← Book details Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 30

Sashe 10

Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami tana cikin kitchen tana warming din abinci yusleem ya shigo yana sanye da farar shadda mai mutukar tsada kai idan kaganshi zaka dauka sabon ango ne saboda tsananin kyawun da yayi dama kuma shi haka ka'idarshi take baya taba saka manyan kaya sai ranar juma'a sai ko wani babban muhimmin abu,

"Har kadawo daga masallacin?" Mami ta tambayeshi tana kokarin sauke tukunya daga kan wuta,saida yaje yadan jingina da jikin bango sannan ya amsa mata da,

"Ehhh, ina kukun naku yake naga kina girki dakanki mami?"

"Ba girki nakeyiba dumame ne nayi bakuwa ne shine zan kai mata abinci"

"Ok" shine kawai abinda yace yajuya zai fita, dakatar dashi mami tayi,

"Bazaka shiga ku gaisa da bakuwar tawa ba?"

"Ina zuwa mami, ai ba tafiya nayiba" daga fadin haka yasaka kai yafice,

Filet mami ta dauko ta zubawa Hafsat abincin, macaroni da miyar danyen kifi sai abinsha da fruits, har mami takoma su Hafsat suna ta hira itada surayya wani dadi mami taji wanda ita kadai tasan ma'anarsa acikin zuciyarta,

Saida mami ta karbe wayar tace Hafsat taci abinci sannan hirar tasu ta katse, kasa cin abincin tayi saboda kunyar mami wanda har mamin saida ta fahimci haka, dakyar dai tadan ci ta tattara kayan zata fitar mami ta hanata,

Wuni guda tayi domin sai la'asar sannan hajiya kubra taturo driver yadauketa, mami kam wannan karon kaya sosai ta hada mata domin acikin kayan da take ajiyewa na auren yusleem ta dauko mata duguwar riga dark blue da takalmi da turarruka,

Kin karba Hafsat tayi amma mami saida tasaka mata acikin mota tatafi da kayan,

Lokacin da takoma gidan hajiya kubra taga kayan rasa abin cewa tayi sai can ta nisa tayi magana,

"Hafsat wannan matar haka zatayi ta miki hidima batareda wani abu aranta ba? Nifa ina tsoron rayuwar yau domin wallahi akwai ayar tambaya aciki"

Murmushi Hafsat tayi,

"Wallahi Ummi babu komai sai alheri domin yau munyi waya ma sosai da yartata.."

"To shikenan tunda hakane"

Koda suka nunawa Alhaji sa'id kayan fada yashiga yi sannan yace kar Hafsat takara zuwa gidan shi bai yadda da mami ba,

Tun daga wannan rana Hafsat bata sake zuwa ba amma da aka kwana biyu ita mamin sai gata tazo, ranar kuma tayi Sa'a Hafsat din nagida tana kan keken sakarta tana dinki,

Kyakkyawar tarba hajiya kubra da Hafsat din sukayi mata, ta dan jima agidan kafin tayi musu sallama tatafi, sai bayan tafita ne maigadi yashigo da kaya wanda takawowa Hafsat,

Kayan makulashe ne da turaruka masu tsada, ita kanta hajiya kubra yanzu tafara kuma wani tunani akan mami Wanda dai tabarwa zuciyarta bata furta ba.

Lokuta zuwa lokuta mami kanzo ganin Hafsat kuma duk lokacin da zatazo bata zuwa haka sai ta Kawo mata kayan makulashe irinsu biscuit, chocolate, sweet da sauransu banda mayukan shafawa da turaruka, akwai wani lokaci da taje dubai tadawo tsarabar da takawowa Hafsat abin ba acewa komai domin akwati guda medium ta ciko mata taf da kayan sawa,

Shiyasa tun su ummi na zargin akwai wani abu aran mami har sun dawo sun daina daga ita har Alhaji sa'id din,

Haka mami taci gaba da yiwa Hafsat hidima baji babu gani, lokacin da watan azumi yakama kaya sosai mami tabada aka kai mata kamarsu fruits, madara, sugar da dai sauran kayan hada tea da tarkacen kayan da akafi amfani dasu a lokacin azumi,

