Sashe 37
Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haseena ta fito harabar gida ta tsaya, can sai ga fitowar Don da Aisha, wani bacin rai da bakin ciki ya ziyarce ta da taga Don shike rike da Leemat, ta hada rai, bacin ranta ya baiyana a fili
Don ko kallanta bai yi ba ya mikawa Aisha Leemat ta amsa, saiya shiga mota bangaren direba, Haseena tai sauri ta bude gidan gaba ta shiga, Aisha ta bude gidan baya ta shiga
Don ya juyo baya ya kalli Aisha "ki bata nono ta sha"
Aisha ta ce Leemat bata gajiya da tsotso, duk bayan minti biyar saita nemi tsotso
Don ya ce ai nata ne
Haseena ta hada rai, ji take kamar ta mutu tsabar bakin ciki amma saita hadiye
A haka Don ya ja motar suka tafi, mini mini ya juyo ya kalli su Aisha duk hankalinsa na kansu,
Abin ya ishe Haseena sai ta kalli Don "malam ka natsu ka dinga kallan gabanka karka sa mu yi hatsari, ban shirya barin duniya yanzu ba"
Watsa mata kallan banza yai batare da ya ce komai ba
Malam Dan Sudan ya shigo gari, bada bata lokaci ba Bilkisu ta zo ta sami Feedo suka tafi wurinshi, nan take Feedo ta shiga yi masa bayanin abin daya kawo ta
"Akwai wani farkana sunansa Umar ana kiransa da Don, yana da mata guda biyu, daya Haseena, daya Aisha, so nake a sanya kiyayya tsakaninsa da matayensa, ya sake su, sai kuma asa tsananin soyayya a tsakanina dashi da zai kai ga aure"
Malam Sudan ya ce wannan karamin aiki ne, wannan aikin shi yafi komai sauki a wurina, zan baki abinda zaki yi amfani dashi
Feedo tai smile sannan ta ce dakyau malam
Dakko wasu kulli yai guda biyu ya shiga yi mata bayani
"Wannan ke zaki yi amfani dashi ki shiga bayi ki yi tsirara da misalin karfe biyu na dare, ki zuba a cikin ruwa ki doraye jikinki dashi, wannan kuma hayaki zaki yi dashi kina kiran Umar sau uku"
Feedo ta amshi kullin cikin farin ciki tana fadin dole nai maka alheri, ciro kudi tai daga cikin Jakarta, da kimaninsu zai kai dubu hamsin
"Ga wannan, idan bukata ta biya zan ninka maka sau ashirin"
Yai murmushi "to Hajiyata, sai na ji ki zuwa gobe, nasan dole zaki neme ni"
Feedo ta kara yiwa Malam Sudan godiya sosai sannan suka yi masa sallama suka wuce ya bisu da kallo
Su Aisha suna karasowa asibity Don yai parking ya fito, Haseena da Aisha suka fito, Don ya amshi Leemat da take bacci daga hannun Aisha, ya kwantar da ita a kafadarsa, wani karamin tsaki Haseena tai sannan ta shiga cikin asibitin Aisha tabi bayanta, Don kuwa yana rike da yarinyarsa ya Jingina jikin mota
Haseena da Don suka shiga suka sami likita, Aisha ta ce masa tana so a duba lafiyar Babyn Haseena
Likita ya shiga da Haseena wani daki, bincike ya shiga yi mata sosai, ya dauki tsawon minti talatin sannan suka fito
Aisha ta ce Doctor Baby na nan lafiya ko?
