Sashe 29
Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na shiga uku, idan har yarinyarnan gaskiya take fada rayuwar Don ya kare, HIV, anya Haseena za tai haka, yanzu na fadawa Don ne ko kuma nai shuru da bakina, gwara dai na fada masa yasan matsayin da ake ciki"
Kiran Numban Don yake ta yi amma ba'a dauka sai can zuwa anjima da Yamma Don ya kirashi ya fada masa aiyuka ya yi masa yawa a can inda yaje, idan ya dawo gobe zai zo su yi magana
Ta bangaran Bilkisu gidan Feedo ta wuce direct tai smile tana fadin "I know you can do it"
Bilkisu ta ce tun yaushe ai nan da kwana biyu labari zai isoki Don ya saki Haseena
Feedo ta fashe da dariya sannan ta ce kinga daga Haseena sai Aisha
Bilkisu ta ce a zuciyarta sai kuma ke shashasha karuwar mijinsu
Feedo ta hada musu shisha suka fara sha suna busar da hayaki, jin karan mota suka yi Feedo ta kalli Bilkisu
"Kamar motan Haseena, shige uwar daka ki kulle Kanki a ciki"
Bilkisu ta tashi ta shige bedroom din Feedo ta kulle kanta a ciki dai dai da shugowar Haseena ta karaso ta rungume Feedo
"My sweety ya kike?"
"Oyoyo my Haseena"
Haseena ta ce tun a hanya nake jin fitsari bari na shiga na yi
Feedo zaro ido tai cikin tsoro ta shiga fadi a zuciyarta "ohni Feedo ya zanyi idan Haseena ta ga Bilkisu, nasan ma me zance mata"
"Ke kawata ban fada miki ba"
"Ina jinki"
"Bilkisu ta shigo hannu, yanzu hakama tana Bedroom dina
Haseena ta ce dakyau Feedo, sai yasa nake yinki over
Haseena ta tunkari Bedroom din, ta murda kofar ta jishi a kulle ta juyo ta kalli Feedo
"matsiyaciyar ta kulle ta ciki kamar tasan zata sha bakar azaba dani"
Feedo ta turawa Bilkisu text message akan karta taba bide kofar, ta tashi tazo bakin kofar suna ta bibbigawa
"Dan ubanki ba zaki bude ba"
Bilkisu ta ce ba zan bude ba
Haseena ta ce kinji matsiyaciya ko to yau ina gidan nan sai kin bude, saina miki rashin mutunci
Bilkisu ta murmusa ta ce a zuciyarta "Haseena kenan ai da Feedo ta bani damar bude kofar nan wallahi budewa zan yi nafi karfin ki duke ni, sai dai ni na yi miki shegen duka
Feedo ta ce muje musha shisharmu kafin zuwa anjima ta gaji ta bude kofar
Suka je suka zauna suna shan shishansu, Feedo ta turawa Bilkisu text message akan idan tana jin yunwa ko kishin ruwa ta bude fridge din dakin akwai shawarma da lemu da ruwa
Ta turo mata da reply "ok"
Haseena ta zauna a gidan har dare Bilkisu bata bude kofar ta fito ba, ta kalli Feedo
"Tsinanniyar matan nan ba zata bude bafa"
Feedo ta ce idan yunwa da kishir ruwa suka addabeta dole zata fito
Haseena ta ce nidai tafiya gida zanyi, gobe da sassafe ina nan shugowa
Feedo ta mike tai mata rakiya har harabar gida, bayan Haseena ta ja motar ta ta wuce Feedo ta dawo ciki ta tarar da Bilkisu zaune, Feedo ta fashe da dariya
"Kin zaunu yau gaskiya"
Bilkisu ta ce wallahi don dai kece kawai kika ce kada na bude amma ba don haka ba wallahi saina fito nayi mata tsinannan duka
Feedo ta ce ai akwai lokaci yana zuwa da zaki yi mata dukan, amma ki bari sai kin gama min aiki na sallameki, kin ga saiki yi mata duk abinda kika ga dama
Bilkisu ta watsa masa wani kallan kiyayya sannan ta mike "ni zan tafi gida"
Feedo ta ce to sai gobe, Bilkisu ta fice
Washegari Haseena tunda sassafe taje gidan Feedo amma ta tarar da babu Bilkisu, zaro ido tai ta kalli Feedo "ina Bilkisu?"
Feedo ta ce jiya nasha Codine na yi makil, bachci ya debe ni, ban tashi bama sai yanzu da kika shigo, bansan ya akayi ta gudu ba
Haseena ta zauna kan kujera cike da takaici "gaskiya na yi bakin ciki, wallahi naso na gurje bakinta yai jini, na ja gashin kanta har saiya tsinke"
Feedo ta ce ai bai baci ba, zan sa akara kawo min ita, sai ki yi mata duk abinda kika ga dama
Haseena tai wani ajiyar zuciyata "ai kuwa dai kisa akara kamo mim ita, don ba zan barta ta ci banza ba"
Feedo ta ce maman Baby kenan dafatan dai ana shan magani?
Haseena ta ce ina sha sosai, ai bana wasa, kinma san miye kuwa?
"A'a sai kin fada
"Ina son zan baki wasu kudi kije Italy ki sayo kayan Baby"
Feedo ta ce dakyau Haseena kinyi shawara me kyau, yanzu yaushe ne tafiyar?
Haseena ta ce ni ba zai yu naje ba, ke kadai zaki je, nan da wata daya insha Allah
"To Allah ya kaimu"
"Amin"
Suka kawo wani hirar daban suka fara yi
Aisha ta fito ta sami Ammi zaune a falo "Ammi sannu da kokari"
"Yauwa Aisha, ya nauyi?"
