← Book details Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 40

Sashe 2

Angon Mata Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"What is wrong with you Baby?" Yin tambayar tayi tana shafa jikinshi, tuni tsigar jikinshi ya tashi, ya juyo da sauri yayi hugging dinta ya shiga yi mata wani hot kiss, itama kuma tana ta faman inda tafi so a taba a jikinsa, sai wani nishi yake yi, sun dade suna abu daya kafin ya wurgata gado, zai hau samanta ta dakatar dashi

"Ni ce a sama yau" ta fada tana lumshe ido kuma cikin shagwaba, sai ya ji wani yarrrrr

Kwanciya yayi ta hau kanshi, tofa anan labari ya fara, jin Don muka yi yana sunbatu "Wayyo Feedo, zaki kashe ni, Wayyo dadi" hakadai wannan daren ya kasance Feedo ta mantar da Don damuwar da yake ciki

Washegari, gida ya cika da yen uwa da abokan arziki, harda maroka da mabarata, shuru Abba bai ga zuwan Don ba, yanzu karfe goma sha biyu kuma karfe daya za'a daura aure, hakan yasa ya dinga danna masa kira amma ba'a daukawa

Ta bangaran Don yana tare da Feedo a kan gado suna ta bachci, can ya farka ya dauki wayarsa ya shiga ganin missed calls na Abba, tashi yayi da sauri ya shiga bayi ya yi wanka sannan ya fito ya saka kananun kaya ya saka sunyi masa kyau sosai, ya feshe jikinsa da turaruka dai dai lokacin Feedo ta tashi, kallanta yayi rai a bace, Bude durowansa yayi ya kwaso Dollars din ciki gaba daya ya watsa mata a kan gado

"Ni zan fita, kiyi ki fita don akwai bakin da zasu zo gidan nan yau"

Bata ce masa komai ba, ya kwashi wayoyinsa da kin motansa ya fita, ta bishi da kallo

Abba hankalinnshi ya tashi sosai, gashi babu damar ya fita yabar abokansa, suna shirin tafiya daurin aure sai ga Don ya shugo, Abba kunyar abokansa yaji yadda Don ya shugo cikin kananun kaya kamar bashi bane Ango

Maroka suka nufi wurin Don suna masa kirari "ANGON MATA BIYU" Dollars ya watsa musu ya taho wurin Abba

"Abba ina kwana"

Galla masa harara Abba yayi sannan ya ja sa suka tafi bangaransa, har Bedroom din Abba

"Kai wani irin shashasha ne, baka san kai ango bane, zaka wani saka kananun kaya"

"To Abba ai kasan dai banda manyan Kaya"

Abba bude durowansa yayi ya ciro manyan kaya hadda babbar riga ya mikawa Don

"Saka"

Don ya zaro ido

"Inaaa, Dad ba zan iya ba"

"Me ka ce, ka ce ba za ka iya ba, to yau zan ga dani da kai waya haifi wani"

"Haba Abba meyasa kake min irin haka ne, I am your only child, ta kamata ka dinga tarairayata, auran nan ma fa ba so nake yi ba"

"Saboda kai kadai ne dana saina dora maka soyayyar da bai da amfani, Umar yakamata kasan ka girma, karka bari duniya ta ganar da kai, ni zan fita, ka saka kayan nan ina jiranka a waje mu wuce wurin daurin aure"

Abba ya fita, Don ya yatsine fuska bashi da yadda zaiyi, haka ya saka kayan ya fito, Abba na ganinshi yayi murmushi sannan suka tattara suka tafi wajen daurin aure

A wurin daurin aure ne Don ya gane matan da aka aura masa sanadiyar jin sunayensu, da kuma ganin iyayensu, ranshi ya baci sosai ganin har da Aisha yer kanin Abba, fadi yake a zuciyarsa, me zanyi da Aisha, amfanin me zata min, har gwara Haseena zata fi yi min amfani, haka dai ya cigaba da maganganu a zuciyarsa, yen uwa da abokan arziki sai fatan alkairi suke masa, daga wurin daurin aure gida suka dawo

Guda kake ji na tashi, kakannin Don mata suka zagaye shi suna masa tsiya

"Angon mata biyu kenan, Allah ya tayaka riko"

Murmushi ya yi ya san dubaran da ya yi ya zame daga gidan, Hotel ya je ya kama ya daki, ya kira Wizzy yazo ya same shi

"Don yanzu ya kenan?"

