← Book details Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 30

Sashe 23

Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Khadija kenan kin san dai ai komai yana faruwa ne da dalili, kawai dai ki kalli wannan a matsayin wata kaddara wacce take tawa kuma dole saita sameni.."

Jijjiga kai tayi,

"Hakane, to Allah ya rufa asiri.. Sannan insha Allah nayi alkawari zan baka gudun mawa dari bisa dari acikin rayuwarka.."

"Nagode khadija amma ni babu wata gudun mawa da nake nema daga gareki.."

Jin abinda yace yasa Hafsat saurin kallonshi, tashi khadija tayi tai musu sallama tafita, har kofar daki hafsat ta rakata bayan taga fitarta ne takoma wurin yusleem,

"Yaya yusleem gaskiya banji dadin abinda kafada ba, ai ni sai nake ganin ko babu komai wanda ya nuna yanayi dakai yafi..."

Bai barta takarasa ba yajata jikinshi ya rufe mata baki da hannunshi yana kallonta,

"Nanah akwai dalilin dayasa kikaji nafadi haka, wallahi ba dan Allah khadija zata taimaka mana ba, akwai wata manufa atare da ita.."

"Taya kasani?"

"Saboda khadija matatace ada, saida muka rabuda ita sannan na aureki.."

"To ai ba lallai bane abinda kake zargi yazama gaskiya ba, nidai dan Allah idan tasake dawowa next time karka yi mata irin wannan.."

Kura mata ido yayi saboda jin abinda tafada, lallabashi takoma yi har ya amince,

Washe gari da safe misalin karfe 11 saiga khadija tasake dawowa gidan lokacin hafsat na gyarawa yusleem farcenshi, da fara'a Hafsat ta karbeta suka gaisa, fuskar yusleem kuwa babu yabo babu fallasa,

Cigaba da yimishi gyaran farcen Hafsat tayi yayinda ita kuma khadija ta zauna tana kallonsu aranta tana tunanin yanda akayi har Hafsat tasamu irin wannan damar awurin yusleem domin abisa dukkan alamu tasamu fada mai girman gaske awurinshi sabanin su da ko kallo basu isheshi ba lokacin da yana tareda su,

Ajiyar zuciya ta dan sauke sannan ta kalli yusleem wanda idonshi ke kan hannayensu shida Hafsat wanda ta rike nashi cikin nata acikin zuciyar shi kuwa dan murmushi yakeyi saboda ganin yanda kalolin fatarsu guda biyu ta hadu tashi fari tata kuma bak'a,

"Uhmm yusleem dama cewa nayi bari nabiyo na dubaku saboda naga kamar baka da lafiya ko? Domin duk ka sauya"

Kafin yayi magana Hafsat ta amsa,

"Ehh wallahi zazzabi yake fama dashi amma hakanma da dan sauki.."

"Ayya Allah yakara bashi lafiya.."

"Amin.."

Kallo na tsanaki khadija ta rinka bin dakin dashi aranta tana mamakin tayadda akayi wai yusleem yadawo haka duk da cewar jiya yayi mata bayani amma gaskiya har yanzu bata gamsu da bayanin dayayi mata ba duba da irin tarin dukiyarshi da matsayinshi ada,

Mikewa tayi tsaye tana murmushi,

"Yawwa bari naje na tafi sai wani lokacin idan nadawo.."

Cikeda fara'a Hafsat ta kalleta,

"Zaki tafi? To mun gode madalla Allah yasaka da alkhairi.."

"Nagode khadija, sai anjima" yusleem ya fada yana damke hannun hafsat acikin nashi, fita khadija tayi tana fita yusleem yaja hafsat jikinshi yana murmushi, lakuce mata hanci yayi,

"Yau fa banga kinci abinci ba?"

"Kaima ai bakaci ba, gara ma ni amma kai yaushe rabonka da abinci"

Murmushi yayi ya matse kanta akan kirjinshi tayanda har tana iya jiyo bugun zuciyarshi,

"Hafsat wani tunani nafara gameda ke da rayuwarki..., ni ina ganin kodai in sawwake miki ne kitafi gidanku kije kici gaba da rayuwarki cikin kwanciyar hankali saboda nasan na takura rayuwarki da yawa ba kadanba..."

