Sashe 31
Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru Ammi tai tana nazari, fadi take a zuciyarta "na shiga uku kenan idan da gaske kina da HIV, dana yana dashi kenan, ya shafawa Aisha, na shiga uku, Allah yasa ba gaskiya bane"
A zahiri ta ce yanzu dai abin daya fi muhimmanci bari na kira Umar ya zo
Ammi ta dauki wayarta ta kira Don, ta fada masa kome yake yi, ya yanke ya zo, tun daga jin haka yasan akwai matsala, barin masana'antan yai ya dawo gida, yana ganin Haseena yasan dalilin kiran, zama yai kan kujera yana kallan Ammi
Ammi ta ce Umar meyasa zaka jefi matarka ta sunnah da kalmar iskanci kuma har ka ce tana da HIV
Ajiyar zuciya Don ya yi sai ya ce Ammi kawarta tazo ta same ni, ta fada min cewa Haseena ba mutuniyar kirki ba ce, kuma ta ce tana dauke da cutar HIV (ya boye Wizzy a cikin maganar, baya so a zarge shi)
Ammi ta ce kasan kawarta ta?
"A'a ni ban santa ba gaskiya"
Ta tsaya tana kallanshi cike da takaici "kawai saboda wata kawar matarka da baka santa ba tazo ta sameka ta fada maka maganganu a kan matarka sai ka hau ka zauna, ban san kai shashasha bane sai yau"
Don ya ce Ammi banyi musu ba don nasan Haseena zata aikata, nasan abinda zata iya aikatawa, nasan Haseena sosai
Cikin muryar kuka Haseena ta ce wallahi Ammi bana yin komai, kafinma nai aure ne nake dan taba rashin ji kadan, lokacin ina makaranta a Dubai nakan je club, kuma Ammi wiwi kawai nake sha sai shisha, yanzu ma kawai shisha nake sha, amma ni bana layin iskanci
Don ya galla mata harara cikin tsananin jin haushi sannan ya kalli Ammi "Ammi kinji ko har shisha da wiwi take sha"
"To ai kaima kana sha"
"Wallahi sai nai miki tsinannan duka yanzun nan"
Ammi ta galla masa harara "ai baka da kunya saika duke ta ina jiranka"
Aisha zaune ta kasa magana, tsoro fal a zuciyarta "HIV fa, na shiga uku, ni dai Allah yasa maganar nan ba gaskiya bane"
Ammi ta dauki wayarta dake gefenta ta shiga kira Family doctor, bugu daya ya dauka ta fada masa tana son ganinshi yanzu kuma yazo da na'urar gwajin HIV, ya ce ba damuwa gashi nan zuwa
Duk shuru suka yi babu mai yiwa daya magana, kowannansu kuwa da sake saken da yake yi, shi dai Don hankalinsa kwance yasan bai da komai sannan yasan Aishansa ma bata da komai
Ko mintin arba'in ba'a yi ba sai ga Family doctor ya karaso
Ammi ta ce yauwa Doctor, sannu da karasowa
"Yauwa Hajiya"
Ta nuna masa Don "ka fara yi masa gwajin"
"Ok"
Nan take likita ya fara yiwa Don gwaji bayan ya gama ya kalli Ammi, Ammi hankali a tashe take kallansa hakama Aisha take kallansa hankali tashe tana fargaban abinda likita zai ce
"Negative"
Ammi tai ajiyar zuciya hakama Aisha, Don ya ce ai nasan banda shi
Ammi tace to yanzu kayi wa Aisha
Likita ya koma kan Aisha, cikin kankanin lokaci ya yi mata gwaji ya gama ya kalli Ammi ya ce Negative
Ammi ta ji wani dadi a ranta tunda Don da Aisha basu dashi
Don ya kalli Aisha ya ce dama nasan ai baki dashi, ban dauka ba bare nasa miki
Ammi ta ce likita gata karshen nan Haseena, ta nuna Haseena, Likita ya dawo wurin Haseena ya shiga dubata cikin karamin lokaci ya gama
Duk sun tasa kunne suna son jin sakamakonta, zuciyar Haseena sai dukan uku uku yake, Don ya tsare ta ido, Ammi kuwa na kallan Likita ta ce muna sauraranka
Likita ya ce a gaskiya Haseena bata dauke da cutar HIV
Wani farin ciki ya baiyana a fuskar Haseena, ta ji wani sanyi ya ratsa ta, ta kalli Ammi "Ammi kin yarda dani sosai ko yanzu"
Murmushi Ammi tai ta ce na yarda dake Haseena, Don ya fara sosa keya yana fargaban fadan da Ammi za tai masa
Nan dai Ammi ta sallami likita ya tafi, Ammi ta kalli Don ta watsa masa wawan kallo
"Wata tazo ta sameka ta fada maka matarka nada HIV, ta sakaka ka hantari matarka harka jefeta da yar iska, Umar yaushe zaka canza"
Don dukar da kansa yai kasa muryarsa kasa kasa ya ce ayi hakuri Ammi
"Ni bani zaka ba hakuri ba, Haseena zaka ba hakuri"
Don ya dago da sauri ya kalli Haseena suka hada ido, sai ya hada rai "ki yi hakuri Ammi ba zan iya ba Haseena hakuri ba"
Ammi ta kalleshi cikin tsananin fushi "wato har ni zan saka ka ka yi abu, sai ka ce min ba za ka yi ba"
Don ya mike "Ammi ki yi hakuri, ni zan tafi sai zuwa anjima"
"To Umar ka tafi, amma karna kara ganin kafarka a gidan nan koda wasa"
Don ya kalli Ammi a tsorace "saboda ban ba wannan (ya nuna Haseena) hakuri ba shine zaki haramta min zuwa gidan nan? to shikenan (ya kalli Haseena) Haseena yi hakuri"
