← Book details Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 30

Sashe 9

Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_

*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*

_Dedicated to MISS XOXO_

*18*

***Cike da mamaki Mami take kallonta bayan ta amshi jakar tata daga hannunta,

Tabbas wannan jakar tace nan tayi hanzarin bude jakar tafara duba kudinta da abubuwanta dake ciki,

Tsawon mintuna biyu tayi tana duban cikin jakar kafin ta dago fuskarta kunshe da mamaki saboda yanda ta yasar da jakar haka take babu abinda aka taba bare har acanja masa muhalli,

Ita kam Hafsat komawa tayi ta zauna bayan tabawa mami jakar, hankalinta kwance lokacin da taga mamin tana kokarin duba jakar saboda yanda ta tsinceta haka ta ajiyeta bata kara koda tabawa ba sai yau dinnan da zata Kawo mata,

"Yan mata ya sunanki?" Mami ta tambayeta fuskarta dauke da fara'a,

"Sunana Hafsat hajiya"

"Hafsat gaskiya kadanne irinku yanzu aduniya domin ba kowane zai tsinci makudan kudi da sauran muhimman abubuwa ya mayarwa mai kayanba sai wanda yake mutukar jin tsoron Allah, dama ni tun farkon ganin da nayi miki wallahi nayaba da hankalinki da nutsuwarki sannan lokaci guda naji kin shiga raina,nagode madalla..."

Dan murmushi hafsa tayi akaro nafarko domin jin dadin yabon da mami tayi mata,

"Ai babu komai hajiya, nima nagode Allah yabar zumunci"

"Ai nice da godiya hafsa, wallahi naji dadi mutuka domin ATM card dina yana ciki niduk dashi nafi damuwa ma wallahi saboda yarana sun koma makaranta last week to kuma yayansu account dinshi yadan samu problem babu damar ya tura musu kudi shine yasaka musu kudin a account dina inyaso sai atura musu tanan..."

"Ayya Allah sarki Allah yabasu sa'a"

"Amin amin, ai da har natura shi ma bankin yaje yakai musu report saboda kar asamu matsala sai gashi kuma kin Kawo min, wallahi nagode miki mutuka"

"Hajiya wallahi babu komai dama tunda naganta nace taki ce domin mu biyu ne aciki.."

"Allah sarki, kuma sai kika gane gidan nawa ma"

"Ehh dama nace koda ace banan ne gidan nakiba to zan Kawo saboda nasan kila idan nayi musu kwatance su ganeki.."

Murmushi mami tayi ta mike cikeda fara'a akan fuskarta,

"Allah sarki,Allah yayi miki albarka.."

Dining area taje,jimm kadan sai gata ta fito rikeda dan madaidaicin farantin silver,

Agaban Hafsat ta ajiye farantin tasake komawa ta dauko mata cup da juice na roba takawo mata,

Kallon farantin Hafsat tayi taga dambun nama ne da snacks,

"Ga lemo nan kisha kinji 'yata, ai ni danaga kin shigo nazaci kawar yatace surayya"

"Au Allah sarki ai inajin ma banma santa ba.."

"Ehh gaskiya bazaki santa ba saboda ba anan takeba tana can akasar Malaysia tana karatu yanzu haka saura shekara daya da yan watanni ta kammala, akwai kuma yayunta maza guda biyu Abdul da khalifa suma suna outside suna karatu sai babban yayansu shi yana nan anan.."

"Allah sarki" Hafsat tafada tana kallon agogon wayarta,

"Hajiya bari inje intafi saboda mamana tace kar injima"

"To ai hafsa bakici snacks dinba kuma ko juice dinma baki shaba"

"Babu komai hajiya, akoshe nake wallahi nagode madalla"

"To tsaya, ina zuwa" mami tafada tareda mikewa tashiga bedroom dinta tafito,

Kitchen ta wuce Jim kadan ta sake fitowa,

"Hafsat to ai sai ki fada min a inda gidanku yake ko saboda inason zan hadaki kawance da yata surayya, koda yake bari sai insa driver yakaiki kinga sai yagano min gidan ko"

Fuskar hafsa da murmushi tace,

"Hajiya nima driver ne yakawoni, kuma gidan namu ma bashida wuyar kwatance"