"Dole zan siya wani gidan da zamu rika zama saboda hutawa"

"Kai amma gaskiya Abba ya kwafsa mana"

"Fada ka kara, ni wallahi ma abin daya dameni wata kwailar Yarinya fa ya aura min, kama santa"

"Wace ce kenan?"

"Yer kaninsa Aisha"

"Kamar na wayeta"

"Ba kama bane, ka wayeta ma"

"Idan na ganta zan gane ta, amma dayar fa?"

"Gwara ita, Haseena yer gidan minister of finance"

"Itama ban waye ta ba, amma fa my Guy kana ruwa"

"Kusa da kada kuwa"

Haka suka cigaba da tattaunawa

Haseena ita ce aka fara kawowa gidan Don, kawayenta yen iyayi da kaudi, sun kosa a kawo Aisha su ga ya take

Ta bangaran Aisha lokacin da za'a kawota kaita gidanta, ta dauki abin wasa sai ta ga fa da gaske ne, kuka ta fara yi tana birgima a kasa

"Ni ba zan je ba, ku kyale ni nafasa zuwa, Daddy ka taimake ni, wallahi bana son zuwa" kuka take tsakaninta da Allah, hawaye da majina sun dabaibaye fuskarta"

Aunty Rasheeda ce ta zo ta ja hannu ta ta kaita wajen Prof Attahir dake zaune a falonsa yana hada shayi a kofi

Aunty Rasheeda ta zaunar da ita a kujera sannan ta fita tabarsu, mikewa yayi da kofin shayi a hannunsa ya je ya zauna gefenta ya kira sunanta, ta dago ta kalleshi da jajayen idanunsa

"An ce min yau baki ci abinci ba gabadaya, amsa kisha" ya kafa mata kofin shayin a bakita ta shanye dukka

"Meyasa kike kuka" ta dago ta kalleshi

Ta fara magana cikin muryar kuka

"Daddy bana son na barku, ina sonku sosai, ya zanyi rayuwa batare daku ba, Daddy na fasa auran, ba zan je ba"

Tausayinta ya kamashi sosai, ya dan kawar da kansa ya goge hawayen daya cikan masa a idanu

"Kin tuna min da ranar dana auri Mumminku, tana ta kuka ba za ta zo ba, sai Dadinta ya rarrashe ta ya kawota, haka muka yi rayuwa har muka saba, a zamanmu da ita muka haifeku, muna farin ciki da junanmu, har gashi yau kin yi aure bakya son tafiya ki barmu, kenan zaman aure rayuwa ce ta farin ciki da zaka yada zuri'a su ji son junansu har basa son rabuwa, Mamana hakuri zakiyi kamar yadda Mumminku tayi hakuri ta zauna dani, kije ki yada zuri'arki kamar yadda Mumminku ta yada nata, Yata ina rokwanki daki saka mijinki farin ciki, ki gina muku rayuwa mai inganci wanda yayenku zasu tashi suyi alfahari daku, ina rokwanki da ki zama uwa ta gari"

Aisha ta share hawayen ta ta dago ta kalleshi, "Daddy naji nasiharka, insha Allahu ba zan baka kunya ba"

Murmushi yayi "I am proud of you mamana, tashi muje, ni da kaina zan kaiki"

Ta tashi ya rike hannunta suka fita ta kofar baya, babu wanda yasan da fitarsu, ya dauki wata motarsa mai bakin gilashi a ciki suka tafi

