← Book details Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 40

Sashe 23

Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi ta ce Prof yaron nan fa ka kalli rashin imani, ya nuna baya son abin dake cikin Aisha, hakan yasa na nisanta shi daga ita saboda kada ya cutar da ita, amma ya lallabo yazo kamar abin arziki ya bata maganin da ya yi sanadiyar barewar cikinta

Da sauri Don ya mike "what?" Ya nuna kanshi "ni Umar na bawa Aisha magani cikinta ya bare, da yaushe aka yi haka"

Ammi cikin fushi ta ce karka kawo min rainin hankali, karka mayar dani bansan me nake yi ba

Hankalin Don ya yi matukar tashi "wallahi banda sa hannu, ina son cikin Aisha, ina son Babyna"

Prof ya kalli Don sannan ya kalli Ammi "ina hujjarki akan Babana ne ya aikata hakan"

"Hujjata shine baya son cikin"

Don cikin sanyin murya ya ce wallahi ina so

Tunani da nazari Aisha ta shiga yi fadi take a zuciyarta "kenan wani ne ya bani magani nasha domin cikin Jikina ya bare, to waye wannan, ba mijina bane, mijina ba zai min haka ba" ta cigaba da tunani daga sama ta tuno da Haseena, ta shiga tuno dazu a dining data zuba mata juice "tabbas Haseena ita ce ta aikata min wannan aikin"

Dube dube ta shiga yi ta ga babu Haseena, hakan ya kara tabbatar mata da ita ce ta aikata wanna aikin

Mum ta ce Hajiya kiyi hakuri tunda kaddara ya riga daya faru, kawai Allah ya kiyaye na gaba

Shuru kawai Ammi ta yi

Don ya kalli Aisha "Aisha kin yarda zan iya halaka Bebinmu"

Aisha kallan Ammi ta yi sai ta kawar da kanta, bata bashi amsa ba don bata son karyata Ammi

Wani bakin ciki ne ya cika shi, kawai ya fice yabar falon Ammi ta bishi da harara, Aisha ta dukar da kanta, tsananin tausayin mijinta ya dabaibaye mata zuciya, sai hawaye ya fara fita daga idanunta

Hakadai Prof da Mum suka cigaba da bawa Ammi hakuri har suka samu ta dan sakko, sun kai har yamma a gidan kafin suka wuce gida

Don wurin Wizzy ya wuce, Wizzy na ganinshi ya ce wata sabon gani, Don amsar wiwin hannun Wizzy ya yi ya fara sha yana samun sauki

Wizzy ya ce Don kwana biyu, ka share ni gabadaya

Don ya ce to ka yi hakuri

Wizzy yai mamaki "Don yau kai kake bada hakuri"

Don ya kalli Wizzy "to miye a rayuwar, nifa nafara tsanar duniyarnan babu komai a ciki sai bakin ciki da tashin hankali, abinda ka yi da wanda baka yi ba sai ace kayi, rayuwa ba yarda"

Wizzy ya girgiza kai yana yar dariya "abokina kenan, wallahi ka bani dariya, wai waya bakanta maka rai ne haka?"

"Cikin Aisha ne ya zube, dalilin bacin raina kenan"

Wizzy ya kalleshi "kasan me kake cewa kuwa, to ai idan ya zube farin ciki zaka yi, ai dama haka ake so"

Don ya mike yana fadin na kula kai ba mutumin arziki bane, zama da kai illa ne, ka ga tafiyarta

Don ya yi hanyar fita Wizzy na kiransa yana fadin ya dawo, Don ya yi kamar bai ji ba, ya yi tafiyarsa

Wizzy ya ce ai dole na lallabaka ka dawo, taya rayuwa zata yi min dadi babu kai, bayan kaine rufin asirina

A lokacin da Feedo ta kai Haseena wurin likita, duba Haseena ya yi sosai, bayan ya kammala ya tabbatar da Haseena tasha kwayar da zai yi wuya ya barta ta dauki ciki