Ranar da aka kai azumi na 10 bayan ansha ruwa Hafsat ta shirya taje yimata sannu da shan ruwa, suna zaune ita da yusleem yatashi yafita, yana fita Hafsat ta shiga, ba karamin dadin ganinta mami tajiba nan ta cikata da kayan abinci iri iri,

Har Hafsat tabar gidan tatafi yusleem bai dawoba, da salla tazo kuwa mami kaya ta dinkawa Hafsat kala biyar daya materia, daya leshi daya shadda biyu atamfa super masu kyau da tsadar yan gaske kuma kowanne da takalminsa da mayafinsa banda turare da sarka da abun hannu, wannan sallar saida Hafsat tasamu kaya kala goma domin agida ma kala biyar Alhaji sa'id yayi musu itada amal,

Ranar salla kwalliya Hafsat taci bayan sun gama aikin Gida da hajiya kubra tace mata zataje gidan kawarta Amina nan tatafi mata da abincin sallar da Ummi tayi wainar shinkafa da miyar agushi,

Acan gidan Amina tawuni sai bayan sallar magrib driver yaje ya dauketa yamayarta gida tana zuwa taga wasu sabbin food flasks zama tayi tafara budewa tana gani, fried rice ce da kaza guda daya akai gasasshiya sai sinasir da miyar ganye wanda yaji kaji,

"Ummi wannan abincin fa?"

"Daga gidan mamanki hajiya siyama aka Kawo miki abincin salla"

Murmushi tayi ta mike,

"Allah sarki mami kinga ni namanta ma ban kai mata abincin salla ba"

"Gobe ai sai ki kai mata idan zaki mayar mata da kwanukanta"

Washe gari hajiya kubra tayi girki musamman saboda mami shinkafa da miyar kaji Hafsat ta shirya bayan taci kwalliya tatafi kai mata,

Da murna mami ta tareta tayi mata iso har cikin dakinta,

Zama tayi suka fara hira kamar yadda tasaba yi da Hafsat idan tazo mata, wuni cur Hafsat tayi sai yamma tatafi.

Ahaka rayuwa taci gaba da wakana mami tana mutukar kaunar Hafsat kuma tana kyautata mata wanda harsu hajiya kubra sun yarda da hakan adalilin hakanne ma zumunci mai karfi yashiga tsakanin hajiya kubra da mami domin kawance sukeyi sosai,

Sannu sannu Hafsat ta kammala makarantar secondary wannan dalilinne yasa yanzu bata zuwa ko ina sai makarantar islamiyya saiko dinkin sakarta wanda tasaka agaba,

Cikin weekend tashirya takaiwa mami ziyara,

"Hafsat ankammala karatu ko? Yanzu kuma me kikeda ra'ayin yi?"

Murmushi hafsat tayi,

"Mami karatu zanci gaba dayi"

"To hafsat banki ba amma dai da zakiyi aure shiyafi, idan kikayi aurenki sai kiyi karatunki agidan mijinki"

"Hakane mami amma to wazan aura? Nida ko zance banay.."

"Dana zaki aura hafsat, yarona nakeso ki taimaka min ki aureshi, dan Allah kiyi min wannan taimakon....!.

*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_

*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*

_Dedicated to MISS XOXO_

*20*

***Cikeda mamaki Hafsat ta kalli mami saboda jin abinda tafada,

"Kidaina mamaki Hafsat sannan kuma narokeki dan girman Allah kada ki k'i amsar bukatata domin yin hakan na iya zama dalilin faruwar abubuwa da dama ciki kuwa harda dawwamar bacin rai da bakin ciki acikin zuciyata..."

Sunkuyar da kai Hafsat tayi tai shiru takasa yin magana acikin zuciyarta kuwa tunani takeyi shin shi yaron mamin da take burin hadata dashi shine yaganta yake sonta ko kuwa kawai mamin ce keda burin yin hakan a matsayinta na mahaifiyarsa domin ita tunda take zuwa gidan bata taba ganin daya daga cikin yaran mamin ba kuma surayya kadai ta sani har suke yin waya da ita,

"Hafsat ya naji kinyi shiru? Kodai bakya son dan nawa?"

Muryar mami ta katse mata tunaninta da takeyi,

"Mami to ai bai taba ganina ba kuma nima ba taba ganinshi nayiba.."