"To duk da haka dai zansa driver yabiku ya gano gidan naku"

"To shikenan hajiya nagode"

"Yawwa ga wannan babu yawa"

Dan tsorata Hafsat tayi saboda ganin girman ledar da mami ke mika mata,

"A'a hajiya bazan karba ba, nagode madalla amma kibarshi"

"Haba Hafsat karki maida hannun kyauta baya mana"

Dakyar dai mami tasamu har Hafsat ta karbi kayan, rakiya mami tayi mata har compound din gidan, nan sukayi sallama Hafsat tashiga mota drivern mami yana biye dasu suka fice daga gidan,

Kallon Salisu driver Hafsat tayi bayan sun hau titi sakamakon wasu kaya da tagani a sit din baya,

"Wannan kayan fa?"

"Nakine, daga ciki wannan matar tasa aka fito dasu tace asa miki acikin mota"

Sake waiwayawa Hafsat tayi ta kalli kayan nan taga katan din juice guda daya sai na biscuit shima guda daya sai snacks da dambun nama cikin wata leda mai dan kyalli, murmushi tayi tana yaba kirkin mami acikin zuciyarta wato duk abinda takai mata da bataci ba shine saida aka biyota dasu,

Har gida drivern mami yarakasu saida yaga shigarsu ciki sannan yajuya yakoma....

*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*

*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_

_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*

_Dedicated to MISS XOXO_

*19*

***Da murna akan fuskarta ta shiga cikin falon hajiya kubra, zaune ta sameta akan carpet tana goge wata doguwar rigarta mai dan santsi,

"Ah Ummi akan kibari nadawo sai ingoge miki shine kike yi da kanki?"

Hafsat tafada bayan tayi yozali da hajiya kubran,

"A'a Hafsat to ai bawani aiki ne mai yawaba, zaman kadaici ne ya isheni shine nadauko ina gogewa, abbanku ma kinga har yanzu bai dawoba nayi masa waya yace yana gidan abokinshi sunje meeting"

"To Kawo in karasa miki.."

Mika mata iron din hajiya kubra tayi tana cewa,

"Abinda yasa ban hada da ita acikin kayan gugar nanba bana so akona min itane tunda kinga tanada santsi..."

"Wannan kam sai anbita ahankali"

Bude kofa akayi aka shigo, Salisu driver ne yashigo bakinsa dauke da sallama,

Kayan da Mami tabaiwa Hafsat yashigo dasu ya ajiye yafita,

Saida Hafsat tagama goge duguwar rigar sannan ta tashi taje ta kinkimo kayan takawo gaban ummin tana fadin,

"Ummi kinga wai daga zuwa shikenan matar nan ta hadoni da wadannan kayan.."

Cikin fara'a hajiya kubra tafara bude babbar ledar da mami tabawa hafsan,

Manyan turarruka ne masu kamshi guda biyu irin na larabawa sai mansu da sabulai suma masu kyau sai abin hannu da sarka fation amma kuma mai mutukar kyauce,

Kallon kayan Hafsat keyi cikeda mamaki haka itama hajiya kubra mamakin ne ke bayyane akan fuskarta,

"Hafsa anya kuwa duk murnar mayar da jakar nan zatasa matar nan tabaki wadannan uban kayan? Anya kuwa?"

Murmushi Hafsat tayi ta gyara zamanta,

"Wallahi Ummi nima dai haka nace to amma yanda naga ta sake dani tanata yimin hira tana bani labarin yaranta sai nima nadan saki jiki domin harfa cemin tayi wai tanada yarinya budurwa tana kasar waje tana karatu idan ta dawo zata hadamu kawance.."

"Kawance...?" Hajiya kubra ta tambayeta tana dariya,

"Wallahi haka tace Ummi, kinga fa har drivern ta taturo ya biyomu wai yazo yagane mata gidanmu.."

"Allah sarki ai akwai mutane masu kirki a duniya, wasu sunada son jama'a.."

