← Book details Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 40

Sashe 28

Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru yai na wani lokaci kamin ya ce gaskiya a binciken da na yi gaskiya bakya dauke da juna

A rikice cikin tsananin tsoro Haseena ta zaro ido waje

"Ya zaka yi ka ce min bani da ciki"

"Abinda bincike ya nuna kenan zaki iya zuwa wani asibitin"

"Amma likita watana uku bana ganin al'adana"

"Baki da ciki"

"Wallahi karya kake yi ina da ciki"

Taja tsaki cikin fushi ta fice ya bita da kallo

Haseena wani asibitin ta kara zuwa amma abu daya aka sake fada mata bata da ciki, karyatawa ta yi sai tafi wani asibityn daban amma duk zancen daya, daga karshe ta wuce gidan Feedo ta same ta

Feedo ta ce yana ganki haka kamar akwai damuwa

Haseena tai wani ajiyar zuciya "Feedo wai banda ciki"

"Waya fada miki baki da ciki?"

"Yanzu haka daga asibity nake, na je asibity ba daya ba ba biyu ba sun tabbatar min da single nake"

"Taya haka zai kasance"

Feedo ni abinma da yafi damuna wata uku fa bana ganin al'adata taya za'a ce banda ciki

Feedo ta ce to abinda zai faru yanzu muje wurin Likitan da ya yi miki aiki ya sai ya bincika ya ga meke faruwa

Feedo ta tashi suka fita, Asibitin da aka yiwa Haseena aiki suka tafi, tun a hanya Feedo ta rubuta text message ta turawa likita abinda zai fada idan sun karaso

Suna isowa Asibityn suka wuce office din likita direct suka sameshi zauns, suma suka zauna

Feedo ta shiga magana cikin zafi zafi "Haba Doctor ya zamu biyaka milliyoyin kudi akan ta samu ciki kuma har yanzu shuru, kuma wata uku bata ga al'adanta ba"

Likita ya ce ai haka na faruwa kuma alamun nasara ne, ya kalli Haseena "muje na kara duba ki

Haseena ta tashi suka shiga wani daki bada dadewa ba suka fito suka zauna

Feedo ta ce ya ake ciki

Likita ya ce Haseena tana dauke da ciki har na tsawan wata uku sai yasa bata ganin al'adanta

Haseena ta ce meyasa sauran Asibitin da naje suke fada min banda ciki

"Haj Haseena binciken su daban nawa daban, kuma ba zasu gani ba saboda cikin yazo da matsala"

Feedo ta ce wani irin matsala kenan?

"Abin dake cikinta baya girma yana nan har yanxu a gudan jini but zan bata wani magani da zata rika amfani dashi nan da wata uku cikin zai yi girma"

Wani farin ciki ya baiyana a fuskar Haseena, Feedo tai ajiyar zuciya ta kalli Haseena

"To saiki kwantar da hankalinki, tunda bincike ya nuna kina da ciki"

Haseena ta rungume Feedo tana fadin thank you my Feedo, you are so sweet

Feedo ta ce kema haka Haseena

Daga asibity gidan Feedo suka dawo cikin farin ciki, suka kunna shisharsu daya sha mix da tabar wiwi, suna sha suna hira

Haseena ta ce ina ganin yadda Aisha zata ganni da ciki, wow nasan zata kusa mutuwa

Feedo ta ce kuma gashi dakyar ta kara samun wani cikin, kinga kenan yanzu ke zaki yi ta tara yara a gidan

Haseena ta ji wani farin ciki a ranta sai ta ce wallahi har na kosa wata ukun nan ya cika cikina ya fito, kawata akwai feelings fa

"Nasan zaki aikata"

Suka fashe da dariya gami da tafawa

Aisha Don kwance kan gado a bedroom din Ammi, Don sai shafa cikin Aisha yake yi yana jin yadda Bebinshi ke motsawa

"Kamar na taba kai"

