← Book details Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 40

Sashe 14

Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu ya dakko a gefe ya mika mata "kinga dan wannan abun, shi zaki barbadawa kishiyarki a abinci, idan har ta ci abincin shikenan cikinta zai zube kuma babu wanda zai taba zarginki, sannan mahaifarta ba zai sake daukar ciki ba, idan mijinku ya ganta ransa zai dinga baci, yana jin tsanarta"

Ya kalli gefenshi yana suruttai sai ya dakko wani dan kulli ya mika mata "wannan na mallaka ne, idan kinyi wanka ki shafe jikinki dashi, mijinki zai dawo hannunki sai yadda kika yi dashi"

Haseena ta yi wani farin ciki ta amshi magungunar tana godiya, sannan suka yiwa Malamin sallama suka wuce

Suna cikin motan, Haseena na jansu suna hira

Haseena ta ce kai amma bokan nan na musamman ne

"Bana fada miki ba, ai bai da wasa"

"Wallahi jina nake kamar babu wanda ya fini farin ciki yau, burina zai cika, mijina zai zama nawa ni kadai"

Suka cigaba da hira suna tafiya

Aisha zazzabi ya lullube ta sosai sai rawan sanyi take yi, hakoranta na harhadewa, hankalin Ammi da Abba ya tashi, tuni suka kira family doctor ya karaso ya shiga duba Aisha, bayan ya gama gwaje gwajensa, ya tabbatar musu da jininta ya hau sosai

Ammi da Abba sun tausayawa Aisha sosai, sunyi alkawarin bata farin ciki da kulawa na musamman

Likita ya yi mata allurori har dana bachci, sai yasa ma bachci ya yi wuf da ita sannan ya bada wasu magungunar da za'a rika yi mata amfani dasu

Ammi ta cigaba da kula da Aisha sosai

Da daddare Haseena ta shiga wanka ta fito, ta shafe jikinta da maganin da Malam gobe da nisa ya bata sannan ta saka kayan bachci mai matukar kyau da sheki, rigar bachcin tsawonshi ba zai wuce rabin cinya ba

Ta dawo falo ta zauna tana jiran dawowan Don, ta jira sa har ta gaji, ta kira wayarsa baya dauka, hankalinta ya tashi,

Harta fara cire tsammanin dawowarsa sai wurin karfe daya sai gashi ya shugo, da alamu daga club yake, idanunsa sunyi ja sosai, ta je ta rungumesa da sauri tana yer kukan munafurci

"Mijina meyasa ina kiranka baka dauka, ina shiga damuwa sosai wallahi, na yi kewarka sosai"

Ya kara kankame ta a jikinsa yana shafar bayanta, ya kai bakinsa kunnanta yana magana "I need sex baby"

Ta danyi murmushi "nima shi nake bukata mijina"

Suka kalli juna suka yi murmushi

Haseena da Don suka shige bedroom Haseena sai sha shi take yi tana buga ruwan cikinsa

"Yanzu shikenan kai baka son haihuwa kenan"

Don ya kalleta cikin ido "ba wai bana son haihuwar bane, kawai yanzu ban shirya bane"

Dadi ta ji a ranta ta cigaba da shafa shi "to yanzu ya zaka yi da Aisha da take son rushe maka burinka"

"Dole na zubar da cikin jikinta, ba zan taba yarda ta haihu ba"

Haseena ta rungume Don sosai tana jin wani farin ciki a ranta

Aisha washegari ta farka Ammi ta kawo mata breakfast, Aisha na gama ci ta shiga yin amai ba kadan kadan ba, Ammi hankalinta ya tashi sosai, da kyar ta samu amman ya tsaya, Ammi da kanta ta kwashe aman batare da tasa wata me aiki ba