Shuru Likita yai ya kalli Haseena, Haseena ma kallanshi take yi, girgiza kai yai
"Gaskiya babu ciki a jikinta"
Haseena ta zaro ido tana kallanshi "kai malam karka fada min banda ciki, ina da ciki, cikin yazo da Matsala ne bai baiyana ba"
Likita ya kalli Haseena "Madam baki da ciki kuma ba zaki taba daukar ciki ba saboda a binciken da na yi baki da mahaifa, an cire mahaifarki"
A rikice cikin tsananin tsoro Haseena ta kalli Likita sannan ta kalli Aisha, bakinta na rawa ta kasa magana, tsananin tausayi ya baiyana a fuskar Aisha
Aisha ta kalli Likita "haba Doctor taya zaka ce an cire mata mahaifa, ka dai kara bincike"
Haseena ta shiga tuno aikin da da aka yi mata, a hankali ta shiga furta sunan Feedo "Feedo ke ce zaki yi min haka" wani jiri ya dibeta ta yanke jiki ta fadi, Aisha tayi kanta tana salati, tuni ta fashe da kuka, fita tai da gudu ta fito ta sami Don a harabar asibityn
Yana ganinta cikin gigicewa ya shiga tambayarta hankali a tashe "Aisha meya faru?"
"Aunty Haseena ta yanke jiki ta fadi"
Karamin tsaki yai "shine kika wani daga hankalinki kamar wani naki ya mutu"
"Don Allah Yayana kazo muje"
Haushin Aisha ya shiga ji, ba don yaso ba ya bita suka shiga ciki
Tuni aka shiga da Haseena cikin wani daki aka shiga yi mata taimakon gaggawa, Aisha hankalinta a tashe sai faman kuka take yi, Don kuwa rike yake da Leemat hankalinsa kwance, Aisha tuntuni ta kira Ammi ta fada mata Haseena bata da lafiya, ta kalli Don idanunta sunyi jawur tsabar kuka "Yayana ina tausayin Aunty Haseena, ban san wani hali take ciki ba"
Don ya kalleta cike da jin haushi sannan ya ce Aisha wallahi tunda Haseena ta nuna a fili bata son jinina ta fita daga raina, ko dai dai da kwayar zarra bana jinta a zuciyata, Aisha ta kara fashewa da kuka dai dai lokacin likita ya fito, Aisha ta karasa wurinsa da sauri
"Ya Aunty Haseenata take?"
Likita ya ce kece Aisha?
Aisha ta ce eh ni ce Aisha
"Sunanki take ta kira, wai tana son ganinki"
Aisha ta fada cikin dakin da sauri ta samu Haseena kwance kan gadon jinya, hawaye na zarya daga idanunta, ta karasa ta zauna gefenta ta shiga yin kuka sosai
"Aunty ki kwantar da hankalinki karki sawa kanki damuwa, na baki Leemat, na mallaka miki ita har abada, ba zan taba kallan Leemat a matsayin ni na haifeta ba"
Wasu hawaye masu zafi suka shiga fita daga idanun Haseena, muryarta na rawa ta shiga magana
"Aisha nagode da kyautar Leemat da kika bani, ina alfahari dake a matsayin kishiyata kuma ina jan hankalin sauran mata da suyi koyi da kyawawan halayenki sannan kalubale ga mata masu irin zuciyata, Aisha na zalunci kaina, na yaudari kaina, na biyewa zuciya ta kaini ta baro"
Aisha cikin kuka ta ce Auntyna don Allah ki daina magana, ni baki yi min komai ba, idanma kinyi min na yafe miki duniya da lahira
Haseena ta ce barni kawai na fada miki abubuwan da nayi miki, na yi miki abubuwa da yawa, na zalunceki matuka sai Allah ya hada ni da dai dai da zamanina, Feedo ta cuce ni
"Waye kuma Feedo?"
