Sashe 19
Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aisha kukanta ya kara tsananta, Ammi tsayuwa ya gagareta, zuciyarta na yi mata suya, ta kokarta ta zauna kan kujera tana numfashi dakyar
Don har yanzu kwance yake kan gadon Aisha, yana rungume da rigarta yana samun natsuwa, ji ya yi ba zai iya hakuri ba, tashi ya yi ya fita, ya wuce harabar gida ya dauki mota, ya ja ya wuce
Aisha ta yi kuka harta gaji, Ammi kuwa dakinta ta wuce ta dakko maganin hawan jininta ta sha sannan ta dawo falon
Feedo ta kalleta
"Yunwa nake ji, ki samo min wani abu na ci mana"
Ammi bata tanka ta ba sai Feedo tai murmushi ta dafe cikinta
"Yi shuru yi shuru dan baba, me kake so ka ci? Dan wake? To karka damu bari Grandma ta shiga kitchen ta yi maka"
Feedo ta kalli Ammi "ki tashi kije ki kawo masa dan wake, shi dan baba yake bukata"
A fusace cikin fushi Aisha ta mike ta nunawa Feedo hannu "ke dakata mana, karki nema mana hankali mana, kar ki ga an kyale ki"
Feedo ta taka ta je ta tsaya gaban Aisha tana kallanta cikin rainin wayau "wallahi idan kika kara magana sai na daka ki"
Don da yanzu ya shugo tsayawa ya yi cak yana kallan Feedo, zuciyarsa ta fara bugawa, babu wanda yasan shugowan shi
Aisha ta ce ai kuwa baki isa ki hanani magana ba, karki manta tsakanina dake akwai banbanci ni matar aure ce ke kuma karuwa ce
Tunda Feedo take babu wachca ta ta taba fada mata maganar da Aisha ta fada mata yanzu, Cikin tsananin fushi ta daga hannu zata saukewa Aisha mari, sai Aisha ta yi sauri ta rike hannun dai dai Don ya dakawa Feedo wani tsawa mai rikitarwa
"Ke dakata! Diyar marasa kunya"
Kallansu ya koma kan Don da idanunsa suka sauya zuwa ja tsananin fushi
Feedo ganin Don yasa ta rude, Don ya karaso tsakiyar falon cikin tsananin fushi, ya tsaya gaban Feedo
"Ba matata zaki mara ba, ni zaki mara"
Ta dan kawar da kanta tana yar harara "da ita zanyi don ita ce sa'ata"
Ammi ta daure ta kalli Don ta ce "to tunda ka karaso akan lokaci saika dauke ta ku tafi, bana son ganinku"
Don ya watsawa Feedo wani kallo "ke don ubanki meya kawo ki gidanmu?"
Feedo ta jure ta ce cikin da ka yi min shiya kawo ni gidan nan, na zo na haife shi ne
Fushin Don ya tsananta sosai, daga hannunsa ya yi ya shiga sauke mata mari, sai daya sauke mata zafafa biyar, a take fuskarta yai jawur
Cikin kuka Feedo ta fara magana "wallahi saina dauki mataki akan abin da ka yi min, ka yi min ciki kuma ka wulakanta ni"
Don ya ce idan kin fasa kin raina uwar data kawoki duniya
Ta rike akwatinta zata tafi Aisha ta dakatar da ita "dakata" Feedo ta dakata, Aisha ta tako tazo gaban Feedo ta tsaya
"Babu inda zaki je, kina gidan nan, yanzu zamu kira family doctor dinmu, zai bincike ki, ya gano kina dauke da ciki ko bakya dauke dashi, idan har kina dauke dashi, zai yi bincike akan cikin na mijina ne ko bashi da halaka dashi"
Feedo zuciyarta ta yi wani bigawa, tsoro ya kamata
Don ya yi sauri ya ce kawai ki barta ta tafi don karya take yi
Aisha ta ce taya zan barta ta tafi haka bayan tayiwa mijina kazafi, ai kawai maganar nan gaba zai yi, sai an dauki mummunar mataki a kanta
Feedo ta rikice gabadaya saukar da kai ta yi ta ce wallahi karya nake yi ki barni na fita don Allah
Ammi ta kalli Feedo cikin tsananin mamaki "amma yarinyar nan kin cika yar duniya, wato ma karya kike yi"
Nidai don Allah ku rufa min asiri
Aisha ta ce to waya saki, nawa aka biya ki?