Haseena da sassafe ta farka, amma bata ga Don ba, ta leka bayi baya nan, ta shiga falo ta duba nan ma baya nan, mamaki ya ishe ta, tana tunanin ina ya je bai sanar da ita ba, ta dawo dakinta ta shiga bayi ta yi wanka sannan ta dawo ta shirya, ta yi matukar kyau, ta daukin makullin motarta ta fita harabar gida, ta ja motan har wani restaurant, ta yi parking ta sauka ta shiga ciki

Tambayarsu ta shiga yi dame dame suke sayarwa, suka ce mata "birabisco da tuwon shinkafa sai kuka da miyar yakuwa"

"Ku sa min tuwon shinkafa da miyar yakuwa kuma kadaku sa min man shanu ko nama, haka nake so"

Nan take suka sa mata tuwon shinkafa da miyar yakuwa a cikin robber takeaway sannan suka sanya mata shi Leda mai dauke da suna da tambarin restaurant din

Ta amsa ta biyasu kudinsu sannan ta koma gida, ta shiga kitchen ta dakko kula mai kyau tasa tuwon shinkafar sannan a karamin kulan ta saka miyar yakuwar sannan ta dakko maganin da Malam ya bata ta zuba ta motsa da cokali, ta zuba kulolin a basket sannan ta fito falo, tsayawa ta yi cak tana kallan wachca ta shugo gidan

Feedo ce rike da akwatinta tana yatsine fuska tana shan kamshi, Haseena ta yi mata kallan sama da kasa "kefa? Daga ina?"

"Baki da hurumin da zaki min wannan tambayar"

"Ni kuwa nake da wannan hurumin tunda ni ce matar gidan"

Feedo tai yer dariya "to nima ai matar gidan ce"

Feedo ta ja akwatinta ta karasa tsakiyar falon ta zauna a kujera

"Fitar min daga gida" Haseena ta fada cikin tsawa tana nuna mata hanyar fita

Feedo ta tashi da sauri "idan har kika kara daga min murya wallahi sai na yi miki mugun duka, har ni ina cikin bariki zaki gwadawa bariki"

Haseena ta tsaya tana kallanta cike da mamaki

"Idan har kin cika ke cikakkiyar yer bariki ce, ki jirani bari na je na dawo"

Haseena komawa ta yi kitchen ta ajje basket din kulolin sannan ta fito, bata tanka Feedo ba ta fita, Feedo ta bita da kallo tana harararta

"Wawiya karamar yer bariki"

Feedo ta tashi ta kai akwatinta dakin Haseena ta ajje sannan ta shiga bayinta ta yi wanka ta fito ta canza kaya marasa nauyi sannan ta dawo falo ta dakko wiwi a jakarta ta zauna ta shiga nadawa bayan ta gama ta shiga sha tana busar da hayaki

Can Feedo tana more rayuwarta sai ga Haseena ta shugo tare da yen sanda

"Gata nan ku tafi da ita"

Feedo ta mike da sauri "babu Wanda ya isa ya tafi dani"

Cikin tsawa Haseena ta ce ku tafi fa ita kuma kadaku kuskura ku bayar da bailing ta

"Kada daya a cikinku ya taba ni"

Bin umarnin Haseena suka yi suka kama Feedo suka tafi da ita, "Haseena ta ce non sense" ta shiga kitchen ta dakko basket din abinci ta fita tabar gidan

Aisha kwance kan gado babu abinda yake mata dadi, ta sa hannu ta shiga shafa cikinta tana murmushi

"Allah sarki Bebina, ka kwanta a cikin mahaifiyarka babu wanda zan bari ya cutar da kai, ni ce garkuwarka, sannan ka yi hakuri da Dad dinka, karka damu dashi, shima yana sonka"

Ammi ce ta shugo ta zauna gefen Aisha "my Baby ya jikin?"

Aisha ta danyi murmushi "da sauki Ammi"

"Yanzu me zaki ci kenan?"

"Ammi bana jin cin komai"

"Oh ni, wannan cikin na azabtar dake, kamar yadda cikin mahaifinsa ya wahalar dani"

Aisha ta ce "shima Yaya ya wahalar dake kenan?"

