← Book details Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 30

Sashe 8

Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiranta hajiya kubra tayi itada alhaji sa'id domin suji ra'ayinta dangane da kudin,

"Hafsat kudin naki ajiyewa zakiyi a banki ko kuma wani abu zaki siyo ki ajiye?" Alhaji sa'id ya tambayeta,

"Abba ba ajiyewa zanyi ba, kaya nakeso insiya inkaiwa gidan marayu gudun mawa" tabashi amsa idonta yana kallon kasa,

Murmushi Alhaji sa'id yayi,

"Allah sarki hafsat hakika ke tagari ce kuma kinada hankali da nutsuwa, Allah yayi miki albarka, yanzu abinda za ayi shine, gobe idan Allah yakaimu zan hadaki da driver sai yakaiki kasuwa ki siyi duk abubuwan da kike ganin zaki siya sai kuje ki kai musu.."

"Allah yabaki lada ya biyaki da gidan aljanna kinji.." Hajiya kubra tayi magana cikin marerecewa,

Tashi hafsa tayi tafita domin malamin dake koyar da ita karatun arabi duk yamma yazo yana jiranta.

Washe gari kamar yadda alhaji sa'id ya alkawarta haka yasa driver ya dauketa yakaita kasuwa tayi siyayya wadda saida ta karar da kudin tass ko kwandala baiyi saura ba, daga nan gidan marayu suka wuce, koda sukaje kuma akaga irin gudun mawar da takai saida kowa yayi mamaki domin kayane na amfanin yau da kullum irinsu sabulun wanka da na wanki, omo, sugar, man shafawa da makamantansu,

Rungumeta Amina tayi tana kukan farin ciki tareda yi mata addu'ar alkhairi, bama Amina kadai ba kowa addu'ar da yake yi mata kenan....

*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*

*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_

*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*

_Dedicated to MISS XOXO_

*16*

***Haka rayuwar Hafsat taci gaba da tafiya akoda yaushe burinta shine taga ta taimakawa yan uwanta marayu wadanda basu samu gataba suke zaune acikin gidan marayu,

Rikon da hajiya kubra keyi mata kuwa rikone na tsakani da Allah wanda ko yar cikinta iya abinda zata iya yimata kenan,

Kasancewar Hafsat din ta maida hankali akan karatuttukan da ake koya mata yasa malamin dake koyar da ita fadawa Alhaji sa'id cewar lokaci yayi wanda yadace asata a makaranta duk da cewar bata faro karatun daga tushe ba amma yana kyautata zaton cewar zata iya, shawarar malamin Alhaji sa'id yabi aka sa Hafsat din awata makaranta ta day,

Zuwanta makaranta yasata sake samun gogewa da wayewa domin ta hadu da yan mata irinta wadanda suka fita wayewa,

Haka rayuwarta taci gaba da gudana sannan duk da ta shiga makaranta hakan bai hanata cigaba da yin saka ba tana saidawa idan ta hada kudin sai taje kasuwa tayi siyayya kamar yadda tasaba ta kai kayan gidan marayu.

Kwanci tashi har Amina kawarta ta samu mijin aure daya daga cikin ma'aikatan gidan marayun ne zai aureta,ba karamin dadi Hafsat tajiba domin Amina itama zata bar rayuwar kunci da talauci gamida maraici, tareda ita aka gudanar da komai aka daura aure suka rakata gidan mijinta wanda keda makobtaka da gidan marayun.

Akwana atashi ahaka Hafsat tashiga aji biyar na secondary domin dama a aji hudu aka sakata, kuma acikin wannan lokacin ne amal tazo gida hutu daga kasar Malaysia, kai idan kagansu kamar wasu yan biyu domin ko Alhaji sa'id dakyar yake iya banbance su musamman ma idan suka saka kaya iri daya domin hajiya kubra tun zuwan Hafsat gidan iri daya take yimusu dinki tareda amal bata taba banbantawa ba,

Saida amal tayi wata uku sannan takoma makaranta tana cike da kewar Hafsa domin komai tare suke yi gashi jininsu ya hadu sosai, itama Hafsat din tana mutukar kewarta.