Feedo idonta ya cika da ruwa "ni nasa kaina kawai saboda soyayyar da nakewa mijinki"
Ammi ta ce ai kuwa baki isa ki tafi ba yanzu zamu kira jami'an tsaro su tafi dake, ayi miki hukunci dai dai da abin da kika aikata
Feedo ta durkusa gaban Aisha cikin kuka "don Allah ku rufa min asiri, wallahi ni marainiyace banda kowa, ku min rai, hakan ba zai kara faruwa ba"
Aisha zuciyarta ta yi laushi, tausayin Feedo ya kamata
"Babu damuwa kawai tashi ki tafi, mun yafe miki"
Ammi ta ce taya zata tafi haka ai ba zai yuhu ba
Aisha ta je da sauri ta rike hannun Ammi ta marairaice
"Please Ammi ki barta ta tafi, ta ci albarkacin Baby"
Ammi ta yi murmushi "to shikenan ta ci albarkacin Baby zata iya tafiya"
Ai kuwa da sauri Feedo ta ja akwatinta ta fita da sauri duk suka bita da kallo
Don ya zauna kan kujera Ammi ta juyo ta kalleshi
"Ba zama zaka yi ba, tashi zaka yi ka fitar min daga gida, ba don kai ba babu karuwar da zata shugo gidan nan harta samu damar fada mana magana, ashe har yanzu kana neman matan banza
Don ya ce Ammi nifa rabona da yarinyarnan ya jima, tunda Abba ya yi min aure na daina neman yen mata
Ammi ta yi shuru cikin takaici sai ta ce Umar wallahi kana sani cikin bakin ciki, watarana sai naji kamar na yi kuka, Umar yaushe zaka canza
Aisha ta ce Don Allah Ammi ki yi hakuri, kar kiyi fushi dashi
Aisha ta kalli Don "ka bawa Ammi hakuri mana"
Ammi ta kalli Aisha sannan ta kalli Don "Umar ne zai bani hakuri? ai girman kanshi ba zai barshi ya bani hakuri b.... "
Bata kai da idar da maganar ba sai kunnanta ya jiyo mata Don na fadin "yi hakuri Ammi" muryarsa na rawa
Abinda bata taba ji ba daga bakin Don, ta tsaya tana kallanshi, Don ya zube gwiwowinsa a kasa
"Don Allah Ammina ki yi hakuri ki yafe min duk wani bakin ciki da kuncin dana saka ki"
Wani farin ciki ya dabaibaye zuciyar Ammi sai murmushi ya baiyana a fuskar Ammi
"Na yi farin ciki Umar, Allah ya yi maka albarka, na yafe maka, Allah ya kara shiryaka"
Aisha tai murmushi ya shafa cikinta ta ce kana jin Grandma da Dad dinka ko, Don ya kalleta yana murmushi yana jin tsananin soyayyarta, ji yake kamar ya je ya rungume ta
Don ya tashi ya zauna ya kalli Ammi "Ammi na yi missing din girkin Aisha, zata iya shiga kitchen ta sama min wani abu yunwa nake ji"
Ammi ya watsa masa harara cikin wasa "taya zata shiga kitchen, ai ko bata dauke da ciki ba zan barta ta shiga kitchen ba bare kuma tana dauke da ciki, akwai ma'aikatan kitchen ka je ka fada musu abinda kake bukata"
Don ya marairaice suka hada ido da Aisha "please"
Aisha ta mike Ammi ta kalleta "ina zaki je?"