Zaro ido Haseena ta yi ta ce Doctor wallahi ban taba shan wani magani ba na hana daukar ciki

"Ki daiyi tunani, bincike ya nuna akwai kwayar a jikinki"

Shuru Haseena ta yi tana tuna abubuwan da suka faru a baya, a hankali ta shiga tuno lokacin da Don ya bata magani, sai kuma ta tuna baya son haihuwa, tsoro ne ya kamata ta fara yin baya tana fadin na shiga uku ni Haseena

Feedo ta rike ta "meya faru?"

"Tabbas Don ya bani wani kwaya nasha, tabbas shine ya yi min haka"

Feedo ta kalli Likita "yanzu babu wani hanyar da za'a bi ta samu ciki, kudi ba matsala bane"

Likita ya ce akwai hanya amma aiki za'a yi mata kuma zai ci kudi har million bakwai

Da sauri Haseena ta ce babu damuwa zan biya, nidai bukata ta na samu ciki

Likita ya ce karki damu idan kin shirya kawai ki biya kudi sai ayi miki aiki

"Ni gobema ya yi min, yau zan biyaka kudin sai gobe agyi min aikin"

"To shikenan"

A take Haseena ta biya likita kudin aiki cash suka aje magana gobe karfe tara za'a shiga da ita aiki

Gidan Feedo suka koma Haseena ta shiga tattauna rashin adalcin da Don ya yi mata

Feedo ta ce kenan bai bama Aisha ba sai yasa ta samu ciki, kenan ke baya son hada zuri'a dake yake nufi ko miye

Haseena tai zuru tana kallan Feedo "Jikina ya mutu sosai, nina sake jiki Don yana sona, ashe Aisha yake so, gaskiya ba zan taba kyaleshi ba"

"Gaskiya nima ban baki goyon baya ba ki kyale shi, karki raga masa"

Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakaninsu

Aisha kwance kan gadon Ammi sai faman kuka take yi, tana bukatar mijinta kusa da ita, gashi babu dama ta yiwa Ammi magana, Ammi ce ta shigo ta sameta cikin yanayin, ta zauna gefenta da sauri

"My meya faru, ko cikin ne yake miki ciwo?"

Aisha ta girgiza kai alamun a'a

"To miye damuwarki?"

Cikin muryar kuka ta ce Ammi wallahi babu ruwan Ya Umar, yana son Baby na, ki taimaka ki yafe masa

Ammi ta tsurawa Aisha ido kafin ta ce shiya kiraki ya ce ki fada min haka

"A'a babu ruwansa, ni banda ma numbanshi, ni nasan bashi bane"

"To idan bashi bane wane ne ko kece kika sha"

Shuru Aisha ta yi ta dukar da kanta kasa tana fadi a zuciyarta "na fada mata gaskiya kawai Haseena ce ta aikata, to idan ta yi fushi da ita fa, fada mata baida amfani"

Aisha ta dago ta kalli Ammi ki yarda dani Ya Umar bai da hannu, idan shine ba zan boye miki ba, wallahi zan fada miki

Ammi ta yi shuru tana nazari daga karshe ta ce to shikenan tunda kince bai da hannu to abin dake bani mamaki wanene, ma'aikatan gidan nan ne ko su waye, zan yi bincike a kai, ki cigaba da zama a matsayin cikinki ya zube

"To Ammi"

Ammi ta tashi ta fita

Don gida ya wuce ya zauna kan kujera a falo yana tunani

"Ammi tana zargin ni na yi sanadiyar zubewar cikin Aisha, kuma alamu ya nuna Aisha ta yarda da hakan, gaskiya ina cikin matsala, to abinma dubawa anan waye ya yi sanadiyar zubewar Babyna, waye ya rabani da Baby, yakamata na gane ko wane ne, me Babyna ya tsarewa mutum"

Haseena ce ta banko kofa ta shigo, da alamu tana cikin fushi, hanyar dakinta ta yi batare da ta yi masa magana ba ya dakatar da ita

"Ke daga ina kike"

Ta juyo tana kallanshi "daga inda na fito"

"Karki nemi ki gaya min magana sannan ina zarginki"

"Zargin miye?"