Aisha tai smile "kodai bayansa ka taba"

"A'a kaine, na gane shape din daga gani ma irin kaina ne"

Aisha tai dariya kamar cikinta zai fashe "mijina kenan mai abin dariya"

Don ya sauka daga kan gadon "to ni na gama miki sallama, zan wuce ki kulan min da Kanki da kuma Baby"

Aisha ta marairaice tai dai dai da ido kamar za tai kuka "uhm uhm ni nafara gajiya da tafiyar da kake yi gaskiya"

Don ya ce wannan tafiyar da nake yi don ke da Baby nakeyi kuma ya fi zaman da nake yi a baya babu aikin yi, kinga yanxu ai nafi mutunci kuma abin ki yi alfahari ne

Sauka tai daga kan gado ta je ta rungume shi "a kullum ina alfahari da kai mijina, Allah ya tsare min kai ya kuma daukaka min kai, ya kareka daga sharrin makiya"

Yai murmushi yana dan jan hancinta "ameen my love"

Ta kai bakinta kan bakinsa suka shiga tsotsar miyaun junansu sun kai kusan minti Bihar suna kissing sannan suka fita

Ammi da Abba zaune a falo suna hira Haseena ta shigo cikin sallama suka amsa fuskarsu dauke da annuri, ta zo gabansu ta durkusa "sannunku Ammi ina wuni"

"Lafiya lau Haseena"

Ammi ta ce ya kwana biyu?

"Lafiya lau wallahi Ammi"

Abba ya ce Haseena babu dai wani abu ko?

Haseena ta girgiza kai alamun a'a "Abba babu komai wallahi, muna zaune lafiya"

"To dakyau haka ake so"

Tun daga nesa Haseena ta hango Don da Aisha suna takowa daga matakan bene zasu shigo falo, wani bakin ciki ta ji ya ziyarci zuciyarta amma ta jure ta mike ta tana fadin Oyoyo sister na ina kewanki

Cikin Aisha bai fito ba saboda tana sanye da wani doguwar riga, dinki buba, kuma dama cikin nata girmarsa a marane bai fitowa

Haseena ta zo ta rungumeta "sister ki dawo gida mana"

Aisha ta ce nan kusa insha Allah

Haseena ta ce yar uwa ki tayani murna fa ina da juna biyu wata uku

Aisha cikin farin ciki ta ce wow yar uwa gaskiya na tayaki murna

Aisha ta je wurinsu Ammi da sauri tana fadin Ammi yar uwata Haseena tana da ciki wata uku

Farin ciki ya baiyana a fuskar Ammi da Abba

Ammi ta ce masha Allah ina farin ciki sosai

Abba ya ce wallahi baki kaini farin ciki ba

Don kallan Haseena ya tsaya yi cikin mamaki fadi yake a zuciyarsa "me wannan kuma take nufi da tazo tana wani karyar tana da ciki, taya zata yi ta dauki ciki, ko zata dauki ciki ai ba yanzun ba, saita kai shekarun da zata dauka"

Ya gaji da jin shirme ya ce Ammi abba ni zan wuce

Aisha ta ce Ya Umar a cikin wannan halin zaka wace, Aunty Haseena na bukatar kulawarka, tana dauke da Baby

Smile din karfin hali yai ya ce ga amanarta na baki saiki kula da ita, ni sai na dawo

Bai jira ya ji me za'a kara fada ba ya fice Haseena ta bishi da kallo tana murmushi

Abba ya ce Babana ya dage sosai, ya maida hankali a harkar kasuwanci

Ammi ta ce baka dan yadda nake jin dadi ba a raina

Iyayi Haseena take ta yi, mini mini ta ce tana son cin wannan, anjima ta ce wancan, haka ta wuni ranar a gidan tana iyayi wai ita a lallai mai ciki zata haifi dan masu gida, haka ta wuni a gidan sai wurin karfe takwas da rabi ta wuce gida