Jin abinda yafada yasa gabanta mummunan faduwa bayan zuciyarta ta harba da karfi, dagowa tayi ta kalleshi idanuwanshi sun danyi ja kadan, ganin ta kura mishi ido abinda bata taba yiba yasashi sake mayar da kanta ya kwantar bisa kirjinshi,

Daga shi har ita shiru sukayi babu wanda ya iya cewa uffan domin kowa da abinda yake sakawa acikin ransa.

Abangaren khadija kuwa bayan tafita daga wurinsu yusleem tafi minti goma sha biyar tana tsaye ajikin motarta takasa shiga, tunani take anya kuwa yadace tabar yusleem acikin wannan halin?

Girgiza kai tayi,

"Am sorry yusleem dan gaskiya yazama dole nasan abinyi..."

Shiga motarta tayi tai mata key tafita daga unguwar, fitarta keda wuya bata zame ako inaba sai gidan mami mahaifiyar yusleem, cikin sa'a kuma mamin na gida bata fita ko inaba,

Lokacin da khadija ta shiga kawataccen falon na mami mamin na cikin bedroom dinta tana shiryawa kamar me shirin zuwa unguwa, jin sallamar khadija yasata fitowa falo,

Kallo khadija ta dan bita dashi, tana sanye cikin wani swiss les dan gaske golden colour sannan tasaka sarka da earrings da warwaro duk golden gashi tasha jan lalle kai idan kaganta bazaka taba cewa ta ajiye samarin yara ba,zama mamin tayi tana murmushi saboda ganin khadija......

_Fans kuyi hakuri da wannan please,ina cikin hidima ne..._

*_Ummi Shatu_*👌🏻

© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_DEDICATED TO MISS XOXO_

*Sakon fatan alkhairi gareku members na haske writers asso fans, this page is for u...*

*39*

***Gaisar da mami khadija tayi bayan sun gaisa ne khadijan tafara tunanin ta inda ya kamata ta bullowa da mami maganar yusleem, zuwa can dai ta dan nisa tace,

"Mami nikuwa yusleem yana kasar nan..?"

Murmushi mami tayi,

"Yusleem baya nan khadija, nikaina rabon da inyi magana dashi kota wayane anjima, daga yin tafiya shikenan shine har yau..."

Jijjiga kai khadija tayi,

"Ai kuwa Mami naga yusleem, yana nan agarin nan babu inda yaje domin naganshi da idona kuma har magana munyi dashi jiya da yau, yanzu ma daga wurinshi nataho nan.."

Mamakine ya bayyana akan fuskar mami,

"A ina kika ganshi khadija? Yaushe yadawo..?"

"Ai dama mami babu inda yusleem yaje yana cikin garin nan kawai dai wurin zama ya sauya, agaskiya mami na tausayawa halin da naga yusleem aciki.."

"Meya sameshi khadija? Dan Allah fada min idan wani abune ya sameshi" mami tayi maganar cikin rudewa,

"Ba wani abun tada hankali bane mami, kawai dai muje inkaiki gidan da yake ki ganshi da idonki.."

Da hanzari mami ta tashi tashiga bedroom dinta ta dauko mayafi ta fito jikinta har wani yar tsuma yake saboda taraddadin halin da zataje taga yusleem aciki,

Acikin motar khadija suka fita, ganin irin yanayin unguwar da khadija ke kokarin shigar dasu yasanya mami fara kokwanton anya kuwa khadija yusleem dinta tagani kuwa? Kasa hakuri mamin tayi har saida tayi magana,

"Khadija anya kuwa idanuwanki sun gane miki gaskiya?, me yusleem zaizo yayi anan? Sannan tayaya za ace waima yadawo kasar nan amma ni a matsayina ta mahaifiyarshi inkasa sani..."