"Zubewar cikin Aisha"

Yar dariya ta yi sannan ta ce nima ina zarginka da ka bani magani har yanzu na gagara daukar ciki, ka cuce ni wallahi, ba zan taba barinka ba

Ta shiga dakinta tabarshi tsaye a wurin, ya sha jinin jikinsa yana mamakin taya ta yi ta gane hakan

Bin bayanta ya yi

Haseena ta aje Jakarta da mayafinta Don ya shigo cikin fushi ya tsaya yana kallanta itama kallansa take yi

"Ina hujjarki da zaki ce nina baki kwayar da zai hanaki daukar ciki"

"Karka mai dani ban san abinda nake yi ba mana, wallahi kaine ka bani kwayar da ba zan dauki ciki ba saboda baka san hada zuri'a dani, to meyasa baka bawa Aisha na"

"Wato bakin ciki kike mata ta samu ciki ke baki samu ba, shine kika kika yi sanadiyar zubewar cikinta"

"Kar ka yi min sharri, babu ruwana, ni ina ji da nawa damuwar daka jefa ni ne, ka bani mamaki wallahi"

"Kin san Allah idan kika kara cewa nina baki kwayar daya hanaki daukar ciki sai na yi miki rashin mutunci wallahi, sannan idan nagane kina dasa hannu a zubewar cikin Aisha wallahi ba zan barki ba, sai na dauki mummunar mataki a kanka"

Cikin fushi ta kalleshi "tunda ka nuna kafi son Aisha a kaina wallahi baka nemi zaman lafiya ba, kuma kadan ka gani"

Taje wurin durowanta ta bude tana neman kayan da zata canza, cikin tsananin fushi Don ya fita, dakin Aisha ya shiga, ya fada kan gadonta yana ajiyar zuciya, zuciyarsa sai zafi take yi masa, ji yake kamar ya yi hauka, muryar Aisha yake son ji, yana son sanin ya take, daukar wayarsa ya yi da niyyar kiranta sai ya tuna baida numbanta, tashi ya yi zaune yana tunanin yadda zaiyi magana da ita, ya kasa jurewa ganin Aisha yake son yi, fita ya yi ya wuce harabar gida ya dauki mota yai wucewarsa

Ammi zaune ita kadai a falo tana tunani, tunaninta idan ba Don bane zai rabata da jikanta to waye, waye baya son cikin Aisha, Haseena ta fado mata a rai, kodai Haseena ce, a'a ba Haseena bace, tana kulawa da Aisha sosai, babu alamun mugunta a zuciyarta, to wanene?

Don ya shigo cikin sallama yana ganin Ammi gabansa ya fadi yana fargaban me zata ce masa, Ammi ta dago ta kalleshi gami da amsa sallamar

Samun wuri ya yi ya zauna kan kujera kansa a duke, kiran sunansa Ammi ta yi, ya dago ya kalle ta

"Na'am"

"Ka ce bakai ka yi sanadiyar zubewar ciki Aisha ba, to ka fada min wa kake zargi"

Don ya ce Ammi wallahi banda sa hannu a zubewar cikinta sai dai ina zargin Haseena

Ammi ta girgiza kai alamun a'a "Haseena ba za ta aikata ba, tana son Aisha, ka yi tunani wani daban banda Haseena"

"Gaskiya nidai Haseena nake zargi"

Ammi tai shuru tana nazari sai maimaita sunan Haseena take yi "Haseena, Haseena, anya kuwa" ta kalli Don "kai ka taba ganin wata alama daga wurin Haseena da zai nuna bata son cikin Aisha"
Chapter 23 · 0% Book details