***

Abangaren yusleem kuwa har yanzu bai fitar da matar aureba duk kuwa da irin Matsin lambar da Mami keyi masa akan ya zabo matar aure amma shiru to shi girman kanshi ma bazai barshi ya tunkari mace da maganar soba,

Kullum idan yaje gidan Mami sai ta tisashi agaba da tambayoyi amma sai dai yayi mata shiru daga karshe ma sai cemata yayi shifa har yanzu bai samu budurwar ba, kyaleshi Mami tayi ta zuba masa ido domin ta dade da sanin cewar aljana ce ta aureshi.

***

Misalin karfe 2:30 narana agogon hannunta ya nuna, dan karamin tsaki taja ta fito daga cikin motar tata ta kulleta ta tsaya bakin titi tana jiran adaidaita sahu,kallo daya kawai zaka yimata ka fahimci ko wacece ita domin sanye take cikin atamfa exclusive purple colour da mayafi shima purple sai takalmi da jaka duk purple colour,

Bakowa bace face Mami wadda ta dawo daga al hikima clinic dubiyar yar kawarta hajiya maryam wacce aka yiwa cs adaren jiya, ganin motarta ta bata matsala yasata tsayawa tanata kiran driver dinta amma bata sameshi ba wannan dalilin ne yasata barin motar awurin ta zabi tasamu adaidaita sahu yakaita gida inyaso daga baya sai drivern yazo ya dauki motar,

Adaidaita sahu ta tare tashiga yaja suka tafi, akan hanyarsu ne daidai queen ihsan restaurant akofar wata private school ta hangi wata yar budurwa tana tsaye sanye da uniform wanda yayi mutukar karbarta tana tare adaidaita sahun,

Da a niyyar Mami ta dauki drop yakaita gida kawai amma ganin budurwar wacce da alama itama agajiye take sannan ga rana yasa mami barin mai adaidaita sahun ya tsaya yadauki budurwar,

Lokacin da budurwar ta shigo ciki saida tagaida mamin, binta da dan kallo mamin ta yi tana yaba hankalinta,

"Hajiya ina zan saukeki..?" Mai adaidaita sahun ya tambayi budurwar,

"A titin fahad mangul zan sauka.."

"Ok to sai nafara sauke wannan hajiyar kenan saboda ita a madaci road zata sauka"

"Babu damuwa" inji budurwar,

Suna tafe dukkaninsu sunyi shiru saiko karar radio din da mai adaidaita sahun ya kunna dahaka suka karasa gidan mami, hand bag dinta ta bude ta fito da karamar jakar hannunta ta fiddo naira dari biyar ta mikawa mai adaidaita sahun, key din motarta da yafadi ta dauka ta fita tana gyara mayafinta,

Saida sukaje kofar gidan su wannan budurwar tana shirin fita bayan tabawa mai adaidaita sahu kudinsa sai kawai tayi ido hudu da yar karamar jakar hannun Mami wacce ta Jefarta aciki bata kulaba lokacin da zata dauki key din motarta,

Batayi magana ba tasa hannu ta dauki jakar tafita batareda tabari mai adaidaita sahun yaganiba....

*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_

_Dedicated to MISS XOXO_

*17*

***Tana makale da jakar acikin hijabinta ta shiga gida, afalo ta iske ummi tana lissafin wasu kayan yara da aka Kawo mata domin ta sara,

Ganinta yasa ummin yin murmushi,

"Hafsa na yau kam nayi miki laifi driver baije ya daukoki ba na aikeshi bakin kasuwa shagona yaje yakai kayan nan da aka Kawo jiya kinga shine har yanzu bai dawoba.."

Murmushi Hafsat tayi tazauna tana cire takalmi da safar dake kafarta,

"To ai babu komai ummi tunda gashi nadawo.."

"Ame kika dawo?"

"Adaidaita sahune dama kuma inada canji acikin jakata, kinga ma har na tsinci jakar wata mata wacce muka zauna tareda ita aciki" takarasa maganar tana nunawa ummin jakar,

"Yarwa tayi? To yanzu taya zaki ganta har abata, kodai cikiya zamu kai gidan radio?"