Haseena da kawayenta sunyi mamaki da ganin Mahaifin Aisha shine ya kawota da kanshi, ya kaita har dakinta ya zaunar da ita bakin gadon ta ya kara mata nasiha, daya gama har zai tafi ya juyo ya kalleta, kiran sunanta yayi ta amsa, ya nuna mata gadon da take zaune da yatsa

"Ki gyara gadonki, ki gyara shimfidar mijinki, yafi komai muhimmanci a zamantakewar aure"

Yana gama fada ya tafi amma ya barta a cikin duhu don bata san me yake nufi ba, kuka ta shiga yi babu mai rarrashin ta.

Kawayen Haseena sunyi ta jiran ango da abokansa amma shuru suke ji har wurin karfe goma, daya daga cikin kawayenta ta ce anya angon nan bai zo ba kuwa ya wuce dakin kishiyarki, Haseena ta dago ta kalleta, to ai wurina zai fara zuwa tunda ni ce aka fara kawowa, haka dai suka kara hakuri suna jira can daya daga cikin kawayenta ta ce to ki kira sa a waya mana, rarraba idanu Haseena ta shiga yi don bata da numbansa, sai ta wayince ta ce nifa kin sanni d aji ba zan kira shi ba ya ga ko na damu da wani abu ne, tafawa suka yi su kai shewa suna dariya, daya daga cikin kawayen Haseena ta fara habaici, "Gaba salamun baya salamun, Haseena kenan ga ki fara, gaki doguwa, ga diri ga asali, ga boko, duk wata mace da mijinki zai aura a bayanki take" sai guda kake ji kawai na tashi

Aisha tana daga dakinta tana jiyo duk abinda suke cewa, maganarsu bai dameta ba, tashi ta yi ta ga kofar bayi, budewa ta yi ta shiga, alwala ta yi ta dawo ta shiga jera nafilfilu tana kaiwa Allah kukanta

kawayen Haseena sun ga sha daya yayi ba alamun ango da abokansa, sallama suka mata zasu wuce akan gobe zasu dawo, haka tana gani suka wuce suka barta ita kadai, mamaki ta shiga yi sosai ganin Don bai zo ba, sai zuciyarta ta fara raya mata kodai yana dakin Aisha ne, bata tsaya tayi wani dogon shawara ba ta mike ta fita, direct dakin Aisha ta nufa babu sallama, ta samu Aisha kan sallaya tana wuridi

Haseena ta tabe baki "au ashe malama ce" ta fita tabar dakin Aisha ta cigaba da wuridinta, Haseena ta koma daki ta zauna tana tunanin me Don yake nufi da ita

A wannan daren Don da Wizzy club suka tafi suka sha casun su sannan suka kwaso yen mata suka dawo Hotel aka cigaba da sharholiya, Don yama manta dashi Ango ne

Washegari da sassafe Don ya duba wayansa ya ga missed calls na Abba da yawa, hankalinshi tashi ya yi, "ka da dai a ce Dad yasan ban kwana a gida ba, wanka ya shiga ya yi sannan ya fito ya sallami yen mata ya kara gaba

Haseena ta ci kwalliya cikin atamfa riga da siket, ta yi kyau sosai, ta zauna a falo ta daura kafa daya akan daya tana latse latsen wayarta, bata kula da shugowar Don ba sai dai kawai ganinshi ta yi a tsakiyar falo, kallanta yake yi sama da kasa, ta mike cikin murna ta je ta yi hugging dinsa, ya ji wani yarrrr, ta sake jikinshi tana fuskantarsa ta shagwabe fuska gami da turo baki "jiya ka barni na kwana ni kadai sai tsoro nake ta ji"
Salonta ya birgeshi sosai amma bai nuna mata ba, tsayawa ya yi kawai yana kallanta
Chapter 2 · 0% Book details