Aisha ta dukar da kai cikin jin kunya "kitchen mana"
Ammi tai yar dariya "au abin haka ne, haka zamu yi dake Aisha"
Don ya ce to Ammi kema kije wurin mijinki mana ko
Ammi ta ce Allah ya dawo min dashi lafiya
Duk suka amsa "Amin"
Aisha ta wuce kitchen tabar Ammi da Don suna hirar da suka dade basu yi ba cikin farin ciki
Aisha tana shiga kitchen ta shiga hada Rice and spaghetti da stew and chicken, sannan ta yi strewberry juice, bayan ta gama ta yi salad ta soya Arish kadan, bayan ta kammala ta dakko kuloli masu bala'in kyau ta zuba abincin sannan tasa masu hidima su kai Dining area
Ta dawo falo ta samu Ammi da Don har yanzu hira suke yi cikin nishadi
"Ku zo mu je Dining abinci ya kammala"
Ammi tai murmushi "da wurwuri haka"
"Ai babu wuya"
Don ya tashi Ammi itama ta mike suka wuce Dining duk suka zauna, Aisha ta yi serving dinsu, sannan ta yi serving kanta
Ammi ta fara cin abinci tana santi "dama haka Aisha ta iya girki, wow"
Don ya ce Ammi ai Aisha Excellent ce, sai dai na yiwa Abba godiya daya zaba min daya tamkar dubu
Aisha ta rufe fuska tana jin kunya, Don ya debi abinci a cokali ya kai saitin bakinta
"Amsa" Aisha kallan abincin ta yi sai ta fara yunkurin amai, tashi ta yi da sauri, tana kokarin barin wurin sai aman ya subuce mata, amai take yi kamar kayan cikinta zai fito, Ammi da Don tsaye a kanta
"Sannu sannu Aisha"
Dakyar Aman ya tsaya Don ya cincibe ta ya kaita dakin Ammi
Ammi kuwa ta kwashe amai
Don ya tubewa Aisha kaya ya kaita bayi ya yi mata wanka sannan ya dawo da ita ya nemi wani doguwar riga a kayanta ya saka mata, ya kwantar da ita kan gado ya lullube ta da bargo, Ammi ta shugo ta zauna gefen Aisha "Sannu ko Aisha"
Aisha lumshe ido kawai ta yi
Feedo tana jan akwatinta ta shugo falonta ta samu Haseena zaune tana shan shisha, Haseena ta kai kallanta ga Feedo
"Ya na ganki haka kamar ba'a yi nasara ba"
Feedo ta zauna gefen Haseena ta amsa shishan ta fara sha tana dan samun sauki daga radadin da zuciyarta yake mata
"Ki fada min ya kuka yi"
Feedo ta kalleta "wallahi dakyar na sha, yanzu kawai miko min yan chanjina"
Haseena ta bude Jakarta ta ciro daloli ta aje a gaban Feedo
"Gashi saiki fada min ya kuka yi"
"Yadda kika ce na yi haka na yi"
Haseena ta ce dafatan dai baki kira suna na ba ko?
"Taya zan kira sunanki bayan yarjejeniyar da muka yi"
"Dakyau Feedo, yanzu na tabbata gidan ya tarwatse, babu zaman lafiya, Ammi da Abba da Aisha duk za su yi fushi dashi, sai ya dawo wurina, ni kuma na mallake abina"
Feedo ta zuka shisha ta busar da hayakin ta kalli Haseena
"Kin san miye kuwa?"
"A'a sai kin fada"
"Na tsani Aisha, kuma wallahi sai na sata ta yi nadama tunda ta jefe ni da kalmar karuwa"
Haseena ta ce nima na tsane ta sosai, me zai hana mu hada kai dake wajen ganin bayanta
Feedo ta kalli Haseena saita mika mata hannu, Haseena itama ta mika mata hannu, suka hada hannun alamun sun yi maja, suna murmushi