← Book details Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 40

Sashe 22

Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Ammi ta je ta dauki waya ta kira likita tai masa bayani, cewa ya yi a kawo ta asibity da sauri, nan take aka fara cuku cukun kai Aisha Asibity, Haseena sai kuka take yi, Don ya rikice tunda yake hankalinsa bai taba tashi irin na yau ba

Cikin kankanin lokaci aka kawota Asibity, a ka shigar da ita wani daki likita ya shiga bincike

Ammi, Don, Haseena, Mum da Prof duk hankalinsu a tashe, Ammi bata san lokacin data fashe da kuka ba, tunaninta kar ta yi asarar jikanta Mum ta rungumeta tana rarrashinta

"Ba kuka zaki yi ba, addu'ar zaki yi"

Prof ya kasa cewa komai, Idan an barshi shima kukan zai yi amma ya jure yana tunanin halin da mamanshi take ciki, tsananin tausayinta yake ji

Don ya jingine kansa da bango, ya rasa meke yi masa dadi, wani zafi da radadi yake ta ji a zuciyarsa, Haseena ce ta karaso ta tsaya gefenshi idanunta sunyi jawur tsabar kuka

"Mijina ka kwantar da hankalinka, Aisha zata samu lafiya"

Juyowa ya yi ya kalleta "ina tsoron ta fada wani hali, ina tsoron ta rasa Babyn mu"

Haseena ta zaro ido Cikin mamaki "baka ce baka son Baby yanzu ba"

"Haseena yanzu ina son Baby, Aisha ta kwadaita min son Baby, ina son abin dake cikin Aisha kamar rayuwata"

Gaban Haseena ya yi wani mummunar bugawa fadi ta yi a zuciyarta "ashe gwara dana lallata cikin, Allah nagode maka, yanzu tunda yana son Baby dole zan yi kokari na yi"

Ta ce karka damu ba zamu rasa Babyn mu ba, za'a haifa mana Baby lafiya

Feedo ta tsai da motanta a kofar gidansu Bilkisu, bada dadewa ba sai ga Bilkisu ta fito, bude motar ta yi ta shiga

"Kawata ya dai"

Feedo tai murmushi "nazo miki da wata magana ne"

"Ina jinki"

"Kin san Haseena matar Don"

Bilkisu ta ce niko na san Haseena karamar yar bariki amma ke a ina kika santa

"Mijinta saurayina ne, a baya ma munyi dadiro dashi, to tazo ta hada kai dani ne akan mu cutar da kishiyarta sannan ta kawo min kararki akan kin damfareta kudi har naira million uku, tana son a hukuntaki ni Banma san ke ba ce sai data nuna min hotonki, kuma kinga dai ni da ke ai amana ne, babu yadda za'ai na cutar dake"

Bilkisu ta dafe kirji "ni Haseena take so a hukunta, ai kuwa saina tona mata asiri"

Feedo ta ce haba ta wurina ai wannan kauyancine, nidai yanzu abinda nake so dake, so nake mu hada kai dake, ina son Don sosai ba zan iya rabuwa dashi ba, amfani zanyi da Haseena na rabata dashi sannan na rabashi da dayar matarshi Aisha, ni kuma saina aure shi

Bilkisu ta ce to ke Idan kin aureshi ai kinci riba, to ni mecece ribata

Feedo ta danyi murmushi "kwantar da hankalinki mana yan mata, na yi miki alkawari zan baki million goma indai har na auri Don

Murmushi Bilkisu ta yi ta ce na yarda kuma a shirye nake na yi duk wani abinda kika sani

Feedo ta ce dakyau ta wurina, ta ciro wasu kudi ta mika mata

"Ga wannan ni zan tafi, zan fara tsare tsare na, Idan amfaninki yazo zan neme ki"