Murmushi mami tayi,

"Hafsat kenan ni awurina duk wannan ba wani abu bane kuma abune mai sauki domin na isa da dana duk abinda nasashi baya k'in bin umarni na, matsalar dai kawai kece idan baiyi miki ba,ga hotonshi nan akafe abango ta bayanki, juya ki gani..."

Waiwayawa Hafsat tayi cikeda mamaki ta kalli wurin domin tunda take shigowa bedroom din mami Allah bai taba bata ikon damar kallon wurinba bare har taga hoton,

Hadadden saurayi tagani zaune akan kujerarshi ta office wanda abisa dukkan alamu acikin office dinshi akayi masa hoton,

Farine kyakkyawa mai daukar hankali wanda baduk macece zata ganshi takau da idonta a lokaci guda ba,fuskarshi zagaye take da saje mai hadeda kasumba,bakaken suit ne ajikinshi wadanda sukayi mutukar amsarshi domin sun sake haska farar fatarshi,

Manyan idanuwanshi farare tatass ta zubawa ido har ta gangaro izuwa kan dogon hancinshi mai tsini wanda yake daf da bakinshi dan madaidaici mai dauke da zagayayyun lips wadanda suka kasance jajaye jur,

Ita kanta bata san tsawon mintunan data dauka tana karewa halittar yusleem kallo ba,

"Masha Allah, tsarki ya tabbata ga ubangijin halittu wanda ya kawata halitta da surar wannan bawan nashi.." Ta fadi hakan acikin zuciyarta wanda har lokacin takasa dauke idanuwanta daga kallon hoton,

"Hafsat..." Taji mami takira sunanta sai lokacin ta iya tunawa ma da ashe mamin na zaune wurin, cikin sauri ta dauke idonta daga kan hoton ta sunkuyar da kai cikeda jin kunya,

"Hafsat ko baiyi miki bane?"

Shiru Hafsat tayi bata amsaba tasake sunkuyar da kanta kasa,

Juyin duniya haka mami tayi tana tambayar hafsat amma taki amsawa tayi shiru,

Murmushi mami tayi,

"To Allah dai yasa hasashe na yazama gaskiya hafsat idan har kuwa hakan ya tabbata to nasan zanfi kowa farin ciki....."

Dan murmushi hafsat ta kuma yi cike da kunya,

"Insha Allah zanzo gidan gobe goben nan muyi maganar da umminki kafin asan ta inda za afara kuma"

Mami tafadi hakan cikin jin dadi, ita hafsat yanzu sai taji tana jin kunya da kuma nauyin mamin shiyasa taji duk zaman ta takura,

"Haba hafsat ai tsakaninmu babu yar surukunta, ki dauka cewa kece yata ba yusleem ba, ko aurenku ya tabbata karkiji kunyar sanar dani laifinsa matsawar yayi miki ba daidai ba.."

Shiru hafsat tayi takasa cewa komai,har mami takaraci maganarta ta gama bata iya daga ido ta kalleta ba daga karshe ma sai cewa tayi zata tafi duk kuwa da cewar ba wannan lokacin tayi niyyar tafiyar ba amma wannan maganar da sukayi da mamin itace ta tilasta mata barin gidan.

Ko drivern gidansu bata zauna zaman jiraba sai mami ce tasa drivern ta yakaita gida,

Hatta ummi saida tayi mamakin ganinta a lokacin saboda bata zaci zata dawo dawuri hakaba,

Tambayarta ummin taringa yi akan dalilin dawowarta da wuri haka bayan kuma ba haka tasaba dawowa ba idan taje,

"Hafsat ko unguwa hajiya siyaman zataje ne shiyasa kika dawo?"

"A'a Ummi babu inda zataje tana nan.."

"To meya faru?" Tasake tambayarta,

"Babu komai, tace zatazo wurinki gobe ma"

"Amma dai lafiya ko?"

"Ehh lafiya lau"

"To shikenan Allah yakaimu.."

Acikin zuciyarta ta amsa amin din bata bari ummin tajiba,

Ita kanta bazata iya fassara yanayin da zuciyarta ta karbi yusleem ba kawai dai tanajinta cikin nishadi wanda bata san dalili ba,

Daren ranar tayishi ne batare da tayi isasshen bacciba.
Chapter 10 · 0% Book details