"Ai naga gidanta ummi, naga gidan data shiga koda ace ba gidanta bane tunda dai nan taje idan naje ai zan sameta"

"To shikenan tunda kinga gidan da taje sai kije ki kai mata koda gobe ne"

"To ummi Allah ya kaimu"

"Amin, kije kicire uniform din ki shiga kitchen akwai abinci yana nan"

"Toh" ta amsa tareda mikewa ta shiga bedroom dinta.

Washe gari da yamma ta shirya bayan tayi wanka, wani jan leshi tasa mai adon blue ajiki, farin hijab tasa tafito tana rikeda jakar data tsinta,

A balcony tasamu hajiya kubra zaune ta dan kishingida tana sauraren radio,

"Ummi bari inje indawo"

"To hafsa sai kin dawo, zaki gane gidan dai ko?"

"Ehh zan gane, to kije ku tafi da salisu driver sai yakaiki"

"Toh ummi" ta amsa tareda wucewa,

Abakin gate ta iske drivern yana zaune wurin mai gadi suna hira, ganinta yasashi tasowa domin yagane unguwa zasu fita, gidan baya yake kokarin bude mata taki tahanyar bude gidan gaba tashiga ta zauna.

Mami kuwa tunda ta koma gida take faman duba yar karamar jakarta domin makudan kudi ne aciki sannan uwa uba akwai muhimman abubuwanta aciki irinsu katin shaidar dan kasa, gashi ATM card dinta yana ciki,

Ganin bata ganta ba ya tabbatar mata da cewar jefarwa tayi, zama tayi tasoma kiran wayar yusleem amma shiru bai daga ba har takatse tasake kira, saida ta kirashi sau uku bai dauka ba,

Tana kokarin tashi taji shigowarshi domin shi shigowarsa cikin gidan ma daban banci dana kowa saboda awani hankali yake bude kofa ya rufeta,

Yana shigowa ko zama baiyi ba tafara magana,

"Kana inane haka nayita kiranka bakai picking ba? Nafita da mota ta dazu tabani matsala akusa da al hikimah clinic naje duba yar gidan hajiya maryam"

Saida ya zauna yadan jingina kanshi da jikin kujera sannan ya kalli mamin yayi magana,

"To amma mami meyasa zaki fita ke kadai? Meyasa baki tafi da driver ba? Saboda irin wannan na ajiye miki driver fa"

"Yusleem drivern ai baya nan yatafi gareji gyaran daya motar tawa shine naga basai na jirashi ba gara kawai naje nadawo"

"To meye matsalar motar?"

"Ina zan sani, tana can nabarta awurin ai saboda taki tashi, ni duk ma ba wannan ba, jakata na yar ahanya ko akofar gidan nan ko kuma acikin adaidaita sahun da nahau.., Kiran da naketa yi maka dama shine so nake kayi maza kaje bank kakai repot saboda ATM card dina yana cikin jakar"

"Mami shiyasa ai nace kidaina yawo dashi.."

"Babu komai, kai ai ba a ketarewa kaddara"

"To Allah ya rufa asiri, bari naje"

Tashi yayi yafita ita kuma ta mike zuwa cikin bedroom dinta.

Har mami ta fidda rai da samun wannan jakar kwatsam washe gari da yamma tana falo zaune tana kallo gabanta kuma snacks ne ajiye tana dauka jifa jifa tana ci taji sallama,

Amsa sallamar tayi tadan gyara zamanta tana jiran wanda keyin sallamar yashigo,

Wata yar budurwa tagani wacce kamar ta dan san fuskar amma dai bazata iya tunawa yanzu ba,

Ciki Hafsat ta shiga ta tsugunna tagaida mamin,

"A'a tashi mana, tashi ga kujera nan ki zauna" ita Mami ma duk tunaninta ko kawar surayya ce,

"Hajiya dama jiyane bayan mun saukeki a adaidaita sahu mun tafi yakaini gida sai naga jakarki kin mantata aciki shine nakawo miki yanzu..." Hafsat ta kammala zancen tana mikawa mami jakar.....

*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
Chapter 8 · 0% Book details