Bilkisu ta amsa tana godiya sannan ta fita, Feedo ta ja motarta ta wuce

Bilkisu ta bi ta da kallo "ji shashasha, waya fada miki akwai amana a bariki, kawai mu hada kai muyi aiki ke ki auri Don ni kuma ki hada ni da million goma, gani jaka"

Taja tsaki ta shiga gida

Likita ya fito da sauri suka karaso wurinshi, kowa ya tasa kunne yana son jin me zai fada

Likita ya kalli Ammi muje Office dina mu yi magana

Ammi ta ce zaka iya yin magana kowa daka gani anan dan gidane, duk daya muke, Likita ya ce akwai abinda nake so mu tattauna ne

Don ya ce Likita ya mata ta take?

Likita bai bashi amsa ba ya kara gaba Ammi tabi bayanshi

Mum ta ce oh ni Allah yasa lafiya

Prof ya kasa cewa komai

Don kasa tsayuwa ya yi, ya durkusa ya rike kai kamar ya ji sakon mutuwa

Likita da Ammi suka shugo Office suka zauna

"Ya ake ciki?"

"lallai sirikarki ta kasance me sa'a, ban taba ganin macen da Cytotec ya shiga cikinta ba, bai lallata abin dake cikinta ba, amma wallahi Aisha da abin dake cikinta suna cikin koshin lafiya"

Cikin rashin fahimta Ammi ta ce menene Cytotec?

"Wani kwaya ne na abortion, mafi yawa karuwai da yan bariki ne suke amfani dashi wajen zubar da ciki"

Ammi ta ce amma Aisha ba za tasha wani abu da zai cutar da abin cikinta ba

Likita ya ce zai iya kasancewa ba ita tasha kwayar ba, kila wani yasa mata a ruwa ko a abin sha

Shuru Ammi ta yi tana nazari sai ta mike da sauri

"Umar, Umar yana kan bakanshi sai ya rabani da jikana"

A fusace ta fita

Haseena ta karaso wurin Don

"Ni bana son ganinka cikin damuwa, please"

Mikewa Don ya yi ya kalli Haseena "kina damuna don Allah ki barni"

Babu dadi ta ji a zuciyarta sai ta jure ta ce

"Nima fa ina cikin damuwar nan amma ya zanyi"

Ammi ce ta karaso a fusace cikin tsananin fushi, duk kallansu ya koma kanta, kodawa Don mari ta shiga yi tana fadin Umar ba za ka kashe ni ba, ni zan kashe ka kafin ka kashe ni, da sauri Prof da Mum suka karaso, Mum ta rike Ammi

"Haba Hajiya kiyi hakuri koma menene ki bari mu koma gida"

Ammi ta fashe da kuka "Umar zai kashe ni"

Don bai san hawa ba bai san sauka ba, ransa ya baci sosai, idanunsa sunyi jawur, bai ce komai ba shuru ya yi

Mum ta ja Ammi tana rarrashinta gami da kwantar mata da hankali

Haseena kuwa farin ciki ya cika fam a zuciyarta, a tunaninta cikin Aisha ya zube, kuma an gano magani tasha, kenan Ammi na zargin Don, murmushi ta yi gami da ajiyar zuciya "burina ya cika"

Ammi ta shiga dakin da Aisha take, ta sameta kwance a gadon jinya, da sauri ta karasa ta zauna gefenta

"Aisha kina nan lafiya kuma Babinki na cikin koshin lafiya"

Aisha murmushi tai "Ammi na ji a Jikina zan haifi Baby na lafiya, in Allah ya yarda babu wanda zai cutar min dashi"

Ammi ta ce ina son zan fada miki wani magana kuma ina so ki yi min alkawari

"Ina jinki Ammi"

"Daga ni sai ke kawai muka san cikinki yana nan, karki taba bari wani yasan cikinki yana nan, sai dai kowa ya ji kin haihu"

"Wannan mai sauki ne Ammi yadda kika ce haka za'a yi"

"Dakyau sweetie na"