"Sosai kuwa"

Ammi ta shiga shafa kan Aisha tana murmushi, Haseena ce ta shugo cikin sallama tana rike da basket na abinci

"Ammi Sannu ina kwana"

"Lafiya lau Haseena"

"To ya me jiki?"

"Jiki da sauki"

Haseena ta zauna gefen Aisha tana kallanta, tsoro ya kama Aisha bakinta na rawa ta ce ina wuni Aunty

"Lafiya lau yer uwata, ya jikin?

"Da sauki"

Ammi ta ji dadi a ranta "ga abinci na girka musamman saboda Aisha, nasan zata ji dadinshi"

Mum ta ce ai ba dole ta ci ba don kuwa ta kasa cin komai, komai ta ci sai ta dawo dashi

Haseena tai murmushi "zata ci ai tuwon shinkafa ne da miyar yakuwa" kawai sai Aisha ta hadiye miyau daga jin an ce miyan yakuwa amma sai ta shiga yin wani tunani daban

"Ban yarda da Haseena ba, bana tunanin zata bata lokacinta ta girka abinci saboda ni, tabbas akwai wani abu a zuciyarta"

Ammi ta bude kulolin tana abincin tana gani, wani kamshi ya shiga hancin Aisha, bata da wani buri irin ta ci tuwon nan amma ba yadda zata yi

Ammi ta ce ai kuwa miyan ya yi kyau, tashi ki ci

Haseena ta ji wani sanyi a rai, sai farin cikin Haseena ya koma bakin ciki da jin Aisha ta ce ba yanzu zata ci ba sai anjima

Ammi ta ce "to" sai ta rufe kulolin ta ajje gefe, Haseena kamar tasa ihu tsabar bakin ciki

Feedo taki shiga cell, tana zaune a wurin daukar statement, kiran Don ta yi ta sanar dashi tana police station bai jima ba sai gashi ya zo yana tambayar ta meya faru? Fashewa da kuka ta yi tana fada masa rashin mutuncin da Haseena ta yi mata, ransa ne ya baci sosai, a take aka bayar da bailing ta ba tare da an kira Haseena ba anji ta bakinta

Don ya dauki Feedo suka dawo gida, sannan ya fita ya barta ita kadai, zuwa ya yi ya samu Wizzy kan maganar abin da Haseena tayi wa Feedo, hankalin Wizzy ya tashi ya shiga fadin

"Matanka suna bayar da kai wallahi, da nine kai sakinsu zanyi gabadaya"

Don ya kalleshi da sauri "an maka ni mahaukaci ne?"

"Au hakama zaka ce"

"To meya kawo maganar na saki matayena bayan ina son su"

"Wani so kuma bayan ba kai ka gansu ka ce kana so ba, aura maka su aka yi"

"Eh bani na gansu ba na ce ina son su aura min su aka yi, amma ina son su, please karka kara min maganar rabuwa da matayena"

"To na ji ba zan kara yi maka maganar ba amma meyasa ka ce Feedo ta je gidan ka inda matanka suke zaune?"

"na sata ta je gidana saboda Haseena ta fahimci ina da yen mata kala kala masu hauka a kaina, hakan zai sa ba za ta dinga kawo min raini ba"

"Dakyau abokina kuma ka yi shawara sosai, to ya maganar cikin Aisha"

"Ai shawarar daka bani jiya da ita zanyi amfani kawai"

"Crazy sex ko?"

"Yes" suka tafa suna yer dariya

Aisha kwance Ammi da Haseena duk zaune suke bakin gado suna hira, Ammi ta mike

"Bari na je na duba ma'aikatan nan, na ji su shuru"

Haseena ta ce ok

Ammi ta fita, Haseena tai murmushi ta kalli Aisha, Aisha ta kawar da fuskarta cike da tsoro

Haseena ta jawo kulolin ta bude ta ajje gefen Aisha
Chapter 14 · 0% Book details