"Alhamdulillah, Ammi ni zan shiga kitchen"
Ammi ta kalleta "me zaki je kiyi a kitchen, komai kike so ki fadawa ma'aikata su kawo miki"
Aisha ta marairaice "Ni Ammi fa Ya Umar yau zai dawo, ni nake so nayi mishi abin tarba"
Ammi ta danyi smile sannan ta ce to me dadi miji kafin ki yi min kuka saiki shiga ki yi masa
Aisha ta ji wani farin ciki saita wuce kitchen ta shiga hada nau'ikan abinci da abin sha, bayan ta gama ta kai komai Dining ta aje sannan ta wuce daki tai wanka ta yi kwalliyarta cikin wani shadda mai uban tsada da kyalli, dinki riga da siket ne, ta rangada daurin dan kwali, ta feshe jikinta da turaruka, ta yi matukar haduwa, ta tsaya tana kallan kanta a madubi, ta ce a zuciyarta "na yi kiba ba laifi" saita shafa cikinta tana murmushi
"Baby ka yi missing Daddy ko? yana kan hanya yau tare zaku kwana ko?"
Ta cigaba da magana da Bebinta cikin shauki da tsananin soyayya
Wizzy shi ya je ya dakko Don daga Airport suka zo gidanshi domin tattauna maganar da Wizzy da matsu yai dashi, Don ya kalli Wizzy
"Ina jinka Wizzy"
Wizzy ya ce a zamanka da Haseena me ka taba experience na rayuwarta, ya halinta yake karka boye min pls
Don ya ce meya kawo maganar nan, miye dalilin wannan tambayar
Wizzy ya ce nine babban abokinka, ba zan ga abinda zai cutar da kai ba na bari, a jiya wata Yarinya ko mata zan ce maka tazo ta same ta fada min maganganu marasa dadi akan Haseena kuma wani abin daya bani mamaki na nemeta sama da kasa ban ganta ba kamar aljanah
Don da sauri ya ce me ta fada maka akan Haseena
Wizzy ya ce ta nuna min Haseena mutumiyar banza ne amma ni duk bai dameni ba, abin daya fi damuna cutar da ta ce tana dauke dashi
Don ya zaro ido cikin tsoro "wani cuta kenan?"
Wizzy shuru yai yana fargaban fada masa, Don ya ce ka fada min Wizzy wani cuta ne?
"HIV"
A sittin Don ya mike yana fadin "na shiga uku"
Wizzy ya ce karka tayar da hankalinka don Allah
Don ya ce Wizzy na ga ta kaina, HIV fa ba cutar wasa bane, Haseena ta cuci rayuwata
Wizzy ya ce calm down Don, ba dole bane ace kana dashi yanzu asibity zamu je su binciki lafiyarka
Don ya ce ba zan iya zuwa asibity ba, ina tsoron ace ina dauke da HIV, ina tausayin Aisha da abinda yake cikin ta
Wizzy ya mike yazo gabanshi ya dafa kafadarsa "ka daure muje asibity, ka ga idanma kana dauke dashi sai a dau mataki da gaggawa"
Wizzy ya cigaba da lallabar Don har ya yarda suka wuce asibity, suna karasowa, Wizzy ya yi wa Likita bayanin abin daya kawo su don kuwa Don bai iya cewa komai ba
Likita ya shiga duba Don bayan ya gama Don ya dawo wurin Wizzy ya rike kai yana fadin "Wizzy ni nasan ma ina dashi"
Wizzy ya ce calm down, komai zai zo da sauki
"Kai amma Haseena ta cuce ni wallahi"
Likita ne ya karaso rike da result, zuciyar Don ya yi wani bugawa
"Likita don Allah karka fada min ina da HIV, wallahi ina cikin tashin hankali"
Murmushi Likitan yai ya ce wallahi baka da komai, lafiya lau kake
Wani ajiyar zuciya Don ya yi suka hada ido da Wizzy sai sukai murmushi "Allah nagode maka"
Suka sallami Likitan suka fito, Don ya kalli Wizzy ya ce ban gama yarda da kai na ba muje wani asibity
Wizzy ya ce nifa dama naji a Jikina bakada shi ko ita Haseenan ma zai iya yuhuwa sharri aka mata don a hada ku da ita
Don ya ce nasan Haseena, Haseena sai a hankali, kawai ka yarda zance na muje wani asibity zanfi samun natsuwa, Wizzy ya ce to muje
Wani asibity suka tafi, anan ma aka tabbatar da lafiyarsa kalau, suka kara zuwa wani asibity nanma shima lafiyarsa kalau, sai yanzu Don ya ji ya koma normal, hankalinsa ya dawo jikinta
Don da Wizzy a cikin mota suna tafiya suna tattaunawa
Wizzy ya ce kawai ka kaita asibity ai mata test, idan ya tabbata tana dauke da cutar sai kasan yadda zaka yi
Don ya ce ni dai jindadi na daya tunda banda shi bare na shafawa Aisha sannan idan ya tabbata Haseena tana dauke dashi ka ga kenan kowa zai kama gabanshi
Wizzy ya girgiza kai alamun a'a "taya haka zai kasance, kawai fita da ita zaka yi waje ayi mata magani"
Don ya ce to wai taya ma ta yi ta samu cutar, kenan tana biye bien maza kenan
"Meya kaika da fadan wannan maganar, bai kama ce ka ba, duk maganar nan fa da muke yi bamu tabbatar ba har sai an gwada ta"
Don ya ce hmm Allah dai ya kyauta
Family house suka wuce
Ammi da Aisha zaune a falo Ammi ta kalli Aisha "wannan kyau haka, gashi har yanzu bai karaso ba"
Aisha tai smile "hmmm Ammi kenan"