Murmushi Haseena tai, ta ji wani dadi a ranta sannan ta ce na hakura, komai ya wuce
Cikin fushi ya fice, Ammi ta koma kan Haseena
"Ki yi hakuri da abinda Umar yai miki don Allah"
Haseena ta ce wallahi Ammi bakomai, sai dai ma nagode miki kin goge min bakin fentin da aka shafa min
Ammi ta ce abu na biyu Haseena batun wani shisha da kike sha yanzu don Allah ki daina, ke mace ce, gwara namiji komai yai ado ne, bare yanzu da kike dauke da juna biyu zaki so ki zama uwa ta gari a wurin yayanta
Shuru dai Haseena tai Ammi ta cigaba da yi mata nasiha
Don masana'anta ya koma ya sami Wizzy suka zauna office din Don, Don ya shiga yi masa bayanin abin daya faru
Wizzy ya ce ai dama na fada maka karka yanke hukunci har saika yi bincike
Don ya ce amma ya kamata ka gano wacca tazo ta fada maka wannan maganar, ina son ganinta ba zan barta haka ba saina hukunta ta
Wizzy ya ce gaskiya ban santa ba amma idan na ganta zan iya ganeta, har yanzu ina ganin kamanninta a fuskanta
Don ya yi shuru yana nazari, ya kalli Wizzy "kwanakin baya Feedo ta zo gidanmu wai tana dauke da cikina yanzu kuma wata tazo wurinka wai matata tana dauke da HIV, Feedo ta ce min wasu ne suka biyata ta aikata haka kenan itama wannan sata aka yi, aka biyanta, akwai wani abu a kasa"
Wizzy ya ce kenan kana tunanin duk mutum daya ne?
"Tabbas mutum daya ne, amma ina zanga Feedo, idan na ga Feedo gaskiya zata baiyana"
Wizzy ya ce ni rabon da naga Feedo na manta amma zan bada cigiyarta
Don ya ce ka bada cibiyarta ina son ganinta, ina son sanin meyi min wannan aika aikan
Suka cigaba da tattaunawansu
Haseena daga Family house gidan Feedo ta wuce ta sameta da saurayinta zaune a falo suna shan wiwi, janta tai harabar gidan ta shiga bata labarin abin daya faru
"Feedo ki ji fa wai ni nake da HIV, ban san wata yar iska bace a cikin kawayena ta je ta yi min sharri ba"
Feedo ta ce sai yasa banda kawaye dake kadai kawai na yarda
Haseena ta ce wallahi daga yanzu nima na watsar da kawaye, ke kadai ce yanzu kawata
Feedo ta ce daya fi miki
"To ni bari na tafi gida tunda na ganki da bako kar ya yi tunanin wani abu"
Feedo tabe baki tai "ke manta dashi, na kosa ma ya wuce, baida wani amfani"
Haseena ta danyi dariya "shiko yake da amfani tunda yana biya miki bukatarki"
Feedo ta zaro ido "wani bukata, raggo ne fa, yana hawa sau daya ko minti biyar baya yi yake sauka, shikenan ba zai kara yi ba, ga abin nashi dan minini baya kai min labari, ai kayan aiki sai Don, idan yana cina har kwakwalwa yake kai min labari"
Wani faduwar gaba ne ya ziyarci zuciyar Haseena, ta dafe kirji tana kallan Feedo
"Feedo Don fa mijina ne kike wannan maganar a kansa?"
"Oh Sorry my Haseena, tuntuben harshe ne, yanzu ke kawata ce, babu wani abu tsakanina da mijinki, na yi miki alkawari babu abinda zai faru"
Haseena tai ajiyar zuciya "wallahi na ji tsoro, baki ji yadda zuciyata ta buga ba"
Feedo ta rungume ta "ki kwatar da hankalinki, ina yinki sosai, ba zan ga abinda zai cutar dake ba na bari, bare kuma ni da kaina na cutar dake, ina tare dake a kowani hali"
Haseena tai murmushi "nima I a yinki Feedo, nasan ba za ki taba yi min haka ba"
Sun dan taba hira kadan kafin Haseena tabar Feedo tsaye a harabar gidan
Feedo ranta ya baci ji tai Kamar tai hauka "yanzu kenan anyi solving matsalar nan, ni da nake jira ta kawo min labarin Don ya sake ta, ba zai yu ba dole na nemi wani hanya daban, dole na raba Don da matayensa, ni kadai zan zama matarsa, wai har da wani jin haushi don na fada yadda nake jin Don idan yana cina, to akwai namijin da zai iya gamsar dani ne idan bashi ba"
Ta ja tsaki ta shiga ciki ta sami saurayinta
A ranar Ammi kulla kofar shiga ciki ta yi tun magriba sannan ta gargadi ma'aikatan gidan akan karsu bade kofa ko waye yazo, bangaren Abba ta je ta same shi suka shiga biga soyayyarsu, Aisha kuwa kwance ita kadai a bedroom sai dai rungumar filo tai tana tuno irin soyayyar da mijinta yake mata, sai murmushi take tana kara rungume filo
Ai kuwa bayan sallahn isha'i Umar yazo gidan, yazo shiga ciki ya ji kofa a bude, bibbigawa ya shiga yi amma shuru, ya kai awa daya a tsaye babu wanda yazo ya bude masa kofa, gashi bai da numbern Aisha bare ya kirata, tsayawa yai ya yi shuru kamar yai kuka, fadi ya shiga yi zuciyarsa "kenan Ammi bata manta abin daya faru dazu ba kenan, fushi take yi dani, ya yi kyau"
Zuciya ya yi ya wuce inda yai parking motansa ya shiga ya yi wucewarsa, ya tafi gidanshi