ne ma yasa na fito"

Mum ta tsurawa Haseena ido "amma ai kin ce babu kowa a gidan"

Haseena ta ce na fada muku babu kowa ne saboda bana son ku ga halin da take ciki ku daga hankalinku

Prof Attahir ya ce taya kika yi kikasan mu iyayenta ne?

Haseena ta yi murmushi "Habadai ya ba zan sanku ba kuna Iyayen mijina, Mijina ya nuna min hotunan danginsa gabadaya"

Prof Attahir ya kalli Aisha da idanunta suka yi ja "mamana hakane duk abinda ta fada?"

Aisha ta kalli Haseena sannan ta kalli prof Attahir ta gyada kai alamun Eh

"To mamana ai hakuri ake yi, baki ga yer uwarki ta yi hakuri ba, kuma ai zai dawo, uncle dinki yau yake fada min ya tafi lagos kulla wani kasuwanci, ki yi masa addu'ar kin ji"

Aisha bata ce komai ba, Haseena ta shiga kitchen ta kawo musu kayan marmari da drinks da sauransu sannan ta zauna ta sake jiki suna hira sosai, sun kai wurin karfe goma sannan suka yi shirin tafiya, Aisha ta hau yin kuka sai dai su tafi da ita, suka yi ta rarrashin ta sannan suka kara damkawa Haseena amanarta, dakyar dai ta barsu suka wuce

Haseena wani rankwashi ta yi wa Aisha a kai, sannan ta ja kunnanta daya da karfi, Aisha sai ihu take yi

"Idan har kika kuskura kika fadawa wani wani abu dake faruwa sai na miki tsinannan duka, shashasha kawai"

Haseena ta ja tsaki ta wuce dakinta, Aisha rusune a falo tasa kanta a tsakankanin gwiwowinta tana ta faman kuka

Haseena ta tsaya a tsakiyar dakinta tana tunani "au ashe tafiya ya yi, kuma ya je kulla wani kasuwanci, to yaushe zai dawo kenan" sai ta shiga gwada numbobinsa amma basa shiga, ta shiga safa da marwa

Aisha daga karshe ta tashi ta koma dakinta, ta kwanta tana tunanin iyayenta

Don da Wizzy, Naira Marley ya kaisu wani club da mata tsirara suke rawa, eh lallai iskancin Lagos ya fi na Abuja, Don ya zabi lafiyayyun yen mata da zasu tayashi kwana

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya har tsawan kwana goma, Aisha ta rame, ta yi wani fari, zazzabi ya tasa ta a gaba, Haseena kuwa kullum saita kira Don amma har yanzu bai cire ta a blacklist ba, ga tsinannan azaban da take bawa Aisha, Aisha tsoron Haseena take kamar ita ce zata zare mata rai

Don da Wizzy suna ta rayuwarsu a Lagos, Wizzy ya yi mamakin ganin Sallahn jam'i baya wuce Don, kullum sallahnsa sau biyar a masallaci yake yi, hakan yasa jefi jefi yana binshi masallac, kusan kullum sai ya yi tunanin Aisha, amma yana mantawa da Haseena Matarsa ce, Sannan iskancin Don ya karu, shan Wiwi da zuwa club, wasa da yen mata duk sun karu, kuma akidarsa na rashin son haihuwa ya karu, a ganinshi duniya yanzu aka fara, yana da sauran lokaci, gwara ya ci karanshi ba babbaka bayan wasu shekaru sai ya haihu

Haseena tasa Aisha ta yi mata sinasir da miyan gyada, Aisha na cikin yin aikin, zuciyarta ya rika tashi, ta kasa control din kanta, sai ta barke da amai, tun daga falo Haseena take juyo karan aman, da sauri ta tashi ta shiga kitchen din ta tsaya tana kallan Aisha cikin mamaki dake amai kamar zata fito da kayan cikinta

"Ke kada dai ace ciki kika yi?"

Haseena ta karasa wurin Aisha bayan aman ya yi sauki, ta shiga kallan kwayar idonta tana kallan tafin hannunta, Haseena fita ta yi tabar kitchen, Aisha ta cigaba da aikinta jikinta na rawa, can sai ga Haseena ta dawo da abin gwajin fitsari na ciki, ta mikawa Aisha wani karamin roba

"amsa roban nan ki tsugunna ki yi fitsari a ciki"

"Aunty bana jin fitsari"

"Don uwarki ina wasa dake ne, amsa ki yi, kwakulowa zaki yi"

Hannun Aisha na rawa ta amshi roban

Aisha ta tsugunna ta rufe jikinta da zanin jikinta, ta yi fitsari a roban, bayan ta gama ta tashi

"Aunty na gama" Haseena ta galla mata harara ta je wurin fitsarin ta duka sannan ta tsoma abin gwajin cikin a cikin fitsarin sannan ta fito dashi ta tsaya tana kallo, ta dade tana kallo amma shuru babu amsa, fita ta yi ta dawo falo ta je wurin AC ta tsaya saboda result ya fito amma shuru, gabadaya babu wani layi daya fito, wurin na nan yadda yake, hankalinta ya kasa kwanciya

Aisha bata san me Haseena take nufi ba data sata ta yi fitsari ba, kawai ta cigaba da aikinta, sai ga Haseena ta shugo a fusace

"Bar aikin nan, zo mu je asibity"
Babu musu Aisha ta ajje aikin tabi Haseena har harabar gida, Haseena da kanta ta jasu a mota har zuwa asibity

Da isarsu asibity Haseena ta yiwa likita magana akan su bincika mata Aisha ko tana da ciki

Nan aka shigar da Aisha dakin gwaji, aka shiga bincikata

Haseena ta shugo cikin Office din Likita jikinta na rawa ta zauna tana son sanin sakamako, Likita ya mika mata result ta amsa, cikin sauri ta shiga dubawa, Haseena ta mike a rikice

"Na shiga uku na lalace, tawa ta kare, Don Allah Doctor ka taimake ni a cire cikin nan, wallahi zan biya ko nawa ake bukata"

Likita ya girgiza kai, "ki yi hakuri bana abortion"

"Doctor zan biyaka daga million daya zuwa sama ka taimaka min a zubar da cikin nan"

"Zaki iya fitar min daga office, na fada miki bana zubar da ciki"

Ta watsa masa kallon banza sannan ta ja tsaki, ta fita ta samu Aisha tsaye a harabar asibitin

"Yau sai kin ci ubanki dani, wato ciki kika yi Aisha"

Aisha ta zaro ido "Aunty ina da ciki ne?" Sai kuma ta yi mrmushi

Haseena ta ce au murmushi ma kike yi

"Aunty ina son baby sosai"
Chapter 11 · 0% Book details