"Wannan kam tanada son mutane wallahi Ummi, kinga snacks din wai dan banci ba shine ta hado min dashi"

Jan kayan sukayi suka ciro suna dubawa, cake ne da meat pie da sauran tarkacen snacks,

Ajiyewa kayan sukayi har saida Alhaji sa'id yadawo suka nuna masa, tun daga wannan rana ita hafsa tama manta da batun mami amma ita kam mami Hafsat tana makale aranta,

Ranar alhamis da rana ta dawo daga super market siyayyar kayan amfanin gida ta biya ta gidansu Hafsat,

Hajiya kubra tana kitchen tana kokarin sauke girkin rana da tayi taji sallamar mami, da fara'a ta karbeta tamkar dama ta santa tayi mata jagora zuwa cikin falonta,

Ruwa da abinci da juice takawo mata sannan tazauna suka fara gaisawa,

"Hmm nace yarinyarki kuwa tana nan?"

"Wacce daga ciki?"

Murmushi mami tayi ta daga kanta takalli hoton amal wanda ke kafe ajikin bangon dakin wanda sak bashida maraba da Hafsat,

"Wannan, gata nan ajikin hoto" mami tafada tana murmushi,

"Ayya to ai tana makaranta, tatafi school tun watanni hudu da suka wuce"

"A'a, anya kuwa? Ai naga last week takai min jakata dana yar acikin adaidaita sahu.."

"To ai shiyasa nace miki wacce aciki domin su 2 ne kuma duk kamanninsu daya,wannan wacce kika nuna amal ce.." Hajiya kubra tafada tana dariya,

"Allah sarki to ba wannan nake nufiba, dayar nake nufi wacce taje gidana tace min sunanta hafsat"

"Ehh,itama tana makaranta amma karfe 2 zata taso.."

Kallon agogon hannunta mami tayi, karfe 12:30 narana,

"To gashi nikuma sauri nakeyi, idan tazo agaisheta, zanje intafi"

"Insha Allah zataji, gashi bakici abincin ba"

"Alhamdulillah, nagode sosai"

Tashi tayi tafita nan hajiya kubra ta bi bayanta ta rakata har bakin gate mami kuwa sai jaddadawa take cewar agaida Hafsat idan tazo,

Koda hafsat tadawo hajiya kubra tafada mata murmushi kawai tayi batace komai ba, ita harkokin gabanta kawai takeyi yanzu daga makarantar boko sai makarantar islamiyya kuma cikin hukuncin ubangiji duk tana fahimtar karatun nako wanne fanni,

Bayan sati biyu da zuwan mami tasake komawa ranar laraba da yamma amma ranar ma bata samu hafsat ba domin tatafi islamiyya,

Sam bataji dadin wannan sabanin da suke yiba wanda har hajiya kubra saida ta fahimci haka,

"Hajiya kiyi hakuri insha Allah zan turo miki ita gobe ko ranar juma'a, hafsan ce wallahi uzururrukanta yawa garesu amma insha Allah zata zo miki.."

Sai lokacin damuwar dake kan fuskar mami takau har ta maye gurbinsa da murmushi,

"To ina jira amma dai dan Allah hajiya kicika alkawari kuma ranar juma'a ma yakamata ki turo min ita yanda zamu dade muna hira.."

"To insha Allah zata zo, agaida mutanen gida"

Sallama sukayi mami tafita tatafi, kamar yadda hajiya kubra ta alkawartawa mami haka ta cika alkawari ta hanyar saka driver yakai Hafsat gidan ranar juma'a da musalin karfe 1 narana,

Lokacin da Hafsat taje gidan mami tana cikin bedroom dinta zaune agefen gado suna yin waya da surayya jin sallama yasata fita ganin Hafsat dince tace ta karaso, har cikin bedroom dinta takaita tace ta zauna agefen gado amma fur hafsa taki zama sai akasa ta zauna kan dan madaidaicin carpet din dake shimfide akusa da gadon,

Wayar hannunta ta mikawa Hafsat,

"Ungo amshi ku gaisa da yar tawa surayya, ina zuwa bari inkawo miki ruwa kafin ku gama"

Karbar wayar Hafsat tayi tana murmushi tafara kallon screen din wayar saboda video call ne, surayyan ma daga can kurawa screen din ido tayi tana kallon Hafsat nan suka shiga gaisawa kamar dama can surayya tasanta domin hira sosai take yimata,
Chapter 9 · 0% Book details