Haseena ta shiga zaiyanowa Aisha komai daga farko zuwa karshe, bata boye mata komai ba, tun lokacin da Bilkisu ta kaita wurin malamin karya suka damfareta zuwa hada kansu da Feedo
Don dake tsaye bakin kofar dakin ya tsaya cak yana mamaki, ya ji duk bayanan Haseena, hankalinsa ya tashi matuka, a take ya shiga furta "Feedo, Haseena, Feedo ita ta bawa Haseena magani ta bawa Aisha domin cikinta ya zube, sannan ta maida Haseena karamar yarinya ta cire mata mahaifa saboda kada ta dauki ciki, to me haka yake nufi"
Haseena ta cigaba da magan "Aisha ki yafe min, na yi miki abubuwan da ko kallo ban isheki ba, hatta yarki naso kashewa amma ke zuciyarki daya dani"
Aisha rungume Haseena tai tana kuka mai taba zuciya "na yafe miki har abada, kuma Leemat ma ta yafe miki"
Don ya budo kofa ya shigo, duk kallansu ya koma kanshi, kallan Haseena yake yi
"Dama shi ramin mugunta ance idan zaka ginashi, ka ginashi dan karami, yanzu Haseena wa gari ya waya, ke ce dai a kasa, Aisha bata da hakkinki Allah ya nuna miki aya"
Haseena ta shiga yin sabon kuka "Don Allah mijina ka yafe min, ka gafarce ni, na yi nadama"
Don ya ce tunda duniya ta nuna miki iyakarki nina yafe miki sai dai nima zan nemi gafararki, ki yafe min don nasan ina da hannu a halin da kike ciki, da ban baki kwayar da zai hanaki daukar ciki ba da yanzu kila kin haihu
Haseena ta ce mijina ni baka min komai ba ko kayi min wani abu na yafe maka, Allah ya ga zuciyata ne babu kairi a ciki sai sharri sai yasa ya hukunta ni ya hanani haihuwa
Aisha ta kalli Don cikin mamaki "Yaya meyasa ka bata kwayar da zai hanata daukar ciki"
Don ya kalli Aisha "ba ita kadai ba hatta ke idan zaki tuna na baki kinsha amma Allah ya nuna min banda dibara
Aisha tai nisa cikin tunani ta shiga tuno lokacin daya bata maganin tasha, ta kalleshi da sauri "hakika na tuno lokacin amma maganin bai shiga cikina ba, don sam sam bana son magani, amayo da maganin na yi"
Ammi ce ta shigo duk kallansu ya koma kanta, ta karaso wurinsa suka shiga kawo mata gaisuwa tana amsawa
"Haseena ya jiki?"
"Da sauki Ammi"
Ammi ta kalli Don "meke damunta?"
Shuru Don yai bai ce komai ba, Ammi ta mayar da kallanta kan Haseena "ina cikin ki Haseena?"
Haseena ta fashe da sabon kuka, Aisha ta rike hannunta tana dan murzawa "ki yi hakuri, duk wani tsanani na rayuwa ba dauwamamme bane"
Ammi ta ce wai meke faruwa ne?
Don ya kalli Ammi "Ammi gaskiya Haseena bata da ciki kuma ba za ta taba daukar ciki ba saboda bata da mahaifa"
Ammi ta zaro ido gami da dafe kirji cikin firgici "na shiga uku ni Halima, garin yaya?"
Don ya ce "hada kai tai da Feedo, ta bata yarda sai tai amfani da wannan damar ta cutar da ita"
Ammi ta shiga yin lissafi "wacece Feedo kuma ban fahimci me kake son fada min ba"
Don ya kalli Haseena "ki yi mata bayani da bakinki amma kafin nan ki bani sabon address din Feedo don ba zan taba barinta ba"
Nan take Haseena ta bawa Don full address na Feedo, bai tsaya wata wata ba ya mikawa Ammi Leemat ta amshe ta, sannan ya fice, sai Ammi ta zauna gefen Haseena, "ina sauraranki Haseena"
Haseena bata boyewa Ammi komai ba ta sanar da ita iya gaskiyarta, Ammi hankalinta ya tashi ta shiga kallan Haseena cikin tsananin mamaki "lallai kuwa, dama kece dai wacca kika son rabani da jikana, kin sa na dauki alhakin Umar"
Haseena ta ce Ammi don Allah ki gafarce ni, na gane kuskure na, rayuwata bata da wani amfani yanzu