Aisha kwance kan gadon tana rike da cikinta tana tuno mijinta tana murmushi, Ammi ce ta shigo da waya ta mika mata

"Gashi Inji Umar"

Da sauri Aisha ta tashi zaune ta amsa wayar ta manna a kunne, jin muryar Don tai ya ce Hello wifey, wani farin ciki ta ji a ranta kuma ya baiyana a fuskarta

Ammi fita tai don su samu suyi wayarsu

Aisha ta ce Habibaty ina missing dinka sosai

Don ya ce tun dana sauka na kasa tabuka komai kawai tunaninki nake ta yi

Ta marairaice kamar za tai kuka "yaushe zaka dawo?"

"Jibi insha Allah"

"To Allah ya dawo min da kai lafiya"

"Ya Baby na?"

"Ga Bebinka yana ta tokari na"

Yai yar dariya "Dakyau Babyna, samin wayar a kan ciki naji Baby na"

Aisha ta dora wayar a kan cikinta na wani lokaci kamin ta mayar ta manna kunnanta

"Kaji ko?"

"Eh naji"

"Amma ka kira Aunty Haseena kuwa ka ji ya take ya Baby?"

Bata rai ya yi sannan ya ce ke wai waya fada miki tana da ciki, karya fa take yi

"Ya aka yi kasan bata da ciki"

Shuru Don ya yi na wani lokaci sannan ya ce ai nine mijinta banyi mata ciki ba gaskiya

Aisha ta ce Habibaty ya kake hakane, Aunty Haseena fa tana da ciki ka kula da ita

Don ya ce to shikenan na ji tana da ciki zan kira ta na duba Baby

"Yauwa Habibaty"

Haka suka cigaba da hirarsu cikin soyayya

Haseena kuwa an kasa bachci me kyau, wai imagine take yi wai ita ce take da ciki, farin ciki ya hanata bachci, washegari kuwa tunda sassafe ta shiga kiran yan uwa da abokan arziki tana fada musu Allah ya kawo ciki, sai fatan alkairi suke mata suna tayata farin ciki

Wizzy ya fito harabar gidansa ya je zai shiga motarsa sai ga Bilkeesu ta shigo gidan, ya dakata yana kallanta, ta karaso har gabanshi ta tsaya, yar madaidaiciya fara, tai kyau, budan bakin Wizzy ya ce Baiwar Allah ni yanzu na daina neman mata, ki fita kawai

Bilkisu ta dan murmusa sannan ta ce nima ba wai nazo nemanka bane domin muyi iskanci, nazo ne domin na fada maka wani magana

Ya gyara tsayuwarsa "to ina jinki"

"Inata neman hanyar da zan hadu da abokinka Don ban samu ba, sai na samu labari kaine na kusa dashi sosai dalilin dayasa nazo wurinka kenan"

"Menene hadinki da abokina Don?"

Ta dan murmusa "taimakonsa nake son yi, ana son halaka shi ni kuma ina son tsamo shi"

"Halaka kuma ban fahimce ki ba?"

"Matarsa Haseena tana dauke da cutar HIV"

Wizzy ya zaro ido cikin tsoro ya nunata da yatsa "ke karki kawo min rainin hankali mana, ya zaki ce matar abokina tana dauke da HIV"

"Mijinta abokinka ne, ni kuma kawarta ce tun kafin tayi aure, nasan sirrinta da dama, da ita muke zuwa club, nasan mazan da take hulda dasu kuma ni nake rakata wurin malamai domin fitar da kishiyarta Aisha"

Wizzy ya rikice gabadaya, hankalinshi ya tashi, cikin kankanin lokaci kuma ya nemi Bilkisu ya rasa, bai san yaushe ma tabar gabansa ba, fita yai yana dubata a layin, babu ita babu kamanninta, ya dawo ya tsaya yana tunani da sake sake a zuciyarsa
Chapter 28 · 0% Book details