"Mami ai magana kam takare tunda gamu munzo kofar gidan da yusleem ke ciki, zaki ganewa idonki komai"

Shiru kawai mami tayi amma bawai dan ta yarda da khadija bane a'a sai dan dai kawai ba abokiyar yin mahawararta bace shiyasa bazata yita jayayya da itaba,

Bude kofa kowaccensu tayi ta fito daga cikin motar, nan suka tasamma cikin gidan gadan gadan bayan khadija tarufe motarta,

Wani mamakin ne yasake lullube mami lokacin da suka shiga cikin gidan saboda yanda taga tsarin gidan yake dakuna ratata banda kaca kacan da gidan yayi sannan ga mata nan atsakar gidan kowacce tana harkar gabanta, watama ko riga babu saiko daurin kirji,

Kofar dakin da su yusleem suke khadija ta karasa dasu suka tsaya khadija tafara doka sallama,

Cikin barcin da ya daukesu sama sama kunnuwansu suka fara amsar sallamar da khadija keyi,

Hafsat ce ta dan bude idonta gamida sake kankame yusleem wanda take kwance ajikinshi,

Jin ansake kwada sallamar da karfi yasanyata tashi tana jan dan karamin tsaki, shi kanshi yusleem din shima baiji dadin wannan katse mishi baccin da akayi ba, juyi yayi yasake gyara kwanciyarshi ita kuma Hafsat ta dauki dan kwalinta tafita,

Tana yaye labulen tayi arba da mami da khadija wadanda ke tsaye akofar dakin, tamkar acikin mafarki haka Hafsat tagani, take kuma gabanta yashiga faduwa,

Tunda mami taga Hafsat tasan abinda khadija tabata labari gaskiyane dan haka yanzu bata da sauran kokwanto kuma,

Cikin rawar baki Hafsat tace,

"Mami..."

"Na'am Hafsat, ashe dagaske kuna nan kuna rayuwa batare da sanina ba..?" Mami tayi maganar cikin sanyin jiki,

"Mami shigo daga ciki"

Shiga cikin dakin mami tayi bayan tacire takalminta, cikeda mamaki take bin kowacce kusurwa ta cikin dakin da kallo wanda take ganinshi kamar dakin girki irin na kauye,

Har lokacin da suka shigo yusleem baisan cewar mami bace domin baccinshi yakeyi hankali kwance amma jin maganarta yasashi juyowa da sauri bayan yatashi,kallon mamin yakeyi fuskarsa dauke da mamaki gamida al'ajabi,

"Mamie..." Yakira sunanta yana mutsutstsuke ido,

"Yusleem wacce zuciyarce tabaka wannan mummunar shawarar har kazo nan kake rayuwa batare da sanina ba? Meyasa zakayi min karya?"

Wadannan sune tambayoyin da mami ta jefo masa batare da ta amsa kiran da yayi mata ba, fuskarta kunshe da fushi da bacin rai take kallonshi.......

*_Ummi Shatu_*👌🏻

© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_DEDICATED TO MISS XOXO_

*40*

***Rasa abinda zaice yusleem yayi illa kallon mamin da yakeyi wadda itama shi take kallo kafin daga bisani ta mayar da kallonta kan Hafsat wacce ta sunkuyar da kanta kasa,

Dakin nasu mami takoma tafara kallo kusurwa bayan kusurwa,

"Mami dan Allah kiyi hakuri wallahi akwai kwakkwaran dalilin da yasa kikaga hakan tafaru, zamuyi miki bayanin komai...." Hafsat tayi karfin halin yin magana,

Mami bata bawa Hafsat amsar maganarta ba illa sake balbale yusleem da fada da tayi,

"Ka dauko yarinyar mutane kazo ka ajiyeta anan kana wahalar da ita, dubi yanda takoma, kalli kaima yanda ka zama duk kabi ka rame kayi baki daga gani kana cikin mawuyacin hali, to da ace khadija bata ganku taje ta fada minba da sai yaushe zaku nemeni? Da sai ka kashe musu 'ya sannan zakaje min da mummunan labari? Yayi kyau"

Mikewa mami tayi ta kalli khadija wacce ke zaune ta sunkuyar da kai tana sauraren duk abubuwan dake faruwa,

"Tashi mu tafi khadija"

Kallon yusleem mami tayi,

"Kai kuma na baka nanda mintuna 20 ku tattaro duk kayanku kuzo gida ku sameni, idan kuka wuce haka to ina mai tabbatar maka ranka sai ya baci.."

Fita mami tayi daga cikin dakin khadija ta rufa mata baya,

Kallon yusleem Hafsat tayi bayan mami tafita,

"Yaya yusleem katashi mu bita, idan munje gidan sai muyi mata bayani atsanake kaga kamar fa tayi fushi..."

Dafe kanshi yayi wanda ke yimasa wani irin ciwo,
Chapter 23 · 0% Book details