Prof da Mum suka shigo Aisha ta kallesu tana murmushi

Mum ta ce dafatan cikinta yana nan

Aisha girgiza kai ta yi alamun a'a

"Inna lillahi wa Inna ilaihir raji un"

Prof ya ce to tunda Mamana tana cikin koshin lafiya Alhamdulillah, sai dai muyi addu'ar Allah ya kawo wani mai albarka, Allah yasa haka shi yafi zama alkairi

"Amin"

Don yana tsaye kofar dakin jinyar shida Haseena, yana tunanin shiga yana tsoron Ammi, daga karshe ya yi ta maza ya shiga, yazo kusa da Aisha Ammi ta watsa masa wani kallo

"Ka bace min, bana son nakara saka a idanuna"

Don ya kalleta a tsorace "Ammi wai mena aikata, wani laifi na yi ki fada min"

Ammi ta galla masa harara "au bama kasan me ka yi ba, kai kafi kowa sanin abin daka aikata, wallahi Umar kana sani bakin ciki"

Mum ta ce wai meya aikata haka Hajiya, wa'innan maganganun da kika yi sam bai dace ba, aiko akwai matsala saiki bari idan an koma gida sai a zauna a tattauna, a warware matsalan

Ammi shuru kawai ta yi amma tunani fal a zuciyarta

Haseena kuwa tuni ta je ta hau motarta ta wuce, tunda bukatarta ya biya mai kuma zata tsaya bata lokacinta

Likita ya sallami Aisha, da aka zo tafiya gida Ammi tai mamaki da bata ga Haseena ba, da suka je wurin parking ma bata ga motar ta ba hakan ya tabbatar mata da wucewa ta yi

Suka shiga motocin da suka zo suka tafi

Feedo kwance a kan kafet din falonta Haseena ta shigo cikin tsananin farin ciki

"Feedo ina sonki, Allah ya barni tare dake"

Feedo tai murmushi "ki ce bukata ta biya"

"Ai bukata ta biya, yanzu ma daga asibitin da aka kaita nake, ciki ya zube, babu shi"

"Gaskiya na tayaki farin ciki Kawata"

"To yanzu damuwata daya, ya za'ayi na yi ciki?"

"Ciki kike so ki yi?"

"Shi nake bukata"

"To ki mannewa mijinki sosai bayan kin gama al'adarki ba safe ba rana ba dare"

Haseena ta ce duk na yi wallahi, duk jarabarsa har nazo na fara isansa, cewa yake yi ma na fishi jaraba, ammafa shuru babu ciki

Feedo ta ce a zuciyarta "taya zan yarda ki haihu da Don, ai daga ke har Aishan fita zaku yi batare da kun haihu ba"

A zahiri ta ce akwai wani Likita dana sani yana taimakon masu bukatar haihuwa kuma ana dacewa sosai, idan kin shirya sai muje wurinshi

Haseena a zabire ta mike "na shirya, kawai tashi muje"

"Da wurwuri haka"

"Karfe tun yana zafi zafinsa ake lankwasa shi"

Feedo ta ce hakane

Feedo ta mike tsaye, janyo after dress ta yi ta daura sannan ta yafa gyale

"To muje"

"Da kyau Tawan, ina yinki over"

Fita suka yi

Da su Ammi suka karaso gida, duk zama suka yi a falo, Don ya kasa zama, hankalinsa na kan duk wani motsi na Aisha,

Prof ya kalli Ammi "bansan wani laifi Babana ya aikata ba amma ina rokwanki daki yi hakuri ki yafe masa"

Ammi ta ce da kasan me yaron nan ya aikata hankalinka sai ya tashi

"Hakuri ake yi, kuma yana bukatar addu'arki ne, kuma a ganina yaron nan ya sauya ba kamar da ba, kenan Allah yana amsa addu'ar mu"
Chapter 22 · 0% Book details